Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 7

Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba

Book 1 


Part 7


Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini


Posting: Abubakar Saleh

Huzaik yayi murmushi yace, "abba ni kam ina ganin babu wata buƙata kawai ana so a yaudare ka ne a tura ka wani wurin inda zaka hallaka don a bayar da sarautar ga wani."

Halufa yayi murmushi yace, "a'a ina ganin ba haka bane koma dai mene ne nayi mku izini gobe da safe ku zo ku duka kuyi mini rakiya zuwa fadar domin ku gani kuma ku ji komai da kunnenku."

Da wannan furuci ne Nazmir da abokan sa suka yi sallama suka bar Halufa da Zuwaisa zaune su kaɗai a harabar gidan. Zuwaisa ta dubi Halufa tace, "ya kai miji na kayi sani cewa ni da kai duk tsufa ya riskemu ga shi ɗan mu guda ɗaya ne kacal a duniya, saboda me za ka ja shi izuwa fada alhalin tun da yake bai taɓa zuwa fadar ba. Shin baka tsoron ya zama bawan azzalumin wanann sarki namu?"

Yayin da Halufa ya ji wannan batu na Zuwaisa sai hankalinsa ya dugunzuma ya yi shiru bai ce da ita komai ba, har tsawon lokaci. Daga bisani sai ya miƙe tsaye ya juya mata baya yana mai cewa. "Yake matata ki yi sani cewa ko mun so ko mun ƙi dole ne mai rabawa ta raba mu da ɗan mu domin tsufa da mutuwa aminnan juna ne. Zuwan Nazmir fada ɗaukaka ce a gareshi amma kuma wata sila ce da za ta iya zama sanadiyar rabuwarmu da shi ta har abada."

Koda Halufa ya zo nan a zancensa sai ya juya suka haɗa idanu da Zuwaisa kawai sai ya ga hawaye na zuba a idanunta. Nan da nan shi ma zuciyarsa ta karaya, idanunsa suka ciko da ƙwallah. Zuwaisa ta miƙe tsaye suka rungume juna, suna kuka tana mai cewa, "Haƙiƙa mafarkina ya zama gaske, ranar da nake tsoron ganin zuwanta ne ya yi."

Kashe gari fadar sarki Bashakur ta cika maƙil da jama'ar gari,domin tuni labari ya bazu cewa yau ne sarkin yaƙi jarumi Halufa zai dawo kan kujerarsa ta fada. Sarki Bashakur na zaune fadawa sun kewaye shi, yana mai tunƙaho da ƙarfin mulkinsa sai ga sadauki Halufa ya shigo, jarumi Nazmir tare da abokansa guda shida na take masa baya.

Koda ganinsu sai sarki Bashakur ya ƙarewa Nazmir kallo sama da ƙasa, ya ga irin halittar da Allah ya yi masa ta kyau da surar jarumta, sai ya cika da ɗumbin mamaki domin bai taɓa ganinsa ba sai yau kawai dai yana jin labarin bajintarsa ne amma bai taɓa sha'awar ya sa shi a idonsa ba saboda kishi da girman kai irin na sarakai.

Koda zuwan su Halufa sai suka risina a gaban sarki suka kwashi gaisuwa. Sarki Bashakur ya karɓi gaisuwar yana mai farin ciki da nuna walwala yace, ''An gaisheka sarkin yaƙi kuma muna murna da ka amsa kiranmu da gaggawa muna fatan ka karɓi abin da muka dawo maka da shi bayan ka rasa shi tsawon shekaru ashirin baya."

Cikin nutsuwa sadauki Halufa ya yi gyaran murya ya ce, "Ya sarkin sarakai haƙiƙa na yi farin ciki da wannan saƙo, to amma ina da uzuri guda,ina son sarki ya dube ni da kyau don ya gane cewa jiya ba yau ba ce. Haƙiƙa yanzu tsufa ya riskeni, ba zan iya yin abin da na yi ba a shekarun baya. Ina neman alfarma da a baiwa ɗana Nazmir wannan sarauta a maimakona domin ya cancanta,kuma na tabbatar da cewa zai iya yin abin da yafi wanda na yi."

Koda jin wannan batu sai sarki Bashakur ya tuntsire da dariya, sannan ya ce, "Ai shi kenan faɗuwa ta zo daidai da zama, domin dama akwai wani gagarumin aiki da ya taso don biyan wata muhimmiyar buƙata tawa. Na yarda zan baiwa ɗanka sarautarka amma sai bayan ya je ya biya mini buƙata ya dawo cikin nasara. Yana dawowar zan sa a shirya bikin naɗa shi wannan matsayi na sarkin yaƙin ƙasata. Idan kuwa ya kasa samun nasara zan kashe shi tun da ban ga amfanin đan da ya kasa gadon mahaifinsa ba. "

Koda jin wannan batu sai jarumi Nazmir ya dube sarki Bashakur ido da ido ya ce, "Na amince da wannan tsari kuma ina mai rantsuwa da darajar mahaifina kowacce irin buƙata ce kake da ita zan biyata, domin na nuna cewa na cika ɗan halak, ɗan da ya sha jarumta a nonon mahaifiyarsa."

Koda jin haka sai fadar ta ruÉ—e da shewa ana yiwa jarumi Nazmir jinjina. Sarki Bashakur ya É—aga hannu aka yi tsit. Sannan ya ce, "Nima na amince da hakan, shin akwai wanda zai ce wani abun?"

Huzaik ya risina ya ce, "Ya sarkin sarakai ina son na roƙi wata alfarma da yawun abokan Nazmir."

Sarki Bashakur ya yi murmushi ya ce, "Faɗi buƙatar ku na ji."

"Muna son inda za ka tura Nazmir tafiya biyan buƙatarka a yi mana izini mu yi masa rakiya."

Koda jn haka sai sarki ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "An yi muku izinin. Yanzu na sallame ku amma ku dawo nan fada gobe war haka cikin shirin barin ƙasarman don aiwatar da buƙatata."

Da wannan furuci ne aka sallami kowa fada ta watse. Kowa ya kama gabansa. Tun da su Nazmir suka dawo gida ya kasance cikin tsananin damuwa har ma ya rufe su Huzaik da faɗa yana mai cewa, "don me zai jefa kan su a cikin wannan masifa. Ya sani cewa aikin da za'a tura shi ba ƙaramin bala'i bane,duk da cewar bai san mene ne ba, duk za su iya hallaka."

Koda jin wannan batu sai Huzaik, Sharhil,Bagwan,Husuf,Iklam da Bardil suka haÉ—a hannyensu waje guda suka buÉ—e baki a lokaci guda suka ce,

"Mun kasance abokan juna tun ƙuruciya mun shaƙu da junanmu kuma bama rabuwa komai ruwa komai iska. Ya kai Nazmir gamu mu shida da kai ne cikon na bakwai shin kana tare da mu ko kuwa za ka ware daga cikin mu ne?"

Yayin da Namzir ya ji wannan jawabi daga bakin abokan sa sai zuciyarsa ta karaya idanunsu akan na su ya ce, "Ina tare da ku har abada,zumuncinmu da soyayyarmu ga juna ta ratsa jini da tsoka." Take suka rungume juna gaba É—aya cikin kukan farin ciki.

A wannan rana su jarumi Nazmir suka gama kimtsa kayansu don yin tafiyar da ba su san inda zasu je ba.

Bayan sun tanadi dawakai da guzuri da kayan yaƙi, sai suka ɗunguma suka tafi gidan su Huzaik don yin sallama da mahaifinsa tsoho Marnush. Da shigarsu inda yake sai suka iske shi a zaune yana sharɓar kuka. Gaba ɗayansu sai hankalinsu ya tashi, suka durƙusa a gabansa, Huzaik ya kama hannayensa ya riƙe yana mai zubda hawaye ya ce, "Ya kai Abbana ina dalilin wannan kuka naka?"

Tsoho Marnush yace, "Ya kai É—ana ka yi sani cewa kai kaÉ—ai nake da shi a duniya, ga shi har tsufa ya riskeni ban ga auren ka ba. Yau dare É—aya labari ya zo mini cewa za ku yi tafiya mai haÉ—ari.

Idan rayuwarka ta salwanta shi kenan, ba ni da kowa a duniya, in da za ka haƙura da wannan tafiya da hankalina yafi kwanciya."

Huzaik ya kasa jurewa zuciyarsa bai san sa'adda ya fashe da kuka ba, yana mai cewa, "Ka yi haƙuri Abbana na rigaya na yiwa abokaina alƙawarin wannan tafiya. Babu abin da zai hanani yinta face mutuwa. Ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa lallai zamu dawo gida lafiya,kuma zan zo maka da kyakkyawar sirika."

Koda jin wannan batu sai tsoho Marnush ya rungume Huzaik a ƙirjinsa ya ƙara fashewa da kuka yana mai cewa, "Ina fatan abin da ka faɗa ya kasance."

Bayan Huzaik ya gama ganawa da mahaifinsa sai kuma suka É—unguma suka tafi, gidan su Sharhil. Da zuwa suka iske mahaifiyara Ushaiya wacce ta kasance makauniya mai kimanin shekaru sittin da shida. Suna shiga suka risketa ita ma tana kuka. Cikin hanzari Sharhil ya matsa daf da ita ba tare da sanin sun shigo ba.

Koda ya durƙusa a gabanta ya taɓa gwiwarta sai tace, "Wane ne?" Maimakon ya bata amsa sai shima ya fashe da kuka,cikin sauri ta shafa fuskarsa da tafin hannunta ta ce, "Au ɗana ne,yaushe ka shigo ban sani ba?"

Sharhil ya ɗago kai ya dubeta, idanunsa cike da hawaye ya ce, "Yake Ummina haƙiƙa na san kina kuka ne saboda samun labarin tafiyar da zan yi."

Ushaiya ta share hawayenta ta ce, "Ƙwarai kuwa ai dole ne na yi kuka, ka tuna cewa tun dana haifeka ban taɓa ganin kamanninka ba, kuma taɓa rabuwa da kai ba tsawon kwana guda ba. Kai kaɗai gare ni a garin nan ga shì na kasance makauniya, tun sa'adda ka zama mutum ka ɗauke wahalar cina da shana, kuma ka kula da lafiyata.

Yanzu idan baka nan waye zai samo mini abincin da zanci, ka sani cewa a yadda girma ya kamani ba zan iya yiwa kaina komai ba,kai ne gatana, in na rasaka na rasa komai, babu wanda zai iya taimako na in babu kai face abokanka to kuma ga shi na ji ance gaba É—aya za ku yi wannan tafiya."

Sa'adda Ushaiya tazo nan a zancen ta sai gaba ɗaya jikin su Nazmir ya yi sanyi, suka kamu da tausayinta. Sharhil ya ce, "Yake Ummina ina mai ƙarfafa miki ƙwarin gwiwa da ki kwantar da hankalinki ki, sani cewa ni da abokaina mun kasance jaruman gaske,don haka kowacce irin masifa da zamu shiga zamu dawo gida lafiya."

Ushaiya ta rungume Sharhil sannan ta fashe da kuka tana mai cewa, "Na san kuna da jarumta amma ai ba ku san in da za ku je ba, da kuma abinda za ku tunkara." Haka dai su Sharhil suka yi ta lallashin Ushaiya har suka shawo kanta ta daina kuka,daga nan kuma suka tafi gidan su Bagwan.

A cikin waɗannan abokai guda bakwai waɗanda suka taso tare kai ɗaya Bagwan ne kaɗai ya yi aure, koda yake ya yi aure da wuri sakamakon ya taso a matsayin maraya, domin tun bai fi shekara bakwai ba iyayensa suka yi haɗarin jirgin ruwa, suka rasu. Bagwan ya sha wahalar rayuwa domin tun yana ƙarami ya ke sana'ar dako, leburanci da sauransu don kawai ya riƙe kansa. Lokacin da ƙarfi ya zo masa sai ya yanke shawarar ya yi aure da wuri don ya sami zuri'a ya huce takaicin rashin dangi.

Cikin dacewa ya gamu da wata budurwa mai suna Muslaiya wacce lokaci guda suka kamu da matuƙar

ƙaunar juna.

Muslaiya baiwa ce ta wani attajiri, wanda tsufa ya riske shi ainun amma yana da tarin iyali.

Lokacin da attaiirin ya fahimci cewar Muslaiy na soyayya da Bagwan sai ya 'yanta ta ya yarje mata ta taje tayi aurenta kuma ya taimaketa lokacin aure.

Bagwan suka zauna cikin kwanciyar hankali har tsawon shekaru biyu. A halin yanzu Muslaiya na dạ tsohon ciki wata takwas don haka kusan ko yaushe Bagwan na tare da ita, yana taimaka mata wajen aikace-aikacen gida. Batun soyayya a tsakaninsu kuwa tamkar yanzu suka haɗu da juna.

Lokacin da su Nazmir suka isa gidan

Bagwan sai suka iske Muslaiya zaune a ƙofar gida ta haɗa kai da gwiwa tana ta sharara kuka. Koda ta hango zuwan mijinta sai ta yunƙura ta miƙe tsaye da ƙyar ta nufo shi. Shi kuwa sai ya ruga gareta suka rungume juna kuma suka fashe da kuka. Muslaiya tace, "Yakai mijina abin dogarona, ka tuna cewa ni baiwace bani da kowa a garin na, yanzu haka za ka tafi ka barni da tsohon ciki, waye zai kula da lafiyata har na haihu? Na sami labarin cewa tafiyar da zaku yi mai haɗari ce, ba lallai ba ne ku sami nasara har ku dawo gida lafiya. Ya kai masoyina yanzu idan na rasaka shi kenan abin da zan haifa ya zama maraya kenan?"

Bagwan ya janye jikinsa daga nata,sai ya sa hannayensa biyu ya share mata hawaye ya ce, "Yake matata ki kasance mai ƙarfin zuciya da kyautata zato na alheri, kisa a ranki cewa zan dawo lafiya kuma ki cigaba da yi mana fatan nasara. In kika yi haka nima zan sami ƙwarin gwiwar jajircewa iya yina don na tabbatar da dawowata."

Muslaiya ta yi murmushin ƙarfin hali, ta ce, "Shi kenan zan yi duk yadda ka ce."

Daga nan sai ta ɗaga kanta ta dubi jarumi Nazmir ta ce, ''Ya kai babban jarumi ina son ka yi mini wani alƙawari."

Cikin mamaki Nazmir ya dubeta, yace, "Wane irin alƙawari kike son na yi miki?" Muslaiya ta taka ta matso daf da Nazmir suka fuskanci juna sosai, sannan ta ce, "Ina son ka yi iya ƙoƙarinka wajen kare rayuwar mijina yayin da kuka yi wannan tafiya idan kuma ƙaddara ta yi halinta na roƙe ka da k da ka bar mini gawarsa a jeji, lallai ka zo mini da ita, domin idan ɗansa ko 'yarsa ta taso ta ga kabarin mahaifinta."

Yayin da suka ji wannan batu sai duk suka kama zubar da hawaye. Cikin ƙarfin hali Nazmir yace, "Na ɗauki wannann alƙawari, kuma komai tsanani zan cika shi in dai ina numfashi a doron ƙasa."

Nan take suka yi mata sallama, sannan suka É—unguma izuwa gidan su Husuf.

Husuf ba shi da kowa face ƙanwa, kuma yarinya ce, wacce ba ta wuce shekara goma sha ɗaya ba, sunanta Lamiz. Tsiran sa da ita bai wuce shekaru tara ba. Tun Huhuf na da shekara goma sha huɗu mahaifiyarsu ta bar masa amanarta lokacin da ita mahaifiyar ta su take kwance cikin cutar ajali. Bayan rasuwar mahaifiyar ta su kuwa sai Suhuf ya ci gaba da kula da Lamiz ainun ko kaɗan baya yarda wani

abu ya taɓa lafiyarta, kuma komai take so sai ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya samo mata,kai tun a wannan lokaci Suhuf ne ya zamo tamkar uwa da uban Lamiz,domin shi yake mata wanka da wanki ya sa mata kaya, sannan ya ciyar da ita dare da rana. A kullum sai ya ga ta yi bacci lafiya, sannan shi ma ya kwanta har Allah ya raya su gaba ɗaya, suka kawo iyanzu.

Sa'adda aka iso gidan sụ Suhuf tun da Lamiz ta hango su tun daga nesa don haka sai ta rugo da gudu gare su tana mai kuka. Koda ganin haka sai shima Suhuf ya ruga gareta ya ɖurƙusa ƙasa ta faɗa ƙirjinsa, suka rungume juną, sụna kuka tare.

Al'amarin da ya ƙara jefa su Nazmir cikin tsananin tausayi da damuwa kenan, domin dukkaninsu sun san cewa irin shaƙuwar da ke tsakanin waɗannan 'yan uwa ta kai ainun,cikin shishshiƙar kuka Lamiz tace,

"Ya kai yaya na me zai hana ku yi wannan tafiya tare da ni, domin idan har ka tafi ka barni anan ni kaÉ—ai tabbas zan ji tamkar Ä‘aukeni ka kaini tsakiyar dokar jeji ne in da babu gida gaba da baya,ka sani kai ne gidana, kai ne jina da ganina, kuma kai ne numfashina, in babu kai babu rayuwa."

Nazmir suka cika da mamakin hikimar zancenta a matsayin ta na yarinya ƙarama,kuma suka ƙara kamuwa da tsananin tausayinta,Husuf yace, "yake ƙanwata ki yi sani cewa ba zan iya yin wannan tafiya tare ke ba, saboda haɗarin da ke cikinta. Lallai zan barki a

hannun iyayen abokina Nazmir tabbas za su riƙe ki amana kamar yadda nake kula da ke. Ina son ki kwantar da hankalin ki kisa a ranki cewa lallai zan dawo gida lafiya."

Yayin da Lamiz ta ji haka sai ta janye jikinta daga na Suhuf sannan ta dube shi cikin nutsuwa tace, "Ya kai yayana na sani cewa iyayen Nazmir zasu kula da ni ainun amma kana tsammanin za su iya bani nutsuwa da kwanciyar hankali írin wacce ɗan uwa ke ji yayin da yake tare da ɗan uwansa na jini?

Yayana ka sani cewa jini-jini ne na rantse da darajarka babu wani mahaluƙi da zai nuna mini soyayya a duniyar nan zuciyata ta yi fari face kai, ai kama da wane bata wane."

Koda Huhuf ya ji haka sai jikinsa ya yi sanyi gaba ɗaya ya kasa cewa da ita komai. Kawai sai ya sake rungumeta, suka ƙanƙame juna, suna rusa kuka.

Da ƙyar su Nazmir suka raba su sannan ya yi mata bankwana suka tafi suka barta tana mai ɗaga musu hannu, shi kuwa Suhuf yana waigenta hawaye na cigaba da kwarara a idanunsa. Har sun yi nisa sai Lamiz ta sake rugawa da gudu garesu. Da zuwa sai ta cire mayafin jikinta ta miƙawa jarumi Nazmir, shi kuwa sai ya karɓa cikin yanayin mamaki ya ce, "Mę zan yi da wannan?" Lamiz ta ce, "Ina son ka riƙe shi yayin wannan tafiya ta ku. Idan har yayana ya dawo a raye ka bashi mayafin nan ya dawo mini da shi, idan kuwa ya rasu a can ka ɗaura mayafin nan a gashinka."

Tana gama faÉ—in haka ta sake fashewa da kuka, kuma ta juya ta ruga gida.

A can gidan su Iklam kuwa sun iske mahaifinsa tsoho Kamshur wanda ya kasance gurgu mai ƙafa đaya, kuma shekarunsa sun haura casa'in yana iya tafiya ta hanyar dogara sanduna guda biyu waɗanda ke maƙale a hammatarsa hagu da dama.

Kamshur shahararren mayaƙi ne a birnin Dahamul, kuma ya yi shahara a lokacin da sadauki Halufa ke kan sharafinsa Kamshur shi ne na biyu wato daga Halufa sai shi. Don haka sun kasance aminan juna.

Kamshur ya sami wannan naƙasa ne a wasu shekaru can baya sa'adda sarki Bashakur ya tura shi kai sumame wani gari da ake kira Lamar.

Lambar birni ne wanda waɗansu tsirarun fatake suka ƙirƙira,ƙasar ta kasance mai albarka domin akwai ni'imar ruwa da shuke-shuke kuma akwai daɗin faurata, saboda yawan dabbobin jeji.

Bisa wannan dalili ne fatake ke ya da zango a wajen har ma suka fara zama. Da kaɗan-kađan kuma sai suka fara yawa har wajen ya zama mahaɗar cinikaiya. Shi dai wannan gari yana kusa da birnin Dahamul domin tsiransu bai wuce tafiyar kwana tara ba.

Lokacin da sarki Bashakur ya sami labarin kafuwar wannan gari sai ya aiko musu da saƙon cewa su dunga kai masa haraji mai yawa, a duk wata guda. Su kuwa mutanen wannan birni sai suka karɓi

saƙon hannu biyu amma sai da wata uku cur ya shuɗe basu aika da harajin ba. Wannan tasa sarki Bashakur ya fusata ainun ya aika jarumi Kamshur tare da wasu barade su ɗari uku akan cewar su je su rushe garin su kashe mazaje kuma su kamo bayi,a ɗebo ganima. Ashe lokacin da sarki ya bayar da wannan umarni akwai wani baƙo a wajen kuma ɗan wannan gari ne na Lambar.

Nan da nan ya sulale ya hau dokinsa ya nufi birnin Lambar cikin tsananin sauri. Baƙon na isa ya sanarwa da 'yan uwansa abin da ake ciki. Nan fa suka fara tunanin abin yi domin sun san cewa kafin su tattara inasu-inasu su bar garin tuni mutanen sarki Bashukur sun iso. Bisa wannan dalili ne suka yi shirin yaƙi, kuma suka yi kwanton ɓauna, a bayan gari. Sai da su jarumi Kamshur suka shigo tsakiyarsu sannan suka farmusu da harbi. Daga bisani kuma suka afka musu da yaƙi.


 Karanta Littafi Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Page 8 


Domin sauke Audio sai ku danna Hoton dake kasa 👇👇👇



Post a Comment

0 Comments

Ads