Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 2 Part 4


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 2

Part 4

Marubuci: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh 

   Jarumi Nazmir ya make muryarsa ya ce, "Mu manzanni ne daga kasar Maskur mun zo da sako na musamman ga sarki dagan hannun sarkinmu."

   Koda jin haka sai maigadin ya rufe wannan mitsitsiyar taga. Jim kadan sai suka ji ana kokarin bude kofar gaba daya.

   Ita dai wannan kofar shiga gari ta kasance katuwar gaske, domin tsawonta ya kai kamu dari shida haka kuma fadinta ya kai kamu dari bakwai. An yi ta ne da zunzurutun karfe mai kauri da nauyin tsiya. Mutum arba'in ne ke bude kofar wadanda suka kasance karti majiya karfi.

  Bayan an gama bude kofar sai su jarumi Nazmir suka ga dakaeu sama da mutum dubu dari a tsaitsaye bisa dawakai sun yi sahu a gabansu, kuma gaba dayansu cikin shirin yaki suke. Ba a bar jarumi Nazmir sun wuce ba sai da aka kawo fitila aka haske fuskokinsu aka yi nazarinsu sosai. Bayan hakan ma sai aka hada su da wasu dakarun mutum hamsin don su wuce da su kai tsaye izuwa gidan sarki.

   Yayin tafiya gidan sarki ne zuciyar jarumi Nazmir da ta abokan tafiyarsa ta cika da mamaki domin ba su san dalikin wannan tsatstsauran matakin tsaro ba da aka dauka a garin. Haka kuma sai suka kasance cikin fargaba, domin idan suka bari aka kai su gidan sarki kai tsaye an tarwatsa shirinsu gaba daya.

  Nan fa suka fara tunani da sake-saken zuci. Dabara dai bata fado musu ba, har suka shigo wata siririyar hanya matsatstsiya. Sai da suka zo tsakiyar hanyar sannan jarumi Nazmir ya dubi Bardil da Bagwan ya yi musu wata irin inkiya suma sai suka yiwa sauran baradensu. Cikin gaggawa Nazmir, Bardil, Bagwan da baradensu suka zare takubba suka afkawa wadannan barade hamsin masu yi musu rakiya izuwa gidan sarki. Cikin abin da bai wuce dakika dari da ashirin ba, suka karkashe su gaba dayansu ba wanda ya tsira.

  Nan da nan suka kwashe gawarwakin suka jefa cikin wata tsohuwar rijiya wacce babu ruwa a cikinta suka rufe, sannan suka sauya hanya suka nufi gidan mahaifin jarumi Nazmir wato sadauki Halufa. Abin ka da 'yan gari duk inda suka bullo suka ga dakarun tsaro sai su sauya hanya. Haka dai suka ta kauce-kauce da rabe-rabe har suka iso gidan sadauki Halufa ba tare da wani ya gansu ba.

   Koda suka hango gidan a kulle kuma suka ga dakarun sarki a kofar gidan a tsaitsaye suna kai-komo sai suka labe suka tsaya suna mamaki. Jarumi Nazmir ya dubi su Bardil ya ce, "Yaku abokaina ku yi sani cewa ruwa baya tsami banza. Lallai akwai wani mugun abun da wannan azzalumin sarki namu ya shirya a kanmu. Yanzu mene ne abin yi?"

  Bardil ya yi gajeran tunani, sannan ya ce, "Bai kamata mu yi komai ba face mun gano abin da aka shirya a kanmu, ina ganin zai fi kyau mu je gidana da kuma gidan Bagwan don muga halin da suke ciki tun da mun ga halin da gidanku ke ciki.

      Ba tare da wata gardama ba suka tafi gidajen biyu. Abin da suka gani a gidan su jarumi Nazmir shi suka gani a gidan su Bardil da Bagwan. Nan fa hankalinsu ya dugunzuma ainun suka rasa abin da zasu yi. Daga can sai dabara ta fado musu suka haura gidan wani makocin Bagwan wanda ya kasance tsoho dan shekara tamanin da hudu ana kiransa Hamlabi.

   Lokacin da suka shiga, Hamlabi na ta sharar barci har da munshari kai ka ce wata dabbar ce ke gurnani. Sai da suka zo kansa suka tsaya bai sani ba. Nan take Bagwan ya bugi tulelen cikin Hamlabi mai kama da kwarya. Hamlabi ya farka a firgice. Koda yaga zarata a gaban sa rike da takubba tsirara, sai ya takarkare zai kwalla ihu. Cikin sauri Bagwan ya toshe masa baki da hannu ya ce.

  *UMAR MUHAMMAD SANGARU*

    "Kada ka yi ihu ya kak Hamlabi ka yi sani cewa ni ne Bagwan makocinka, wadannan kuwa su jarumi Nazmir ne abokaina da kuma sauran dakarun nan wadanda sarki ya hadamu da su don zuwa dauko gimbiya Luzaiya a can kasarsu."

   Koda jin wannan batu sai jikin Hamlabi ya kama karkarwa alamun tsoro ya bayyana karara a fuskarsa. Cikin sanyin jiki Hamlabi ya mike tsaye ya je ya dauko fitila, sannan ya zauna ya dubi Bagwan ya ce, "Yakai makocina ya ya akai kamanninka suka sauya haka gaba daya? Na rantse da darajar tsufana ko kadan fuskarka ba ta yi kama da ta makocina Bagwan ba, haka kuma suma wadannan abokan tafiyar taka basu yi kama da su jarumi Nazmir ba, amma kuma gaskiya na ji cewar muryarka na nan kamar yadda na santa."

   Koda jin wannan batu sai Bagwan ya yi murmushi, nan take ya debi ruwa ya wanke fuskar tasa, sai ga kamanninsa sun bayyana karara. Al'amarin da ya jefa tsohi Hamlabi cikin matukar mamaki kenan, ya bude baki galala yana kallonsa. Daga can kuma sai yayi ajiyar zuciya ya dubi Bagwan ya ce.

  "Hakika kun yi babbar hikima, in ba don kun batar da kamaninku ba da tuni yanzu kun dade da zama gawarwaki."

    Koda jin haka sai mamaki ya kama su Bagwan. Nazmir ya ce, "Yakai wannan tsoho wai shin meke faruwa ne? Ka sani cewa mun je gidajenmu mun iske su a kulle, kuma dakarun sarki na gadinsu."

  Yayin da tsoho Hamlabi ya ji wannan tambaya sai ya gyara zama gami da gyaran murya, kuma ya saita muryarsa tasa kasa-kasa ya ce, "Bayan tafiyar ku izuwa birnin su gimbiya Luzaiya wani hatsabibin boka ya bayyana a kasar nan, kuma ya nunawa sarki duk abin da ya faru gareku a cikin wani madubin tsafi. Duk yakin da kuka yi har da yadda mahaifin gimbiya Luzaiya ya sallama kansa gareku, ku ka sare kansa, ku ka taho mun gani a wannan madubin tsafin. Kai na takaice muku labari dai har lokacin da gimbiya ta fada kasan tsaunin nan don kashe kanta jarumi Nazmir ya bita kawo izuwa haduwarku akan dutsen nan inda Nazmir ya harbe barewa duk kowa a garin nan ya gani a cikin madubin tsafin can a fadar sarki. Bayan an gama ganin hakan ne boka Sharmadu ya sanar da sarki cewa kada ya kuskura ya bar iyayenku da ku a raye. Muddin ya yi haka kuwa har abada ba zai auri gimbiya Luzaiya ba, kuma ku ne zaku zama sanadiyar ajalinsa.

   A dalilin haka ne sarki ya sa aka kamo iyayenku gaba daya aka kai su cikin turakarsa aka daddaure subda sarkoki, yanzu haka ana jira ne ku iso a kamaku a hada da su a kashe ku lokaci guda dan haka dokar boka Sharmadu ta kasance. Bisa wannan dalili ne na yi mamaki matuka da na ganku a cikin gidana don nasan cewa an saka matakan tsaro masu tsauri akanku, wai shin ma ya akai kuka shigo nan ba tare da an kama ku ba? Ina mai yi muku ta'aziya bisa rashin abokanan ku, kuma masoyanku wadanda kuka taso tare tun yarinta."

   Sa'adda tsoho Hamlabi ya zo nan a zancensa sai idanunsa suka ciko da kwalla, domin tausayin su jarumi Nazmir ne ya turnuke shi. Jarumi Nazmir ya dafa kafadar tsoho Hamlabi ya ce, "Yakai wannan tsoho hakika ka taimakemu da ka sanar da mu halin da ake ciki. Yanzu wacce irin shawara za ka bamu domin mu tsira da rayuwarmu da kuma rayuwar danginmu?"

   Tsoho Hamlabi ya yi shiru bai ce komai ba, yana tunani. Nan take Bagwan ya shiga tunanin matarsa Muslaiya, wacce ya tafi ya bari da tsohon ciki wadda a halin yanzu bai san halin da take ciki ba. Shi kuwa Bardil sai ya shiga nasa tunani. Jarumi Nazmir ya katse musu tunani da cewa.

   "Ba mu da isasshen lokaci na tunani mai zurfi. Ya kai tsoho Hamlabi me zaka iya cewa damu yanzu?"

   Hamlabi ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Shawarar da zan ba ku guda daya ce kacal. Lallai kada ku je gidan sarki sai kun tabbata kun fara zuwa dakin bauta inda boka Sharmadu yake kun riske shi kun kashe shi. Muddin yana raye ba za ku iya kubutar da iyayenku da danginku ba daga gidan sarki. Ku yi sani cewa kashe boka Sharmadu daidai yake da neman jaki mai kaho. Babu wani abu da zan iya sake fada muku face na yi muku fatan samun nasara, kuma ina roko a gareku da ku hanzarta barin gidana don kada ku shafa mini kashin kaji."

   Yayin da tsoho Hamlabi ya zo nan a zancensa, sai su jarumi Nazmir suka yi tsuru-tsuru suka hau duban juna. Bardil ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Hakika anan nahiyar bamu san irin karfin bokaye ba, amma ga yadda nake samun labarinsu sun kasance ababan tsoro. Kai an ce ma idan boka ya bunkasa yana zama ubangijin mutanensa, saboda tsananin tsoro da girmamawa a gare shi. Ashe kuwa fada irin wadannan mutane ba karamin bala'i ba ne."

   Koda jin haka sai jarumi Nazmir ya ce, "Ai kuwa komai bala'insa ba zamu kasa tunkararsa ba. Ai dama yanzu haka rayuwarmu na cikin daya-biyu. Kodai mu mutu ko kuma mu rayu. Tsakaninmu da sarki sai gaba, sai yaki. Ko dai yaga bayanmu ko mu ga bayansa. Ku tashi mu tafi dakin bauta don mu riski wannan shegen, tsinannen boka mu fara kaddamar da shi, sannan mu tunkari gidan sarki. Gimbiya Luzaiya kuma ba zamu bayar da ita ba face dayanmu baya numfashi a doron kasa."

  Jarumi Nazmir ya daga takobinsa sama, ya ce, "Waye zai bi bayana?"

  Take Bagwan da Bardil suka daga nasu takubban suka kara a jikin takobin Nazmir. Cikin hadin baki suka ce, "Muna tare da kai, komai wuya, komai dadi, mutuwa ce kadai zata raba mu."

   Sa'adda sauran baradan suka ga haka sai suma suka daga nasu takubban suka yi ikirarin abin da su Bardil suka yi. Nan take jarumi Nazmir ya wuce gaba ya kama katanga ya haura. Bardil, Bagwan, Luzaiya da sauran baradan suka yi yadda ya yi.

   Sannu a hankali su jarumi Nazmir suka yi ta kudawa cikin gari, suna masu labe-labe su shiga nan, su fita can, har suka sami nasarar shiga cikin dakin bauta inda boka Sharmadu yake. Da shigarsu suka hau yin sanda da labe-labe, suna duddubawa don su yi masa kwaf daya.

   Sai da suka duba ko'ina a cikin dakin bautar, amma ko kuda ba su gani ba. Al'amarin da ya fusata su kenan, kuma hankalinsu ya yi mummunan tashi. Ba zato, ba tsammani kuma sai suka ji an bushe da dariya. Dariyar ta cika dakin bautar gaba daya, babu dadin ji. Cikin fushi da kekasar zuciya jarumi Nazmir ya tsawa ya ce.

   "Yakai bakin la'ananne in ka isa namiji ka fito fili mu yi gaba da gaba. Ai ba a san maza da buya ba. Na rantse da darajar iyayena muddin za mu yi fito na fito sai na kai ka kushewa."

   Koda gama fadin hakan sai aka sake bushewa da dariya. Lokaci guda kuma dariyar ta dauke, sai ga boka Sharmadu ya bayyana a tsakiyarsu jarumi Nazmir rike da wata isgar tsafi wadda aka yi da jelar zaki.

  Boka Sharmadu ya kasance matashi, dan kimanin shekara talatin da bakwai. Garjejen kato ne, mai kirar sadauki. Hannayensa biyu a cike suke da layu. A kugunsa akwai wani gurun tsafi ja, babu takalmi a kafarsa. A kansa babu gashi ko sili da daya, kuma a aske yake ban da shekin da kyalkyali babu abin da kan ke yi. Idanunsa manya-manya ne, kuma kwala-kwala ababan tsoro. Ba shi da gemu ko saje sai wani murtukeken gashin baki tamkar tsumma aka nannada masa. Yana da katon hanci mai fadin kofofi. Bakinsa kuwa wangameme ne, cike da wargatsatstsun hakora marasa kyan gani. Kai duk inda ake neman mummuna da an ga boka Sharmadu an gama neman, don shi ne karshen muhawara.

   Sharmadu ya dubi jarumi Nazmir ya ce, "Kai samari iya bakinka kada kuruciya ta dubeka, ta debe ka, ta jefa ka cikin bakin kura ka halaka a banza. Ka yi sani cewa nine boka Sharmadu shiryayyen da y shirya tun masu neman shiri basu farka daga barci ba. Nine dodan mazajen duniya, kuma nine sa gudu maganu ki gudu. Nine daya tamkar dubu."

Nazmir ya sake daka masa tsawa ya ce, "Karya kake karamin barde yau ka hadu da gwarzo daya maganin gwarzaye dubu. Yau sai takobina ta sha jininka sannan ta je ta sha jinin mai gidanka, wannan azzalumin sarkin wanda ya dade yana cutar da iyayenmu da sauran talakawa."

Koda jin wannan batu sai boka Sharmadu ya turbune fuska, muninsa ya karu kamar an shake alade. Kafin wani daga cikin su Nazmir ya yi wani yunkuri Sharmadu ya nuna jarumi Nazmir da wannan isgar tsafi da ke hannunsa, kawai sai wata irin iska mai karfi ta daga Nazmir sama ta rinka makashi a jikin ginin dakin.

   Koda ganin haka sai Bardil, Bagwan da sauran barade suka ruga kan boka Sharmadu da nufin gididdiba shi. Kawai sai ya juyo ya dube su. Take wani haske ya fito daga cikin idanunsa ya buge su duk suka kame, suka zama gumaka. Sharmadu ya ci gaba da kyalkyala dariya. Har a yanzu iskar nan ba ta daina gwara jarumi Nazmir ba a jikin ginin dakin.

***

Domin Sauke Audio sai ku danna bulun Rubutun dake ƙasa ko kuma hoton 👇👇


https://youtu.be/cQYWm2GetuM
Post a Comment

0 Comments

Ads