Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 4


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba

Book 1 

Part 4

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh

Kafin wani daga cikinsu ya ce wani abu tuni aljani Gulzum ya daka tsalle ya yi sama.

Ɗayan su bai yi motsi ba sai bayan sun kintaci lokacin da Gulzum ya faɗi, sannan suka leƙo sama. Ai kuwa suka sha mamaki, domin kuwa aljani Gulzum suka gani riƙe da majajjawa guda yana baƙin gumurzun yaƙi, duk inda ya kai farmaki sai dai ka ga ya shaƙo wuyan sama da mutum ɗari na Galbasa ya shaƙe a cikin majajawa yana wulwula su a cikin sararin iska.

A cikin hanzari Jafar, Yelisa,Mashrila da Azbir suka daka tsalle suka ɗane bayan aljani Gulzum. Koda sauran mutanen Galbasa suka ga irin ɓarnar da Gulzum ya soma yi musu, sai da yawansu suka yi kukan kura suka afko gare shi, amma kafin su cim masa tuni sun makara domin har ya sami nasarar finciko waɗansu majajjawun guda biyu. Kawai sai ya miƙawa su Jafar guda, sannan ya riƙe guda a hannunsa, ya zamana shi kaɗai yana amfani da guda biyu.

Koda Jafar, Yelisa, da Mashrila suka kama majajjawar da niyar riƙeta sai nauyin ta ya rinjaye su, suka suɓuto daga kan aliani Gulzum za su faɗo ƙasa. Cikin tsananin zafin nama sarki Azbir ya riƙe majajjawar da hannu đaya sai ga su Jafar suna reto a jikin majajjawar. Azbir ya dawo da su kan Gulzum kowannensu ya zauna daram, sannan shi kuma ya kama majajjawar da hannu biyu ya fara kaiwa mutanen Galbasa farmaki kamar yadda aljani Gulzum ke yi.

Al'amarin da ya jefa su Jafar cikin matuƙar mamaki kenan. Jafar ya dubi Mashrila ya ce, "Ke kin ga wannan mutumin da kike rainawa ko, ashe ma duk ya fimu ƙarfi ba mu sani ba. Lallai sai miya ta ƙare sannan ake sanin maci tuwo."

Yelisa ta yi ajiyar numfashi, ta ce, "tab ɗijan daga yau na daina raina ƙananan mutane ni kam ban taɓa tsamanin cewa wannan mutum zai iya ɗaukar wani abu mai nauyin mutum ba, sai ga shi yana sarrafa wannan ƙatuwar majajjawar wadda nauyinta wuce na gawarwakin bil'adama guda dubu, kuma manyan ƙarata ababan kwantace."

Cikin ƙanƙanin lokaci Gulzum da Azbir suka tashi hankalin mutanen Galbasa suka ƙuntata musu, suka hana su saƙat, duk da cewa kuwa suma ba su fasa ɓarna ba, domin sun sha jinin sama da mutum miliyan uku da ɗoriya. Yayin da masifa ta yi masifa, gumurzu, runguntsumi, artabu, đauki ba daɗi da tsananin turnuƙu ya yawaita, sai Dauduf ya sake yin sama cikin tsananin gudu ya isa inda su sarki Galbasa suke. Wannan karon sai ga shi ya zo cikin mugun tashin hankali yana ta haki ya risina gaban Galbasa yace,

"Ya shugabana wani baƙon aljani tare da sarki Azbir da wađannan baƙin bil'adama sun sami nasarar ƙwatar majajjawa guda uku, daga hannun jama'armu har sun yi mana gagarumnar ɓarna. Gaba runtuma ihu yake, yana rusa kuka jin azaba. Cikin tsananin mugun gudu tamkar an harba tauraruwa mai wutsiya, Mazalish ta bi bayan su sarki Galbasa amma kafin ta isa tuni Galbasa ya riski su Gulzum.

Da zuwa ya yi wani tsafi sai ga shi ya fincike majajjawar hannnunsu tamkar mayan ƙarfe ya zuƙe guntun ƙarfe da ke ajiye a gefe guda. Nan take ya sake yin wani tsafin sai igiyar tsafi ta ɗaɗɗaure su tamau, suka kasa motsi.

Anan ne fa Yelisa ta tuna cewa ita ma fa matsafiya ce 'yar babban matsafi,kawai sai ta rufe idanunta ta yi kiranye-kiranye da 'yan tsatsube- tsatsube amma sai ta ji shiru kamar maye ya ci shirwa. Sarki Galbasa ya dubeta ya tuntsire da dariya yace,

"Ke yarinya daina É“ata lokacinki, babu wani irin tsafi da zai yi aiki anan in ba irin namu ba. Kin manta ne cewa a wata duniyar kuke dabam ba irin taku ba. Lallai zan tafi da ku izuwa fada ta, don na yi muku mugun kisa, sanadiyar É“arnar da kuka yi mini."

Sarki Galbasa na gama faɗin haka ya bada umarnin a ci gaba da shan jinin mutanen garin. Nan aka sa musu wawa tamkar an ajiyewa karnuka akan yankan nama guda đaya cal. Nan fa gari ya sake hargitsewa da iface-iface, sai dai ka ga jini na ambaliya da fantsamuwa tamkar teku ta ɓalle. Ana cikin haka ne Mazalish ta iso tamkar walƙiya. Cikin

abinda bai wuce daƙiƙa guda ba ta tsitstsinka igiyar da ta ɗaure su Jafar da ƙarfin tsafi, sannan ta sure su ta ɗora su a gadon bayanta ta kuma suri kibiya guda irin wacce Mashrila ta sa aka ƙera tare da da na'urar harbata, duk da hannu guda ta ɗora su a gadon bayanta kusa da su Jafar ta sake cillawa da gudu ta ɓace, a cikin sararin sama tamkar walƙiya.

Su dai su Jafar sai ganı suka yi sun daina hango birnin sarki Azbir gaba ɗaya. Suna cikin tafiyar ne Mazalish ta ce da su, "Kar ku yi zaton mun tsira da ni da ku. Daga yanzu zuwa kowanne lokaci za ku iya ganin mahaifina sarki Galbasa domin shi kaɗai ne zai iya cim mani. Ƙarfin gudunsa da ƙarfin damtsensa iri đaya ne da nawa, amma dai a cikin baradansa babu wanda zai iya zuwa nan ya riske mu. Abin da nake so da ku ku ɗora wannan kibiya akan na'urarta ku saita ta da zarar kun ganshi a bayanmu ku harbe shi. Lallai ku tabbata kun same shi a karon farko, in kuwa kuka kuskure tabbas dani da ku rayuwarmu na cikin haɗari."

Koda jin wannan batu, sai mamaki ya kama su Jafar gaba Ä‘aya. Yelisa tace, "Yake wannan maiya ke kuwa me ya sa kika ceci rayuwar mu alhalin kince ke 'ya ce ga wannan azzalumin sarki masha jini?"

Koda jin haka sai Mazalish ta ce, ''Ai kin san ruwa baya tsami banza don haka akwai dalilin faruwar hakan sai dai yanzu babu lokacin bayani,kuma ina son ku kwantar da hankalinku domin ni ba maiya ba ce, kamar mahaifina da jama'arsa. Ni mutum ce kamar ku amma zan yi muku bayani nan gaba in dai muna da sauran numfashi "

Ai kuwa Mazalish ba ta gama rufe bakinta ba, sai suka ga sarki Galbasa biye da su cikin tsananin gudu tamkar an harbo musu kibiyar tsafi.

Jikinsu Jafar na karkarwa suka shiga saita shi da kibiyar nan dama tun É—azun sun É—ana ta, amma da sun saita shi sai ya É“ace, ko kuma ya zama haske. Shi kuma sai ya dunga harbo musu kibiyoyin tsafi da wutar tsafi ba don Mazalish na zillewa da gocewa ba da tuni sun hallaka gaba É—ayansu. Kai in da a ce mutum na ganin wannan artabu sai ka yi zaton kare ne ya biyo kyanwa a tsiyace, tana neman tsira da rayuwarta. Sai da aka shafe sa'a biyar cur ana wannan gumurzu sarki Galbasa bai cim musu ba,suma ba su sami damar harbinsa da kibiyar ba.

Ba zato ba tsammani sai wutar tsafin Galbasa ta fara ƙona su Jafar. Sai da ya zamana babu wanda bai ƙone ba daga cikinsu. Yayin da Mazalish ta tabbatar da cewa in dai aka ci gaba da wannan gumurzu a haka Galbasa zai samu nasarar hallaka su sai ta juyo cikin shammace da zafin nama ta kama bakin kunamar harba kibiyoyin nan da hannunta ta saita mahaifinta ta sakar masa harbi a tsakiyar ƙirjinsa. Nan take kibiyar ta huda ƙirjinsa ta ɓulla har gadon baya, sai ji suka ji ya kurma uban ihu, sannan yayì ƙasa luuu.......

Tun suna hango shi har ya ɓace musu da gani. Dama a wannan lokaci Mazalish ta tsaya cak a sararin samaniya. Nan take idanunta suka ciko da ƙwalla ta fara zubar da da hawaye. Kafin waninsu ya ce wani abu ta fashe da kuka tana mai nadamar abin da ta aikata. A daidai wannan lokacin ne shi ma sarki Azbir ya fashe da kuka, Jafar ya dafa kafaɗarsa yace, "Ya kai wannan sarki ina dalilin kukanka?"

Azbir ya yì ajiyar numfashi ya ce, ''Ba komai ne ya sani kuka ba face sanin cewa a halin yanzu gaba đayan mutanen ƙasa ta sun zamą mayu domin na tabbata babu wanda zai tsira daga sharrin mutanen Galbasa, nì kam na san bani ba komawa ƙasata har abada, shi kenan na rasa iyalina, dangina,mutanena, mulkina da ƙasata."

Yayin da sarki ya zo nan a zancensa, sai tausayi ya kama su Jafar gaba đaya. Ita kuwa Mazalish sai da ta ci kukanta ta ƙoshi, sannan ta ci gaba da tafiya a sararin samaniya, tana đauke da su Jafar a gadon bayanta.

Ba ta gushe tana tafiya ba, sai bayan sun shuɗe sa'a bakwai, sannan ta sauko ƙasa suka a tsakiyar wani irin jeji mai ababan al'ajabi kala-kala.

Bayan su Jafar sun sauka daga kanta, sai ta girgiza ta dawo cikakkiyar siffa irin ta mutane sosai. Mazalish ta dubi su Jafar har yanzu hawaye na zuba a idanunta tace, "Yanzu na dawo cikin ainihin halitta ta siffar da kuka ganni da ita É—azu ba komai ba ce face sirrin tsafi."

Yayin da Mazalish ta zo nan a zancenta, sai Jafar ya dubeta yace, "Yake 'yar uwa ya akai kika zama mutum kamar mu alhalin kin kasance jinsin mayu?"

Nan Mazalish ta basu labarin yadda aka yi mahaifinta ya cire mata maita da kuma yadda ya bata rabin ƙarfin damtsensa da rabin tasirin tsafinsa.

Jafar ya sake duban ta ya ce, "To mene ne dalilin da yasa kika ceci rayuwarmu kuma har kika harbi mahaifinki da hannunki?"

Koda jin wannan tambaya sai Mazalish tayi ajiyar zuciya sannan tace, ''Ba wani abu ba ne ya sa na ceci rayuwarku face hujjoji guda biyu. Huja ta farko itace mahaifina ya bayar da ni ga wani bafadensa wanda na tsana fiye da komai a rayuwata.

Kuma na san cewa idan na aure shi har na sami ciki dole ne maita ta dawo jikina,ni kuwa da na zama maiya irin mahaifina da mutanensa gwara na rasa rayuwata. Hujja ta biyu ita ce kimanin shekaru biyar baya na taba ziyartar wani boka a wata babbar ƙasa na sanar da shi cewa ni kam na gama kewaye wannan duniya tamu amma ban ga wani namiji dana ji ina ƙaunarsa a zuciyata ba, har na iya aurensa, shin ina ne zan ga wanda zai iya aurensa? Lokacin da bokan ya ji wannan tambaya tawa sai ya ƙyalƙyale da dariya,sannan ya yi nuni da hannunsa izuwa ga wani ƙaton madubi sai ga hoton wani kyakkyawan saurayı yana gagarumin yaƙi tare da wani hamshaƙin barde kuma matsafi, a cikin wata duniya dabam ba irin wannan da muke ciki ba. Ina ganin wannan saurayı na ji ina mutuwar sonsa.

Boka Arjiwala ya dube ni yace, "Ya kika ga wannan saurayi kina sonsa?" Cikin tsananin murna nace ai tunda nake ban taba jin SO ya shiga zuciyata ba sai akan wannan saurayi, ya kai wannan boka maza ka sadani da duniyar wannan saurayi ni kuwa na saka maka da duk abin da kake buƙata iya tsawon rayuwarka. Boka Arjiwala ya sake bushewa da dariya yace, "yake wannan 'yar sarki ki yi sani cewa ba ni da ikon kai ki duniyar da wannan saurayi yake amma idan kika yi haƙuri nan da shekara biyar masu zuwa waɗansu mutane za su zo daga can kuma sanadiyar sune za'a yi gagarumin yaƙi tsakanin mutanen ƙasar sarki Azbir da mutanen ƙasarki,zaki rabu da mahaifinki da ƙasarki da kuma wannan duniya amma idan kina son ki je ki ga wannan saurayi wanda zuciyarki ta kamu da son sa sai kin ceci rayuwar waɗannan baƙin mutane, ki sani cewa hanyar da suka bi suka zo hanya ce mai matuƙar wahala, domin ta cikin wani sihirtaccen littafi ne da ake kira KUNDIN TSATSUBA ba kuma za su fita daga cikin sa ba,su koma duniyar su sai bayan shekara ashirin daidai. Za su yi ta ziyarar duniyoyi iri-iri ne suna shiga masifu kala-kala."

Lokacin da boka Arjiwala ya zo nan a zancensa sai na dube shi cikin matuƙar damuwa nace, "Ya kai wannan boka ka yi sani cewa koda zan tsufa tukuf a yawan neman wannan masoyi nawa ba zan kasa ba. Zan jira waɗannan mutane nan da shekara biyar har su zo kuma zan jure kowacce irin masifa da zamu tunkara a cikin littafin KUNDIN TSATSUBA. Abin da nake so da kai shi ne kawai ka sanar da ni sunan wanann saurayi. Boka Arjiwala yayi murmushi yace, "sunansa Hubalru, kuma ya kasance ma'abocin wani addini da ake kira Musulunci. A yanzu haka yana tsakiyar soyayya da wata kyakkyawar mace wai ita gimbiya Sima." Koda jin wannan batu sai kishi ya turnuƙeni nace, "wacece kuma gimbiya Sima? Shin ta fini kyaune ko kowa mahaifinta yafi nawa ƙarfin mulki?"

Arjiwala ya ce ba ta fiki komai ba, amma za ku iya yin kunnen doki a fagen kyau. Babu ruwana da ita abin da na șani kawai koda zan zama baiwa mafi ƙasƙanci sai na auri Hubairu. Nan take na kawo alheri mai yawa na baiwa boka Arjiwala sannan nayi masa bankwana na tafi. Daga wannan rana na cigaba da jira har izuwa yau ranar da na sadu da ku."

Yayin da Mazalish ta zo nan a zancenta sai Jafar ya dubeta cikin mamaki yana mai tunani.

Mazalish ta dube shi tace, "Tunanin me kake yi?"

Jafar yace, "Ai sunan da kika faÉ—i na saurayin da kike so nake tuno mai shi. Tabbas mun san waye Hubairu kuma mun yi hulÉ—a da shi."

Koda jin haka sai murna ta kama Mazalish tace, "Ba ni labarinsa na ji."

Jafar yace, "Haƙiƙa ya cika kyakkyawa kuma cikakken jarumi ne, domin shi ne ya taimake mu ya kashe sarki Lu'umanu har muka samu damar sato wani aljani wai shi Markahul sabus wanda ya đauko mana kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce da ita ne muka buđe littafin KUNDIN TSATSUBA. Littafin daya zame mana alaƙaƙai kuma shine sanadin zuwan mu wannan duniya taku."

Koda jin haka sai Mazalish ta dubi Jafar cikin rashin fahimta ta ce, "Ban gane wannan jawabi na ka ba?"

Jafar ya nuna Mashrila ya ce, "Kin ga wannan a cikin KUNDIN TSATSUBA muka haÉ—u da ita,kamar yadda muka haÉ—u da ke."

Nan take Jafar ya kwashe labarinsu kaf tun daga farko, har ƙarshe ya sanar da Mazalish. Bayan ya gama ne ta cika da tsananin mamaki, kuma ta ɗauki alƙawarin tafiya tare da su har a gama karanta shafukan KUNDIN TSATSUBA, don ta haɗu da masoyınta jarumi Hubairu bin Mas'ud wanda ba ta taɓa ganinsa ba sai a madubin tsafi kusan shekaru biyar baya.

Bayan Jafar ya gama baiwa Mazalish labarinsu, sai suka miƙe gaba ɗaya suka nausa cikin wannan jeji suka yi ta tafiya ba tare da sanin inda suka dosa ba. Kwatsam sai suka ga wata rijiya,dama ƙishirwa ta addabe su.

Ita dai wannan rijiya tsohuwa ce ainun kuma an rufe ta da ƙaton murfin ƙarfe. A bakinta an yi rubutu da ruwan zinare kamar haka.

"BABU MAI BUƊE WANNAN RIJIYA YA SHA RUWAN CIKINTA SAI BAƘIN DA SUKA ZO DAGA WATA DUNIYAR."

Koda gama karanta wannan jawabi sai Jafar ya dubi Yelisa da Gulzum yayi murmushi ya ce, "Ai domin mu aka yi rijiyar nan. Yakai Gulzum maza ka buɗe mana mu sha ruwa ko ma huta da ƙishirwa."

Cikin fushi Gulzum ya ce, "Waye bawanka har da za ka bani umarni na bi?"

Koda jin haka sai Yelisa ta dakawa Gulzum tsawa, ta ce, "Daga yau umarnin Jafar umarnina ne,maza ka yi abin da yace."

Cikin hanzari da biyayya Gulzum yasa hannu ɗaya ya ɓanɓare murfin rijiyar da ƙarfin tsiya. Yana yaye shi wata irin iska mai tsananin ƙarfi tayi fitar burgu daga cikin rijiyar ta zuƙe Jafar,Yelisa, Gulzum, Mashrila da Mazalish, ta bar sarki Azbir shi kaɗai, su ka zama 'yan ƙanana suka shige cikinta, sannan murfin rijiyar ya koma ya rufe kansa. Azbir ya fashe da kuka.

Su Jafar dai ba su tsinci kansu a ko'ina ba sai a cikin ainihin tasu duniyar gaban KUNDIN TSATSUBA.

Har yanzu shafi na goma sha biyu ne a buɗe. Koda Mazalish ta miƙe ta ganta a cikin wata sabuwar duniya sai ta kama kalle-kalle kamar ɗan ƙauyen da bai taɓa shigowa birni ba.

Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar bayan sun shiga shafi na goma sha biyu a cikin KUNDIN TSATSUBA.


*****************************************


Al'amarin su Jarumi Hubairu kuwa lokacin da sarki Hudais ya haɗa shi da manyan dakarun Musuluncin nan don zuwa gidan bokanya Samaratu ɗauko gimbiya Sima wacce har yanzu tana nan a kwance tana barcin tsafi, saura 'yan sa'o'i kaɗan ta rasu in dai ba a tashe taba daga barcin. Sai suka ƙara himma wajen gudu da sauri a cikin samaniya.

Ba su isa gidan Samaratu ba sai da ya rage saura sa'a đaya da rabi gimbiya Sima ta rasa rayuwarta. Da zuwa suka iske hadiman Samaratu a shirye suna tsaron gidan. Da yake an fi ƙarfinsu. Nan da nan aka kashe su a cikin abin da bai wuce daƙiƙa ɗari da ashirin ba.

Daga nan su Hubairu suka shiga neman inda gimbiya Sima take. Ɗaki-ɗaki, lungu-lungu, sako-sako,nan ma sai da suka shafe sa'a guda da kusan rabin rabi na sa'a sannan suka risketa a cikin ɗakin tsafin Samaratu kwance bisa wani gadon ƙarfe wanda wata irin tsafaffiyar wuta ta kewayeshi sama da ƙasa. Hubairu ya ruga da gudu don isa gareta,koda yaje daf da gadon sai ja da baya da sauri saboda tsananin zafin wannan tsafaffiyar wuta domin ji yayi kamar naman jikinsa zai narke, koda ganin haka sai wani dakare waishi labahan yace, "ya kai Hubairu shin kamanta cewa mun shigo gidan ma'abota tsafine,lallai bazaka iya dosar wánnan gado ba face da neman tsari daga Ubangiji." Sa'adda Hubairu ya ji wannan batu sai kawai ya fara karanta addu'o'i,kai tsaye ya nufi wannan gado. Yayin da ya tunkare shi sai yaji zafin wutar na raguwa ya yin da yake kusantarsa, a hankali sai wutar ta rinƙa zuƙewa da kanta tana ƙanƙancewa,koda ya je daf da gadon kuwa sai wutar ta ɓace gaba đaya. Ba tare da ɓata lokaci ba Hubairu ya soma karanta addu'ar nan wacce sarki Hudes ya bashi yana tofawa a jikin gimbiya Sima.

Yana gama tofawa kuwa sai hannayenta da ƙafafunta suka fara motsi, daga can kuma sai idanunta suka buɗe a hankali. Cikin firgici ta miƙe zaune zumbur tana mai kalle-kalle, koda taga jarumi Hubairu a gabanta sai tayi hamdala ta rungumeshi cikin farin ciki sannan tace "ya kai masoyina ina wazirina Kuddaru,ina su Jafar, wai shin nan ma a ina muke, su waye waɗannan a tare da kai?" Ya yin da jarumi Hubairu ya ji wannan tambaya, sai ya janye jikinsa daga nata suka fuskanci juna sannan yace, "yake abar ƙaunata kiyi sani cewa yau kwananki casa'in da huɗu kina barci sai yau Allah ya nufa kika tashi, su kuwa su Jafar da wazirinki Kuddaru bansan a inda su ke ba,nima ina da sauran shan ruwa a duniya shi yasa muka sake saduwa." Cikin tsananin mamaki gimbiya Sima ta tattaro nutsuwarta ta ƙurawa Hubairu idanu ta ce, "Ban gane wannan batu na kaba.

Ya akayi nayi barci har na tsawon kwana casa'in da huɗu aini tsammani na duk bai wuce suman 'yan daƙiƙu bane." Hubairu ya yi murmushi sannan ya kwashe labarin duk abin ya faru garesu shi da waziri Kuddaru lokacin da sarki Lu'umanu yasa aka đauresu don ya hallakasu har mahaifinsa Mas'ud da aljani Abtarul Hudes suka kawo muşu ɗauki ya kawo izuwa lakacin da suka yi gumurzun faɗa shi da sarki Lu'umanu har a karo na biyu da yadda ya koyi yaƙi a wajen sarki Hudes har ya sami labarin inda take yazo yanzu don ceton rayuwarta. Koda Hubairu yazo ƙarshen labarinsa sai farin ciki ya lulluɓe gimbiva Sima ta fashe da kuka ta sake rungumeshi tana mai cewa, "da yardar Allah wannan karon babu mai rabamu har sai mun zama miji da mata." Sima ta ƙara da cewa, "kai amma fa lamarin sarki Lu'umanu akwai al'ajabi. Yanzu ashe bai mutu ba yana nan a raye. Ni fa a gaban idanuna ka karya masa wuya. Tabbas wannan mutum ya cika shaiɗani kuma hatsabibn matsafi."

Hubairu yace, "ƙwarai kuwa ai abin da na fahimta shine duk wannan artabun da nayi dashi ba dashi bane da wani aljanin dabam nayi. Gangar jikin tasa ce kawai amma ba ruhin saba ne. Yake masoyiyata ki sani cewa yanzu bamu da wani lokaci na doguwar hira zaifi kyau mu hanzarta tafiya."


Karanta>>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 4


Domin sauke Audio sai ku Danna hoton dake kasa 👇👇👇




Post a Comment

0 Comments

Ads