Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 11


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 1 

Part 11

Marubuci: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh 

Al'amarin su Jafar kuwa bayan Mazalish ta gama kalle-kallenta suka faɗo duniyar su Jafar sai hankalinta ya koma kan KUNDIN TSATSUBA, wanda ke buɗe a gabansu ta ƙare masa kallo tsaf a cikin nutsuwa. Sannan ta dubi Jafar,Yelisa,Mashrila da Gulzum tace, "Yanzu a cikinku nan babu wanda zaí iya tsayar da littafin nan daga ci gaba da buɗe kansa don na tafi neman masoyina jarumi Hubairu."

Koda jin wannan batsu sai Yelisa ta yi tsaki tace, "Wannan kuma wace irin maganar banza kike yì, inda muna da wannan ikon ai da tuni muma mun yì ko dan mu huta da tsananin azabar da muke sha a cikinsa."

Jafar ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Haba yayata ai kawai ki rungumi ƙaddara kawai domin kin sayi wahala da kuɗinki tun da kika yi gangacin biyo mu. Da dai kin yì zamanki a can duniyarku ta mayu da ya fiye miki kwanciyar hankali."

Gama faɗin haka ke da wuya sai shafin KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na goma sha uku inda suka yi arba da hoton wani surƙuƙin daji a samansa an yi rubutu kamar haka:

"WANNAN JEJI, JEJI NE NA ABUBUWAN MASIFA IRI-IRI. AN ƘIRƘIRESHI NE KIMANIN SHEKARU DUBU BAYA."

MAI KARATU SHIGO CIKINSA KA SHA KALLO."

Wata siririyar murya ce ta karanta wannan jawabi. Muryar na đaukewa iskar cikin kundin zuƙe su Jafar suka zama 'yan mini-mini suka faɗa ciki. Kawai sai suka tsinci kansu a tsakiyar wannan jeji irin wanda ba su taɓa gani ba a rayuwarsu,domin komai na cikin sa ya kasance babba mai girman gaske. Ma'ana bishiyoyi, duwatsu da tsirai. Manya-manya ne, girmansu ya wuce ƙima domin bishiya ɗaya sai kaga girman ta ya ninka irin ta duniyar su Jafar sau arba'in. Kuma kowacce bishiya siffar fuskar mutuntaka wato tana da ido,baki da hanci har da ma kunnuwa,kuma suna motsi wato suna harkokinsu kamar yadda sauran halittu masu rai da jiki keyi, saidai ka ga bishiya na tafiya da ƙafafunta ko kuma ka ga tana aiyuka iri-iri. A cikinsu kuma akwai manya da ƙanana.

Ba zato ba tsammani sai gaba ɗayan bishiyoyin dake wajen suka yi wa su Jafar ƙawanya ya zamana babu wata hanya da za su iya bi su tsere.

Mafi girma daga cikin bishiyoyin ta buɗi baki tace, "Yaku waɗannan mutane mene ne ya kawo ku duniyarmu? Shin kun zo neman wani abu ne ko kuwa kun zo leƙen asiri ne?"

Cikin firgici su Jafar suka ƙurawa bishiyar idanu aka rasa wanda zai bada amsar tambayar har sai da bishiyar ta daka musu tsawa gami da maimaita tambayar. Jafar ya ɗaga kansa sama ya dubi wannan ƙatuwar bishiya mai kama da tsauni a gabansa yace, "Yake wannan bishiya ki yi sani cewa ba mu kawo kanmu nan ba kawo mu aka yi, kuma bamu da nufin komai a kanku kuma ba mu zo neman komai anan ba,muna neman alfarma idan har zaku iya mayar damu in da muka fito to ku taimakamana."

Koda jin wannan batu sai babbar bishiyar ta tuntsire da mahaukaciyar dariya mai kama da tsawa.

Nan take sauran 'yan uwanta bishiyoyin suma suka tayata dariyar. Al'amarin da ya hargitsa jejin gaba ɗaya kenan,ya kama girgiza kamar ƙasa zata daddare. Wata irin ƙara mara daɗin ji ta cika kunnuwansu Jafar bisa dole suka toşhe kunnuwansu suka farfaɗi ƙasa.

Lokaci guda bishiyoyin suka daina dariyar,komai ya tsaya cak. Babbar bishiya tace, "Yaku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa mun san duk irin makircinku da wayonku lallai ba ku isa ku yaudare mu ba, domin a shekarun baya ire-iren ku sun zo mana don leƙen asiri da nemạn wasu abubuwa don bunƙasa harkokin ƙere-ƙerensu na zamani wanda da sune suke yi mana ɓarna. Bisa wannan dalili yanzu zamu tafi da ku izuwa fadar sarkinmu don a bincike ku,a gane ko kuna ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane. Kafin wani daga cikin su Jąfar ya ce wani abu tuni wasu bishiyoyi guda biyar sun jeho rassansu sun kanannaɗesu kamar yadda ake naɗe tabarmå,kuma kowacce bishiya mutum đaya ta ɗauka. Kawai sai suka ga bishiyoyin sun tashi da su sama kamar ɓacewar taurari,sannan aka bayyana da su a wani jejin dabam wanda babu komai a cikinsa face jerin bishiyoyi irin waɗannan masu tsananin yawan gaske. Ko'inà ka duba sune iya hange ba adadi.

A can gefe guda bisa kan wani Æ™aton tsauni wata jibgegiyar bishiya  ce wadda duk ta kere sauran a girmÄ…. Nan take gaba É—ayan bishiyoyin suka yi mata sujjada alamar gaisuwa. Jibgegiyar bishiyar ta buÉ—e baki tace, "An gaisheku mutanenn birnin tsirrai."

Daga nan sai aka gurfanar da su Jafar a gaban bishiyar. Ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauko su tace, "Ya sarkin sarakai ɗazu ne muka kama waɗannan bil'adaman a cikin gonarka ta bayan gari,muna zargin suma sun zo ne leƙen asiri, ko neman ma'adanai babu mamaki ma suna daga cikin al'ummar Sukardas."

Koda jin haka sai sarauniyar bishiyoyi ta dubi su Jafar ta ƙare musu kallo cikin nutsuwa,sannan ta buɗe baki cikin wata irin siririyar murya mai taushi tamkar ta ƙaramar yarinya 'yar shckara huɗu,tace, "Ammą dai fadawannan nawa kun cika shashashai. Shin makafi ne ku ba ku yi nazarin waɗannan mutanen bą sosai? Ai ko kaɗan ba su yi kama da irin waɗancan masu zuwa leƙen asiri ba,ko ncman ma'adanai haką kuma ba su yi kama da irin al'ummar Sukardas ba."

Sarauniyar ta dubi su Jafar tace, "Yakų waɗannan baƙi ina son ku saki jikinku damu lallai ba zamu cutar da ku ba, kuma ku matso nan kusa dą ni."

Nan take su Jafar suka ƙarasa gaban sarauniyar bishiyoyi suka zazzauna. Sarauniya ta sa aka-kawo musu ruwan sha da 'ya'yan itatuwa masu zaƙi da daɗin ɗanɗano iriin wanda ba su taɓa ci ba sukq kimtsa cikinsu. Bayan sun nutsu ne sarauniyar ta sake dubansu tace, "To ina son yanzu ku bani labarinku da yadda kuka zo nan."

Ba tare da wata gardama ba Jafar ya kwashe labarinsu tun daga lokacin da suka É—auko KUNDIN TSATSUBA a rijiyar gidan Riziyal shi da Yelisa kawo i yanzu ya zaiyane shi. Koda ya gama bada labarin sai sarauniyar ta hau yi musu tafi suma sauran bishiyoyin sai suka yi koyi da ita. Daga can kuma sai suka daina tafin tace, "Yakai Jafar haÆ™iÆ™a kai da abokan tafiyarka kun cancanci yabo da jinjina domin kun yi matuÆ™ar Æ™oÆ™ari wajen kare kan ku abisa wahalar da kuke sha a cikin KUNDIN TSATSUBA,kuma kun cika jarumai. Muma yanzu zamu sanar daku masifar da ke addabarmu a garin nan,kuma muna fatan zaku taimaka mana mu kawo Æ™arshenta,domin idan ma ba ku taimaka mana ba in ta zo sai ta haÉ—a da ku. 

Mun sani cewa ku bil'adama kuna da basira da hikima fiye da kowacce irin halitta shi yasa muke son ku taimaka mana,ku yi sani cewa a bayan kowanne kwana goma akwai wasu irin halitta masu kawuna irin na batoyi da kuma fufafukai irin na jemagu suna zuwa mana su yi ta feso mana wuta daga sama suna ƙonemu.

Sai sun yi mana ɓarna mai yawa sannan suke tafiya. Babu irin hikimar da ba mu yi ba don ganin mu harbosu ko mu kama su amma abu ya faskara domin komai ƙarfin makami baya iya huda jikinsu.

Haka kuma jikin na su na da matuƙar santsi baya ruƙuwa."

Koda jin wannan batu sai Mashrila tace, "Ai wannan matsalar taku mai sauƙi ce ni na san hanyar da za'a bi a iya kama waɗannan halittu."

Cikin zumuÉ—i sarauniyar bishiyoyi tace, "Yarinya maza ki sanar da mu wannan hanya domin yau saura kwana uku waÉ—annan halittu su zo."

Mashrila tace, "Kada ku damu yanzu dai ku barmu mu huta tukunna domin mun sha wahala mai yawa a duniyar su Mazalish. Nan da wani lokaci kaÉ—an zan sanar da ku hikimar da ke raina."

Sai da su Jafar suka yi baccin sa'a bakwai sannan suka farka. Farkawarsu ke da wuya aka sake kawo musu nau'in ya'yan itatuwan suka ci suka ƙoshi. Sannan Mashrila tace aje a samo mata ɗanyar jijiyar bishiya mai tarin yawa. Nan take wata ƙatuwar bishiya ta bugi ƙirji tace, ita ta yarda a yanki tata jijiyar. Kawai sai ta fiddo da jijiyoyinta aka yi ta tsinka sai da aka tara mai yawa, a sannnan ne bishiyar ta faɗi ƙasa summmiya sai da aka yayyafa mata ruwa ta farfaɗo.

Mashrila tace, "Waye gwanin iya saƙa a cikinku?" Wata mitsitsiyar tace itace. Mashrila tace mata, "ina so ki ɗauki jijiyar nan ki saka mini raga mai ƙananan ƙofofi kuma mai girman gaske, kuma ki yi mata mariƙai guda huɗu a ƙarshen bakunanta. A ƙallah ina son ki yi ragar guda dubu."

Mitsitsiyar bishiya tace, "An gama" Nan take ta zauna ta fara aiki. Ai kuwa a cikin rabin sa'a ta kammnala abin da aka umarce ta,koda ta gama sai Mashrila ta dubi sarauniyar bishiyoyi tace, "To kin ga waɗannan abubuwan da su zamu yi amfani muna lulluɓe waɗannan halittu muna ɗaure su a jikin duwatsu. Ko sun fesawa wannan raga wuta ba za ta ƙone ba,saboda danshin ruwan da ke jikinta."

Koda jin haka sai mamaki ya kama kowa a wajen. Sauraniyar bishiyoyi tace, "Haƙiƙa wannan yarinyar kin cika mai basira, tabbas wannan hikima ta ki za ta yi aiki sosai."

Kwana uku na cika sai ga waɗannan halittu masu kan batoyi da fukafukan jemagu,sun iso sai shawagi suke a sararin samaniya. Suna feso wuta tana ƙone bishiyoyi. Nan da nan jejin ya hargitse gaba ɗaya bishiyoyin sukai ta guje-guje da iface-iface. Idan mutum na wajen ya ga yadda rayukan bishiyoyin ke salwanta dole ne ya tausaya.

A wannan lokaci su Jafar tare da wasu manyan bishiyoyi sun ɓuya a cikin wani kogon dutse ɗauke da waɗannan raga-raga guda dubu. Sai da suka barí halíttun nan sun fara saukowa ƙasa-ƙasa,sannan suka yi fitar burgu suna lullube su da ragar,sannan su ɗaure su a jikin duwatsu, cikin zafin nama da sauri.

Kafin a jima an kama halittun sama da guda ɗari tara. Sauran kuwa duk saí suka tsere. Waɗanda aka kama ɗin sai suka kasa ceton kansų daga cikin ragar suka yi ta ruri suna fesa wuta,amma a banza don ba su sami damar kuɓuta ba. Koda ganin abin da ya faru sai gaba ɗayan bishiyoyin garin suka rugo suka hau tsalle-tsalle da waƙe-waƙe don murna. Sarauniyar bishiyoyi ta zo gaban Mashrila ta tsaya tace, "Yanzu ya zamu yi da waɗannan halittun da muka kama?"

Mashrila ta ce, "Haka za ku bar su su yi ta zama a cikin ragar nan har yunwa da ƙishirwa su kashe su."

Nan fa bishiyoyi suka yi ta godiya ga Mashrila da abokan tafiyarta,bayan an nutsu sai Jafar ya dubi sarÄ…uniya yace, "Yanzu ya za'a yi mu fita daga wannan garin naku,mu shiga wani?"

Koda jin wannan tambaya sai sarauniyar bishiyoyi ta dubi wata basamudiyar bishiya tace, "yake Kalbaladu na uwarce ki da ki fitar da su daga birnina."

Tana gąmą faɗin hakan saita zuro rassanta ta suri Jafar, Yelisa, Mashrila, Mazalish da Gulzum ta yi sama dąsu sannan ta wangame bakinta ta jefa su a ciki. Kawai sai su Jąfar suka ga an watso su cikin duniyar su ta KUNDIN TSATSUBA. Har yanzu shạfi na goma sha uku ne a buɗe. Gaba đayansų suka dubi juna kamar waɗanda suka farka daga mafarki. Jafan ya ce, "Kai amma fa wannan shafin na goma sha uku ya zo mana ɖa alheri domin ba mu sha wata wahala mai yawa a cikinsa ba."

Yelisa tace, "Ƙwarai kuwa ai sai ka buđe mana shafin gaba babu mamaki mun fita kenan daga cikin wahala."

Caraf Mashrila ta tari numfashinta, tace, "Waye ya gaya miki cewar mun fita daga wahala?

Ina tabbatar muku da cewa yanzu ne ma zamu fara shiga wahala duk wadda aka sha a baya sharar fage ce."

Gulzum yace, "Kun ga ba hira zamu tsaya yi ba aikin shekara goma sha tara da wata shida ne a gabanmu,ku yi sauri ku buđe mana shafin gaba ko mun ragewa kanmu tsawon lokaci."

Cikin yanayin mamaki Jafar ya dubi Gulzum yace, "Ya akai ka san cewa sai mun shafe wannan lokacin muna karanta KUNDIN TSATSUBA?"

Gulzum yace, "Kai dai na ga alama daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa gareka. Yanzu ashe har ka manta cewa an gaya mana shekaru ashirin za mu yi muna karanta littafin kuma duka-duka yanzu a cikin wata na huɗu muke?"

Kafin Jafar ya ƙara cewa wani abu sai Yelisa ta yunƙura ta buɗo shafi na goma sha huɗu inda suka yi arba da hoton wani kogon dutse. A samansa

an yi rubutu kamar haka.

"WANNAN KOGO,KOGO NE NA MASIFA DA BALA'I IRI IRI.

AN ƘIRƘIRESHI FIYE DA SHEKARU DUBU GOMA BAYA. MAI KARATU SHIGO CIKINSA KA SHA KALLO."

Koda Yelisa ta gama karanta wannan jawabí a fili sai iskar KUNDIN TSATSUBA tayi fitar burgu ta zuƙe su gaba đaya su biyar ɗin suka zama 'yan ƙanana mini-mini suka faɗa ciki.

Kawai sai gani suka yi sun faɗo cikin wani jeji mai girman gaske,babu komaí a cikinsa face wani katafaren dutse mai ƙaton kogo. Ko'ina ka duba a jejin iyakar ganinka wannan dutse ne ba'a íya ganin ƙarshen sa. Lokaci guda su Jafar suka mimmiƙe tsaye suka yi nazarin dutsen sannan suka dubi junansu. Yelisa tace, "Yanzu mene ne abin yi?"

"Abin yi kawai mu shiga cikin kogon nan tunda babu wata hanyar da zamu iya samu a jejin nan ko ina dutse ne." Mashrila ce ta ba da wannan amsa.

Gulzum,Jafar Mazalish suka amince da wannan shawara ta Mashrila. Ba tare da É“ata wani lokaci ba,suka kunna kai cikin kogon. Wani abin mamaki shi ne koda shigar su cikin kogon sai duhu ya yaye haske ya baibaye cikinsa ya zamana suna ganin komai.

Babu komai a cikin kogon face tsiraron duwatsu da ƙananun bishiyoyi. Haka dai su Jafar suka yi tafiya a cikin kogon be tare da sun ga komai ba,kuma ba su ji motsin komai ba har tsawon sa'a hudu. A wannan lokaci duk sun gaji ainun Gulzum ne kaɗai bai gaji ba.

Jafar da Yelisa kam har haɗa ƙafa suke suna rangaji a hanya tamkar waɗanda suka bugu da giya.

Kwatsam sai suka yi kiciɓis da wata ƙatuwar rijiya wadda aka rufe ta da murfin ƙaton mummulallen ƙarfe mai nauyin tsiya. Dukkaninsu sai suka yi turus a gaban rijiyar. Jafar yace, "Me ya kamata mu yi da rijiyar nan?"

Mazalish ta ce, "Kawai mu buɗe ta ai dama duk muna jin ƙishirwa sai kowa ya jiƙa maƙogwaronsa."

"Kai anya kuwa za'a iya samun ruwa a cikin rijiyar nan ku duba fa ku gani bakinta a bushe yake ƙyamas babu alamar ana ɗiban ruwa a cikinta.'' Yelisa ce tayi wannan jawabi. Ita kuwa Mashrila sai ta daka mata harara tace, "Ke dai kin cika tsoro,to ki sani har abada matsoraci baya zama gwanı."

Cikin fushi Yelisa tace, "To na ji ni matsoraciya ce, tun da ke jaruma ce ai sai ki buÉ—e mana rijiyar ko."

"Wannan kuma aikin sarkin ƙarfi ne Gulzum." In ji Jafar.

Gulzum ya murtuke fuska duk da cewar an yabeshi. Nan take Gulzum ya sa hannu É—aya da nufin É—auke murfin rijiyar amma sai ya kasa.

Mamaki ya kama shi ya saka hannayensa biyu ya taƙarƙare iya ƙarfinsa ya ɗago murfin,amma sai ya

kasa đaga shi gaba ɗaya. Nan fa su Jafar suka cika da mamaki, domin ba su taɓa ganin aikin ƙarfin da ya gagari Gulzum ba sai yau,tun sa'adda suka shigo cikin KUNDIN TSATSUBA.

Koda ganin abin da ya faru sai Mazalish tace, "Gulzum gafara nan ka bani wuri tunda ka kasa buÉ—ewa."

Gulzum yace, "To 'yar sarkin mayu ai sai ki jarraba ƙarfin maitarki anan mu gani."

Mazalish ta daka masa tsawa,tace "Kar ka sake kirana maiya tunda dai ni ba maiya ba ce, kuma na baro maita a can mahallinta."

Kawai sai Mazalish ta nuna murfin rijiyar nan da É—anyatsanta guda. Take wata siririyar iska ta fito daga cikin É—anyatsan ta É—aga murfin rijiyar nan sama ta ajiye shi a gefe guda. Mazalish ta dube su gaba É—aya tace, "Ni kaÉ—ai ce zan iya yin tsafi ya yi aiki a cikinku saboda na sami tsafina ne a cikin duniyar KUNDIN TSATSUBA,ku kuwa kun samo naku tsafin daga wata duniyar dabam."

Mazalish na gama rufe bakinta kenan sai wasu irin halittu suka yo fitar burgu daga cikin rijiyar nan suna yin wata irin ƙara mara daɗin ji wacce ka iya kashe dodon kunne.

Karanta >>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 12



Post a Comment

0 Comments

Ads