Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 12 Takun Karshe


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 1 

Part 12 Takun Karshe

Marubuci: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh 

Mazalish na gama rufe bakinta kenan sai wasu irin halittu suka yo fitar burgu daga cikin rijiyar nan suna yin wata irin ƙara mara daɗin ji wacce ka iya kashe dodon kunne.

Su dai waɗannan halittun 'yan ƙanana ne mini-mini,domin girmansu ba zai wuce na fara ba,amma kuma surar aljanu gare su. Gaba đaya jikinsu,hannaye ne masu zaƙwa-zaƙwan farata. Adadin su ya kai dubu,kuma gaba ɗayansu suka fito waje daga cikin rijiyar nan. Ai kuwa nan take suka hau yakusar jikin su Jafar. Cikin ƙanƙanin lokaci suka yi musu fata-fata,kowa ka duba jini ke zuba a jikinsa,kuma jiri na ɗibarsu suna faɗuwa da miƙewa da ƙyar.

Koda Mazalish taga zasu hallaka gaba ɗaya sai tayi tsafi suka zama hayaƙi. Hayaƙin ya shige cikin rijiyar nan,sannan murfin ijiyar ya taso daga

inda yake ya rufe rijiyar ya zamana halittun ba su sami damar binsu cikin rijiyar ba. Sai duk suka yanyame kan rijiyar suna ta yin wannan ƙarar ta su mara daɗin ji. Yayin da hayaƙi ya faɗa cikin rijiyar sai ya rikiɗe ya zama Mazalish,Yelisa,Jafar,Gulzum da Mashrila. Cikin fushi Jafar ya dubi Mazalish yace, "Don me za ki shigo da mu cikin rijiyar nan bakya tunanin za mu iya riskar abin da yafi waɗancan halittun haɗari?"

Mazalish tayi ƙwafa tace, "Kash! Dana san zaka faɗi haka da na barka a can kai kaɗai. Shin baka taɓa jin an ce abin da ya koro ɓera ya shiga wuta,yafi cutar zafi ba? Ai da masifar da ka sani gwara wadda baka sani ba."

A daidai wannan lokaci ne kuma hankalin su gaba ɗaya ya koma kan inda suka tsinci kan su sai suka ga ashe a tsakiyar wani ƙaton gari ne. A cikinsa ga gidaje nan da kayayyaki irin na rayuwar mutane sosai,amma kuma ba su ga koda mutum guda ɗaya ba a garin. Garin ya yi tsit,ko kukan gyare babu.

Al'amarin da ya yi matuƙar jefa su cikin mamaki kenan. Kawai sai suka cigaba da tafiya su shiga nan su fita can,har tsawon sa'a uku sannan suka iso ƙarshen garin inda yayi iyaka da gaɓar wata teku.

Kwance a bakin gaɓar tekun wasu gumaka ne bila adadin masu surar ifiritan aljanu. Anan su Jafar suka tsaya suna kallon waɗannan gumaka cikin al'ajabi.

Jafar yace, "Kai amma fa abin al'ajabi baya ƙarewa,wai shin to ina mutanen wannan birnin,kuma me suke yi da waɗannan gumakan?"

"To wa kake tambaya ka san dai a cikin mu nan kaf babu mai iya baka amsa." Gulzum ne ya faɗi haka cikin ɗacin rai. Jafar ya fusata yace, "Wai kai me na tare maka ne a rayuwarka kake tsangwamata ko kuwa mun haɗa neman aure ne?"(🤣🤣🤣🤣 Tambaye sa dai Jafarun mu🤣)

Koda jin wannan tambaya sai kowa ya bushe da darıya har shi kansa Gulzum ɗin. Yelisa tace, "haba Jafar yanzu in banda daraja ta ina kai ina yin hamaiya da Gulzum ai yafi ƙarfin ka ta ko'ina."

Mazalish ta ce, "Kun ga ba hira zamu tsaya yi ba gwara mu yi abin da zai fishshe mu."

Kawai sai ta nufi inda gumakan nan suke. Da zuwa sai ta hau duba su tana tattaɓasu,ko zata ga wani abun da yake akwai raunika a jikinta kuma har yanzu jini bai daina zuba ba sai jinin jikin nata ya ɗiga akan ɗaya daga cikin gumakan. Faruwar hakan ke da wuya sai ruhi ya shiga jikinsa nan take,ya miƙe tsaye ya yi kururuwa yana mai zazzago harshen bakinsa wanda girmansa ya kai na ƙatuwar bishiya.

Cikin firgici su Jafar suka juya da baya suka runtuma da gudu suka bar Mazalish nan tsaye gaban ifiritin ta kasa gudu don tsananin razana,sai ihu take faman yi kawai. Ifiritin nan ya sake taƙarƙarewa ya wangame ƙaton bakinsa yana mai ruri ya rinƙa aman mutane daga cikin bakinsa. Sai da ya amayar da kusan mutum dubu. Sannan hankalinsa ya dawo kan Mazalish wacce har yanzu tana nan tsaye a gabansa tana ihu. Cikin zafin nama ya kawo mata wafta don ya ɗauke ta,ita kuwa ta goce cikin zafin nama sannan ta ruga da gudu ta nufi inda suka Jafar suka yi.

Ifiritin nan kuwa ya bita a guje suka kasa tsere. ldan tayi gudu,tayi gudu,sai ta ga ifiritin nan daf da ita yana jeho harshensa waje don ya lasota, kawai sai ta ƙwala ihu ta ƙara ƙaimin gudu. Haka dai ya cigaba da binta har suka riski su Jafar. Koda su Jafar suka waigo suka ƙaton ifiritin ya kusan cimma Mazalish sai suka ƙara ƙaimin gudunsu. Kawai sai wasu fukafukai guda biyu suka fitar da kansu daga jikin ifiritin nan ya tashi sama ya riski Mazalish ya lasota da harshensa sannan ya haɗiyeta. Daga nan ya bi su Jafar ɗaya bayan ɗaya duk ya haɗiye su.

A gaban KUNDIN TSATSUBA su Jafar suka tsinci kansu,har yanzu jini na zuba a jikinsu sakamakon raunukan nan da 'yan mini-mini aljanu sukai musu.

Kuma shafi na goma sha huɗu ne a buɗe jikin tafin KUNDIN TSATSUBA. Nan take su Jafar suka yanke jiki suka faɗi ƙasa kamar sumammu. Sai bayan sa'a guda sannan kowannansu ya dawo cikin haiyacinsa. Yelisa ce ta fara miƙewa zaune ta dubi kowa tace, "Tabɗijam amma fa wannan karon mun sha baƙar wuya."

Mashrila tayi tsaki tace, "Ai in dama wahalar ce zallah babu tashin hankali ai da sauƙi."

Shi kuwa Jafar sai ya dubi Mazalish yace, "Wai ke ina ƙarfin tsafin naki ya tafi,me ya sa baki cece mu daga sharrin wannan ifiritin ba?"

Mazalish tayí murmushi,sannan tace, "Lallai yanzu na tabbatar da cewa kai yaro ne. Ai idan ka ji ana cewa ga ƙi gudu to sa gudu ne bai zo ba."

Jafar yace, "Wai ina ruwan filfilwa ai ban san cewa Gulzum na da gudu ba, sai sa'adda ifiritin nan ya biyo mu,kafin na waiga bayana tuni Gulzum ya wuce mu gaba É—aya,duk girman nan na sa da nauyin jikinsa bai hanashi gudu ba, don sai ya zamo kamar soso akan ruwa."

Gaba ɗaya aka tuntsire da dariya,shi kuwa Gulzum sai ya turɓune fuska yace a ransa, 'Ina fatan naga ranar da zamu gama karanta KUNDIN TSATSUBA sai na nunawa yaron nan cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne. Tabbas rainin da ke tsakaninmu yayi yawa."

Kafin wani daga cikin su ya ƙara cewa wani abu KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na goma sha biyar. Nan take suka yi arba da hoton wata alƙarya.

A ƙasanta an yi rubutu kamar haka....

".....WANNAN ALƘARYA,ALƘARYA CE TA BALA'I, AN SAMAR DA ITA KIMANIN SHEKARU DUBU HUƊU. MAI KARATU SHIGO CIKINTA KA SHA KALLO..."

Siririyar muryar nan ce ta karanta wannan jawabi iskar cikin KUNDIN TSATSUBA ta sake zuƙe su Jafar gaba ɗayansu. Kawai sai tsintar kansu suka yi a tsakiyar wani babban birni mai yawan cikowar mutane,maza da mata,yara da manya,duk inda suka duba sai su ga kowa na ƙera kwale-kwale ɗan ƙarami daidai shigar mutum ɗaya.

Duk inda suka wuce sai dai su ga ana kallansu kawai,amma babu wanda ya kula su.

Al'amarin da ya jefa su cikin mamaki kenan. Haka dai suka yi ta yawo a cikin garin har suka gaji,sannan suka sami wuri suka zauna, don su huta.

Jafar yace, "Kai ku tsaya fa an ce ruwa baya tsami banza. Ina ganin zai fi kyau mu ma kowannan mu ya ƙera nasa kwale-kwalen domin an ce idan ka je gari kaga kowa ya ɗaura jela a bayansa kaima ka ɗaura."

"Ƙwarai kuwa ka zo da shawara mai kyau domin babu mamaki akwai masifar da zata zo kuma in mutum ba shi da kwale-kwalen hallaka zai yi."

Ba tare da wani da gardama ba suka miƙe tsaye gaba ɗaya don tafiya neman kayan aikin ƙera kwale-kwale. Kawai sai suka ga wani babban mutum ya tunkaro su yana sanye da hular saurata akansa,mutane na biye da shi. Koda zuwansa gare su sai yace, "Yaku waɗannan baƙi ku yi sani cewa kun kawo kanku mahallaka,domin akwai masifar da zata zo mana nan da kwana biyu,damu daku babu wanda zai tsira da rayuwarsa, sai mai nisan kwana."

Cikin mamaki Jafar ya dubi mutunin yace, "Wace irin masifa ce wannan take zuwa muku?"

Mutumin ya yi gyaran murya yace, "Ni sunana sarki Makanul Habasi,gaba ɗaya mutanen garin nan a ƙarƙashin mulkina suke,muna da wata matsala guda ɗaya. Kimanin shekaru dubu huɗu baya wani taƙadarin maridi ya taɓa zuwa mana, koda zuwansa sai ya kama gaba ɗayan mazajen garin nan ya ɗaure su tamau da sarƙoƙi. Su kuwa matayen mu ya bisu ɗaya bayan ɗaya yayi lalata da kowacce. Da ya gama wannan ɓarna sai ya ɓace aka neme shi sama da ƙasa aka rasa.

Bayan tafiyarsa ne matayenmu suka yi ta kuka da baƙin ciki,da ƙyar suka samu suka kwankwance mu daga ɗaurin sarƙar da muka sha.

Haka dai muka rungumi ƙaddara muka ci gaba da rayuwa har tsawon wata tara bamu ƙara ganin wannan maridiba. Koda wata taran nan ya cika sai gaba ɗayan matayenmu suka kama zubar da jini tamkar annobar amai da gudawa. Wannan jini ya rinƙa yawo a cikin gari ya malale ko'ina kai ka ce teku ce ta ɓalle. Ba zato ba tsammani kuma sai jinin ya rinƙa rikiɗa yana zama tsutsutsi masu girman gaske, waɗanda ka iya haɗiye mutum. Nan fa tsutsotsin nan suka hau yagar naman jikin mutane,aka yi ta guje-guje da iface-iface. A wannan rana babu waɗanda suka tsira face waɗanda suka faɗa cikin teku. A cikin tekun ma wasu da yawa sun mutu saboda haɗuwa da muggan halittun cikin ruwa.

Waɗannan tsutsotsi ba su iya shiga cikin teku. Daga sannan wannan masifa ta ci gaba da wakana bayan kowanne kwana arba'in. Wannan shine dalilin da ya sa kuka ga muna ta ƙera kwale-kwaleka ba don komai ba ne sai don mu shiga cikin teku akansa don neman tsira da rayuwarmu. Yaku waɗannan baƙi gashi yanzu kun zo a rashin sa'a domin yau saura kwana biyu rak wannan masifa tu zo."

Yayin da sarki Makanul Habasi yazo nan a zancensa sai hankalin su Jafar ya dugunzuma suka rasa abin dake musu da daÉ—i,Yelisa tace, "Yakai wannan sarki yanzu wane irin taimako zaka yi mana?"

Makanul Habasi yace, "Babu abin da zan iya yi muku face na baiwa kowannen ku kyautar kwale-kwale da zarar kun ga wannan masifa tazo sai ku ruga izuwa cikin teku,idan kuna da nisan kwana sai ku rayu. Idan kuwa ba ku da shi a cikin tekun zaku hallaka.

Yana gama faÉ—in hakan ne ya sa aka kai su Jafar masauki aka ba su abinci da abin sha,kuma aka sa musu magani a jikin raunikan da ke jikinsu.

Kwana biyu na cika wannan annoba ta wakana wato matayen garin suka kama zubar da jini,jinin ya rinƙa malala yana yawo a cikin garin ya game ko'ina sai dai ka ga mutane na ta guje-guje akan jinin kowa na ƙoƙarin zuwa bakin teku. A wannan ranar har dasu Jafar ake wannan gudun ceton rai,sai da ya rage saura ƙiris gaba ɗayan mutanen su riski bakin teku sannan tsutsotsin suka rinƙa ƙurewa mutane gudu suna kama su,suna yagar naman jikinsu suna ci,kai kace karnuka ne ke walima da naman ɓeraye.

Lokacin đa su Jafar suke ƙoƙarin isa bakin teku wata tsutsa guda ɗaya ta tuso su a gaba tana neman ƙure musu gudu. Gulzum ne a gaban kowa,sai Jafar ne ya zamo na ƙarshe, sai da ya zamana tsakanin Jafar da wannan tsutsa bai wuce tazarar taku biyu ba. Duk inda ya đauke ƙafarsa sai ka ga ƙafarta ta dira a wajen ta caki ƙasa. Take wurin zaiyi rami zururu kamar an haƙa rijíya. Sa'adda Jafar yaga tsutsar ta kusan cimmasa sai ya rinƙa ihu yana kiran sunan Gulzum,yana roƙonsa daya kawo masa đauki. Duk da cewar Gulzum na cikin tashin hankali saida dariyar mugunta ta ƙwace masa yace,

"Shegen yaro sai yau ka san ina da amfani to ai ni ba wawa bane bare na koma da baya a ƙoƙarin cetonka ayi biyu babu."

Da yake Yelisa na kan kafaɗar Gulzum ne sai taji abin da ya faɗa. Nan take ta dakawa Gulzum tsawa tace, "Maza ka juya da baya ka ceto rayuwar masoyina Jafar in kuwa ka ƙi na rantse da darajar mahaifina duk sa'adda muka koma duniyar mu sai nayi maka hukunci mai zafi."

Koda jin wannan batu sai Gulzum ya fashe da kuka don tsananin takaici,domin babu abin da ya tsana a rayuwarsa sama da Jafar. Gashi kuma yanzu an tilasta shi akan ya juya ya ceto rayuwarsa. Wanda yin hakan na iya jefa tasa rayuwar cikin ƙila-wa-ƙala.

Bisa dole Gulzumn ya juya da baya cikin tsananin gudu har ya riski Jafar ya sure shi ya aza bisa kafaɗarsa kusa da Yelisa,sannan ya juya cikin zafin nama don ya cigaba da gudu. Kafin ya juya tuni tsutsar nan ta kawo sara kawai sai ta zabtare wani ƙaton nama a duga-dugin Gulzum.

Gulzum ya ƙwalla ihu,cikin tsananin juriya da jarumta ya daɗa mannewa da gudu jinı na zuba sharaf daga dugadugin nasa,amma bai fasa gudun ba,har suka isa bakin teku kowa ya shiga kwale-kwalensa suka miƙa cikin ruwa.

Shigarsu cikin tekun ke da wuya wata irin ƙatuwar macijiya mai tsananin tsawo,kuma mai kawuna bakwai ta taso sama daga cikin ruwan ta rinƙa bugun mutane tana farfasa kwale-kwalensu. Kafin wani lokaci ta zama sanadiyari gawarwaki akan ruwan. Lokaci guda ta wangame bakinta ta haɗiye su Jafar su duka biyar ɗin hár ma da kwale-kwalensu gaba ɗaya. Su Jafar dai sai gani suka yi an jefo su cikin ta su duniyar tare dá kwale-kwalensu sun faɗo gaban KUNDIN TSATSUBA.

A dugadugin Gulzum akwai wannan ƙaton rauni,kuma jini bai dai na zuba ba. Köda raɗaɗi da zogi ya ishi Gulzum sai ransa ya ɓaci yace, 'Ai kuwa tunda na shiga wannan hali a dalilin ceto rayuwar wannan yaron banga amfanin hưtún mu ba,gwarama mu ci gaba da shan wahala kówa jikinsa ya gaya masa."

Kafin wani yace wani abu tuni aljani Gulzum ya daka tsalle ya buÉ—e shafin KUNDIN TSATSUBA na goma sha shida. Take suka yi arba da hoton wata guguwa. A samanta an yi rubutu kamar haka........

"WANNAN GUGUWA,GUGUWA CE TA MASIFA DA BALA'I. ẢN HALICCE TA KIMANIN SHEKARU DUBU SHIDA BAYA,MAI KARATU SHIGO CIKI KA SHA KALLO........."

Gulzum na gama karanta wannan jawabi a fili sai iskar cikin KUNDIN TSATSUBA tayi fitar burgu ta zuƙe su gaba ɗaya suka zama 'yan mini-mini suka faɗa cikin KUNDIN TSATSUBA.



YAYA ƘARSHEN HIKAYAR JARUMI NAZMIR DA GIMBIYA LUZAIYA ZATA KASANCE??

SHIN JARUMI HUBAIRU ZAI IYA SAKE ƘWATO GIMBIYA SIMA DAGA HANNUN SARKI LU'UMANU??

INA LABARIN BOKA SHAMHARU WANDA HAR YANZU BAI FITO BA DAGA HALWAR TSAFIN SA TA ZAMA

MATSATSUBI??

SHIN YAUSHE NE ZA'A GAMA AIKIN RUBUTUN SABON KUNDIN TSATSUBA?? 

SHIN SU BOKANYA SAMARATU ZASU SAMI NASARAR SAMO ABUBUWAN DA SUKE NEMA DON YIN GALABA AKAN SHAMHARU??

WACE IRIN MASIFA SU JAFAR ZASU GANI A CIKIN WANNAN GUGUWA??




Mu haÉ—u a cikin MATSATSUBI littafi na biyu don jin cigaban wannan labari.

DAGA MAI ÆŠEBE MUKU KEWA

ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI


Karanta >>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 12


Post a Comment

0 Comments

Ads