Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 3


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba

Book 1 

Part 3

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh


Al'amarin macen nan guda ɗaya wadda ta tsira daga harin kibiyar nan wadda Mashrila tasa aka ƙera, wato ɗaya daga cikin cikon mütum biyar na Galbasa, wacce ake kira Darzil sai ta ƙara ƙaimi,taci gaba da tafiya a sararin samaniya, har tsawon kwanaki bakwai sannan ta iso fadar Galbasa.

Sarki Galbasa na zaune bisa karagarsa ta mulki, fadawa sun kewayeshi, sai ga-Darzil ta faÉ—o gabansa tana haki da numfashi. Cikin fushi da zafin nama Galbasa ya cakumo gashin kanta ya kara fuskarsa daidai tata, ya ce, "Ke Darzil ina sauran abokan tafiyarki kuma ina mutane hamsin É—in da kuka saba kawo mini a kowanne mako?"

Cikin ƙarfin hali Darzil tace,

"Ya shugabana ka yi sani cewa wannan karon sabon al'amari ya faru domin wasu baƙin shaiɗanun mutane sun bayyana a birnin Azbir har sun ƙera wata ƙatuwar kibiya wadda ta hallaka abokan tafiyata da ƙyar na tsira da rayuwata."

Jin wannan batu sai Galbasa kwarara uban ihu, wanda ya sa fadar gaba É—aya yin girgiza.

Cikin tsananin fushi ya yi wurgi da Darzil tamkar yayi jifa da 'yar tsana,sannan ya É—auko wani zagayayyen farin dutse ya shafa shi da tafin hannun sa. Nan take hoton abinda ya faru tsakanin su Darzil da su Gulzum ya bayyana. 

Galbasa ya ƙarewa su Jafar kallo tsaf ya jinjina kai sannan ya waigo ya dubi babban bafadensa Barzuzu yace,

"Yakai Barzuzu ka yi sani cewa waɗannan baƙin mutane ba ƙananan shaiɗanu ba ne. Haƙiƙa mun fi ƙarfinsu to amma sun kasance masu matuƙar hikima. Lallai ina so ka je ka yi tunani akan yadda zamu iya hallaka wannan mugun makami da suka ƙirƙira domin mu, sannan mu yi gagarumin shiri mu je mu shafe garin gaba ɗaya yadda ko a tarihi ba za'a tuna da shi ba."

Yayin da Barzuzu ya ji wannan batu sai yace, "Ya shugabanmu yanzu don wannan ɗan makamin na su guda ɗaya zamu yi gayya da shiri. Ai ina tabbatar maka da cewa ni kaɗai ma idan ka turani zan iya hallaka su, na ƙone makamin na su."

Koda jin haka sai Galbasa ya yi murmushi ya ce, "Kai ƙaramin mayaƙi ne baka san tuggun yaƙi ba. Kar ka yi tsammani za su tsaya ne jira kawai,suma sabon shiri za su yi don sun tabbatar da cewa ba zan kasa ɗaukar mataki ba. Ka yi sani cewa waɗannan mutane sun karya mana darajarmu a wannan duniya tamu, domin fiye da shekaru dubu baya ba'a taɓa cinmu da yaƙi ba, don me za mu yi sakaci wasu mitsatsan mutane kuma baƙi daga wata duniyar su shigo har tamu duniyar su cimu da yaƙi. Lallai ka hanzarta yin abin dana umarce ka."

Barzuzu ya sunkui da kai ƙasa, ya ce, "An gama."

Barzuzu ya miƙe tsaye ya fice daga cikin fadar. Galbasa ya dubi Galadimansa ya ce, "Ya kai Hutum ka je kasa a yi shela a gari cewar ban ɗaukewa kowa wannan yaƙi ba, babba da yaro,mace da namiji. Lallai kowa ya fara shiri nan da kwana bakwai za mu ɗunguma ƙwanmu da kwarkwatarmu mu tafi birnin Azbir sai mun shafe garin gaba ɗaya, mun zuƙe jinin kowa da komai, kai ko tsuntsu guda ba zamu bari ba a garin face ya zama maye kamar mu."

Hutum ya risina, ya ce, "An gama ranka ya daÉ—e."

Nan take fada ta watse, kowa ya kama gabansa.

Lokacin da sarki Galbasa ya shiga cikin gidansa zuciyarsa baƙin ƙirin take, kuma tana tafarfasa kamar za ta faɗo ƙasa, sai ya iske matarsa Hatimal tare da kyakkyawar 'yarsa, Mazalish zaune sun yi jugum. Koda ganinsa sai Mazalish ta miƙe zumbur cikin yanayin damuwa ta tare shi, tana mai cewa,

"Ya kai Abbana wane irn yaƙi ne ya taso mana haka har da za ka ƙi ɗaukewa kowa da kowa yaro da babba?"

Koda jin wannan tambaya sai sarki Galbasa ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Yake 'yata mafi soyuwa a raina, kin sani cewa a duniyar nan tamu kaf babu abin da nake so sama da ke, saboda tsananin son da nake yi miki ne ya sa na raba ƙarfina da tsafina na baki rabi-rabi. Kuma saboda tsananin son da nake yi miki ne na cire miki maita ya zamana ke kaɗai kika fita dabam da kowa a garin nan. To ki ƙara sani ke ma ɗin ban ɗauke miki wannan yaƙi ba,domin da na yi asarar wannan yaƙi gwara na rasaki.

Asarar wannan yaƙi daidai take da asarar mulkina,ƙasata da al'ummata gaba ɗaya. Tabbas idan ba mu yi nasara a wannan yaki ba, shi kenan sai dai a tuno da mu a tarihi domin hatta ƙasar nan tamu shafe ta za'a yi."

Yayin da sarki Galbasa ya zo nan a zancensa sai hankalin Hatimal da na Mazalish ya ƙara dugunzuma fiye da da. Nan take idanun Mazalish ya ciko da ƙwallah, ta dafa kafaɗunsa da hannu biyu tace,

"Ya kai Abbana ka tuna cewa ni a iya sanina ban taɓa ganin jarumi mai tsananin ƙarfin damtse da iya yaƙi kamar ka ba. Haka kuma ban taɓa ganinbmashahurin matsafi irin ka ba, domin a matsayinka na bil'adama har takai cewa ka juye ka zama ruwa uku. Za'a iya kiranka aljani ko fatalwa ko maridi,domin ba ka mutuwa ko an kasheka tashi kake yi.

Ga shi shekarunka a duniya sun linka irin na bil'adaman wannan zamani, don na tabbata kafi shekara dubu biyu a duniya.

To don me wani mahaluƙi zai zo lokaci guda rana tsaka har ya firgitaka ka ce da jama'arka kowa ya fito yaki, bacin ni a zatona kai kaɗai ma zaka iya tashin ƙasa guda ta bil'adama?"

Sa'adda sarki Galbasa ya ji wannan tambaya daga bakin 'yarsa Mazalish sai ya yi shiru gami da sunkuyar da kai ƙasa, cikin yanayin damuwa, sannan yace,

"Yake 'yata ki yi sani cewa kamar shekaru goma sha tara baya lokacin da ya rage saura shekara ɗaya a haifeki na yi wani dogon nazari a cikin bincikena na tsafi na gano cewa akwai wasu irin mutane da za su zo daga wata sabuwar duniya dabam su yaƙe ni har su cini da yaƙi. Tabbas ba wasu ba ne waɗannan mutane face waɗanda zamu tunkara yanzu. Ina tabbatar miki da cewa siffofinki irin na waɗannan mutane ne domin in kikai tunani duk a ƙasar nan babu mai ƙaramin jiki irin na ki.

Babu irin ƙoƙarin da banyi ba akan na gano hanyar da zan bi na hallaka waɗannan mutane idan sun zo,amma na kasa. Da naga haka sai na ci gaba da bincike akan ya za'a yi na tsira da rayuwata idan sun zo ɗin, sai na gano cewa in dai ina son tsira saidai idan na haifeki na cire miki maita kuma na raba ƙarfin jikina da tsafina na baki rabi.

Tabbas indai ina tare da ke zan kuɓuta. Haka kuma na gano cewa a sanadiyar wannan yaƙi ne zan rabu da ke rabuwa ta har abada, amma ban ga yadda zamu rabu ba."

Ko da Galbasa ya zo nan a zancensa sai idanunsa suka kaÉ—a suka yi jawur, suka fara shirin zub da hawaye, ita kuwa Hatimal tuni ta fara kuka tun sa'adda ta ji batun ccwa za ta rabu da 'yarta. Mazalish ta rungume Galbasa tana mai rusa kuka, tace,

"Yanzu in na rasaka ina zan sami uba kamar ka?"

Koda ganin haka sai ita ma Hatimal ta ruga gare su ta rungume su gaba É—aya tana mai taya su kuka.

A can birnin sarki Azbir kuwa sai da aka kwana ana walimar farin cikin samun nasara akan mutanen Galbasa. Har aka ƙare walimar su Mashrila ba su saki jikinsu sosai ba, domin duba ɗaya za ka yi musu ka san cewa suna cikin damuwa, kai ko murmushin arziƙi ba sa iya yi, sai dai ka ga suna yaƙe. Ana ƙare walimar ne Mashrila ta ce babu wanda zai je ya kwanta sai dai a ci gaba da ƙera kibiyoyin nan da na'urorin harba su kuma ba za'a tsaida ba,dare da rana. Hakan kuwa aka yi domin sai da aka kwana shida ana wannan aiki har aka kai gacin ƙera kibiyoyi dubu ɗari uku da sittin da na'urorin harba su guda dubu ɗari shida da arba'in, wato dai na'urorin sun fi kibiyoyin yawa. Nan take aka ware mutane da yawa adadin yawan na'urorin aka koyar da su sarrafa na'urar da iya harba kibiya. Ba'a gama wannan shiri ba, sai a daren kwana na bakwai.

Yayin da dare ya raba, mutane sun gaji saboda gajiyar wannan gagarumin aiki da suka sha fama a dalilin hakanne aka fara tafiya ana kwantawa.

Mashrila,Jafar,Yelisa,Gulzum,sarki Azbir da manyan dakarun ƙasar kuwa basuje sun kwanta ba,duk sai suka hau kan na'urar harba kibiyoyi suka yi fako suna jiran farmakin mutanen Galbasa don sunsan ako yaushe suna iya zuwa. Da yawa daga cikin suma gyangyaɗi sukeyi, amma har gefin asuba basu ji motsin komaiba kuma kusan ko yaushe hankalinsu akan sararin samaniya yake, kai har gari ya waye rana ta buɗe sosai ba'aji komaiba ba kuma ba aga komaiba, wannan tasa mutane suka fara sakin jikinsu,Karfan yazo gaban sarki Azbir ya ce "Ya shugabana ina ganin Galbasa da Jama'arsa sun tsorata damu baza su sake kawo mana hariba." Koda jin wannan batu sai sarki Azbir ya turɓune fuska yace,

"Ashe baka da hankali to dakata na gayamaka kaji har abada karka saki jiki da abokan gaba komai shirinka da ƙarfin ka. Kai a tsammanika don munyi musu ɓarna zasu ji tsoronmune su daina zuwa. Dubi canfa kagani mutanen sune guda huɗu tsire da kibiyoyi a kwance,har yanzufa da ransu motsi sukeyi inda zasu iya cire kibiyoyin jikinsu da tuni sun halakamu, ina tabbatar maka da cewa tuni labari ya isarwa Galbasa kuma tabbas zaiyi shirin ɗaukar fansa. Babu mamaki yana kan hanyarsa ta kawo mana mamaya.........." Kafin Karfan ya ƙara buɗe baki yace wani abu sai suka ga

wasu abubuwa acan Æ™ololuwar sama kamar tsuntsaye. Saboda yawansu sun lulluÉ“e saman wajen gaba É—aya har sun dusashe hasken rana kuma sun tsaya cak su ba su sauko Æ™asa ba kuma basu Æ™ara yin samaba,nanfa kowa ya É—aga kansa sama hankali ya dugunzuma kowa ya fara faÉ—in albarkacin bakinsa,wasu suce ai tsuntsaye ne wasu kuma suce wannan dai wata sabuwar masifarce, cikin tsawa mashrila tace, "ku shashashai ku nutsu kowa ya É—ana kibiyarsa, waÉ—ancan abubuwan da kuke hangowa ba komai bane face gungun dakarun Galbasa." 

Koda jin haka sai kowa ya saita na'urarsa ta dubi sama cikin firgita, wasuma gashi sun É—ora hannayesu akan kunamar harbin amma hannayen na ta karkarwa saboda tsananin tsoro.

Maso abinka yafika dubara, a ɓangaren Galbasa da jama'arsa tunani sunyi tunani akan hanyar daza su ɓullowa makamin mutanen sarki Azbir wato sun samo dabaru guda biyu na lalata waɗannan manyan kibiyoyi. Abu na farko shine sun ƙera wata irin ƙatuwar garkuwar ƙarfe wanda aka yita da zallan ƙarfen đemon saboda girman garkuwar kowace ɗaya mutun ɗari tara da saba'in da bakwai ke riƙe da ita. Babu wani abu dazai iya bugun wannan garkuwa ya hudata. Abu na biyu sunzo da wata irin majajjawa itama mai girman gaske wadda zata iya haɗiye na'urar harba wannan ƙatuwar kibiya ta ɗauketa tayi sama da ita kuwa wannan majajjawar guda miliyan ɗaya da dubu ɗari uku da talatin da uku ce kowa ce majajjawa ɗaya mutum dubune ke iya sarrafata.

Bayan kamar daƙiƙa sittin sai kawai aka ga tsuntsayen nan na sama sunyo ƙasa riƙe da wasu manyan garkuwoyi irin wanda ba'a taɓa ganiba.

Koda suka zo ƙasa ƙasa sai akaga ashe mutanen Galbasa ne. Nanfa aka fara sakar musu manyan kibiyoyin nan amma a banza domin da kibiyoyin sunyi karo da garkuwarnan sai su ɓaɓɓalle,sukuwa mutanen Galbasa sai suka fara ɗauki ɗai ɗai sai dai kawai kaga sun suri mutum da hannu ɗaya sunyi sama dashi, cikin daƙiƙa guda sun zuƙe jininsa.

Nanfa gari ya hargitse aka fara iface iface da guje guje. Ana cikin hakane mutanen Galbasa masu majajjawa suka sauka ƙasa suma suka fara nasu aikin sai dai kawai kaga majajjawar ta nannaɗe na'urar harba kibiya da mutanen dake kai ta suresu tayi sama dasu ko ruɓurɓushinsu ba zai dawoba,wannan al'amari yasa hankalin su jafar ya dugunzuma suma bisa dole suka sauka daga kan na'urar harba kibiyoyin nan suka ruga izuwa ƙarƙashin ƙasa inda birnin ƙira yake don neman mafaka suka bar sauran jama'a a filin daga ana tayi musu ɗauki ɗai-ɗai.

Acan sararin samnan kuma sarki Galbasa tare da 'yarsa Mazalish da uwargidansa Hatimal da kuma manyan baraden yaƙin sane a tsaitsaye cak kamar gumaka suna jiran aka masu bayanin abin dake faruwa a ƙasa. Ai kuwa basu ɓata sama da daƙiƙa đari biyu da arba'in ba sai ga wani gwarzo da ake Gardus yayo sama ya dira a gaban Galbasa cikin yanayin girmamawa fuskar sa cike da annuri yace,

"ya shugabana ai muna samin gagarumin nasara akan mutanen nan kuma ina tabbatar maka da cewa nan da rabin sa'a zamu gama dasu gaba ɗaya,haƙiƙa kayan yaƙin nan da Barzuzu ya ƙirƙira sunyí babban tasiri." Koda jin wannan batu sai sarki Galbasa ya tuntsire da dariya cikin tsananin farin cikin ya dubi Gardus yace, "saboda wannan labari da ka kawo mini mai daɗi nabaka 'yata Mazalish muna komawa gida za'a ɗaura aurenku." Koda jin wannan batu sai Gardus ya ƙwala ihun farin ciki yayi sujada ga sarki Galbasa yana mai tayin godiya kamar bazai dainaba. Take ya buɗe fuka fukansa yayi ƙasa dan ya isa inda ake ta ɗauki ba daɗi.

Dama tuntuni gardus ya daɗe yana nuna wa Mazalish so da ƙauna amma sai aka sami akasi domin yadda ta tsaneshi haka ta tsani mutuwarta kai ko haɗa fuska tayi dashi to a wannan rana bazata iya ci da sha komai ba don tsananin ƙiyayya,kai ta kan kira wannan rana da muguwar rana ta rashin dace don koda tayi sharri zai zama mata. Babu irin baƙin cikin da Gardus baiyiba saboda ganin irin ƙiyayyar da Mazalish ke nuna masa har takai cewa kusan kullum sai yayi kuka ya zubar da hawaye dominta. A yau da Gardus yaji sarki Galbasa ya bashi Mazalish sai yaji kamar shine sarkin duniya.

A gaba dayan mayaƙan sarki Galbasa babu saurayi kyakkyawa mai matuƙar Jarumta kamarsa.

'Yan mata da yawa sun kashe kansu bisa sonsa,sai gashi gimbiya Mazalish bata da ra'ayinsa ko kaÉ—an.

Al'amarin da ya jefa gaba ɗayan mutanen ƙasar kenan a cikin al'ajabi duk sa'adda Galbasa yayi wa Mazalish batun aure sai tace dashi, "ya kai Abba na kabar wannan batu domin har yau banga ɗa namijin daya burgeniba, cikin matuƙar damuwa sarki Galbasa yakan tambayeta yace, "haba 'yata" yaushe ne zaki ga wanda zai burgeki tunda duk faɗin kasar nan tawa babu inda baki shigaba. Haka kuma babu wata ƙasa dake cikin wannan duniyar da baki shigaba, amma ace duk kyawawan samarin dake cikinsu da Jarumai da matsafa har yanzu baki ga gwaniba." Duk sa'adda sarki Galbasa ya faɗawa Mazalish wannan batu sai tayi murmushi tace, "yakai Abbana ina so ka tuna cewa bayan wannan duniya da muke ciki akwai wasu duniyoyin waɗanda kai kanka baka taɓa zuwaba. Tunda ban samu gwani anan tamu duniyar ba tabbas zan samu a wata duniyar. Abin da nake so dakai kayi mini uzuri domin ko mai na da lokacin sa.

Nayi maka alƙawari komai daren daɗewa zan samu gwanina.

Wannan batu na Mazalish na jeta sarki Galbasa cikin tsananin mamaki da damuwa to amma saboda tsananin sonta da yake ne ya ƙyaleta bai tilas ta mata auren doleba.

Ako ina ba'a rasa munafiki lokacin da sarki Galbasa yayiwa Gardus alƙawarin Mazalish sai wani bafade ya dubi Mazalish yaga idanunta sun ciko da ƙwallah ya tabbatar da cewa tana cikin baƙin ciki bisa hukunci da mahaifinta ya yanke, shi dai wannan bafade sunansa Dauduf. Take Dauduf ya matsa kusa da sarki Galbasa yayi masa raɗa a kunne yace, "ya sarkın sarakai ina sanar dakai cewa hukuncin dake yanke a kan Mazalish baiyi mata daɗi ba don naga ƙwallah a idanunta ina mai ba da shawara cewa a zuba a idanu akanta don karta sulale ta gudu ba'a sani ba, kasancewar ko kaɗan bata ƙaunar Gardus." Sarki Galbasa ya jijjiga kansa alamar cewa, wannan shawara ta shige shi, sannan shi ma ya yiwa Dauduf raɗa a kunne ya ce, "Na yarda da wannan shawarar ta ka ɗari bisa ɗari, kuma na danƙa tsaron Mazalish a hannunka, in ta ɓata kaima ka ɓata."

Dauduf yace, "An gama ya sarkin duniya."

Kawai sai ya koma bayan Mazalish ya ja dunga.

Tun lokacin da Dauduf ya dubi idanun Mazalish ya ga ƙwallar nan ashe ta lura da shi kuma tana nazarinsa don haka duk abin da ya gayawa sarki Galbasa cikin raɗa sai da ta aiyana shi a zuciyarta tamkar a fili suka yi maganar. Nan take Mazalish ta ce a ranta, "Komai za ka yi sai dai ka yi ni kam na gama yankewa kaina hukunci,na san abin da zan yi,da dai na auri Gardus gwamma na hallaka na yi asarar rayuwata gaba ɗaya."

Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin

Mazalish da mahaifinta sarki Galbasa a can ƙololuwar sama yayin da aka tafka yaƙi a birnin sarki Azbir.

Al'amarin su Jafar kuwa lokacin da suka shige ƙarƙashin ƙasa inda birnin ƙira yake, suka zube ƙasa suna haki cikin mugun tashin hankali,sai kawai suka ga sarki Azbir na tare da su, Koda ya haɗa idanu da Mashrila sai yace, "Yake ma'abociyar hikima yanzu dai kin ga irin dabarar da mutanen Galbasa suka zo mana da ita. Ma'ana sunzo da ƙatuwar garkuwa da ƙatuwar majajjawa waɗanda ke lalata kibiyoyinmu da na'urar harba su. Yanzu mene ne abin yi? Wace hikima za ki sanar damu,mu hanzarta amfani da ita domin nan da rabin sa'a kacal zasu gama da mu gaba ɗaya?"

Yayin da Mashrila ta ji wannan tambaya sai ta yi shiru tsawon daƙiƙa biyar tana tunani daga bisani ta dubi sarki Azbir tace, "Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa babu wata dabara face abu ɗaya. Abin kuwa shi ne in dai muna son mu samu galaba mu ƙwaci kan mu a hannun mutanan nan saidai mu ƙwaci majajjawar dake hannayensu mu yaƙe su da ita."

Koda jin haka sai ran sarki Azbir ya sosu yace, "Haba yarinya wannan wace irin magana kike ta rashin hankali, ta ya ya zamu iya ƙwatar makami a hannun mutanen Galbasa alhalin sun fi mu ƙarfi,kuma sun ninkamu girma sau goma."

Cikin fushi Mashrila ta nuna Azbir da hannu ta ce, 'Wace ce yarinya shin kana tsammanin za ka girme nine? Dube kafa kamar a kife da kwando!"

Koda jin haka sai Azbir ya yi murmushin ƙarfin hali, ya ce, ''Au dan kin ganni ɗan guntu shi ne kike tsammanin ke sa'a ta ce, ko kuwa don kin ga fuskata irin ta yara ce? To tsaya kiji a wannan watan da muke ciki na cika shekara dubu ɗaya da dari shida da hamsin. Wani matsafi a wata duniya da ake kira Makuk ya gaya mini cewa a wannan duniyar tamu babu wanda zai girme ni face sarki Galbasa."

Koda jin wannan batu sai jikin Mashrila yayi sanyi, ta kasa cewa komai. Gulzum ya dubi sarki Azbir yace, "Ka ga ku bar batun musun shekaru don na san a shekaruna baka ɗauki kaso ɗaya ba. Abinda nake so da kai shi ne mu yi amfani da shawarar yarinyar nan domin ita ce kaɗai mafita. Ku sani cewa a barin tayi akan bar araha, kuma da mu zauna a zo a ci mu da yaƙi gwara mu jarraba iya ƙoƙarin mu don wani lokacin sai an gwada ake dacewa, kuma ai himma ba ta ga rago. Ni na san na fiku ƙarfi da juriya don haka zan yi amfani da damata da kuma dabarun yaƙin da na koya irin namu na aljanu na ƙwato majajjawa ɗaya. In dai kuka ga na yi nasara to ku tsaya a bayana. Yanzu zan yi fitar burgu daga ƙarƙashin ƙasa, amma kar ku fito sai bayan daƙiƙa đari da ashirin."


Karanta>>> Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 4


Domin sauke Audio Sai Ku Danna Hoton Dake Kasa👇👇



Post a Comment

0 Comments

Ads