Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 2 Part 2


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 2

Part 2

Marubuci: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh 

   Koda ganin hakan sai Gulzum ya fashe da kuka yana baiwa Yelisa wasiya cewar "Idan ta koma duniyarsu ta nemi iyayensa ta sanar dasu yadda ya kasance kuma ta nema masa gafararsu domin ba'a son ransu ya bar gida ba, ya shiga duniya."

   Yelisa ta zubar da kwalla don tausayi da sabo ta ce, "Ya kai Gulzum ai abin da ya same ka shine zai same ni sai dai muyi hakuri gaba daya."

  Kafin wani daga cikinsu Jafar ya ce wani abu tuni katon maridin nan ya suro Gulzum, igiyar da ta daureshi ta tsitstsinke, da hannu daya maridin ya aza Gulzum a saman kokon sannan ya daga daya hannunsa ya kaiwa makoshin Gulzum suka da tsinin farcen babban dan yatsansa. Ba zato ba tsammani sai aka ga wata rundumemiyar macijiya mai kawuna dubu arba'in ta zuro bakinta guda ta gutsure hannun wannan  maridi ta hadiye. Damar da bai samu ba kenan ta sukar makoshin Gulzum. Maridin ya kwarara ihu sa'adda jini ke bulbula ta jikin dungulmin hannun nasa. Ihun maridin ya hade da gurnanin macijiyar a lokaci guda. Nan fa maridan nan suka firgice kowannensu ya fara neman hanyar gudu amma tuni macijiyar mai kawuna dubu arba'in ta fara yi musu dauki dai dai, sai dai kaga kawunanta na saukowa kasa suna wangame bakuna suna yin loma daya da maridan. Shi kansa sarkin maridan bai san sa'adda ya kama rarrafe ba a kasa, sai da ya isa kofar dakinsa dake kan dutsen har ya tura kansa cikin dakin, sai macijiyar ta finciko shi da....


 (Afwan, an sami typing error pagen babu rubutu.)

 Bayan su Jafaru sun kubuta daga wajen wannan macijiya sai suka samu rairayi suka zauna suna haki, har suka sami 'yar nutsuwa. Jafar ya dubi Gulzum ya ce, "To kai in ban da abinka me wannan macijiya za ta ji idan ta hadiye mu nan duka? Ka duba fa yadda ta rinka loma daya da manyan maridan nan tamkar mutum ya jefa kwayar hatsi a bakinsa."

   Gulzum ya murtuke fuska, ya ce, "To ban da abinka ai mai kwadayi bashi da ramuwa. Komai kankantar abin lasawa baya bari."

   Mazalish ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Kai jama'a wanda bai yi yawo a duniya ba bai sha kallo ba. Ni kam tun da uwata ta haifeni ko a labari ban tana jin labaran macijiya irin wannan ba mai tsananin girma, kuma mai duban kawuna haka barkatai ba. Tabbas in muka sami nutsuwa sai na roki Mashrila ta zana mini taswirarta. Kun ga ku tashi mu kama gabanmu don an ce zama waje daya tsautsayi ne, inji kifi."

  Koda jin haka sai Jafar ya bushe da dariya ya ce, "Wannan shi ne abun mamaki kare da tallar tsire, wai ya za'a yi a ce aljani yafi bil'adama tsoro. Gaskiya Gulzum kana bani haushi saboda raguwar zuciyarka."

   Cikin tsananin fushi Gulzum ya yunkura don ya make Jafaru in yaso komai ta fanjama-fanjam, amma haka ba ta yiyu ba, sakamakon ganin wata irin katuwar inuwa da ta lullube su gaba daya daga sama. Cikin firgici suka daga kawunansu sama don su ga abin da ya yi musu inuwar, kwatsam suka yi arba da wata katuwar macijiyar nan wadda ta cinye maridan nan ta zubo kawunanta kas reras, barkatai ba kyan gani suna fesar dafi. Kafin daya daga cikin su Jafar ya yi wani yunkuri tuni ta lankwame su gaba daya.

  Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar ya yin da suka fuskanci kadan daga cikin azabobin muguwar guguwa da ke cikin shafi na goma sha shida a kundin tsatsuba.

  *UMAR MUHAMMAD SANGARU*

  A can fadar sarki Dujalu kuwa bai ci gaba da baiwa su Ruziyal labarin hikayar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya ba, sai bayan an zo da kan wannan bawa mai kula da damisar sarki wanda tsautsayi ya sashi ya manta bai kulle kofar kejin damisar ba a jiya da daddare har ya zamana damisar ta yi fitar burgu ta shigo fada, kuma har ta hallaka mai gidanta.

 Nan take sarki Dujalu ya bada umarnin a yi waje da kan bawan a hada da mushen damisar aje a binne a jeji. Bayan tafiyar masu cika umarni ne sai Dujalu ya yi gyaran murya ya ce.

  "To sai ku shirya don zan ci gaba. Lallai ina son na kai karshen wannan doguwar hikaya ko ma shiga ta gaba, don na sallame ku a cikin kwanaki goma daidai, ku kama gabanku."

   Koda jin haka sai boka Hajarul Mukurus ya sunkuyar da kansa kas sakamakon kwallar da ke shirin zubowa daga idanunsa, sannan ya ce, "Ya kai wannan sarki hakika duk a cikin hikayoyin da ka bamu babu mai tausayi kamar wannan, na roke ka da ka hanzarta sanar da mu karshenta don mu ji yadda za ta wakana."

  Sarki Dujalu ya yi murmushi ya ce, "Ai da sauran abin tausayi ma a gaba. Ku dai ku bani aran kunnanku idan na gama sai ku yi muhawara."

  Nan take sarki Dujalu ya ci gaba da bayani kamar haka.

  "Lokacin da jarimi Nazmir ya saba gimbiya Luzaiya a kafadarsa yana laluben hanyar da zai bi ya koma wajen 'yan uwansa su Bagwan. Sai Luzaiya ta yi ta zulle-zulle tana ihu gami da dukan bayansa da hannu biyu, don ya sauketa kasa, shi kuwa sai ya yi biris da ita tamkar wanda ya goya kaza.

  Haka dai ta yi ta wutsil-wutsil a bayansa shi kuwa ya ci gaba da tafiya ta cikin kwazazzabai, duwatsu da ruwa yana dube-dube da kwalawa abokansa kira, amma shiru bai ji komai a jejin face amsa kuwwar muryarsa. Sai da ya jima a cikin wannan hali har ya zamana gimbiya Luzaiya ta gaji da ihu muryarta ta dashe kuma ko hannayen tama ba ta iya daga su. Bisa dole ta rungumi kaddara ta daina motsi. Saboda gajiya sai barci ya kwashe ta akan kafadar jarumi Nazmir. 

  A wannan lokaci duhu ya soma, kuma jarumi Nazmir ya gaji sosai. Koda ya fuskanci cewa Luzaiya tayi bacci sai ya isa gaban wata bishiya ya sauketa a hankali. Har ya mike zai tafi neman itatuwan da zai kunna su ji dumi sakamakon hunturun sanyin dake kadawa a jejin, sai ya tsaya yayi gajeran tunani, don haka sai ya fiddo wata igiya daga cikin jakarsa ya daure kafafun Luzaiya sannan ya kwantar da ita ta yi rub da ciki, ya daure hannayenta ta baya don kar ta gudu.

   Sannan ya tafi neman itatuwan. Bayan kamar dakika dari da ashirin da tadiyar jarumi Nazmir sai sanyi ya bugi gimbiya Luzaiya ta farka daga barcin. Ai kuwa tana bude idanunta, sai tayi arba da wata mayunwaciyar kura nesa can daga inda take.

  Ita dai wannan kura wannan rana ta yini da yunwa domin ta gaji da neman abin da zata ci ta rasa. Koda suka yi ido-da-ido sai kuran nan ta taso a guje haikan don rashin hakuri ma har tsalle take sama tana kara dirga gaba don gani take gudun bai isheta ba. Koda Luzaiya ta yunkura don ga mike tsaye ta gudu sai ta ji kafafunta da hannayenta a daure. Nan take hankalinta ya dugunzuma jikinta ya kama karkarwa don tsananin tsoro ba ta san sa'adda ta kwala uban ihu ba.

   A wannan lokaci jarumi Nazmir ya debo kayan itatuwa niki-niki. Koda ya jiyo ihun gimbiya Luzaiya sai ya yi watsi da itatuwan ya kece da tsananin gudu ya nufi inda ya baro ta. Gudu yake iya karfinsa kuma irin wanda bai taba yi ba a rayuwarsa.

   Har yanzu bai daina jiyo ihun gimbiya Luzaiya ba, al'amarin daya kara fusata shi kenan ya kara kaimi. Kafin ya iso tuni kuran nan tayi tsalle sama ta dira gaban Luzaiya. Nan take kuwa ta kaiwa gadon bayanta cafka da hakoran bakinta. Cikin zafin nama Luzaiya ta mirgina baya amma duk da haka sai da hakoran kurar suka yage rigar Luzaiya kuma suka karce fatarta jini ya tsatstsafo. Kurar ta sake kai mata cafka a karo na biyu bisa rashin sa'a sai ta fada hannun jarumi Nazmir ya shake wuyanta, suka kama kokawa, su fadi nan su tashi can.

   A lokacin ne gimbiya Luzaiya ta zuba musu idanu kawai zuciyarta cike da tunani kuma hawaye na zuba a idanunta ta ce a ranta, 'Wai shin mene ne ma dalilin da ya sa na tsorata da wannan kura? Ashe bani ce wadda ke neman mutuwa ba? Ya akai na kasance mai kokarin neman tsira? Haba Luzaiya me kike so ki yi a duniya alhalin baki da kowa, ba ki da komai. Hakika kin yi kuskure da kika yi ihu har jarumi Nazmir ya kawo miki dauki da wuri. In da kin yi shiru da yanzu haka kin mutu kin huta da takaicin duniya.'

  Tun da jarumi Nazmir yake bai taba haduwa da katuwar kura irin wannan ba, a duk lokutan da ya sha rangama a jeji a yayin farautarsa. Ita dai wannan kura ta kasance mai taurin kai, karfi da jajircewa. Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna gumurzu ya zamana tayi masa rauni sosai da faratan hannunta amma da zarar ta kawo masa cizo sai ya goce ya naushi bakin nata.

 Saboda karfin naushin nasa sai kaga ta zube kasa rikica amma kuma sai ta sake mikewa cikin zafin nama, ta afka masa. Yayin da jarumi Nazmir ya ga kurar nan tana so ta galabaitar da shi  sai ya harzuka zuciyarsa ta yi baki kirin kawai sai ya suri kafafunta biyu na baya ya dagata sama ya rinka haji-jiya da ita tamkar wanda yake wasa da majajjawa.

  Bayan ya wulwulata kamar sau arba'in a sama sai ya rinka rotsa kanta akan wani dutse har sai da ya ga kan ya dagwargwaje sannan ya yi jifa da gawar kurar, shima ya tsugunna kasa yana haki da numfashi. A sannan ne suka hada idanu shi da gimbiya Luzaiya. Koda ya ga raunin da kurar nan ta yi mata a gadon baya sai tausayinta ya kama shi. Cikin sauri ya mike ya je ya bude jakarsa ya dauko magani ya shashshafa mata a raunin, sannan ya kwance igiyar da ya daure mata hannaye da kafafu, ya jinginar da ita a jikin bishiya. Kawai sai ya juya mata baya ya ce, "Idan kin so kina iya yin kokarin guduwa amma ki sani ba za ki iya tsere mini ba a cikin jejin nan, duk inda kika shiga kika buya sai na laluboki."

   Yana gama fadin hakan ya tafi ya barta a wajen cikin tunani. 'Me kike jira ne ga dama ta samu? Walau ki gudu ko kuma ki sami wani icen ki tsire cikinki ki mutu. Ko kya huta da bakin cikin rayuwa.'

  Zuciyar Luzaiya ce ta saka mata wadannan maganganu. Me yasa na rayu har na kawo i yanzu? Lallai akwai wani dalili a karkashin wannan sanadi. Zai fi kyau na tsahirta dan naga wannan dalili da idanuna tun da dai nayi iyakar kokarina akan na ga na halaka kaina, amma abu ya faskara. Duk da kasancewar ban yi imani da daya daga cikin irin addinan zamani ba babu mamaki wani Ubangijin ne yake tsara rayuwata saboda wani boyayyen dalilin."

   Luzaiya na cikin wannan tunani ne jarumi Nazmir ya dawo dauke da itatuwa. Shi kansa ya yi mamaki  da ya iske ta har yanzu a zaune a inda ya barta, kuma hawaye bai daina zuba a idanunta ba. Ban da karkarwar sanyi babu abin da take yi. Nan da nan ya zube icen a gabanta ya kunna musu wuta, sannan ya sake bude jakarsa ya fiddo wata riga wadda aka yi ta fatar damisa ya lullubawa gimbiya Luzaiya. Shi kuwa dogon wando ne kadai a jikinsa na fatar zaki.

  Nazmir ya zauna tsallaken wutar suna masu fuskantar juna. Tsawon dakika biyar wurin ya yi tsit baka jin komai face kukan tsuntsaye da kuma kukan manyan namun dawa, da ke can nesa. Nazmir ya katse shirun da cewa, "Me ya sa ba ki yi kokarin guduwa ba sa'adda na kwance ki na tafi nemo itatuwa?"

  Ba tare da ta dago kai ta dube shi ba, ce...

  (Afwan wannan page dinma babu rubutu a jikinsa; typing error.)

cewa a duk sa'adda na dubi abokinka na kan ji kamar ana sukan zuciyata da tsinin masu. Inda zan kashe shi na yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinsa izuwa sala-sala, mini-mini yadda tsuntsun kanari zai iya tsinta da bakinsa ya ci ba zan huce takaicin zuciyata ba. Bani da wani masoyi a duniya wanda yafi ubana. Na rayu a cikin kaunarsa, da begensa dare da rana, kuma cikinta zan mutu."

   Sa'adda Luzaiya tazo nan a zancenta sai ta fashe da kuka. Tausayi ya kara turnuke Nazmir ya ce, "Na san har abada ba za ki iya yi mana afuwa ba, wato ni da abokaina amma ki sani bamu kashe mahaifinki don bukatar kanmu ba sai don mu ceto rayuwarmu da kuma farin cikin iyayenmu. Kowanne 'da' na gari ba shi da wani buri wanda yafi na nunawa iyayensa tsantsar kauna kamar yadda suka nuna masa tun yana karami kawo izuwa girmansa. Tsantsar kaunar da nake yiwa mahaifina ce tasa na fito wannan yaki, amma ba wai don tsoro da bin umarnin sarkina ba. Hasalima a duniya babu mutumin da na tsana fiye da sarkin garinmu saboda zaluncinsa da rashin tausayinsa ga talakawa."

  Koda gimbiya Luzaiya ta ji wannan batu daga bakin jarumi Nazmir sai ta cika da mamaki ta yi shiru ba ta ce komai ba. Daga can kuma sai ta dube shi ta ce, "Ya kai wannan jarumi ina son nayi maka wata tambaya idan har ba za ka sami damuwa ba?"

 Nazmir ya ce, "Fadi tambayarki in dai ina da amsarta zan sanar da ke."

 "Shin za ka iya gaya mini dalilin da ya sa mahaifina ya ce idan ya bari aka kashe ku ya ci amana? Mene ne dalilin da ya sa ya kawo kansa gareku har ya umarce ka da ka sare kansa kuma ka kamani ka tafi da ni? Kayi sani cewa zuciyata ta dade tana damuwar akan wannan al'amari, kuma ta shiga cikin bakin duhu babu mai fito da ita izuwa cikin hasken fahimta face kai."

   Sa'adda gimbiya Luzaiya ta zo nan a zancenta sai jarumi Nazmir ya yi ajiyar zuciya, ya ce, "Ba komai ne ya sa mahaifinki ya yi haka ba sai don ya sakawa mahaifina abin da alherin da ya taba yi masa a baya kimanin shekaru da suka gabata."

  Nan take jarumi Nazmir ya kwashe labarin abin da ya faru tsakanin sadauki Halufa da sarki Fahalul Bahafus ya zaiyane mata. Koda ya kare labarin sai ta fashe da kuka tana mai cewa, "Hakika mahaifinka masoyi ne a gareni da mahaifina lallai kai ba abokin gabata ba ne, domin ba don darajar mahaifinka ba da na girma a cikin maraici. Hakika mahaifina ya rike amana kuma ya tabbatar da alkawari. Ya kai Nazmir ka yi sani cewa daga yau na rungumi kaddara, kuma zan kasance mai bin umarninka har mu isa kasarku ka dankani a hannun sarkinku, domin yin hakan a gareni shi ne cikar rike amanar da ke tsakanin mahaifina da mahaifinka. Lallai kun yi halacci a garemu, yanzu kuma lokaci ya yi da zamu saka muku, ina mai rokonka da ka yafe mini kura-kuran da na yi maka a baya."

   Nazmir ya yi murmushi ya ce, "Ai duk abin da kika yi mini banga laifin ki ba, domin kin yi ne don sanin martabar mahaifinki."


Karanta >>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 12


Domin sauke cikakken Audi Littafin Matsatsubi Book 2 sai ku danna hoton dake ƙasa 👇 👇👇





Post a Comment

0 Comments

Ads