Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 2 Part 1


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 2

Part 1 

Marubuci: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh 


     Lokacin da su Jafar suka fada cikin shafi na goma sha shida Kundin tsatsuba, wato bayan iskar cikin Kundin ta zuke su, sai suka tsinci kansu a cikin sararin samaniyar wata sabuwar duniyar, kuma a kudundune cikin wata irin gagarumar guguwa mai tsananin karfi. Saboda karfin guguwar sai da ya zamana cewa ta tale hannayensu da kafafuwansu. Gashin kansu ya tsefe sama kamar taron tsintsiya. Idanuwansu suka gwale, kofofin hancinsu da bakunansu suka kara girma, banda ihun azaba babu abinda suke yi. 

Kwatsam sai suka ga wata surar fuskar bil'adama a samansu wacce ta saje da kalar gajimare. Bakin surar ya wangame yana mai kyakyata musu dariya. Al'amarin da ya kara jefa su cikin razana da fargaba kenan. Mazalish ta fara kokarin hannayenta biyu waje guda don tayi tsafi, amma sai abu ya gagara, domin ta kasa hade hannayen nata saboda tsananin karfin guguwar. Fuskar ta sake wangame baki a karo na biyu ta barke da mahaukaciyar dariya mai tsananin firgitarwa, sannan ta ce.

   "Nice guguwar masifa, kuma nice guguwar bala'i, duk wanda ya ziyarceni sai na kai shi cikin mahallaka dubu. Kaicon ku wadannan baki masu karambani, yau za ku san cewa karambaninku ya janyo kun tsokano tsuliyar tashin hankali irin wanda baku taba gani ba, kuma ba ku taba jiba."

    Kafin wani daga cikin su Jafar ya iya bude bakinsa ya ce wani abu tuni wannan fuska ta bi jikin guguwar sun zama iri daya. Kawai sai guguwar ta kanannade su ta rikito da su kasa daga sararin samaniya cikin tsananin gudu, sai da suka tsakiyar wata katuwar teku, sannan guguwar nan ta saki su Jafar ta bace. 

   Koda Jafar, Yelisa, Gulzum, Mashrila da Mazalish suka ga an sake su za su fada cikin tsakiyar teku mai tsananin girma da fadin da ba'a iya ganin karshen tsawonta da fadin ta sai duk suka rafka ihu. Kafin su tsunduma cikin tekun sai wani katon, jibgegen kifi ya wangame bakinsa suka fada ciki. Kawai sai kifin ya rufe bakinsa ya yi nutso izuwa karkashin ruwa ya ci gaba da tafiya abinsa. 

   Lokacin da su Jafar suka fada cikin bakin kifi suka biyo ta cikin makogwaronsa, sannan suka ratsa ta cikin hanji, tuni gaba dayansu sun fita daga hayyacinsu, basu isa cikin kifin ba sai bayan tafiyar dakika dari uku da arba'in. A matukar galabaice suka fado kasan cikin kifin suka zube shararaf kamar tulin tsummokara, da kyar suka mike zaune sannan suka fara kalle-kalle cikin firgici da mamaki. 

    Jafar ya kare nazarin kayan cikin kifin tsaf sannan ya ce, "Yau kuma a tsakiyar shuke-shuken teku aka watsomu, yanzu ta ya ya zamu iya fita daga wajen nan nikam banga alamar akwai wata hanya ba."

   Koda jin wannan batu sai aljani Gulzum ya bushe da dariyar karfin hali sannan ya ce, "Amma dai ka cika dakiki kuma kidahumi, wa ya gaya maka cewa nan acikin shuke-shuken karkashin ruwa muke? To ka duba da kyau ka gani. Nan a cikin cikin kifi muke, tabbas rayuwarmu na cikin mugun hali domin ko zafin dake cikin kifin nan bai kashemu to kuwa yunwa da kishirwa sa kashemu, nan da kwanaki da baza su gaza biyu ba."

   Koda jin wannan batu sai gaba dayansu hankalinsu ya dugunzuma kowa ya rasa abin da ke masa dadi. 

   Daga can sai Yelisa ta dubi Mazalish ta ce, "Waike ina takamarki ta tsafi take? Me yasa baza ki ceci mu ba daga cikin wannan masifar da muke ciki?"

  Mazalish ta ce, "Ai kin san cewa gaba da gabanta ko? Inda tsafina zai iya cetonmu da tun kafin guguwar nan ta jefomu cikin tekun zamu kubuta."

    Jafar ya mike tsaye ya duba gaba da baya ya jinjina kai ya ce, "Kai amma fa Ubangijin da ya halicci wannan kifi ya cika abin tsoro, ku duba fa ku gani sam-sam ban iya hango karshensa. Wai shin yanzu mene ne abin yi?"

   Mashirila ta mike tsaye daf da Jafar suka fuskanci juna sannan ta ce, "Ni ina ganin babu abinyi face muje karshen bindin kifin nan baza mu kasa riskar kofar da yake fitar da abin da ya ci ba, sai mu fita ta wajen."

    Gaba dayansu suka yarda da wannan shawara don haka sai suka kama tafiya acikin cikin kifin suka nufi inda jelar kifin take a sahu guda. Gulzum ne akan gaba sannan Jafar, Mazalish, Yelisa da Mashrila, sai da suka yi tafiyar sa'a guda sannan suka iso bindin kifin inda suka ga kofar da suke nema, nan take Gulzum ya zura kansa ta cikin kofar da niyar fita. Koda kifin ya ji wani irin radadi a bindinsa sai ya yi juyi yana mai karaji. Gaba dayansu suka rikito suka hau tuntsirawa a cikin kifin, a haka suka yi ta kokarin fita amma abu ya gagara. Kokarin nasu ne ya gigita kifin yai ta juye-juye har ma ya fita da gudu sai daya iso gabar tekun sannan ya yi kakarin amai ya amayar da su gaba daya don ya huta da azabar abin da ke kartarsa aciki, ai kuwa yana gama amayar da su ne ya koma cikin tekun ya nutse, kafin daya daga cikinsu ya sake dawowa haiyacinsa tuni guguwar nan tazo ta kanannadesu tayi sama da su  tana mai kyalkyala dariyar mugunta. Guguwar ta ci gaba da gudu dauke da su Jafar a sararin samaniya har tsawon lokaci sannan ta sauko kasa ta watsar da su a tsakiyar wani makeken jeji. 

   Jeji ne mai yawan bishiyoyi, duwatsu, tsaunika da koramai abin gwanin sha'awa sai wanda ya gani. Koda su Jafar suka tsinci kansu a wannan wuri sai suka cika da farin ciki don tsammanin cewa sun shigo wuri mai ni'ima wanda babu abubuwan tashin hankali a cikinsa. Abin da basu sani ba shine sunyi gudun gara sun fada gidan zago domin bala'in da ke cikin wannan jeji ya ninka na fadawarsu cikin cikin kifin sau arba'in. 

    Nan fa su Jafar suka mimmike tsaye suka isa bakin wata korama kowa ya tsuguna ya jika makoshinsa, sannan suka fara zuba ruwan ajikinsu don su ji dan sanyi, sakamakon dumamewar da jikinsu yayi a cikin kifi. Ai kuwa suna gama yin hakan kenan suka ga wadansu abubuwa kamar manyan duwatsu sun kewaye jejin gaba daya. Abubuwan suka rinka matsowa a hankali, ashe wadannan abubuwa ba duwatsu ba ne wadansu irin maridai ne masu tsananin girma, tsawo da fadinsu ya wuce kima. Karamin cikinsu shine wanda tsawonsa ya kai kamu dari, fadin kirjinsa kuwa ya kai arba'in. Koda ganinsu sai hankalin su Jafar ya dugunzuma suka rasa abin yi, kawai sai Gulzum ya yu tsalle sama ya kama reshen bishiya ya fara tsalle-tsalle da nufin guduwa, caraf daya daga cikin maridan ya kamo Gulzum a cikin tafin hannunsa, maridin ya dago hannunsa ya saita Gulzum dai-dai fuskarsa ya kare masa kallo sannan ya kyalkyale da dariya. A lokacin ne maridan gaba daya suka tsaya kyam a waje daya, wannan wanda ya kama Gulzum dama shine mafi girma sai ya sauko da Gulzum kasa ya ajiyeshi kusa da su Jafar suma ya kare kallo sannan ya sake bushewa da dariya. 

   Daga can kuma sai ya waiga ya dubi 'yan'uwansa ya ce, "Ya ku ahalil Bauzuls yau fa mun fito farauta a sa'a domin munyi tsintuwar abin da muka dade muna nema shekara da shekaru wato jinsin aljan da mutum." Ko da jin haka. 

  Sai Jafar ya sha gaban Gulzum ya daga kai sama ya dubi wannan maridi mai magana ya ce, "Ya kai wannan basamudan maridi me yasa kuke neman jinsin mutum da aljan har tsawon lokaci, amma baku samu ba sai yau. Shin kana nufin mutane da aljanu basa shigowa dajin nan ne?" Sa'adda Jafar yazo nan a zancensa sai maridin yasa dan yatsansa guda a cikin kunnensa na hagu tamkar ansa guga a rijiya yayi susa. 

   Sannan ya sosa kunnen dama ya dubi Jafar ya ce, "Ya kai wannan karamar halitta me kake cewa ne wanda ban ji ba? Ina son ka sake maimaitawa." Koda jin haka sai daya daga cikin maridan ya zaro wani kaho dake sakale a kugunsa ya ajiye shi a gaban Jafar tamkar ya ajiye katon kwale-kwale. Ya ce da Jafar yasa bakinsa a bakin bututun kahon sannan yai magana. In ba haka ba kuwa sarki ba zai ji muryar sa ba. Koda Jafar ya doshi wannan kaho sai ya fuskanci cewar ai kofar dake bakin kahon ma takai fadin katuwar rijiya. Kawai sai ya zura kansa gaba daya a cikin kahon ya maimaita maganar daya fadi dazu. Ai kuwa sai nan take muryar Jafar tayi kauri kuma ta cika jejin gaba daya  da amsa kuwwa. Al'amarin da ya janyo tarwatsewar namun dajin dake wajen kenan, gaba daya duk suka kama gabansu. 

   Sarkin maridan ya yi murmushi mai kama da kukan jaki ya ce, "Ba komai ba ne yasa muke neman jinsin aljan da na mutum face maganin wata masifa data addabe mu shekara da shekaru, ya ku wadannan kananan halittu kuyi sani cewa dani da jama'ata mun fi shekara dubu sittin acikin wannan daji kuma tunda muke zaune a nan bamu taba ganin jinsin mutum da aljan ba, sai sau daya tsawon wadannan shekaru. A halin yanzu akwai wata cuta da take addabarmu kuma mun kasa samun maganinta, wannan cuta itace ta rashin haihuwa, matanmu ko sun sami ciki baya zama, kai koda ya tsufa sai dai rana guda aga ya bace. Gaba dayanmu nan mu dubu dari bakwai ne da saba'in da bakwai. Tsawon wadannan shekaru dubu sittin bama haihuwa kuma bama mutuwa, wato dai bama raguwa kuma bama karuwa, kimanin shekaru ashirin da biyu baya wani hatsabibin aljani yazo nan neman wasu abubuwa na sirrikan tsafi. Sunan wannan aljani Shamharu, lokacin da yazo mana mun rufar masa gaba daya don mu hallakashi amma muka kasa. Bayan ya tilasta mu mun samo masa abubuwa biyar da yake da bukata sai muka roke shi da ya taimaka mana bisa cutar data addabemu ta rashin haihuwa. 

     NAN TAKE YA SANAR DAMU cewa ba zamu fara haihuwa ba har sai mun samo jinin bil'adama kimanin cikin kwanson kabewa babba guda uku da kuma jinin aljan cikin karamin kwanson kabewa. Idan muka hada wannan jini guda biyar wadanda muka samo masa, mu da masu gaba daya, kowa daga cikinmu sai ya lakaci wannan tsumi dan kadan ya lashe, tabbas idan muka yi haka zamu rinka haihuwa amma kuma zamu rinka mutuwa. Da yawanmu tsufa ya fara zame mana cuta don haka muna bukatar mutuwa, babu yadda ba muyi ba akan mu rage yawanmu ta hanyar kashe junanmu amma abu ya gagara domin duka, yakushi, sara da suka basa tasiri a jikinmu. Yau gashi mun tsinci dami a kala wato mun sameku don haka yanzu, yanzu bada wani bata lokaci ba zamu kama ku mu tafi daku izuwa gidajenmu inda zamu yankaku mu tara jininku acikin kasko guda don hada wannan magani. Mukam wahalar mu da bakij cikinmu ya kare daga yau."

Kafin daya daga cikin su Jafar yace wani abu tuni an damdamkesu an tafi da su. Nan take maridan nan suka kama kade-kade da wake-wake a haka suka nufi wani katon dutse mai tsananin girman gaske.

  A wannan lokaci tuni su Jafar sun sallama rayuwarsu don sun tabbatar da cewa tasu ta kare, jafar ne ya kalli abokan tafiyarsa yana mai cewa yanzu mu shi kenan haka karshenmu zai kasance.

    Ai kuwa mun sha wahalar duniya a banza kenan, mu ba muyi suna ba kuma bamu sami matsayin komai ba.

    Ita kuwa Mashrila sai ta ce, "Ni kam inda nasan hakane zata faru a gareni da nayi zamana acan garinmu na mutu acikin irin masifar da ta addabe mu."

   Mazalish ta ce, "Ni kam mutuwata anan ta fiye mini alheri akan na rayu a matsayin mayya mai shan jinin bil'adama."

   Jafar ya share hawayensa ya ce, "Ni kam babban abin bakin cikina shine zan mutu banga abin dake cikin shafin karshe na kundin tsatsuba ba."

  Ko da jin haka sai Gulzum ya yi tsaki ya ce, "Amma dai kai Jafar ka cika banza mara tunani, in banda rashin hankali da hauka irin naka wane ne zai yi fatan ya karance wannan tsinannen littafin. Kaga mu bala'in da muka sha a baya ma ya ishemu. Ai gwarama wadannan maridan su kashe mu huta da fargabar sauran masifun dake jiranmu." Haka dai su Jafar suka ci gaba da surutai na tausayawa kansu har maridan nan suka iso gaban wannan tafkeken dutse. Da zuwa sai su Jafar suka ga ashe a jikin wannan dutse maridan suka gina gidanjensu. Ba wai gini aka yi akan dutsen ba, a'a dutsen aka kwakule akayi dakuna. Abin mamakin shine, gaskiyar al'amarin shine da kaifin faratan hannaye maridan akayi wannan gagarumin aiki.

   Da zuwa sai aka sauke su Jafar aka daddauresu tamau da igiyoyi ajikin wasu turaku na dutse, daga nan gaba dayan maridan suka kewaye wani katon kasko wanda girmansa ya kai a sanya bil'adama dubu a cikinsa. Nan take aka ci gaba da kida ana rera wata irin waka mai dadin sauraro kai kace mutane ne masu nutsuwa suke wakar.

   Jafar ya dubi Yelisa ya ce, "Ya ke Yelisa hakika ina mai matukar bakin ciki da ya zamana zamu mutu ba tare da kun cika burin zuciyarmu ba, amma ina jin dadi cewa zamu bar duniya a tare muna masu kallon junanmu, in ba don nasan mutuwa zan yi ba da jace wannan kidan da wakar sun isa su gusar mana da takaicin duk irin wahalar da muka sha a baya."

  Mashrila ta ce "Ya kai abin begena ni kam indai dai ace kai ne ka rigani mutuwa da tabbas hadiyar zuciya zanyi na mutu, amma tun da dai tare zamu mutu ba zanyi takaici da nadamar komai ba. Kuma babu mamaki mu sake tofuwa a wata duniyar dabam muyi sabuwar rayuwa." Koda jin haka sai kishi ya turnuke Yelisa suka fara kace nace.

   Mazalish ta dubesu ta bushe da dariya ta ce, "Hakika kukan dadi kuke yi kawai saboda ganin masoyinku a kusa daku yanzu ni da ban san a inda nawa yake ba kuma ban san a inda zan riske shi ba, ai sai dai naci gaba da kuka tunda gashi ma yau zan bar duniyar gaba daya."

 A dai-dai wannan lokacin ne suka ga an kawo wani garin magani kala biyar an zazzagesu duk a cikin katon kaskon nan. Daga nan kuma sai wani katon maridi ya dubi sarkin maridan yana mai tambayar wanda za'a fara kashewa daga cikin su. Sarkin maridai yai nuni ga aljani Gulzum.


Karanta >>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 12


Domin sauke cikakken Audi Littafin Matsatsubi Book 2 sai ku danna hoton dake ƙasa 👇 👇👇
Post a Comment

0 Comments

Ads