Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 8

Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 1

Part 8

Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini


A wannan yaƙi an yi gagarumin gumurzu kuma daga cikin mutun ɗari ukun nan mutum goma sha biyu ne suka tsira da rayuwarsu, kuma jarumi Kamshur ne mafi sauƙin samun naƙasa da ya rasa ƙafa đaya, amma duk da haka sai da ya ci garin da yaƙi. Wani babban abin baƙin ciki shi ne lokacin da jarumi Kamshur tare da dakarunsa guda goma sha ɗaya suka dawo birnin Dahamul sai gasu ɗauke da tarin mata bayi da kuma ganima, mai yawan gaske,amma dukkanninsu sun zama naƙasassu. Daga wanda ya rasa ƙafa da hannu sai wanda ya rasa ido ko kunne. Koda isarsu fada sarki ya karɓi bayin gaba đaya ya sa aka kai su gidansa. Ganimar yaƙin kuwa aka zubata a baitul mali. Su kuwa su jarumi Kamshur aka yi musu ritaya daga aikin sojan sarki batare da an ba su wata kyauta ba, ko girmamawa bisa wannan gagarumin yaƙi da suka yi.

Koda shigowar su Ikhļam turakar tsoho Kamshur sai suka iske shi a zaune yąna rusa kuka,kamar ƙaramin yaro. Cikin tashin hankali Ikhlam yaje gare shi yace, "Ya kai Abbana ka yi sani cewa tun tasowa ta ina ƙarami zuwa girmana ban taɓa ganin hawaye a idanunka ba, amma yąu ga shi kana rusa kuka, ina dalili?"

Kamshur ya kama hannun Ikhlam ya riƙe da kyau, sannan ya ce, "Ya kai ɗana haƙiƙa zancenka gaskıya ne, amma ka sani cewa dole ne na yi kuka yanzu, ba dan komai ba sai dan sanin cewa da ni da zuri'ata zamu gushe a banza cikin wannan babban birni, kuma har abada ba za'a tuna da mu ba. Na san wannan bayani a dunƙule yake ba lallai ne fahimce shi ba. Ya kai ɗana ina so ne ka sani cewa na yi bauta ga sarki Bashakur tsawon shekaru, amma ga yadda ƙarshena ya kasance wato cikin talauci,ƙunci da naƙasa. Kai kaɗai nake gani zuciyata ta yi sanyi, domin na san cewa ko na mutu na bar baya gashi an wayi gari kai ma ɗin an rabani da kai, kuma an saka ka a irin tafarkin da aka sani, ka ga ashe ni da zuri'ar tawa mun gushe kenan har abadan abidina."

Koda Kamshur ya zo nan a zancensa sai Ikhlam ya fashe da kuka, kuma ya rungeume Kamshur yana mai cewa, "Ya Abbana haƙiƙa ba zan yarda abin da ya same ka ya sameni ba. Lallai ni zan dawo gida lafiya, kuma sai na yì tsawon rai har na yi aure ka samu jika. Tabbas zan kafa maka zuri'a wacce za ta bar abin alfahari, kuma abin tarihi a doron ƙasa."

Kamshur ya sake fashewa da kuka yana cewa, "Fatana kenan, kuma shi ne babban burina."

Haka dai suka ci gaba da alhini har su Nazmir suka lallame shi suka tafi suka bar tsoho Kamshur in da ya ci gaba da kuka abinsa.

Sa'adda suka isa gidan su Bardil sai suka iske mahaifiyarsa Yaluz, wacce ta kasance 'yar shekara arba'in da đoriya. Macece mai ƙwari da ƙarfin zuciya, sai dai ta sami naƙasa guda hudu. Abu na farko gurguwa ce. Gaba ɗaya ƙafafunta biyu a yanke suke iya gwiwa. Hannunta guda na hagu ya shanye, shi kuwa na daman yatsu biyu ne kacal a jikinsa. Da jan jiki take tafiya a harabar gidan, kuma da yatsun nan biyu kacal take iya yin komai.

Koda shigar su Bardil sai Yaluz ta ɗago kai ta yi arba da ɗanta. Take idanunta suka kaɗa suka ciko da ƙwallah. Shi kuwa Bardil dama tuni ya fara zubar da hawaye. Kawai sai ya ruga gareta suka rungume juna, yana mai cewa,

"Yake ummina ki kasance mai haƙuri da juriyar rashin ganina izuwa tsawon lokaci, har mu dawo daga wannan tafiya."

Yaluz ta yi ajiyar numfashi, ta ce, "Ya kai ɗana ai haƙuri tuntuni a cikinsa nake, tun ma kafin na haifeka, kuma a cikinsa zan mutu. Ka tuna cewa an haifeni cikin ƙaddara shanyayyen hannu guda ɗaya, kuma ba cikakkun yatsu. Sannan kuma 'yan fashi suka zamo sanadiyar yankewar ƙafafuna biyu. Ai ko da wannan naƙasa guda huɗu aka barni ta ishe ni shan wahalar duniya da takaici. Yau sai ga shi kuma kai kaɗai da ka rage mini a duniya an rabani da kai. Waye zai ji ƙaina kamar yadda ka ke yi mini? Waye zai ci gaba da yi mini wahala ba tare da ya yi ƙyanƙyamina ba? Ai na ka sai naka tabbas ɗana in babu kai mutuwa zan yi domin takaicı ma kaɗai zai iya kashe ni."

Koda jin haka sai Bardil ya sake fashewa da kuka, ya ƙanƙame Yaluz a ƙirjinsa yana mai cewa,

"Ki daina kiran mutuwa. Tabbas ba zan tafi na barki a duniya ke kaɗai ba. Komai rintsi sai na dawo gare ki don na ci gaba da taimakon ki, ina kula da lafiyar ki."

Yaluz ta ce, "Kaico! Ai bakin alƙalami riga ya bushe. Ya kai đana ka sani cewa nayi mummunan mafarki bisa wannan tafiya ta ku, tabbas an nuna mini cewa in ka tafi ba za ka dawo ba.

Haƙiƙa yanzu muna yin bankwana ne,daga yau mun rabu kenan har abada."

Koda jin haka sai gaba ɗaya hankalinsu Nazmir ya dugunzuma suka fashe da kuka, domin Bardil ya sha gaya musu ire-iren mafarkin da

mahaifiyarsa ke yi, kuma mafarkin ya sha tabbata a gaske suna gani ko sau ɗaya ba'a taɓa samun saɓani ba. Bardil da Yaluz suka ƙara ƙanƙame juna, suka yi ta kuka har tsawon lokaci, sannan suka rabu.

Daga nan kuma su Nazmir suka sake

ɗunguma su bakwan suka tafi gidansu Halufa. Anan ne Halufa da Zuwaisa suka yi bankwana da ɗan su Nazmir inda suka yi musu fatan alheri da nasara,kuma Halufa ya ƙara tunasar da su irin abubuwan da ya kama ta su kiyaye yayin da suke yaƙi ko kuma suka fuskanci bala'i.

A ƙarshe dai Halufa na kuka, suma su Nazmir suna yi aka rabu kowa ya je ya kwanta domin a lokacin dare ya raba. Babu sauran abin yi sai jiran wayewar gari a tunkari fada don wannan gagarumar tafiya.

A yau fadar ta cika ta batse, an yi mugun gangami irin wanda ba'a taɓa irin sa ba,kai ka ce gaba ɗayan mutanen ƙasar ne suka hallara babbba da yaro, mace da namiji. Idan ka duba tsakiyar fadar babu abin da za ka gani face jarumi Nazmir da abokansa guda shida, a tsaitsaye kuma a jere cikin shigar yaƙi. Kai da ganinsu ka san cewa manyan barada ne waɗanda za su iya shafe gari guda,sun kasance masu matuƙar kwarjini da ban tsoro.

A can sama kan tudu inda karagar mulki take sarki Bashakur ne a zaune yana murmushin ƙeta, dakaru da fadawa sun kewaye shi, sauran jama'ar gari kuwa sai hayaniya suke kowa na faɗin albarkacin bakinsa,fadar ta cika da hayaniya. Kawai sai sarki Bashakur ya ɗaga hannunsa sama take fadar ta yi tsit kamar babu wani abu mai rai a wajen, saboda tsananin tsoro da biyayya a gare shi.

Bashakur ya miƙe tsaye yana mai murmushi ya tako da ƙafafunsa takan matattakalar da ke gaban karagarsa ya sauko ƙasa, inda su jarumi Nazmir ke tsaye. Sannan ya dube su daya bayan ɗaya, ka ƙare musu kallo kawai sai yace,

"Yaku waɗannan zaratan samari haƙiƙa na gamsu cewar za ku iya aiwatar da wannan aiki mai muhimmanci, kuma kun fto da kyakkyawan shiri. Duk da haka zan ƙara muku ƙarfi ta hanyar baku barade dubu goma domin duk yadda kuke zaton wannan aiki yafi haka. Wannan aiki ba komai bane face ina son ku tafi izuwa wani birni da ake kira Mahazus ku ɗauko mini 'yar sarkin garin ku kawo mini ita nan don na aureta. Ita dai wannan 'yar sarki sunanta gimbiya Luzaiya. Masu bincike sun gano cewa a halin yanzu duk duniya babu wata 'ya mace kyakkyawa kamarta ku sani cewa tsakanina da mahaifin gimbiya Luzaiya tsohuwar gaba ce wacce samo asali fiye da shekaru ashirin baya. Tun a wancan karo na so na ga bayansa amma ban sami iko ba. Saboda nisan da ke tsakanin ƙasa ta da ta sa,domin tafiya ce ta wata bakwai, da kwana tara.

A halin yanzu wannan sarki ya ƙara bunƙasa ainun a ƙarfin mulki da ƙarfin mayaƙa, kuma a duniya babu abin da yake so sama da wannan 'ya tasa gimbiya Luzaiya. Ina son idan kun je ku kashe shi, kuma ku yanko mini kan shi sannan ku taho da kan tare da 'yar ta sa. ldan kuka saɓa wannan umarni ko kun dawo a raye zaku zama matattu. Idan ku kai nasara zan cika alƙawari na akanka jarumi Nazmir,suma abokan naka zan raba musu sarauta tare da dukiya mai yawan gaske wadda zaku yi taci iyakar rayuwarku ta duniya, na sallame ku zan kasance mai sauraronku nan da wata goma sha huɗu da 'yan kwanaki. Sarki Bashakur na gama wannan jawabi ya koma kan kujerarsa ya zauna,sannan su jarumı Nazmir suka kama dawankansu suka ɗare,dama tuntuni an shirya dakaru dubu goma waɗanda za su take musu baya.

Nan take jama'a suka dare aka basu hanya ana buga musu tambura,maroƙa nayi musu kirari,kai idan kaga wannan zuga sai kayi zaton yaƙin duniya za'a yi saboda kwarjininsu.

Daga wannan rana su jarumi Nazmir suka kama hanya suka yi tafiya suna ratsawa ta cikin dazuzzuka,gari,ƙasa-ƙasa. Duk inda suka iski 'yan fashi ko namun daji sai sun tarwatsasu sun kashe na kashewa, amma duk inda suka riski gari basa yiwa mutane komai kuma basa taɓa dukiyarsu sai dai su tambayi hanyar zuwa birinin Mahazus a nuna musu.

Tafiya kwanci tashi har suka shafe wata bakwai da kwana tara kwatsam suka hango ganuwar birmin Mahazus acan gaba nesa đa su. Nan take farin ciki ya lulluɓesu, kawai sai shugaban tawaga jarumi Nazmir ya bada umarnin a sauka. Nan fa aka sassauka aka kafa tantuna kowa ya buɗe guzurinsa aka ci aka sha aka shiga hutawa.

Acan cikin birnin Mahazus kuwa tuni labari ya riski sarki Falalul Bahafus cewa ga wata tawaga can ta rundunar mayaƙa ta sauka a bayan gari ba'asan da wacce suka zoba. Cikin kwanciyar hankali da taƙama sarki Fahalul Bahafus ya dubi wani bafadensa mai suna Jambu yace, "maza kayi hawa ka tafi ga wannan runduna ka tambayesu abin da ke tafe dasu." Jambu ya rissina yace, "an gama ya mai duniya." Cikin hanzari ya fita daga fadar ya hau doki ya nufi wajen gari. A daidai wannan lokaci ne gimbiya Luzaiya ta shigo cikin fadar kuyangi na take mata baya. Nan da nan hankalin kowa ya koma kanta domin ta tafi da tunanin masu tunani. Tsananin kyawunta ko yaushe yana zare imanin dukkanin wani 'da' na miji kuma yana kankare baƙin cikin zuciya wanda ya dafe tsawon shekaru.

Gimbiya Luzaiya na sanye da wata doguwar riga ce ruwan ɗorawa mai shara-shara, daga ƙasa tayi bazar bazar kamar ɗawisu ya buɗe fukafukansa.

Mutum na iya ganin cikar surarta inda ta kasance mai shamulallen ciki da faffaɗan ƙugu, kirjinta a cike yake kuma ta kasance doguwa mai dogon gashi wanda ya sauka har gadon bayanta, fara ce sol kamar tsada, ko'ina fatar jikinta sumul suɓul tamkar ta jariri. Tana da ƙwala-ƙwalan idanu a ƙarƙashin gira mai ƙyallin baƙi kuma sun kasance masu haske sosai, hancinta dogone siriri kamar alƙalami a ƙasansa an dasa mata ƙaramin baki mai ban sha'awa.(🙄🙄🙄🙄 wannan bayani haka 🙄🙄).

ldan tayi murmushi sai kaga kamar kyawun nata ya linka kansa.(Wata sabuwa😝😝😂).

Tana tafe a hankali cikin izza ta iso gaban mahaifinta shi kuwa sai ya miƙe ya tare ta sannan ya kama hannunta na dama ya sumbaci kan yatsunta sannan ya zaunar da ita kusa dashi suna masu duban juna cikin murmushi da nuna zunzurutun ƙauna.

Luzaiya tace "Ya kai Abbana ina can gidana yanzu ina shirin fita rangadi bayan gari sai ga saƙonka ya riskeni cewar na dakatar da fita shin lafiya kuwa?"

Sarki Fahalul Bahafus yace "E, to lafiyar kenan amma ba ƙalau ba. Abin da yasa nace ki fasa fita shine labari yazo mini cewa rundunar mayaƙa ta sauka a bayan gari kuma ba'a san me ya kawo suba.

Don haka yanzu na tura aje aji dalilin zuwansu ƙasata."

Koda jin haka sai Luzaiya tayi murmushi tace "Ai koma dame suka zo dai dai muke dasu, ya kai Abbana ni kam nasan cewa a halin yanzu yadda kake da tarin gwarzaye mayaƙa babu wata runduna da zata iya cin mu da yaƙi."

Sarki ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Tabbás haka zancenki yake 'yata domin inda na kasance azzalumi da tuni yanzu na mallaki duk ƙasashen dake maƙwabtataka damu." Sarki na gama faydin haka kenan sai ga Jambu ya dawo ɗauke da wasiƙa,da zuwa sai ya miƙa takardar ga sarki shi kuma ya baiwa magatakarda ya umarceshi daya karanta ta.

Take magatakarda ya warware ya fara bayani kamar haka:-

"DAGA JARUMI NAZMIR BIN HALUFA ZUWA GA SARKI FAHALUL BAHAFUS NA BIRNIN MAHAZÜS.

GAISUWA TARE DA BIYAYYA A GAREKA YAKAI WANNAN SARKI, KAYI SANI CEWA NI MANZO NE DAGA SARKI BASHAKUR NA BIRNIN DAHAMUL KUMA BAI TURONI GARE KA DAN KOMAI BA SAI DON NA YANKE KANKA NA KAI MASA KUMA NA TAFI DA KYAKKYAWAR 'YARKA GIMBIYA LUZAIYA DON TA ZAMA SAƊAKARSA,INA MAI SHAWARTARKA DA KASA A YANKO MINI KAN NAKA A HAƊO TARE DA 'YARKA A KAWO MINI DOMIN KA TSIRAR DA RAYUKAN JAMA'ARKA NA TAFI SALIN ALIN IDAN KUMA KA ƘI BIN WANNAN UMARNI NI DA BARADENA ZAMU SHIGO CIKIN BIRNINKA DA ƘARFIN TSIYA MU CIKA UMARNIN SARKIN MU."

Tun sa'adda jama'a suka ji ma'anar wannan wasiƙa fadar ta yamutse da surutu da kuma al'ajabi saida sarki Fahalul Bahafus ya rinƙa daka tsawa sannan magatakarda ya sami damar kammala karantawa, yana gamawa ne sarki Fahalul Bahafus ya bushe da mahaukaciyar dariya. Itama gimbiya Luzaiya tare da sauran manyan fadawa suka yi tsit,Luzaiya ta dubi mahaifinta tace, "ashe mahaukata marasa lissafi da tunani basa ƙarewa a cikin duniyarnan. Yanzu in banda ɓatan basira yaushe wasu mutane zasu yi tunanin cewa zasu iya shigowa har har cikin garin nan suyi mana wannan wulaƙanci.

Sarki Fahalul Bahafus yayi gyaran murya yace, "yake 'yata ai kinsan shi maƙiyi har abada baya fitar da ran samun nasara akan maƙiyinsa, ki sani cewa fiye da shekaru ashirin baya sarki Bashakur ya yi iyakar ƙoƙarinsa akan yaga bayana amma abu ya faskara sai yanzu kuma yake ganin ya yi cikakken shirin da zai iya samun galaba a kaina bai san cewa jiya ba yau bace nima nawa shirin ya linka nasa.

Sarki Fahalul Bahafus ya dubi Jambu yace, "Menene adadin waɗannan dakaru?"

Jambu ya ce "Ya sarkin sarakai ai gaba ɗayansu ba zasu wuce dubu goma da ɗoriya ba domin shi shugaban tawagarma matashine ba zai fi shekara ashirin ba shi ne jarumi Nazmir ɗin. Sai kuma waɗansu mutum shida waɗanda su kadai ne ma suke da cikar sura ta jarumai."

Koda jin wannan batu sai sarki ya sake bushewa da dariya yace,

"Maza a rubuta takardar raddi a kaiwa wannan mara kunyar jarumi kuma a shirya mayaƙa dubu duari su je su maishe dasu abincin tsutsa." Nan da nan kuwa aka cika umarni daga nan fada ta watse kowa ya kama gabansa.

Lokacin da takardar raddi ta riski jarumi Nazmir sai suka cika da baƙin ciki, domin ba sa son abin da zai janyo a zub da jini mai yawa,cikin matuƙar damuwa Nazmir ya dubi su Huzaik yace, "Kaicon wannan sarki amma fa ya yi gurguwar shawara wacce za ta janyo masa babbar nadama.


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 8 


Domin sauke Audio sai ku danna bulun Rubutun nan

Post a Comment

0 Comments

Ads