Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 10


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 1 

Part 10

Marubuci: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh 



A lokacin saura 'yan tsirarun barade a filin. Koda aka hango tahowar sarki Fahalul Bahafus bisa kan doki sai kowa ya tsaya da yaƙin aka zuba masa idanu cikin mamaki,yayin da sarki Fahalul Bahafus ya zo gaban jarumi Nazmir sai ya ja tunga ya sauko daga kan dokin ba tare da ya riƙe wani makami ba. Kawai saí ya durƙusa a gaban Nazmir bisa gwiwoyinsa yace, "Yakai wannan jarumi ka yi sani cewa na sallama kaina da 'yata a gareka. Ina umartarka da ka sare kaina ka kaiwa sarkinku kamar yadda ya umarce ka, amma ina son ka yi mini wata alfarma guda ɗaya."

Cikín sanyin jiki da sanyin murya jarumi Nazmir yace, "Wace irin alfarma kake so na yi maka?"

"Ina son idan ka koma ƙasarku ka fara kaiwa mahaifinka kaina ka gaya masa cewa ni sarki Fahalul Bafus na sallama rayuwata, domin ta ka."

Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama jarumi Nazmir ya ce, "Yakai wannan sarki ban gane manufarka ba."

Fahalul Bahafus yace, "Yakai gwarzon jarumi ka yi sani cewa kamar shekaru ashirin baya mahaifinka sadauki Halufa ya taɓa zuwa nan ƙasata ya kamani da ƙarfin tsiya ya kaini kurkukun sarkinku aka kulleni,amma da ya ji cewar sarkinku yace dole ne ya kashe ni sai ya je kurkukun cikin dare ya tarwatsa masu gadi ya kuɓutar da ni. Yayin da na tambaye shi dalilin da ya sa ya kuɓutar da ni sai ya ce saboda ya san ina da kyakkyawar 'ya guda ɗaya wacce nake matuƙar ƙauna kuma ita ma ta shaƙu dani ainun,saboda haka ba zai yarda ya zama silar raba soyayyar da ke tsakanin đa da mahaifi ba,domin shi ma yana da ɗan da baya son ya zama maraya,kasancewa har yanzu baku kashe kaso ɗaya daga cikin kaso ɗari ba na yawan mayaƙana,na rantse da darajar karagata idan mayaƙana suka fito gaba ɗaya yanzu sai sun ƙarar da ku koda kuwa kun kasance aljanu ba mutane ba.

Ya kai wannan jarumi haƙiƙa ba zan yarda na raba soyayyar dake tsakanin ka da mahaifinka ba,domin ya ceci rayuwata a lokacin da nake son na rayu,don rayuwar 'yata. Dole ne yanzu na sakawa mahaifinka da irin alfarmar da ya yi mini. Lallai ina son ka rayu ka koma gare shi,maza ka sare kaina kuma kaje ka kamo 'yata ka tafi da ita. Babu wanda zai hanaka yin hakan face ni."

Sa'adda sarki Fahalul Bahafus ya zo nan a zancensa sai jarumi Nazmir ya yarda takobin sa wadda ta rine da jini idanunsa suka ciko da ƙwallah ya kasa yin komai. A daidai wannan lokacin ne a kaga ƙofar garin ta sake buɗewa sai ga gimbiya Luzaiya bisa kan doki tare da dubban ɗaruruwan mayaƙa sun fito. Cikin sauri sarki Fahalul Bahafus ya miƙe tsaye ya yi musu nuni da cewar kada kowa ya zo. Gaba ɗaya dakarun suka yi cirko-cirko amma ita gimbiya Luzaiya bata tsaya ba sai ta sukwano dokinta ta zo gaban mahaifinta tace,

"Ya kai Abbana don me za ka dakatar da mayaƙan ka ka bari kawai a yiwa waɗannan tsirarun rubdugu."

Cikin yanayin damuwa sarki ya dubi

Luzaiya ya ce, "Ba zan iya bari ba a hallaka su domin muddin nayi hakan to tabbas na ci amana."

Cikin tsananin mamaki Luzaiya ta dubi sarki tace, "Me kake nufi da cin amana? Shin ka manta ne cewar waɗannan mutane maƙiyanka ne, sun zo ne fa su sare kanka kuma su tafi da ni."

"Ban manta ba, ina sane da komai, yake 'yata ina roƙonki domin ƙaunar da ke tsananina da ke da ki amince kibi wannan jarumi da ke tsaye a gabana ya kai ki wajen sarkin su don ya aureki. Kuma ina son kiyi haƙurin rashina domin yanzu tamkar ina bankwana da ke ne. Lallai ina son a sare kaina yanzu-yanzu."

Sarki Fahalul Bahafus ya sake duban jarumi Nazmir yace, "Kai nake jira ka sare kaina, idan baka yi hakan ba ka cuceni ka sa na ci amanar mahaifinka."

Jarumi Nazmir ya juya masa baya yace, "Ba zan iya aikata wannan ɗanyen hukunci ba da hannuna. Haƙiƙa mahaifina ya taɓa bani labarinka da duk abin da ya faru a tsakaninku."

Koda Bardil ya ga cewar jarumi Nazmir bashi da niyyar sare kan sarki Fahalul Bahafus sai shi ya shammaci kowa da ke wajen ya fille masa kan. Koda ganin hakan sai gimbiya Luzaiya ta faɗi ƙasa sumammiya. Cikin hanzari Bardil ya sureta kuma ya đauki kan sarki Fahalul Bahafus ya ɗora akan doki shima ya hau dokin yana mai baiwa abokan tafiyarsa umarnin su yi sauri su gudu cikin tsawa.

Ai kuwa nan da nan kowa ya haye dokinsa ya sukwane shi. Kafin dakarun nan masu yawan tsiya na sarki Fahalul Bahafus su iso filin yaƙin da niyyar cim musu tuni sun yi nisa sun ɓace sai ƙurarsu kađai ake hangowa.

Su jarumi Nazmir ba su gushe suna gudu bisa dawakansu ba,sai bayan kwana guda da yini Ä‘aya. Koda suka tabbatar da cewa sun yiwa mutanen sarki Fahalul Bahafus tazarar da ba zasu iya riskarsu ba,sai aka tsaya a bakin wata korama don kowa ya huta,a wannan lokaci tuni gimbiya Luzaiya ta daÉ—e da farfaÉ—owa daga suman da ta yi.

Koda ta ga cewa tana hannun maƙiya ne sai ta fashe da kuka,tayì ta kuka har aka zo bakin wannan ƙorama. A sannan ne kowa ya sauko daga kan dokinsa. Bardil ya sauko da gimbiya Luzaiya sannan shima ya ɗebi ruwa ya zuba akansa kuma ya sha haka suma su jarumi Nazmir suka yi,bayan an sami nutsuwa sai jarumi Nazmir ya fara neman abokansa don ya tabbatar da lafiyar su. Nan take ya ga Bardil da Bagwan amma baiya Husuf da Iklam ba,nan fa hankalinsu ya dugunzuma suka fara tunanin ko sun rasune a filin yaƙi,nan take jarumi Nazmir yace dasu Bardil su tsaya anan shi zai ɗan duba baya kaɗan ko wani abu suka tsaya yi. Kawai sai ya hau dokinsa ya dawo da baya, ai kuwa bai daɗe ba yana tafiya ya hango Husuf a can gabansa kaɗan a kwance yana kakarin mutuwa,ga dokinsa a tsaye kusa dashi. Cikin sauri jarumı Nazmir ya ruga inda yake ya sauko daga kan doki ya ɗaukeshi da nufin ɗora shi akan doki,a lokacin jini na zuba ta cikin kafar bakinsa da hancinsa. Koda Husuf yaga Nazmir sai ya yi murmushin ƙarfin hali yace, "ya kai abokina karka wahalar da kanka a kaina domin tabbas mutuwa zanyi yanzu,ka sani cewa abokinmu lkam ya mutu tun a filin yaƙi naga gawarsa da idanuna,ina mai fatan zaka riƙe ƙanwata Lamiz amana kuma ina son....." Koda Husuf ya zo nan a zancensa sai jikinsa ya sandare, idanuwansa suka ƙafe suka daina motsi. Nan take jarumi Nazmir ya kwarara uban ihu wanda ya cika dajin gaba ɗaya yayi ta amsa kuwwa har su Bardil suka jiyo ihun daga inda suke. Koda jin ihun sai Bagwan da dakaru biyar suka biyo sawu suka bar Bardil tare da gimbiya Luzaiya da sauran baraden nan a wajen.

Koda zuwan su Bagwan inda jarumi Nazmir yake sai suka iskeshi zaune a gaban gawar Husuf yana ta rusa kuka. Shima Bagwan sai ya fashe da kukan,anan dai akayi ta rarrashinsu da ƙyar suka bari aka haƙawa Husuf kabari aka binne shi. Bayan an binne shine, jarumi Nazmir ya fiddo mayafinnan na Lamiz ƙanwar Husuf daga cikin kayansa,koda ya dubi mayafin ya tuno da sa'adda Lamiz ta danƙa masa kuma ya tuno da irin kalaman da tayi musu a wannan rana sai ya sake fashewa da kuka, cikin ƙarfin hali jarumi Nazmir ya ɗaura mayafin akansa sannan ya kama dokinsa ya hau,Bagwan ma da sauran barade suka hau nasu dawakan suka nufi inda suka baro su gimbiya Luzaiya.

Tun daga nesa Bardil ya hango mayafin Lamiz akan jarumi Nazmir kawai sai ya fashe da kuka don ya tabbatar da cewa abokinsa Husuf ya mutu.

Yayin da su Nazmir suka iso sai Bardil ya dubi Bagwan ya ce "Ina kuma labarin Iklam." Cikin alamun karayar zuciya Bagwan yace, "Kafin Husuf ya rasu ya gayawa Nazmir cewar yaga gawar Iklam a filin yaƙi." Koda jin haka sai Bagwan ya kurma ihu irin wanda jarumi Nazmir yayi ɗazu sannan ya rugo gaban Nazmir da Bardil ya rungumesu,yana mai cewa shike nan saura mu uku kacal. Dukkaninsu suka cigaba da kuka,duk wanda ya dubesu a wannan lokaci dole ne tausayisu ya kamashi.

Kowa da abin da ya dameshi, kamar yadda su jarumi Nazmir ke kuka da baƙin cikin rasuwar abokansu haka gimbiya Luzaiya ta kasance cikin tsananin baƙin ciki rasuwar mahaifinta.

A duk sa'adda ta É—aga kai ta dubi Bardil sai taji ta tsaneshi bama shi ba har su jarumi Nazmir É—in duk ta tsanesu inda tana da iko da tuni ta hallakasu gaba É—aya sannan ta kashe kanta ta huta da takaicin duniya.

Haka dai suka ci gaba da tafiya,su kwana nan su tashi can. Gimbiya Luzaiya da su jarumi Nazmir basu daina kukan baƙin ciki ba har sai bayan kwana bakwai,domin duk sa'adda suka tuno da masoyan nasu sai dai kawai ai sun fashe da kuka.

Tsawon wannan kwanakin gimbiya Luzaiya bata yi magana da kowa ba kuma bata ci komai ba face ruwa sai kuma ƙwayar dabino guda uku kullum. Nan da nan ta fita haiyacinta ta rame sosai.

A yammacin kwana na bakwaine sa'adda suka ya da zango a ƙarƙashin wani dogon tsauni.

Luzaiya ta zauna ita kaɗai a gefe guda tana rawar đari, ashe zazzaɓine ya rufeta. Koda ganin halin da ta shiga sai tausayinta ya kama jarumi Nazmir,da yake sun gasa naman wata barewa a jiya da daddare kuma akwai sauran naman acikin jakarsu sai ya fiddo dashi yaje ga Luzaiya ya miƙa mata yana mai cewa yake wannan 'yar sarki ya kamata ki rungumi ƙaddara haka ki fara cin abinci mana."

Kamar za taci kawai sai tayi wurgi dashi izuwa cikin wata ƙorama wadda ruwanta ke gudu bisa duwatsu cikin ɗacin rai da kakkausar murya ta dakawa jarumi Nazmir tsawa tace, "Ina ruwanka da lafiyata ka ƙyaleni na mutu mana,daku da mutanenka duk na tsane ku kamar yadda na tsani rayuwata a yanzu. Tsakanina daku sai gaba har abadan abidina kune kuka dakusar min da farin cikin rayuwa kun kashe mahaifina kun rabani da ƙasata da kuma mulkina kun rabani mahaifiyata da duk dangina,mene ne ya rage agareni." Ko da ta zo nan a zancenta sai ta fashe da kuka har tsawon 'yan daƙiƙu sannan ta cigaba da cewa, "Yanzu ku shi kenan buƙatarku ta biya kun rabani da kowa nawa ku kuma za ku koma ga iyayenku da 'yan uwanku ku ci gaba da rayuwar duniya cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Kun cuceni kun gama dani. Na roƙeku da ku kasheni yanzu ku jefa gawata cikin kwazazzabon nan."

Haka dai ta ci gaba da surutai tana kuka amma ko ci kanki babu wanda ya faÉ—a mata.

Haƙiƙa maganganun Gimbiya Luzaiya sun ratsa jarumi Nazmir kuma ya ƙara kamuwa da tausayinta amma sai ya dake ya ƙi nuna tausayin a fili ya yi ta maza. Tun sa'adda ta fara surutan ya koma can gefe guda ya zauna yana kallonta har ta gaji ta yi shiru.

A lokacin ne tunanin iyaye ya faɗowa jarumi Nazmir kuma ya tuno da abokanansu guda huɗu waɗanda suka mutu duk a sanadiyyar wannan mugun yaƙi wanda sarki Bashakur ya turosu. Kawai sai hawaye ya zubo masa. Sa'adda Bagwan da Bardil suka ga hawaye na zuba a idanun jarumi Nazmir sai suka taho gareshi suka zauna tare da shi. Bardil ya dubeshi yace, "Ya kai abokina yanzu saboda tausayin Gimbiya ne ka ke zubar da hawaye?"

Nazmir yayi murmushi yace, "Ba don haka ba ne. Na tuno da irin halin da muka baro iyayenmu ne kuma na tuno da abokanmu waÉ—anda suka rasu na tahbatar da cewa har abada ba zamu sake samun masoya kamar su ba. Kuma ba zamu samu masu Ä‘ebe mana kewa irin su ba."

Bagwan ya numtasa yace, "Lallai kam ba zaku iya samun abokan shaƙuwa ba kamarsu amma babu mamaki nan gaba ku haɗu da masoya waɗanda zasu ɗebe muku kewa su cire muku baƙin cikin rashinsu kuma ku ƙarasa sauran rayuwar ku ta duniya tare dasu." Koda jin wannan batu sai Jarumi Nazmir yace, "Nifa bangane manufarku ba." Bagwan yace, "Ina nufin zaku iya haɗuwa da 'yan matan da zaku aura kuma kuyi gagarumar soyayya dasu iyakar ƙarshen rayuwarku." Koda faɗin haka sai Nazmir da Bardil suka bushe da dariya sannan Nazmir yace, "Ni tunda nake ban taɓa jin ina son wata ya mace ba a zuciyata kuma bana zaton zan iya soyayya nan gaba a rayuwata." Bagwan yayi murmushi yace, "Haba abokina ai bakasan meye so ba shi yasa ka faɗi haka kaga ni nayi soyayya kuma ina kan yinta harma naci ribarta tunda nayi aure. Tabbas yanzu ina sa ran cewa idan mu koma gida zan iske ɗana ko 'yata tunda na baro matata Muslaiya da tsohon ciki,tabbas yanzu ko mutuwa nayi,za ana tunawa dani ina so kusani cewa babu abinda yafi soyayya daɗi a duniyar nan domin idan kana da masoyi duk irin baƙin cikın daka shiga kana ganinsa sai zuciyarka tayı sanyi ka manta da komai yanzu idan muka isa gida kuka sadu da iyayenku wane irin daɗi zakuji a ranku? To ina tabbatar muku da cewa wannan daɗin da zakuji bai kai kaso ɗaya ba daga cikin đari na irin daɗin da mai masoyiya yake ji yayin da ya sadu da ita bayan doguwar rabuwa. Ni kam yanzu ji nake kamar na zama tsuntsu nakai kaina gida dan na sadu da matata Muslaiya." Sa'adda bagwan yazo nan a zancensa sai duk jikin su jarumi Nazmir yayi sanyi suka kasa cewa komai domin maganganun na sa sun ratsasu kuma sun gamsu cewar gaskiya ne.

Haka dai tafiya taci gaba da wakana suka cigaba da ratsa dazuzzuka gari da ƙasa ƙasa har tsawon wata uku,wata rana hanya tabi dasu ta saman wani dogon tsauni wanda ƙarƙashinsa na da nisan gaske kuma ruwane ke kwarara a kan tsaunin yana zuwa ƙasansa inda wasu manyan duwatsu suke da magudanar ruwa. Bìsa dole suka sauka daga kan dawakansu suka fara tafiya a hankali sai da suka zo kan tsakiyar tsaunin kawai sai gimbiya Luzaiya ta faki numfashin su ta daka tsalle ta faɗa ƙarƙashin tsaunin nan ba tare da yin wata shawara ba jarumi Nazmir ya kwaɓe rigarsa da sauri shi ma ya daka uban tsalle yabi bayanta. Al'amarin da ya firgita su Bagwan kenan, suka leƙo ƙasan tsaunin cikin ɗimauta da baƙin ciki don sun tabbatar da cewa Nazmir da gimbiya sun halaka kenan.

Kafin Luzaiya da jarumi Nazmir su faɗo ƙasan tsaunin nan sai da suka yi tafiyar daƙiƙa dubu biyu a sama, tuni a lokacin ƙarfin iska ya sa Luzaiya ta suma,shi kuwa Nazmir bai suma ba sai da ya isa ƙarshen ramin, kafaɗarsa ta fado kan wani dutse.

Cikin sa'a Luzaiya ta faɗo akan ruwa. Gaba ɗayansu su biyun ruwa ya jasu ya tafi da su izuwa gaɓar kogi ya watsar da su.

Bayan kamar rabin sa'a sai gimbiya Luzaiya ta farfaɗo. Tana buɗe idanunta ta miƙe zumbur a firgice. Ta hau kalle-kallen daji tana mamakin yadda aką, yi ta rayu. Ba zato sai ta ga jarumi Nazmir

kwance a kusa da ƙafarta. Ta dube shi cikin mamaki tace a ranta, ya akai wannan ya zo nan alhalin ni kaɗai na faɗo ƙarƙashin tsaunin nan. Na tabbata ba zai jeho kansa ba tunda yana son rayuwarsa. Koda taga wata ƙaramar wuƙa a jikin Nazmir sai ta cirota ta tsaya tana kallonta tana mai yin shawara da zuciyarta tana mai cewa, "Tun da dai na jeho kaina cikin rami ban mutu ba, ai sai na kashe kaina da wuƙar nan dan na huta da takaicin duniya."

Tana gama faɗin haka sai ta zare wuƙar daga cikin kufenta ta daga sama ta saita cikinta zata burma. Caraf ta ji an riƙe hannunta. Cikin sauri ta waiga suka yi arba da juna. Ba wani ba ne ya riƙe hannunta face jarumi Nazmir. Cikin tsananin fushi tace, "Don me ka damu da rayuwata ka ƙyaleni na mutu mana."

Nazmir yace, "rayuwarki ita ce rayuwata da ta abokaina da suka rage. Idan ban kai ki ba ga sarkinmu a raye ba muma kashe mu za'a yi."

Yana gama faÉ—in hakan ya sunkuceta sama ya Ä‘ora a kafaÉ—arsa ya shiga laluben hanyar Ä‘a zai bi ya koma inda abokan tafiyarsa suke."


*************************************


Koda sarki Dujalu yazo nan a zancensa kawai sai aka ga wata ƙatuwar damisa ta shigo cikin fadar a guje kuma a haukace, kawai sai ta daka tsalle da nufin ta dirga kan sarki Dujalu. Cikin tsananin zafin nama tsoho Rafkanagu ya shaƙo wuyanta da hannu đaya ya fyaɗata da ƙasa. Ko shurawa ba ta yi ba,ta zama gawa.

Al'amarin da yayi matuƙar jefa sarkí cíkin tsananin mamaki kenan,domin ba su taɓa ganin tsoho mai ƙarfi irin na wannan ba. Sarki Dujalu ya tambayi kansa cikin zuciya, ''An ya kuwa wannan tsohon mutum mutum ne?"

Wani bafade ya je kan damisar ya duddubata sannan ya dubi sarki Dujalu yace, ''Ranka ya daɗe ai wannan damisar kace wacce ake kiwo anan gidan. Lallai duk yadda aka yi jiya mai bata abinci ya mance bai kulle ƙofar kejinta ba."

Koda jin haka sai sarki Dujalu ya fusata yace, maza aje a kamo mai bata abincin,a tsire shi tunda har ya yi sakaci haka ya janyo tashin hankalin sarki,kuma ya zamo sanadin katse wannan labarí mai daɗi na hikayar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya. Bazan cigaba da baku labarin ba sai bayan an ƙaddamar da mai kula da damisar nan.

Wannan shi ne abin da ya faru a fadar sarki Dujalu na birnin Misra sa'adda su Ruziyal ke aikin rubuta sabon KUNDIN TSATSUBA na biyu.

*****************************************

Al'amarin su Jafar kuwa bayan Mazalish ta gama kalle-kallenta suka faɗo duniyar su Jafar sai hankalinta ya koma kan KUNDIN TSATSUBA, wanda ke buɗe a gabansu ta ƙare masa kallo tsaf a cikin nutsuwa. Sannan ta dubi Jafar,Yelisa,Mashrila da Gulzum tace, "Yanzu a cikinku nan babu wanda zaí iya tsayar da littafin nan daga ci gaba da buɗe kansa don na tafi neman masoyina jarumi Hubairu."

Koda jin wannan batsu sai Yelisa ta yi tsaki tace, "Wannan kuma wace irin maganar banza kike yì, inda muna da wannan ikon ai da tuni muma mun yì ko dan mu huta da tsananin azabar da muke sha a cikinsa."

Jafar ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Haba yayata ai kawai ki rungumi ƙaddara kawai domin kin sayi wahala da kuɗinki tun da kika yi gangacin biyo mu. Da dai kin yì zamanki a can duniyarku ta mayu da ya fiye miki kwanciyar hankali."

Gama faɗin haka ke da wuya sai shafin KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na goma sha uku inda suka yi arba da hoton wani surƙuƙin daji a samansa an yi rubutu kamar haka:

"WANNAN JEJI, JEJI NE NA ABUBUWAN MASIFA IRI-IRI. AN ƘIRƘIRESHI NE KIMANIN SHEKARU DUBU BAYA."

MAI KARATU SHIGO CIKINSA KA SHA KALLO."


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1   Part 11

Domin sauke Audio sai ku danna hoton dake kasa 👇👇👇





Post a Comment

0 Comments

Ads