Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 9

 

Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba 

Book 1 

Part 9

Marubuci: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh 

Huzaik yace, "Ƙwarai haka ne amma kuma fa ni ya burgeni domin abin da ya yi shi ne daidai."

Koda jin haka sai Sharhil ya ce, "Haba Huzaik saboda me za ka faɗi haka? Shin idan kai sarki ne za ka so ka ga an zubar da dumbin jinin talakawan ka, kuma a rushe ƙasarka a yi maka kisan gilla?"

Huzaik ya ce, "Ba zan so haka ba, amma ina so ka ƙaddara cewa kai ne wannan sarkin da zamu yaƙa. Kana da ƙarfin mulki da mayaƙa rana ɗaya a zo a ce za'a rabaka da rayuwarka da kuma 'yarka guda ɗaya tilo da kake matuƙar so, shin ba za kayi yunƙurin komai ba na kare kanka?"

Sharhil ya yi shiru ya kasa bada amsa. Ba zato ba tsammani sai suka ga idanun Nazmir sun ciko da ƙwallah. Koda ganin haka sai Bardil ya taso daga inda yake zaune ya dafa kafaɗar Nazmir yace, ''Haba abokina me ya sa kake da tausayi ne mai yawa,gaka ka kasance cikakken jarumi mai ragargazar maza. Ka saba da tsinke wuya, kuma ka saba da raba gangar jiki. Ka tuna fa kai ne mai cisge sassan jikin bil'adama da ƙarfin damtse yayin da ka yi mummunar fusata."

Nazmir ya share ƙwallar idonsa,sannan yace, ''Abokina ka sani cewa fishina yafi tabbata akan azzalumai. Wannan sarkin da aka turomu mu ruguza farin cikinsa muraba shi da rayuwarsa da kuma 'yarsa ai ba azzalumi ba ne. Ni kam ina jin kunyar zaluntar wanda bai zalunce ni ba."

Bardil yayi ajiyar numfashi, sannan yace, "Nasan da haka amma ka sani cewa babu yadda zamu yi dole mu cika umarnin sarkinmu tun da in muka ƙi tamkar mun salwantar da tamu rayuwar ne,domin hukuncin kisa ne zai tabbata akan mu. Ya kai abokina ka tuna da ivayenmnu da 'yan uwanmu waɗanda muka baro su a cikin tsananin ƙunci da baƙin cikin rabuwa. Tabbas har yanzu suna nan a cikin begenmu dare da rana, ba za su daina ba har sai mun koma sunga lafiyarmu. Ai kuwa ko dan saboda su dole ne mu tsare rayukanmu mu cika umarnin sarkinmu.'

Da wannan jawabi ne jikinsu gaba ɗaya yayi sanyi,kowa ya tuna da danginsa na gida kuma ya yarda ya rabu da su kawai sui suka kama zubar da hawaye.

Cikin ƙarfin hali jarumi Nazmir ya dubi abokansa, sannan ya dubi dakarun nan guda dubu goma yace, "Kowa ya zauna cikin shiri gobe zamu farwa mutanen garin nan ko sun tare mu ko ba su tare mu ba."

Kashe gari tun kafin su jarumi Nazmir su aiwatar da nufinsu suka ga an buɗe ƙofar birnin Mahazus sai ga rundunar mayaka ta fara fitowa suna jeruwa sahu-sahu. Koda suka gama jeruwa su Nazmir suka ga yawansu sai zuciyoyinsu suka karaya. Huzaik ya matso kusa da jarumi Nazmir yace, ''Kai anya kuwa ma yi wannan yaƙi? Dubi yawan dakarun nan fa, na rantse da darajar mahaifina sun linkamu sau goma."

Nazmir ya dubi Huzaik ya daka masa tsawa yace, "Ka zamo namiji mại ƙwarin zuciya,faɗuwar gaba asarar namiji ce,in dai muka daure zamu iya gamawa da su,a cikin sa'a biyar."

Kafin wani ya ƙara cewa wani abu jarumi Nazmir ya yi kukan kura ya sakarwa dokin sa linzami. Dokin kuwa sai ya nufi tawagar sarki Fahalul Bahafus a sukwane cikin mugun gudu.

Koda ganin haka sai Huzaik, Sharhil, Bagwan,Husuf, Ikhalam,da Bardil suma suka sakarwa nasu dakawan linzami suka bi bayansa suna masu ƙoƙarin su riske shi kafin ya ƙarasa cikin abokan gaba don kada su yi masa sarkin yawa su halaka shi,tuni jarumi Nazmir ya basu rata mai yawa.

Kafin kace me tuni ya kutsa cikin baradan sarki Fahaul Bahafus ya hausu da sara ba sassauci,su kuwa suka yanyame shi kamar ansa kyanwa ɗaya a tsakiyar karnuka dubu. Sai dai wannan kyanwar ta zamewa karnukan alaƙaƙai, domin kuwa sun gaza cim mata. Duk inda jarumi Nazmir ya kai sara sai dai kaga kawuna na zubewa kuma duk inda ya durfafa dole a dare hanya ta samu a gare shi.

Kafin su Huzaik su ƙaraso tuni jarumi Nazmir ya yiwa wannan runduna mummunar ɓarna.

Ai kuwa sa'adda su Huzaik suka ƙaraso sai wuri ya ƙara hautsinewa, mummunan yaƙi ya rincaɓe ban da ƙarajin mazaje da na ƙarafa babu abin da mutum ke ji. Jini kuwa ya rinƙa fantsama kai ka ce feso shi ake yi daga sama.

Kafin dakarun nan guda dubu goma masu taimakawa su Nazmir su iso tuni an gama da dakarun sarki Fahalul Bahafus guda dubu ɗari gaba ɗaya sun zama gawa. Ana gamawa da su ne aka ga Huzaik ya dafe ƙirjinsa yana sunkuyawa ƙasa cikin yanayin jiri. Kafin wani ya ƙarasa gare shi tuni ya faɗa ƙasa. Koda ganin haka sai jarumi Nazmir ya ƙwala ihu mai firgitarwa ya ruga inda yake ya tashe shi zaune ya ɗora shi akan cinyarsa, sai ga jini na ɓulɓula daga cikin ƙirjin Huzaik.

Cikin ɗimaucewa Nazmir ya yaga rigar jikinsa ya toshe ƙirjin Huzaik yana mai cewa,

"Abokina tashi muje cikin tantina in sa maka magani, lallai za ka sami lafiya."

A wannan lokaci ne su Sharhil suka ƙaraso gabansu cikin tsananin tashin hankali da matuƙar damuwa. Cikin ƙarfin hali Huzaik ya riƙe hannun Nazmir idanunsa na lumshewa, hannunsa na karkarwa ya ce, "Ya kai abokina ka gafarce ni ba zan iya tashi ba, kuma kada ka ɓata lokacinka akan yi mini magani. Tabbas tawa ta ƙare mutuwa zan yi,kuyi haƙurin rashina,idan ka samu ikon komawa gida ka sanar da mahaifina cewar ga yadda tawa ta kasance ya rungumi ƙaddarar rashin cikar alkawarina na zuwa masa da sirikarsa. Lallai kayi mini wannan aiki amanace na baka."

Koda jin haka sai Nazmir ya fashe da kuka yana mai cewa, "Huzaik na karɓi amanar ka kuma tabbas zan danƙata ga mahaifinka."

Rufe bakinsa ke da wuya idanun Huzaik suka ƙafe, ko'ina a jikinsa ya daina motsi kawai sai suma su Sharhil suka durƙusa gaban gawar suka fashe da kuka. Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su jarumi Nazmir da dakarun sarki Fahalul Bahafus guda dubu đari bayan an fafata baƙin gumurzurn yaƙi a cikin 'yan daƙiƙu bayan birnin Mahazus.

Sarki Fahalul Bahafus yana tare da matarsa Munaiya wato mahaifiyar Luzaiya suna hira cikin nishaɗi a turakarsa sai ga gimbiya Luzaiya ta faɗo cikin yanayin tashin hankali. Koda ganinta sai sarki miƙe zumbur ya tare ta yana mai cewa, "Yake rabin jikina me ya faru kika zo garemu a cikin siffa mara daɗin gani haka?"

Luzaiya ta yi ajiyar numfashi tace, "Ya kai Abbana ga ɗaya daga cikin masu tsaron ƙofar gari yazo da mummunan labari cewar dakarunka daka tura guda dubu ɗari don su yaƙi maƙiyanmu mutum bakwai kacal sun gama da su.''

Cikin firgici sarki Fahalul Bahafus ya saki Luzaiya ya ja da baya kaɗan yace, "Wace irin maganar banza kike faɗa mini haka? Ya za'a yi a ce mutum bakwai sun kashe mutum dubu ɗari a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci da bai kai rabin sa'a ba. Ai kuwa koda mutum bakwan aljanu ne su aikin yafi ƙarfinsu."

"Ya kai Abbana wannan labari ba ƙarya bane ka je ka gani da idanunka domin ni na gani,ganau ce ni ba jiyau ba."

Cikin sauri da ruɗewa sarki Bahalul Bahafus ya ɗauki rawaninsa ya tuma aka sannan ya fita waje da sauri-sauri, gudu-gudu. Yana zuwa ƙofar fada yaga gaba ɗaya 'yan majalisarsa a tsaitsaye sun yi tsuru-tsuru suna tattauna wannan al'amari. Ko tsayawa gabansu bai yi ba ya sa aka kawo masa doki ya hau ya nufi ƙofar fita daga gari. Cikin hanzari suma 'yan majalisar suka yi hawa suka bi shi.

Da zuwa suka iske gawarwakin dakarun nan guda dubu đari,gaba ɗaya filin wajen ya malale da su da kuma jini abin ba kyan gani. A lokacin su Nazmir sun koma tantin su. Nan take zuciyar sarki Fahalul Bahafus ta hau tafarfasa. Kawai sai ya dubi wazirinsa ya ce, "Mene ne abin yi?"

Waziri yace, ''Ranka ya daɗe babu abin yi face gobe mu sake turo wasu ɗari uku."

"A yi hakan." Abin da Fahalul Bahafus ya faɗi kenan, ya kaɗa linzamin dokinsa ya juya da baya ya nufi cikin gari a sukwane suma 'yan majalisar suka bi bayansa.

A wannan rana dai su jarumi Nazmir sun sha kuka mai yawa. Ga shi dai sun sami nasarar yaƙin amma saboda sun rasa abokinsu kuma amini wanda suka taso tare tun ƙuruciya sai suka zamo cikın mugun baƙin ciki,mara misaltuwa.. Har aka haƙa kabari aka binne Huzaik su shidan nan ba su daina kuka ba.

Bayan an binne Huzaik ne jarumi Nazmir ya đauki takobin Huzaik din ya sumbace ta sannan saka ta a cikin kayan sa. Daga nan ya koma gefe ɗaya ya zauna shi kaɗai yana tunano irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninsa da Huzaik tun suna ƙanana kawai sai ya sake fashewwa da kuka.

Sharhil,Bagwan,Husuf,Ikhlam da Bardil suka taso daga inda suke zaune suka zo suka rungume Nazmir suna masu taya shi kuka. Nazmir ya buɗi baki cikin murya mai rawa yace, "Mu bakwai ne yau ga shi mun zama mu shida. Haba mutuwa ya za ki rabamu da masoyinmu,me zai hana ki ɗaukemu gaba ɗaya a lokaci guda,don mụ huta da baƙin cikin rabuwa?"

Sa'adda Bardil ya ji jarumi Nazmir na irin waɗannan zantuka sai ya shiga rarrashinsa yana bashi baki gami da ƙara masa ƙwarin gwiwa don tsoron kada begen Huzaik ya jefa shi cikin zautuwa.

Haka dai suka ci gaba da kuka da baƙin ciki har dare ya tsala sosai,ɗaya daga cikin su bai rintsa ba,kai yadda suka ga rana haka suka ga dare.

Kashe gari tun kafin alfijir ya keto suka fara jin hayiniyar dawakai a can ƙofar gari cikin hanzari su Nazmir suka miƙe suka hau dawakansu cikin shirin yaƙi, suka nufi ƙofar garin. Da zuwa kuwa suka iske gaba ɗaya an kwashe gawarwakin dakarun jiya. Tsaitsaye akan dawakai dakaru dubu đari uku ne cikin mugun shirin yaƙi. Shi kansa jarumi Nazmir sai da zuciyarsa ta buga ys đubi abokansa guda shida,sannan ya dubi dakarun nan mataimaka su dubu goma ya ce, "Yau fa abin na yi ne, maza mu afka musu muga abin da zai yi hali daga nan zuwa faduwar rana."

Ai kuwa nan take kowa ya saki linzanmin dokinsa,ƙura ta tashi, dawakai suka yi ƙaimi kai kace gasar tsere ake yi, suka nufi ƙofar birnin. Koda mayaƙan sarki Fahalul Bahafus suka ga waɗannan tsirarun dakaru sun taso musu sai suma suka ruga gare su don su tare su kafin su iso, ai kuwa sai aka gamu a tsakiya. Gamuwar kowa ta zamo matsiyaciya,domin tafi gaban karon batta, turnuƙu ko ruguntsumi sai dai a kirata annoba. Domin buɗe kasuwar asarar rayuka aka yi. Tabbas a wannan rana Nazmir da abokansa sun nuna tsantsar jarumta,juriya da sanin makama. Wataƙila saboda fushin rasa abokin su ne ya sa suka zage damtse įyakar ƙarfinsu,idan kaga yadda suka rinka ragargazar dakarun sarki Fahalul Bahafus sai kayi zaton ba mutane suke rugargaza ba kwayayen kaji ne,saidai ka rinƙa jin ƙarar fashewar kan bil'adama,tus-tus, raƙaƙaƙa!

Sai da aka kwana aka yini ana wannan yaƙin sannan aka gama da waɗannan mayaƙa na sarki Fahalul Bahafus. Ana gamawa da su ne jarumi Nazmir ya shiga dube-dube don ya tabbatar da lafiyar abokansa. Cikin sa'a sai duk ya gansu a tsaitsaye amma duk sun samu raunika sai dai ba wanda zai zamo abin fargaba ba ne. Kowa ka duba sai ka ga gaba ɗaya jikinsa ya rine da jini. Dakarun nan kuwa guda dubu goma masu taimakawa su Nazmir sun dawo saura su đari uku kacal,wato an kashe dubu tara da ɗari bakwai.

Jarumi Nazmir ya tara abokan sa waje ɗaya ya fara dudduba raunikan jikinsu gami da sa musu magani. Koda ya zo kan Sharhil sai ya ga gumi na tsatstsafowa a goshinsa kuma yana ciza leɓensa alamun yana cikin jin raɗaɗin ciwo. Nan take hankalin Nazmir ya dugunzuma ya ci gaba da duba ko'ina a jikin Sharhil, kawai sai yaga sukan mashi a ƙasan cibiyarsa jini na zuba ta wajen,Nazmir ya rusa îhu ya yi sauri ya sa magani a wajen.

Sharhil ya kamo wuyan Nazmir ya ce,

"Yakai abokina kar ka damu zan rayu ba zan mutu ba."

Kawai sai suka ga ya miƙe ƙyam,ya tsaya bisa dugaduginsa. Cikin farin ciki suka kama shi aka tafi dashi izuwa tanti sannan aka zaunar da shi. Sai da aka sami rabin sa'a ana ta hira da Sharhil tamkar babu wani rauni a jikinsa domin har ana wasa da dariya.

Daga can sai Sharhil ya ce, yana jin ƙishirwa. Koda faɗin haka sai Bagwan ya miƙe ya fito don kawo ruwan,aka ci gaba da hira amma wannan karon sai Sharhil ya daina sa bakinsa a cikin hirar ya yi shiru.

Ashe ciwon jikinsa ke nuƙurƙusarsa don kada su Nazmir su ka gane halin da yake ciki ne ya yi shiru. Jim kaɗan sai ga Bagwan ya dawo ɗauke da ruwa a cikin ƙoƙo. Koda ya miƙawa Sharhil ruwan sai suka ga bai miƙo hannunsa ya karɓa ba. Kawai kuma sai suka ga idanunsa a kafe suke basa motsi.

Cikin tsananin firgici Nazmir ya girgiza shi amma ko motsi bai yi ba. Gangar jikin ta laguɓe ta fadi ƙasa.

A lokaci guda su rusa uban ihu su duka suka fashe da tsananin kuka wanda ya sa ragowar dakarun nan guda ɗari uku suka rugo cikin tantin a guje riƙe da makamansu tsirara don zaton ko maƙiya ne suka kawo sumame. Da zuwa suka iske ashe jarumi Sharhil ne ya mutu.

Baƙin cikin da su Nazmir suka yi a wannan karo har ya fi wanda suka yi lokacin mutuwar jarumi Huzaik domin sai da gaba ɗayansu suka ɗebi makamai suka nufi hanyar ƙofar birnin Mahazuz da niyyar ɗaukar fansa. Da ƙyar dakaru masu taimako suka lallame su suka haƙura. Kuka kuwa tun suna zubar da hawaye sai da hawayen ya ƙare,idanuwansu suka kumbura suka yi suntum. Duk wanda ya gan su a wannan lokaci dole ne ya tausaya musu.

Bayan an ginawa Sharhil kabari a kusa da na Huzaik an binne shi sai jarumi Nazmir ya dubi su Bagwan yace, ''Yaku abokaina yanzu dai kun gani saura mu biyar maimakon mu bakwai. Shin haka zamu ci gaba da binne junan mu ɗaya bayan ɗaya,ya zama dole mu yiwa tufkar nan hanci mu kawo ƙarshen yaƙin nan."

Iklam ya yi ajiyar numfashi yace, "Hanya ɗaya ce zamu bi mu kawo ƙarshen wannan yaƙi,sai dai mu je mu ɓalle kofar garin da ƙarfin tsiya mu banka ciki mu yi kan mai uwa da wabi har sai mu kai ga gidan sarki mun sare kansa,sannan mu kamo 'yarsa mu tafi da birninmu."

Husuf ya ce, ''A'a wannan shawarar ba zata kai mu ga gaci ba. Ku sani cewa ba mu san sirrin garin nan ba, idan muka ce zamu shige shi kai tsaye zamu iya faɗawa cikin tarkon da zamu kasa fita,ni ina ganin a wannan yaƙin mun yi musu mummunar ɓarna babu mamaki su tsorata su su bamu abin da muka zo nema, mu tafi salin-alin,domin saboda rai biyu kacal ba za su yarda mu ƙarar da su ba."

Sa'adda Husuf ya zo nan a zancensa sai jarumi Nazmir ya dubi Bagwan da Bardil yace, ''Ku kuma me za ku iya cewa?"

Cikin haɗin baki suka ce, "Mun yarda da shawarar Husuf."

Kashe gari ihun mazajen ne ya sa su Nazmir miƙewa ba cikakkiyar nutsuwa. Cikin hanzari suka hau dawakansu suka nufi ƙofar birnin. Tun daga nesa suka rinƙa hango gungun dakarun yaki waɗanda adadinsu ya ninka na jiya. Ban da tsinin masu da kaifin takubba babu abin da suke gani. Sai kuma tulin kuttun kibau da baka-baka. Jarumi Nazmir ya ja linzamin dokinsa ya tsaya, suma abokan tafiyar ta sa sai duk suka tsaya a bayansa.

Nazmir ya waigo ya dubi abokansa guda biyar sannan ya dubi ragowar dakaru guda ɗari uku,yayi ajiyar zuciya,sannan yace, "Mu ɗari uku ne da biyar zamu tunkari mutum kusan dubu ɗari shida,bana sa ran wannan karon gaba ɗayanmu za mu tsira da rayuwarmu amma ku sani ba gudu ba ja da baya. Mu ƙarfafa zuƙatanmu,mu cire tsoro da fargabar wahala ko mutuwa. Lallai ko ba muyi nasara ba za mu yi gagarumar ɓarna. Idan mun yi nasara mun kafawa iyayenmu da danginmu tubalin sabuwar rayuwar duniya. Idan muka faɗi mun ruguza zuri'o'inmu kuma za'a manta da tarihinmu a doron ƙasa."

Koda gama faɗin haka sai Bagwan, Husuf,Iklam da Bardil suka ji wani sabon ƙarfi ya shige su irin wanda ba su taɓa jì ba. Zuciyoyinsu suka ƙeƙashe ya zamana babu sauran shakkar komai a tare da su. Kafin jarumi Nazmir ya yi wani motsi tuni sun sakarwa dawakansu linzami sun nufi ƙofar birnin Mahazus cikin gaggawa. Nazmir da dakaru đari ukun suka rufa masa baya.

Wohoho!, a wannan rana sai da su jarumi Nazmir suka zamo tamkar ifiritai a cikin tsakıyar bil'adama domin kamar masu sassabe a gona haka suka kasance. In banda girba da share kan kawunan bil'adama babu abin da suke yi cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta,idan aka harbo musu kibiyoyi komai yawan kibiyoyin sai dai ka ga suna karkaɗe su suna zubewa ƙasa. In kuwa suka kai suka saidai ka ga a lokaci guda sun ɓurma ƙirjin mutum uku.

A wannan yaƙi ne sarki Fahalul Bahafus tare da 'yan majalisar suka zo kan ganuwa suka tsaya suna ganin abin da ke wakana a filin yaƙin,sai da aka kwana uku ana fafatawa ya zamana an yi fata-fata da mutanen sarki Fahalul Bahafus. A lokacin ne fahalul Bahafus ya hango fuskar jarumi Nazmir sai sai ya tuno da fuskar mahaifinsa,wato sadauki Halufa. Nan take ya tuna lokacin da Halufa ya kuɓutar da shi daga kurkuku sai hankalinsa ya dugunzuma,gumi ya tsatstsafo masa.

Ba zato ba tsammani sai aka ga sarki Fahalul Bahafus ya sauko daga kan ganuwa a guje ya hau dokinsa ya nufi bakin ƙofar gari. Da zuwa sai ya dakawa masu tsaro tsawa ya ce su buɗe masa ƙofar.

Jikinsu na rawa suka buɗe masa ƙofar ya sukwani dokinsa ya nufi inda su jarumi Nazmir ke gumurzu.


Karanta>>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 9


Domin Sauke Audio sai ku danna Hoton dake kasa 👇👇👇
Post a Comment

0 Comments

Ads