Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 2 Part 3

Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 2

Part 3

Marubuci: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh 

   Haka dai Nazmir da gimbiya Luzaiya suka ci gaba da hira har dare ya raba sosai, ya umarce ta da yin barci, shi kuma ya yi gadin lafiyarsu. Koda jin haka sai ta mike tsam ta dawo inda yake ta kwanta tana mai dora kanta akan cinyarsabta ce, "Yanzu hankalina ya kwanta da kai na san cewa har abada ba za ka cutar da ni ba, domin kai masoyi ne ba makiyi ba."

   A iya rayuwar jarumi Nazmir mace ba ta taba kusantar sa irin yau ba, sai dai a larura ko a wajen yaki. Don haka lokacin da gimbiya Luzaiya ta dora kanta akan cinyarsa, sai gaba dayan tsigar jikinsa ta tashi, ya ji kamar ya ture ta, amma da ya tuna cewar 'yar sarki ce fa mai mulki, kuma wadda ke cikin bakin cikin rayuwa mai matukar bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali sai ya kyaleta. 

  Ya yin da asuba ta fara gabatowa sai Luzaiya ta farka daga barci ta roki Nazmir da ya kwanta don shi ma ya dan rintsa. Nazmir ya ce, "Ai gari ya kusan wayewa don haka ba sai ya kwanta ba."

   Nan fa gardama ta karke a tsakaninsu da kyar ta shawo kansa ya amince ya kwanta, ita kuma ta ci gaba da tsaron lafiyarsu. Luzaiya ba ta tashi Nazmir daga bacci ba sai da ta gari ya waye sosai, rana ta kwale. Koda farkawarsa kuwa ya ga ashe gari ya dade da wayewa sai ya dubi Luzaiya ya ce, "Ya gimbiya me ya sa kika barni ina ta barci har tsawon lokaci haka?"

  Yayin da Luzaiya ta ji wannan tambaya sai ta yi murmushi ta ce, "Saboda kaima ka bani dama na samu isasshen barci, kuma nasan cewa akwai bashin barci mai yawa a tare da kai, idan ba ka yi ba zaka iya samun matsala da lafiyar ka."

  Wannan batu ba karamin bashi mamaki ya yi ba, domin shi a tunaninsa bai ga dalilin da zai sa ta damu da lafiyarsa ba. Nazmir ya mike tsaye ya dauki kwari da bakansa da kuma takobinsa ya gyara musu zama a jikinsa. Koda ganin haka sai Luzaiya ta dube shi cikin damuwa ta ce, "Ina kuma za ka je?"

  Nazmir ya maida mata murmushi ya ce, "Zan je ne nayi farautar abin kalaci."

 

 Nan Gimbiya ta ce "Ai kuwa sai dai mu tafi tare, don ba zan yarda ka barni ni kadai ba a wannan mugun dajin."

   Wannan batu ba karamin mamaki ya baiwa jarumi Nazmir ba, domin a tunaninsa Luzaiya bata kasance matsoraciya ba, in da kuwa matsoraciya ce ai ba za ta hau doki ba, ta yiwa mayaka jagora a lokacin nan da ake gumurzun yaki tsakanin su Nazmir da baraden mahaifinta. Jarumi Nazmir ya dubi gimbiya Luzaiya ya kyalkyale da dariya, ya ce, "Haba ranki ya dade ai ni zatona ke jaruma ce daga cikin mata, ya kuma kike nuna gazawarki a fili haka?"

 Luzaiya ta yi murmushi ta ce, "Ai ido ba mudu ba ne, amma ya san kima. Tabbas ko kadan ban yi kama da jaruma ba, haka kuma ba ni sura irinta jarumai."

   Ba tare da bata wani lokaci ba jarumi Nazmir ya nausa cikin jeji yana mai sauri-sauri, gudu-gudu. Luzaiya ta bishi a baya duk in da ya dauke sawunsa sai tasa na ta, ko kadan ba ta yarda ya bata tazara ba.

   Suna cikin dube-dube ne a jejin Nazmir ya hango wata barewa. Ai kuwa yana ganinta ya dana baka akan kwari ya sai tata. Koda ya saki bakar sai barewar ta ruga cikin dawa, kibiyar ta wuce ta saman kanta. Koda ganin haka sai Nazmir ya bi barewar da gudu, itama Luzaiya sai ta bi shi a guje iya karfinta don kada ya bace mata. Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna wannan gudu basu cimma barewar ba, ita kuma barewar ba ta bace musu ba. Ya zamana Luzaiya ta jigata ainun sai haki take, kuma tana sassarfa kamar za ta fadi kasa, amma sai ta jure. 

Koda suka iso kan wani katon dutse sai barewar nan ta fara kokarin isa karshen dutsen. Anan ne jarumi Nazmir ya tsaya ya zaro kibiya guda daya cikin kuttun kibbau ya aza akan bakar, sannan ya ja ya tabe yana mai saita barewar nan. Yayin da ya gama tabewa da saitawa iya karfinsa da iyawarsa sai ya saki kibiyar. Cikin tsananin gudu da karfi kibiyar ta tafi ta caki gadon bayan barewar ta faso ta cikinta ta bulla waje. Take barewar nan ta fadi kasa matacciya.

   A sannan ne Nazmir ya waiga bayansa ya yi arba da gimbiya Luzaiya wacce ta zauna dirshan tana kallon abin da ke faruwa cikin nuna al'ajabi. Nazmir ya yi murmushi a gareta, itama ta yi masa fuskarta na nuna yabawa bisa jarumtakarsa. Kawai sai Nazmir ya nufi inda wannan barewa ke kwance da nufin ya daukota. Ba zato ba tsammani sai ya gansu suna saukowa kasa daga saman wannan dutse. Ba wasu ba ne face Bardil, Bagwan da kuma sauran baradan nan abokan tafiyarsa.

   Koda su Bardil suka yi arba da jarumi Nazmir, kuma suka ga gimbiya Luzaiya a bayansa sai suka cika da tsananin farin ciki. Nan take suka rugo gare shi shima ya ruga garesu take aka rungume juna, cikin murna mara misaltuwa. Ba tare da bata wani lokaci ba aka dauko barewar nan aka sauko daga kan dutsen. Nan dai aka gasa barewa kowa ya yi kalaci, sannan aka shiga hira inda jarumi Nazmir ya baiwa su Bardil labarin abubuwan da suka faru bayan rabuwarsu. Al'amarin da ya kara jefa su cikin matukar al'ajabi kenan.

   Bayan nan sai Bagwan ya yi gyaran murya ya ce, "Yakai abokina ka yi sani cewa bayan rabuwarmu da ku muma mun sha bakar wahala sakamakon gamuwa da muggan namun jeji da kuma nau'i-nau'in 'yan fashi, amma duk sai da  muka fatattake su muka tarwatsa su. A hakikanin gaskiya bamu taba tsammanin zamu sake saduwa da ku ba, domin mun zata kai da ita duk kun hallaka a lokacin da kuka fado karkashin tsaunin nan mai kwazazzabo.

  Tuni mun yankewa kanmu hukunci cewar ba za mu koma can kasar mu ba, muddin bamu ganku  ba sai dai mu ci gaba da rayuwa a cikin jejin nan har ajalin mu ya riskemu, domin mun san cewa idan muka koma ba tare da biyan bukatar sarki ba gaba dayanmu mun zama gawa."

  Koda jarumi Nazmir ya ji wannan jawabi sai ya yi ajiyar zuciya, sannan ya dubi Bardil da Bagwan ya ce, "Ya ku abokaina ku yi sani cewa tabbas na ji a jikina cewa dayanmu ba zai sake mutuwa ba har sai mun isa gida lafiya, tare da biyan bukatar sarki sai dai bakin cikin rabuwa da abokanmu shi ne babban abin damuwarmu."

   Yayin da jarumi Nazmir ya fadi haka sai idanun Bardil da Bagwan suka ciko da kwallah suka kama kuka, shi ma sai ya taya su. Al'amarin da ya sa gimbiya Luzaiya ma ta tuno da mahaifinta, mahaifiyarta da kuma kasarsu kenan. Itama dai bata san sa'adda ta fara zubar da hawaye ba, don haka sai ta mike ta koma gefe guda ta zauna ta ci gaba da kukanta. Su kuwa sauran barada sai suka kamu da tausayi suka yi shiru da zugum cikin juyayi.

   Nazmir ya kama hannun Bardil da Bagwan ya jasu izuwa gefe guda suka kebe, sannan ya dube su daya bayan daya sa'adda yake goge hawayen idanunsa, ya ce, "Yaku abokaina ku yi sani cewa jikina ya yi sanyi, haka kuma zuciyata na bugawa ma'ana ina jin tsoro da faduwar gaba bisa abin da zai faru garemu bayan mun isa gida. Jikina yana bani cewar akwai wani mugun abu da zai faru a garemu dangane da sakaiyar da azzalumin sarkinmu zai yi mana, domin halinsa ne ya cutar da talakawansa da kuma wadanda suka kyautata a gare shi."

   Yayin da Bardil da Bagwan suka ji wannan batu sai duk hankalinsu ya tashi suka shiga tunani. Nazmir ya katse tunanin nasu da cewa, ni kam a yanzu tausayin gimbiya Luzaiya ya shigeni har ina jin cewa kamar bazan iya dankata ba a hannun azzalumin sarkinmu, to amma fa idan nayi tunani sai na ga cewa, ba mu da wata mafita don haka dole ne na mikata in ba haka ba kuwa rayuwarmu da ta iyayenmu na cikin hadari. Yanzu ku mece ce shawararku bisa abin da kuke ganin zai fishshe mu?"

   Lokacin da Bardil da Bagwan suka ji wannan tambaya sai hankalinsu ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe duk suka yi shiru suna juya al'amarin cikin zukatansu. Bayan dogon nazari sai Bardil ya dago kai ya dubi jarumi Nazmir ya ce, "Ya kai abokina hakika maganarka abin dubawa ce matuka, to amma ka yi sani cewa yanke hukunci a garemu yanzu yafi komai hadari. Ni a tunanina zai fi kyau mu bari mu isa gida in ya so sai mu yanke shawara bayan mun mika gimbiya ga sarki."

   Koda jin haka sai Bagwan ya ce, "Kwarai kuwa wannan shi ne abin da yafi cancanta a garemu."

   Da wannan shawara aka yi amfani. Wato daga wannan rana su jarumi Nazmir suka ci gaba da tafiya ba dare ba rana, sai dai kawai idan sun gaji su yada zango. Bayan wata da watanni ne suka iso kasarsu. Yayin da suka iso bayan gari dare ya raba, don haka sai suka tsaya suna shawarwari akan shiga gari yanzu ko kuwa su bari sai gari ya waye? 

   Koda mahawara tayi yawa a tsakaninsu sai jarumi Nazmir ya ce, "Wai shin wane ne shugaba a cikin tafiyar nan tamu?"

   Bardil da Bagwan suka ce, "Kai ne shugaba ya jarumin jarumai."

   Nazmir ya yi murmushi ya ce, "Tunda haka ne ni yanzu nake son mu shiga cikin garin, kuma ba zamu shiga ba sai mun batar da kamanninmu domin mu san sirrin abin da gari ke ciki, don kada mu fada cikin tarkon sarki. Kamar yadda kuka sani cewar marigayi mahaifin gimbiya Luzaiya ya rokeni da na fara nuna kansa ga mahaifina tare da yi masa bayanin cewar ya sallama rayuwarsa don ceto tawa. Don haka idan muka shiga cikin gari babu inda zamu fara zuwa face gidanmu don riskar mahaifina. In ya so da safe sai mu tafi gidan sarki mu mika masa gimbiya Luzaiya."

   Yayin da jarumi Nazmir ya zo nan a zancensa sai gimbiya Luzaiya ta dube shi idanunta cike da hawaye ta ce, "Yanzu da hannunka za ka dankani a hannun azzalumin sarki wanda ya zamo sanadiyar mutuwar abokanku wadanda kuka shaku ainun tun yarinta? Ka tuna fa cewa a sanadin wannan azzalumin sarki ne mahaifina ya mutu, kuma a sanadinsa ne aka yi asarar dubannan rayuka, kuma a sanadinsa ne kuka rabu da iyayenku da danginku tsawon lokaci, sannan ku ka jefa kanku cikin muguwar rayuwa mai mugun hadari. Nikam da dai na zama matar wannan sarki gwara na mutu tsuntsaye su cinye gawata, ya zamana an mance da tarihina a duniya har abada."

  

   Lokacin da gimbiya Luzaiya tazo nan a zancenta sai hankalin su jarumi Nazmir ya tashi, suka yi shiru cikin matukar damuwa da kokwanto. Bayan dan gajeran tunani, sai jarumi Nazmir ya dafa kafadunta a karo na farko tun haduwarsu, suka tsurawa juna ido, ya ce.

  "Yake gimbiya, sarauniyar kyawawan duniya ki kwantar da hankalinki ki sani cewa ni jarumi Nazmir na yi miki alkawari cewar har abada ba zan bar rayuwarki ba a cikin kunci da bakin ciki, lallai zan kubutar da ke, kuma na mayar da ke kasarku don ki sadu da mahaifiyarki ki ci gaba da rayuwarki ta sarauta, kamar da a cikin kasarki ta haihuwa."

  Koda jin haka sai gimbiya Luzaiya ta yi murmushin yake, sannan ta ce, "Duk wannan ba zai burgeni ba face ka hana faruwar aure a tsakanina da azzalumin sarkinku."

 Nazmir ya yi shiru bai ce komai ba, domin ya san cewa shi kam bai isa ya hana wannan aure ba. Yayin da Luzaiya ta ga jarumi Nazmir ya yi shiru bai ce komai ba sai zuciyarta ta karaya ta ci gaba da zubar da hawaye, ta ce, "Shi kenan ku yi duk yadda kuka so, amma ku sani cewa na gama yanke shawara cewa lallai a ranar da aka daura aurena da sarki zan kashe kaina."

   Daga wannan furuci Luzaiya ta tsuke bakinta ba ta kara cewa komai ba. Kawai sai ta koma gefe guda ta ci gaba da kuka abinta. Nan fa su jarumi Nazmir suka shiga cikin sabon tsahin hankali da matukar damuwa, sai da suka shafe rabin sa'a suna masu tunanin mafita, amma babu. Kawai sai jarumi Nazmir ya bada umarnin kowa ya sauya kamaninsa.

 Nan take aka ba da umarni. Ita kanta gimbiya Luzaiya sai da aka batar da kamanninta duk da tsananin kyawun nan nata ya dishashe aka mai da ita mummunar gaske. Bayan an gama wannan shiri ne suka hawa dawakansu suka nufi kofar gari.

   Da zuwa suka kwankwasa kofar, maigadi ya leko ta cikin wata mitsitsiyar taga ya dube su, ya ce, "Su waye ku, kuma daga ina kuka fito,har da kuke kokarin shigowar a tsakiyar dare haka?"

Karanta >>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 12


Domin sauke cikakken Audi Littafin Matsatsubi Book 2 sai ku danna hoton dake ƙasa 👇 👇👇
Post a Comment

0 Comments

Ads