Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 5

Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba

Book 1 

Part 5

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh


 Kafin gimbiya Sima ta buÉ—e baki kawai sai suka gaba Ä‘ayan ginin É—akin da suke ciki an daukeshi can Æ™as an barsu a tsakiyar fili tamkar a É—auke murfin tukunya a ajiye a gefe guda.

Kawai sai ganin waɗansu jibga-jigan aljanu kimanin su miliyan ɗaya sun yi musu ƙawanya kowannensu riƙe da mugun makami.

Ba zato ba tsammani kuma sai ga sarki

lu'umanu bisa dardumar tsafi ta sauke shi daf da jarumi hubairu suka fuskanci juna sai ya murtuke fuska yace, "ya kai babban maƙiyina kayi sani cewa babu inda zaka shiga a cikin duniya nan ka ɓace mini,ka tuna cewa munyi gagarumin faɗa ni da kai har sau biyu ko kuma nace sau uku munyi kare jini biri jini, ina tabbatar maka da cewa wannan karan na zo da cikakken shirin irin wanda ban taɓa yi ba don haka dole ne naga bayanka.

Tabbas yau sai nayi gunduwa-gunduwa da sassan jikinka.

Ita kuwa masoyiyar taka dole na mallaketa ko tana so ko bata so."

Jarumi hubairu ya dakawa lu'umanu tsawa yace, "kai tsohon maƙiyin ALLAH babban mushiriki ma'abocin fasiƙanci domin ina tare da ubangijin musulunci addinin da ya zamo shugaban addinai kuma tafarkin gaskiya.

Duk wanda ya riƙe shi yafi ƙarfin masu yin waninsa, da izinin Allah zan samu rinjaye akanka kuma da sannu zamu ƙarar da ire-irenku a doran ƙasa mu kawar da kafirci mu shimfiɗa musulunci ya baibaye duniya gaba ɗaya."

Koda jin wannan batu sai sarki lu'umanu ya sake tuntsirewa da dariya sannan ya dubi waɗannan dakarun aljanu guda miliyan ɗaya waɗanda Shamharu ya tsafance su tsahon shekaru dubu kuma ya tsuma makamansu a tsumin dafi tsawon shekaru dubu yace dasu, "me kuke jira ne da abokan gabarmu maza ku ragargaza su ku ratattakasu banda gimbiya Sima kaɗai har sai sun zama ruɓurɓushi.

Nan take wuri ya yamutse aka fara É—auki ba daÉ—i.

Jarumi Hubairu da sarki Lu'umanu kuwa suka ware gefe ɗaya suna zagaya juna da kallon kallo kowennan su na tunanin irin harin da zai kai. Ita kuwa gimbiya Sima an barta ita kaɗai a tsaye a waje guda jikinta na karkarwa don tsananin razana, domin tunda take bata taɓa ganin gwarazan aljanu ba irin waɗannan. Su kansu dakarun Musuluncin sun isa abin tsoro ballantana kuma kafiran aljanun guda miliyan đaya waɗanda sun ninka musulman sau arba'in. Nan fa aka shiga bugegeniya da sokaiya, ƙarajin aljanu dana makaman su ya cika dodon kunne. Jini ya rinƙa fantsama tamkar ana ruwan samansa. Haƙiƙa gumurzu ya kasance kare-jini-biri-jini domin kowane ɓangare suna wahala da asara, kuma kowane ɓangare na aiki da abin dogaransu. Su kafiran aljanun nan na tsafi suke tayi da amfani da ƙarfin damtse,su kuwa musulman aljanun suna kiran sunan Allah ne tare da nuna tsantsar jarumtaka.

Duk sa'adda suka ambaci sunan Allah saidai kafiran na É“ace É“at, sai dai kawai a sake ganinsu tsulum sun baiyana ta hanyan shammace. Idan kuwa suka yi

nasu tsafin sai ƙarfin addu'a ya hanashi tasiri, saboda haka babu abin da yake tasiri a filin dagar sama da ƙarfin damtse da iya yaƙi.

Sarki Lu'umanu da jarumi Hubairu suka ja da baya taku bakwai-bakwai sannan kowannansu ya rugo da gudu don a haɗu a tsakiya riƙe da makami a sama,shi dai Lu'umanu ihu yake yi da kururuwa mai firgita gungun mayaƙa shi kuwa Hubairu babu abin dake fita daga bakinsa face kabbara.

Yayin da suka haɗu a tsakiya takubbansu suka gwaru sai tartsatsin wuta ya tashi ƙasa tayi girgiza gaba ɗaya wajen ya hau tambal-tambal kai kace naɗe ƙasar wajen za'ayi. Tabbas kasancewa manyan baradene suka yi karo, nanfa sukaci gaba da kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta tamkar jikkunansu bana jini da tsoka bane, na karfene. Sai da suka shafe sa'a shida cur suna wannan mugun gumurzu amma ɗayansu bai samu koda karcewa ba a jikinsa ba. Da kansu suka rabu kowa ya ja da baya yana haki da tunanin dabarar da zata fishsheshi. Tabbas ƙarfi yazo daya,mamaki ya kama sarki Lu'umanu ya ce a zuciyarsa yanzu duk irin shirin nan da mai girma Shamharu yayi mana ni da waɗannan dakarun nasa ya tashi a banza kenan,kai lallai waɗannan mutane sun cika hatsabibai, kamar yadda sarki Lu'umanu ke wannan tunanı haka shima jarumni Hubairu ya kasance domin ya tsinci zuciyarsa na mai cewa dashi kai waishin su Lu'umanun nan waɗanne irin hatsabibai ne.

Haƙiƙa Allah ya ara musu lokaci amma in ba don haka ba ya za ai ace mun kasa samun nasara a kansu har yanzu, duk da cewa kuwa muna addu'o'i da kiran sunan Allah akansu. Bayan kamar daƙiƙa ɗari da tamanin Lu'umanu da Hubairu na kallon juna sai kawai Lu'umanu ya sake yin kukan kura ya tasammasa suka sake garƙamewa da azababben yaki. A wannan lokaci yaƙi ya ƙara tsamari tsakanin kafiran aljanun da kuma musulman masu taimakawa Hubairu domin kusan kowane ɓangaren sun rasa rabin adadinsu, har yanzu gimbiya Sima na nan a gefe guda tana ganin abin dake wakana, tun tana tsaye har sai da ta faɗi ƙasa kuma tun tana iya yin addu'a har sai da ta kasa da saboda ƙura da hayaƙin yaƙi wanda ya turnuƙe wajen gaba ɗaya domin bisa đole ta toshe kunnuwanta saboda ƙarar makamai da ihun mazaje.

Ana cikin hakane Lu'umanu ya faɗo inda Sima ke kwance,sa'adda jarumi Hubairu yayi masa wani wawan duka da ƙafa a ƙirji koda Lu'umanu ya ganta daf dashi sai ya kamobta yasa takobinsa akan wuyanta ya dubi Jarumi Habairu yace in ka ƙara kusantata zan yanke mata maƙogaro. Bisa dole Hubairu yaja da baya kaɗan. Nan take yaƙi ya tsaya cak tamkar babu mayaƙan a wajen,baka jin komai sai nishin naƙasassu waɗanda suka rasa sassan jikin su.

Gawarwaki kuwa gasu nan birjik babu adadi,jini kuwa sai malala yake yana gudu kamar idaniyar ruwa.

Nan take sarki Lu'umanu ya dubi daddumarsa ta tsafi wacce ke tsaye a cikin iska take daddumar tazo gaban sa ta shimfiɗa kanta,kawai sai ya hau kanta tare da gimbiya Sima har yanzu bai cire kaifin takobinsa daga wuyan ta ba kuma ya ƙurawa jarumi Hubairu idanu don tsoron kada yayi wani yunƙuri.

Daddumar tsafin ta bar doron ƙasa ta dira akan ɗaya daga cikin baraden aljanun nasa kawai sai Lu'umanu yayi wani tsafi gaba ɗaya wajen ya gauraye da tsananin duhu cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba,kafin su jarumi hubairu suyi wani yunƙuri tuni su sarki lu'umanu sun ɓace kuma sun ɓace ne tare da gimbiya sima.

Cikin hanzari jarumi hubairu ya karanta

wata addu'a sai wannan duhu ya yaye

haske ya baibaye tamkar ba'a taɓa yin

duhu ba.

Koda hubairu yaga babu su lu'umanu kuma babu gimbiya Sima sai hankalinsa ya tashi cikin sauri ya bada

umarni abi sawun su.

Ai kamar an harba kibiyoyi dakarun

musuluncin suka harba jikkunansu suka luluƙa cikin gajimare suna masu

tsananin gudu cikin sahu sahu abin

gwanin ban sha'awa kaikace tsuntsaye ne ke bikin gasar gwada tsere.

Wannan shine abina ya faru tsakanin

su jarumi hubairu da su sarki lu'umanu yayin da aka fafata baƙin gumurzu a gidan bokanya samaratu don ɗaukar gimbiya sima.


*****************************************


Tun sa'adda aljani durfus ya tafi ya barsu a cikin kejin tsafi bisa sharadin cewa idan sun amince ya zama shugabansu zai dawo ya kuɓutar dasu.

Sai suka kasance cikin halin damuwa

da shawarwari. Markahus sabus ya dubi ummansa bokanya samaratu yace, "yake ummina tun É—azu boka Jinshan da boka sulbaini sunata faÉ—in albarkacin bakinsu bisa shawarar da

ya kamata mu yanke akan sharaÉ—in da aljani durfus ya gindaya mana.

Amma ke kinyi shiru ba kice komai ba

ko kina da dalili?"

Samaratu tayi murmushi tace, "yakai

É—ana kayi sani cewa shifa aljani Durfus bawa ne ga boka sulbaini don haka ya fi saninsa shi ya kamata ya bamu shawarar abin da ya dace muyi."

Koda jin haka sai sulbaini yayi farat yace, "haba Samaratu ai in ki ka faÉ—i

haka baki yi mini adalci ba. Ki tuna fa

cewa wannan durfus din na yanzu ba shine na da ba wanda na sani ma'ana

ina nufin cewa a halin yanzu aljani Durfus ya taka matsayin da ban sani

ba. Ni ina ganin kawai mu amince da

zama bayinsa in yaso bayan ya kuɓutar damu sai muyi masa tawaye ta hanyar yaudararsa har mu kai ga samun nasara akan SHAMHARU."

Yayin da sulbaini yazo nan a zancen sa sai boka Jinshan ya tuntsire da dariya yace, "wai shin kai ina ka kai tunaninka ne ka ajiye shi har ka manta dashi.

Tsaya na gaya muku gaskiya na gaba

yayi gaba na baya sai labari.

Ai dama ance wanda duk ya rigaka barci dole ya rigaka tashi idan har muna so mu sami nasara akan shamharu dole ne muma mubi irin hanyar da yabi ta neman zama MATSATSUBI."

"Ta yaya zamu zama MATSATSUBAI kaima ka zo da zancen banza abinda ba zai yiwu ba." Markahus sabus ne yayi wannan furuci.

Jinshan yace, "to shi shamharu ya aka yi ya shahara har ma yake bin hanyar zama MATSATSUBIN? Duk abin da yayi ya shahara muma shi zamu yi domin ance sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba'a jeba."

Koda jin haka sai Samaratu ta sake

tuntsirewa da dariya a karo na biyu tace, "haƙiƙa na fuskanci kuna neman zautuwa shin kun manta ne cewa shi SHAMHARU aljanine ba mutum kamar ku ba. Ku tuna fa sai da shafe ɗaruruwan shekaru yana tara ilmin tsafi sannan ya shahara.

A cikinku nan waye zai iya daÉ—ewa a duniya kamar yadda ya daÉ—e?

Waye zai iya zuwa wuraren da ya je? waye zai iya jure irin wahalar da ya sha? Tabbas ni kaÉ—ai ce a cikinku nake da damar zama MATSATSUBIYA sai kuma É—ana gashi tunda mun kasance aljanu kamar boka Shamharu."

Ko da jin wannan batu sai jikinsu boka Jinshan ya yi sanyi suka yi shiru ba su ƙara cewa uffan ba. Markahul Sabus ya yi ajiyar zuciya cikin alamun matuƙar damuwa ya dubi mahaifiyarsa Samaratu yace "ya ke Ummina ki yi sani cewa ni yanzu babu abinda ya dame ni face batun masoyiyata gimbiya Sima. Tabbas idan ban mallaketa ba zan iya haɗiyar zuciya na mutu. Yanzu gashi yau kwananmu biyu a cikin kejin nan aljani Durfus ya zo ya ce damu zai dawo don ya ji ta bakinmu har yanzu shiru ba mu ƙara ganin sa ba,anya kuwa lafiya? Ni kam na fara tunanin ko shima ya faɗa hannun aljani Rafkanagu."

Samaratu tace "Komai zai iya faruwa amma abin da nake so da kai ɗana shi ne ka sa a ranka cewa in dai ina numfashi a doron ƙasa sai na mallaka maka Gimbiya Sima ko ta halin ƙaƙa. In.kuwa kaga baka mallaketa ba, ba na raye a duniya."

Lokacin da Markahul Sabus ya ji wannan batu na mahaifiyarsa bokanya Samaratu sai farin ciki ya baibayeshi ya rungumeta yana mai fatan su samu damar kuɓuta daga cikin wannan tsafaffen keji.

Suna cikin wannan hali ne suka ga aljani Durfus ya bayyana gabansu jina-jina, duk jikinsa raunuka ne, sai numfarfashi yake kamar ba zai rayu

ba. Cikin ƙarfin hali ya dubesu yace, "Ku yi sani cewa yau kwana biyu kenan ina tafka yaƙi da wasu dakarun boka SHAMHARU waɗanda ya turosu su hallaka ni. Da ƙyar da siɗin goshi na samu na karkashesu, ko ɗayansu ban bari ya tsira ba. Nayi bincike na gano cewa rayuwata da taku na cikin mugun haɗari don haka dole ne mu haɗa kai idan har muna son mu ga bayan wannan babban maƙiyi namu wato SHAMHARU SHAHARARRE." Yayin da Durfus yazo nan a zancensa sai Markahul Sabus ya dubeshi yace,

"To yanzu yaya batun sharaÉ—in daka

gindiya mana?"

Darfus ya yi murmushin ƙarfin hali yace,

"Ka bar wannan magana yanzu. Abin da nake so da ku shine ku saki jiki dani zan tafi da ku izuwa fadar tsafin a can ne zan iya fito daku daga cikin wannan keji sannan sai mu tattauna akan hanyar da zamu É“ullowa al'amarin."

Ko da jin haka sai murna ta kama su boka Sulbaini. Gaba ɗaya suka amsa da cewar sun amince da wannan shawara. Ba tare da ɓata wani lokaci ba aljani Durfus ya suri tsafaffen keji sannan ya buɗe fukafukansa ya yi sama. Cikin daƙiƙu kaɗan ya ƙule a cikin sararin samaniya.

Aljani Durfus bai iso fadar tsafinsa ba sai bayan yayi tafiyar sa'a bakwai sannan ya sauko ƙasa ya dira a wani baƙin daji mai dogayen tsaunuka da dogayen bishiyoyi. A gaban wata mitsitsiyar bishiya ya dira, a jikinta akwai wani mitsitsin rami wanda saboda ƙanƙantarsa ko allura aka zura a ciki ba za ta shige ba. Nan take aljani Durfus ya shafi tsafaffen keji, da shi da kejin da mutanen dake cikin kejin duk suka zama siriririn farin hayaƙi. Hayaƙin ya dinga shiga cikin wannan mitsitsin rami na bishiyar har ya ƙule gaba đaya. Ba zato ba tsammani sai su Samaratu suka tsinci kansu a cikin wata tangamemiyar fada wadda aka ginata da zunzurutun đanyen gwal. Ko ina ka duba abubuwan al'ajabi ne iri-iri birjik ba adadi. Boka Sulbaini ya ƙarewa fadar kallo tsaf ya tuna tasa fadarsa wacce ya ke taƙama da ita, koda ya ga cewa wannan fadar ta ninka tasa sau arba'in a komai don haka sai ya sallamawa Durfus. Cikin alamun karayar zuciya ya dubi Durfus yace "Ya kai Durfus haƙiƙa yanzu na tabbatar da cewa ka taka babban matsayi a harkar tsafi. Ko da yake ban yi mamaki ba domin ai dama almajiri na iya fin malaminsa wata rana."

Yayin da ya ji wannan batu na tsohon maigidansa sai ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Ya shugabana ai kun yi sake đan zaki ya girma. Koda yake dole ne na girmamaka a matsayinka na ubangidana na da, shi ya sa ma na yi kiranka shugabana domin sai ɗan halak ke tuna alheri. Haƙiƙa na ƙaru sosai da kai to amma fa abin da na sani a hallarar tsafi ba ka san kaso ɗaya daga goman sa ba."

Ba tare da ƙara cewa komai ba sai ya ɗebo waɗansu garin hoda kala uku ja, fari da shuɗi ya zuba su a cikin wani kasko sannan ya ɗebo wani tafasasshen ruwa ya zuba a ciki. Nan take wannan gari kala uku ya cakuɗa kansa ya rikiɗe ya zama tiriri. Shi kuwa tiririn sai ya lulluɓe wannan tsafaffen keji wanda su Markahul Sabus ke ciki. Kawai sai kejin ya narke ya zagwanye ya ɓace ɓat.

Tiririn ya sake lulluɓe jikin su Markahul Sabus waɗanda sun kasance yan ƙanana mini-mini. Kawai sai kowannensu ya dawo izuwa ainihin siffarsa,cikin tsananin farin ciki suka gurfanar da kansu gaban Aljani Durfus kuma cikin haɗin baki suka ce "Mun sallamaka maka ya shugabanmu. Bamu da abin yi face bin umarninka, yanzu menene abin yi?"

Aljani Durfus ya ƙyalƙyale da dariyar mugunta sannan ya haɗe fuska yace, "Kamar yadda na faɗa muku a baya dole ne mu haɗa kanmu idan muna son mu sami nasara akan Shamharu. Abu na farko dole ne mu dawo kan batun mallakar littafin KUNDIN TSATSUBA na biyu wanda ke tare da Rafkanagu. Kun sani cewa ba zamu mallakeshi ba har sai mun mallaki abubuwan nan uku wato Tsumin Dodo Kirayanu, aljani Rafkanagu da kuma makamin farko wanda aka ƙera a duniya wato tsafaffiyar adda ce dake ajiye a fadar boka SHAMHARU wacce ke can tsibirin Bahar Zus. Amfanin aljani Rafkanagu a wajenmu shine mu tsafeshi ya je da kansa ya sato mana wannan adda to amma fa bincikena ya nuna min ccwa yanzu ba zamu iya mallakar aljani Rafkanagu ba, domin shirinsa ya fi namu. Aljani ɗaya ne rak a duniyar nan wanda zai iya zuwa fadar SHAMHARU ya sato mana wannan adda. Ba wani bane face aljani Balbus Sarkin ɓarayin aljanu. Shi kuwa Balbus yana zaune a can wani jeji da ake kira Zarwal a ƙarshen birnin Hindu. Tabbas zai iya zuwa tsibirin Bahar Zus a cikin kwana arba'in kuma zai iya shiga cikin fadar SHAMHARU ya sato wannan adda. To amma fa ku sani ƙarfi ko tsafinmu ba zai iya tilasta Balbus ba akan ya yi mana wannan aiki face mun yi masa alƙawarin wani abu guda đaya wanda ya gagareshi mallaka shekara shekaru. Wannan abu ba komai ba ne face wani kambu dake jikin hannun Sarki Lu'umanu na birnin Teheren. Balbus ya san cewa idan ya mallaki wannan kambu zai iya sace gaba dayan dukiyar sarakunan duniyar nan ya ɓoyeta a wajensa ya zamana babu wani attajiri kamar sa. Yayin da Durfus ya zo nan a zancensa sai Markahul Sabus ya daka masa harara yace, "amma ka ɓata rawarka da tsalle. Haƙiƙa baka san waye sarki Lu'umanu ba, shi yasa kake zaton zaka iya mallakar kambun."

Durfus ya ce dakata ai nasan ba zan iya mallakar kambun tsafinsa ba, amma kuma ai zan iya yaudarar Balbus ya gamsu cewa zan iya ɗin, indai buƙatar mu ta biya ai shike nan tunda munfi ƙarfin kowa a sannan, babu yadda Balbus ɗin zai yi da mu yi shirin kwana biyu sannan mu tafi jejin zarwal domin ganawa da aljani Balbus, kar ku sami damuwar komai, ni ina tabbatar da cewa zamu samu nasara akan sa." Wannan shine abin da faru tsakanin aljani Durfus da su aljani Markahul Sabus bayan ya kuɓutar da su daga cikin tsafaffen kejin aljani Rafkanagu.

(Matsalar page,yazo a blank amma dai zan iya summarizing nasa).

Karanta>>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 5


Domin sauke Audio sai ku Danna hoton dake kasa 👇👇👇



Post a Comment

0 Comments

Ads