Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 6


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba

Book 1 

Part 6

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh

A can fadar sarki Dujalu kuwa,bayan kuyanga ta kawo shayi an zubawa kowa ya sha,sai Ruziyal da boka Hajarul makurus suka yi gyatsa tamkar waɗanda suka ci nama suka ƙoshi.

Boka Hajarul makurus ya dubi sarki Dujalu yace,

"Ya kai wannan sarki mai tarin hikima,kayi sani cewa haƙiƙa yanzu ma mun sake jijjige gajiyar da take jikinmu,kuma babu yunwa ko ƙishirwa a tare da mu ko kaɗan.

Don haka sai ka fara bamu labarin/hikaya ta uku mu ji abin al'ajabin dake cikin ta."

Sarki Dujalu yayi murmushi sannan ya dubi tsoho Rafkangu,shima tsoho Rafkangu sai ya girgiza kai alamun ya gamsu da shayin da ya sha yace,

"Tabbas nima na ji abinda sauran 'yan uwana suka ji a jikin su."

Sarki Dujalu yayi gyaran murya sannan yace,

"To sai ku kimtsa, kai mai rubutu ka aza alƙalamin ka akan takarda domin wannan hikayar da zan baku na ɗauke da matukar abubuwan jarumta,tausayi da kuma ban al-ajabi.

Ni kai na ko tunowa nayi da labarin sai nayi kuka. Hikaya ce ta wani kyakykyawan saurayi kuma jarumi wanda ake kira NAZMIR bin HALUFA da gimbiya LUZAIYA 'yar sarki FAHALUL BAHAFUS.


*****************

A wani zamani can mai tsawo da ya shuɗe anyi wata babbar ƙasa wadda ake kira DUHAMUL. Wannan ƙasa ta bunƙasa a girma,arziƙi da kuma ƙarfin mayaƙa. A bisa wannan dalili ne ƙasar DUHAMUL ta shahara kuma ta zama Gagarabadau a cikin dukkanin ƙasashen kewayenta. Ya zamana ana matuƙar tsoranta.

Sarkin da ke mulkin a wannan ƙasa ta Duhamul wani azzalumin sarki ne ana kiransa Bashakur. Sarki bashakur ba tsoho bane kuma ba yaro bane domin shekarunsa ba zasu gaza arba'in da huɗu ba zuwa da biyar.

Saboda zalunci irin na bashakur ko a cikin garin nasa indai mutum bai shafi jinin sarauta ba ko kuma bai zamo ɗaya daga cikin attajirai ba to yana cikin tashin hankali,domin ba ka da 'yancin kan ka. Dukiyarka da matanka zasu iya zama na sarki a koda yaushe.

Haka kuma ana ɗorawa talakawa haraji mai yawa ta yadda ko kaɗan basa morar arziƙin su, baya ga wannan idan sarki bashakur ya bushi iska sai ya tura mayaƙa izuwa wata ƙasar ya basu izinin murƙushe ƙasar a kamo masa bayi kuma a ɗebo dukiya mai yawa.

Bisa wannan halayya ne ya tara dukiya mai tsananin yawa wacce shi kansa bai san abin da zai yi da ita ba.

A wannan zamanin na sarki Bashakur tsafi bai shahara ba a cikin al'umma. Babu abinda ke tasiri face ƙarfin damtse da ƙarfin yaƙi.

Sarkin yaƙin wannan birnin na Duhamul wani tsoho ne ɗan kimanin shekara saba'in da shida wanda yayi suna a duniya saboda tsagwaran jarumtarsa da kuma iya yaƙinsa. A tarihin rayuwarsa bai taɓa jagorantar yaƙi an rasa nasara ba. Ana kiran sa da suna HALUFA.

Da yake Allah ya kan yi mutane iri-iri kowa da hali dabam. Halufa ya kasance mutum mai tausayi da taimakon talakawa. Duk irin zaluncin da sarki Bashakur ke yi ba'a son ransa ba ne. Duk da kasancewar Halufa sadauki, kuma babban mayaƙi bai son ya ga ana cin zali, sau tari idan ya je yaƙi gari sai ya nemi sulhu da sarkin garin akan ya miƙa wuya ta lallami don bai son zubar da jini face bisa dole. Wannan halaiya ta Halufa na matuƙar baƙanta ran sarki Bashakur domin akwai wani lokaci kamar shekaru ashirin baya, wata ƙasa mai nisa bisa izinin ya yanko kan sarkin da na duk 'yan majalisarsa sai ya ƙi zartar da hakan. Kawai sai ya kamo su ya zo da su a ɗaure kuma ya kai su kurkuku a cikin dare.

Yayin da sarki Bashakur ya sami wannan labari sai ransa ya ɓaci, ya harzuƙa ainun. A daren ya tura aka kirawo Halufa ya rufe shi da faɗa,sannan ya ce da shi lallai ya je ya fito da wannan sarki da jama'arsa ya sare musu kawuna kuma ya kawo masa kawunan yanzu. Cikin matuƙar damuwa yabi umarni ya tafi izuwa wannan kurkukun. Halufa ya tafi yana mai saƙe-saƙen zuci har ya sami dabara.

Kafin ya ƙarasa kurkukun sai ya sauya kamanni yayi wata irin shiga ta baƙaƙen kaya ya naɗe fuskarsa da rawani in banda ƙwayar idanunsa ba'a ganin komai ba. Kawai sai ya zare takobi da isarsa kurkukun ya hau masu gadi da sara. Duk da cewar yawan masu gadin ya haura dubu sai da ya tarwatsa su da ƙarfin tsiya ya ɓalle ƙofar ɗakin da aka sanya wannan sarki da jama'arsa ya fito da su sannan ya nuna musu wata ɓarauniyar hanya ya ce su gudu.

Sarkin da jama'arsa suka waigo suka dube shi cikin tsananin mamaki sai shi sarkin yace, "kai kuwa wane ne kai? Mene ne dalilin da yasa ka kuɓutar da mu?"

Halufa ya cire rawanin fuskarsa suka yi arba dashi sai mamaki ya daɗa turnuƙe su. Ai kaine wanda ka je har cikin ƙasarmu ka cimu da yaƙi,kuma ka kamo mu da ƙarfin tsiya, to ya kuma yanzu ka kuɓutar da mu?"

Halufa ya yi murmushi ga wannan sarki yace, ''Abin da ya sa na kuɓutar da ku shi ne bana son zaluncin da sarkina ke aiwatarwa. Ku yi sani cewa sarkina ya umarce nine da in je ƙasarku na murƙushe mulkinku kuma na yanko kawunan ku ba dan komai ba sai don bakwa yin biyayya ga umarninsa na haraji mai yawa duk shekara. Ni kuma da naje gareku sai na ƙi kashe ku na kamo ku nazo da ku aka kai ku kurkuku.

Koda labari ya riski sarkina sai ya tura aka kirani ya rufe ni da faɗa kuma ya ce lallai yanzu a daren nan na zo na yanke kawunanku na kai masa.

Maimakon na yi hakan ne na yanke hukuncin kuɓutar da ku. Yakai wannan sarki ka yi sani cewa ban kuɓutar da kai don komai ba sai don naga kana da wata 'ya ƙarama kyakykyawar gaske wadda kake matuƙar so itama kuma na fuskanci ta shaƙu da kai, don haka ba zan so na zama sanadin raba wannan soyayya ba ta ɗa da mahaifi domin nima ina da ɗa wanda nake matuƙar so fiye da komai a rayuwata. Ba zan so a ce ya zama maraya tun yana ƙarami ba."

Koda Halufa yazo nan a zancensa sai ƙaunarsa ta mamaye zuciyar wannan sarki da jama'arsa. Dukkaninsu basu san sa'adda idanunsu ya ciko da ƙwallah ba.

Nan take suka yiwa halufa godiya sannan suka yi bankwana dashi. Halufa ya kamo musu dawakai suka haye suka kama gabansu. Tafiyarsu keda wuya yayi sauri ya sauya kayan jknsa sannan yayi wa kansa raunuka a jiki ya koma gidan sarki.

Koda sarki bashakur yaga jini na zuba a jikin Halufa sai ya miƙe zumbur ya tareshi cikin firgici yana mai cewa, "ya kai sarkin jarumai me ya faru gare ka?"

Halufa yace, "ya shugabana ai lokacin da na isa kurkukun sai na iske mayaƙa dubu biyu sun afkawa masu gadi har sun buɗe ɗakin da aka kulle fursunoninka sun fito dasu. Koda nayi ƙoƙarina akan na hana su tafiya da fursunoninka amma sai abu ya gagara don kasan sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi. Da ƙyar ma na kuɓutar da kaina. Kafin na dawo cikin gari na nemi mataimaka tuni sunyi mana nisa."

Koda jin wannan mummunan labari sai zuciyar sarki bashkur tayi baƙiƙƙirin ya cika da baƙin ciki kawai sai ta sallami Halufa ya shiga tunani mai zurfi.

Daga can sai ya miƙe ya yi hawa ya tafi can kurkukun da kansa. Da zuwa ya iske masu gadin a kwankwance cikin jini magashiyan. Dq ƙyar ya samu mutum ɗaya wanda bai raunata ba sosai. Sarki ya durƙusa gabansa ya cakumi wuyan rigarsa cikin tsawa yace, "wane ne ya zo yayi muku wannan ɗanyen aiki?"

Mai gadin ya bude baki da kyar da ƙyar yace "ai wani mutm ne shi kaɗai cikin shigar baƙaƙen kaya ya zo ya tarwatsamu ya fito da fursunoninka ya kuɓutar dasu."

Koda jin haka sai sarki bashkur yayi jifa da mai gadin yace, "wannan zancen banza ne duk faɗin ƙasar mahazus babu wani sadauki mai irin wannan

jarumtarkar. Lallai ka tabbata maƙaryaci."

Kawai sai sarki bashkur ya zare takobi ya fille kan wannan mai gadin. Nan take ya sake hawa dokinsa ya sukwane shi cikin fushi ya koma cikin gari. Da zuwa bai zame ko'ina ba sai gidajen manya mayankan garin yana tambayar su ko jarumi Halufa yazo neman taimakon su a cikin wannan daren bisa farmakin sumame da aka kaiwa kurkukunsa?

Kowa sai yace shi ba a neme shiba hasalima yanzu yake jin labarin abinda ya faru. Yayin da sarki bashkur ya gaji da yawan tambaya sai ya koma gd ya kwanta cikin tsananin baƙin ciki kashe gari da safe sarki bashkur ya tara dukkan 'yan majalisar sa ya sanar dasu duk abinda ya faru jiya da daddare kuma ya tabbatar musu da cewa shi kam yayi tunani kuma yayi bincike ya gano cewa ba kowanne ya aikata wannan mummunan aiki ba face jarumi Halufa.

Nan take ya kawo hujjojinsa guda biyu hujja ta farko itace babu wani sadauki a gaba ɗaya wannan nahiya wanda zai iya tarwatsa barade dubu face jarumi Halufa.

Hujja ta biyu itace halufa yayi masa ƙaryar cewa ya dawo cikin gari ya nemi taimakon wasu mayaƙan amma da aka tambaye su sai suka ce ba wanda ya nemi taimakonsu.

Duk wannan bayani da sarki Bashakur yake Halufa na zaune gefe guda yana saurara kawai sai yayi shiru bai ce komai ba yana muzurai kawai.

Sarki bashkur ya dubi fadawansa yace to kunji laifin da Halufa ya aikata don haka sai ku yanke masa hukunci da kan ku.

Gaba ɗaya 'yan majalisar suka yi tsit aka rasa wanda zai ce wani abu. Daga can sai waziri yace, "ya sarkin sarakuna ai ni a ganina wannan hukuncin ba zai yanku ba yanzu muna buƙatar muyi zama na musamman."

Koda jin haka sai sarki yace, "Ƙwarai kuwa nima na amince da wannan shawara." Suma sauran 'yan majalisar suka amince akan hakan. Daga nan fada ta watse kowa ya kama gabansa. Sai da aka shafe kwana arba'in ana mahawara a majalisa akan irin hukuncin da za'a yankewa halufa.

A ƙarshe dai aka yanke masa hukunci cewa an dakatar dashi daga kan matsayin sa na sarkin yaƙi har tsawon shekara ashirin masu zuwa nan gaba. Kuma dukiyarsa aka raba ta kaso biyu aka ɗauki kaso guda aka raba wa masu gadin gidan kurkukun aka bar masa guda.

Daga wannan rana Halufa ya cire hankalinsa daga harkokin fada gaba ɗaya ya maida nutsuwarsa akan ɗansa guda daya wanda suka haifa tare da matarsa Zuwaisa. Wannan ɗa an rada masa suna NAZMIR.

Nazmir ya taso yaro mai kwarjini ƙwazo da basira ya zamana mahaifinsa na koyar dashi kyawawan ɗabi'u kuma yana koya masa juriya,jarumta da dabarun yaƙi. Nazmir ya shaƙu sosai da iyayensa domin dare da rana yana tare dasu kuma ko kaɗan baya son abinda zai ɓata musu, domin ya kasance mai tsantsar biyayya a gare su. Yayin da Nazmir ya cika shekara sha huɗu sai ya zamo jarumin gaske kuma farin jininsa ya yawaita tsakanin al'umar garin, saboda irin kyawawan halayensa na tausayi da jin ƙai da kuma biyayya ga na gaba dashi.

A ɓangaren jarumta kuwa sai da yabar abin tarihi a kasar Duhamul domin shi kaɗai yake shiga daji ya yi farautar manyan dabbobin dawa masu haɗari. Sai dai aga yazo da gawarsu.

Tun yana jarraba jarumtarsa a tsakanin sa'anninsa har ta kai cewa yana tunkarar manyan baraden ƙasar ɗaya bayan ɗaya.

Duk wanda suka gwada yar ƙashi ko tsagwaron yaƙi sai ya sami galaba akan sa. Cikin ƙanƙanin lokaci labarin jarumi Nazmir ya yadu ko'ina a fadin ƙasar ya zamana ana zuwa ganinsa daga gari-gari.

Shi kuwa Halufa da matarsa Zuwaisa suka kasance cikin tsananin farin ciki bisa wannan da Allah ya baiwa ɗan su. Lokacin da nazmir ya cika shekara ashirin a duniya sai kyawunsa ya ƙara bayyana a fili ƙarara.

Jarumtakarsa ta ninka ta da ya zamana bashi da abokai sai 'ya'yan sarautar ƙasar amma da yake shi mutum ne na mutane mai sauƙin kai bai yar da wasu abokansa ba su shida waɗanda suka taso tun yarinta.

Wandannan abokai gaba ɗaya 'ya'yan talakawa ne. Kuma dare da rana suna tare da Nazmir duk da cewa mahaifinsa yafi iyayensu arziki da ɗaukaka. Daga cikinsu akwai Sharhil, Bagwan, Hasuf, Iklam, Bardil da kuma Huzaik.

A cikin su gaba ɗaya babu wanda yafi shaƙuwa da Nazmir sama da Huzaik domin maƙotan juna suke,gidan su Huzaik yana kallon gidan su Nazmir. Babu abinda ke raba su face kwanciyar baccí kai wani lokacin ma har musayar kwana suke,wato yau idan Nazmir ya kwana a gidan su Huzaik,kashe gari kuma sai Huzailk ya kwana a gidan su Nazmir. Dama mahaifin Huzaik yana zumunci sosai da Halufa. Sai dai tsoho ne tukuf don a ƙallah ya baiwa Halufa tazarar shekara goma sha đaya.

Mahaifiyar Huzaik ta rasu tun yana jariri, a halin yanzu Huzaik ba shi da kowa a duniya face wannan mahaifi na sa wanda ake kira Marnush, kuma ko ƙuda bai son ya taɓa lafiyar Marmush ɗin.

Huzaik yaro ne mai juriya da bajinta, amma ko kaɗan bai kama ƙafar jarumi Nazmir ba. Da yake an ce zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai. Shaƙuwar Nazmir da Huzaik ta sa shi ma Huzaik ɗin ya zama cikakken jarumi, kuma mara tsoro, domin duk sa'adda da Nazmir zai fita farauta jeji tare za su fita.

Yayin da Halufa ya fuskanci amincin da ke tsananin Namzir da abokansa guda shida ya kai ainun sai ya rinƙa koya musu yaƙi tare ko yaushe.

Haƙiƙa kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa,Nazmir ya ƙware wajen iya sarrafa takobi matuƙa gaya, kuma duk ya fisu jarumta da juriya shi kuma Huzaik ya ƙware ne akan iya harbin kibiya, sannan ya kasance magujin gaske. Komai gudun dabba yana iya ƙure mata gudu ya harbota. Idan kuwa ka kabi bayansa da gudu to in dai ya baka rata har abada ba za ka kamo shi ba.

Haka kuma yana da juriyar gudun don yana iya shafe sa'a goma yana gudu a cikin jeji ba tare da ya tsaya ya huta ba. Shi matsalarsa guda ɗaya ce indai babu ruwa a tare da shi ƙishirwa na galaɓaitar dashi nan da nan. Don haka wani lokacin ma yana cikin gudu yana shan ruwa abinsa.

Shi kuwa Sharhil ya ƙware ne a fagen iya faɗa da mashi. Shi kaɗai yana iya shiga tsakiyar mutum đari ya tarwatsa su da mashi guda, ko da kuwa za su rufar masa da sara da harbi don yana da zafin naman iya kaɗe harbin kibiya kuma ya kare saran, idan kuwa ya taɓe ya harba mashinsa in dai ya caki bishiya komai kaurinta sai ya nutse a cikinta.

Sharhil na iya cake mutumin da ke nesa da shi tsawon kamu ɗari uku daga inda yake tsaye.

Husuf, Iklam, Bagwan da Bardil kuwa cikakkun mahaya doki ne,in dai suna kan doki komai yawan taron abokan gaba za su iya ratsawa ta cikinsu su yi ta sara da suka ba tare da an samu galaba a akan su ba. Haƙiƙa sun ƙware ainun akan yaƙin kan doki.

A ranar da Nazmir ya cika shekaru ashirin cif a duniya, sai Halufa ya shirya masa walima,a wannan rana Zuwaisa ta sha ɗawainiyar girke-girke.

In ba don ma ta sami taimakon ƙawayenta ba iyayen su Husuf da aikin yafi ƙarfin ta, gaba ɗaya 'ya'yan sarakan garin sai da suka halarci wannan walima.

Kai daga wasu ƙasashen ma haka 'ya'yan sarakai suka yi ta shigowa cikin birnin Dahamul duk da cewa kuwa da yawansu ba gayyatarsu aka yi ba.

Kawai sunzo ne don su ga jarumin da labarin sa ya cika duniya wato Nazmir bin Halufa.

Yayin da taro yayi taro sai jarumi Nazmir tare da abokanansa suka yi ta gaisawa da baƙi ana bashi kyaututtuka,kai har saida ya gaji da karɓar kyaututtukan ya wakilta su Huzaik suka cigaba da karɓa.

Nan take aka shigo da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,makaɗa da mawaƙa kuwa suka hau aikinsu. Nazmir ya koma inda iyayensa ke zaune cikin farin ciki suma abokansa suka koma gefe guda ana kallon masu yin rawa.

Anan cikin tsakiyar wannan shagali ne aka hangi sarkin dogarai ya shigo wajen kai tsaye riƙe da wata takarda a hannunsa. Nan take wurin yayi tsit kowa ya ƙame tamkar babu mai numfashi a wurin kai kace mutuwa ce ta gifta. Sarkin dogarai ya ƙaraso gaban Halufa ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya miƙa masa takardar yace, "saƙo ne daga majalisar sarki."

Koda Halufa ya karɓi takardar sai ya miƙawa Nazmir ba tare da ya duba ta ba yace, "ya kai ɗa na buɗe takardar nan ka karanta abinda ke ciki a fili mu ji."

Cikin biyayya Nazmir ya buɗe takardar ya fara karantawa kamar haka:-

"DAGA MAJALISAR BIRNIN DUHAMUL ZUWA GA SARKIN YAƘI,JARUMI UBAN JARUMAI, SADAUKI HALUFA.

YA KAI GARKUWAR MUTANEN DUHAMUL KAYI SANI CEWA HAR KWANAN GOBE WANNAN MAJALISA NA ALFAHARI DA KAI A MATSAYIN KA NA SARKIN YAƘIN TA DON HAKA GAISUWA,YABO DA KARAMCI SU TABBATA A GARE KA, KAMAR YADDA KA SANI CEWA SHEKARUN BAYA AN SAUKE KA DAGA KAN AIKIN KA HAR TSAWON SHEKARU ASHIRIN.

TUN DAGA WANNAN LOKACI KAWO IYANZU BA'A NAƊA SABON SARKIN YAƘI BA.

MAJALISA NA SANAR DA KAI CEWA WA'ADIN DA AKA ƊIBAR MAKA YA CIKA DON HAKA ANA UMARTARKA DAKA DAWO BAKIN AIKI.

DA FATAN ZAKA KASANCE MAI BIYAYYA GA MAJALISA."

Yayin da Nazmir ya gama karanta wannan wasiƙa sai ransa ya harzuƙa,har ya yunƙura zai yayyaga takardar sai Halufa yayi masa wani irin kallo.

Nazmir ya ajiye takardar a gefe guda shi kuwa Halufa sai ya dubi sarkin dogarai yace, "kaje ka sanar da majalisa cewa saƙo ya zo mini kuma gobe da safe zan hallara a fada."

Sarkin dogarai yayi godiya ya fita cikin farin ciki. Shi kuwa Halufa sai ya bayar da izinin a cigaba da walima.

Take wuri ya sake hautsinewa da hayaniyar kaɗe-kaɗe da raye-raye. Ba'a gama walimar ba sai da duhu ya fara sannan baƙi suka fara yin sallama suna bankwana ɗaya bayan ɗaya.

A haka dai wuri ya ɗare aka bar su Halufa kaɗai.

Nan take halufa ya koma kan kujera ya zauna sannan ya umarci su Nazmir da su zauna.

Dama Zuwaisa na can gefe ɗaya a zaune. Halufa ya dubi Nazmir yace, "ya kai ɗana haƙiƙa na fuskanci zuciyarka ta sosu sa'adda saƙo yazo mini daga majalisa. Lallai ina son ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi."

Yayin da Nazmir yaji wannan batu sai yace, "ya abbana ai dole ne zuciyata ta sosu domin ban ga dalilin da zai sa majalisa ta buƙace ka ba yanzu,alhalin ta wulaƙanta ka a lokacin da kake ganiyar sharafinka wace gwaninta zaka iya yi mata a halin yanzu da tsufa ya riske ka wacce ba ka yi kamarta ba abaya."

Halufa yayi ajiyar zuciya yace, "yakai ɗana haƙiƙa kayi tunani mai kyau nima kuma jikina ya bani cewa lallai akwai babbar buƙata da ta tasowa sarki wadda dole sai da taimakona zata biya shi yasa aka neme ni."


Karanta>>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 7

Domin Sauke Audio Sai Ku Dannan Hoton Dake Ƙasa 👇👇

Post a Comment

0 Comments

Ads