Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 2


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba

Book 1 

Part 2

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Posting: Abubakar Saleh

 Nan ta fadar ta ruɗe da shewar jama'a. Masu goyon bayan Yelisa na yi, masu goyon bayan Mashrila nayi,kai wasu ma sai suka fara caca, kowa ya zaɓi gwaninsa. Gulzum ya matso kusa da Jafar yace,

"Kai shegen duniya, amma fa ka yi tsiya yanzu duk saboda kai ake wannan tataɓurzar, yanzu a ganinka wacece za ta yi nasara?"

Jafar ya dubi Gulzum ya yi masa murmushi a karo na farko tun sa'adda suka haɗu yace,

"Babu wadda za tayi nasara sai mai rabo."

Gulzum ya yi dariya, sannan yace,

"To wa ka fiso ta samu nasara?"

"Duk su biyun nake so su sami nasara,amma in san samu ne a yanzu nafi ƙaunar Mashrila ta samu nasara."

Koda jin haka sai Gulzum ya turɓune fuska,ya ce, "Amma baka da mutunci yanzu duk irin son da maigidata Yelisa ta nuna maka a baya da irin taimakon da ta yi maka har ka mallaki KUNDIN TSATSUBA, duk ka manta har ka yi watsi da ita kafi son wacce ka gani daga baya a cikin halin wahalar da muka fara sha tare, tun kafin mu haɗu da ita."

Koda jin haka sai Jafar ya turɓune fuska, yace, "Kai Gulzum ɗan baƙin ciki ne kai, inda ka san dalilin da ya sa na fi son Mashrila ta ci wannan gasa yanzu da baka fadi haka ba."

Cikin tsananin fushi Gulzum ya dunƙule hannunsa ya ɗaga sama da niyyar ya daki Jafar, kawai kuma sai ya fasa, ya kama huci da ciza leɓe, cikin tsananin fushi. Shi kuwa Jafar ko gizau bai yi ba.

Jafar ya yi murmushi ya kau da kai ga barin kallon Gulzum yana mai cewa, "Me ya hana ka tatsice ni, ai da ka yi nadama irin wacce baka taɓa yin kamarta ba."

Duk da cewa Gulzum na cikin tsananin fushi bai san sa'adda da dariya ta ƙwace masa ba, saboda mamakin wannan batu na Jafar. Ba wani abu ba ne ya bashi mamaki face wai shin nadamar me zai yi dan ya kashe wannan banzan Jafar? Wanda ba zai iya tsinana musu komai a cikin wannan tafiya ba.

Asalima shi ne ya jefa su a cikin masifar KUNDIN TSATSUBA. Kuma duk bala'in da șuka shiga Jafar baya iya tare musu komai face ya ƙara janyo musu bala'in.

Gulzum ya ƙudurce a ransa cewa duk  ranar da suka gama karanta KUNDIN TSATSUBA, sai ya tambayi Jafar wai shin wace nadama zai yi don ya kashe shi?

"Ka ci albarkacin uwagidana Yelisa na san idan na kashe ka ta rasa masoyi kuma har abada ba zata yi min afuwa ba,ƙarshe ma ta halaka ni."

Gulzum ya faɗi cikin alamun takaici. Jafar yace,

"To me zai hana in ka kashe ni itama ka kashe ta ka ga shi kenan ka huta da fargabar komai,tunda yanzu tsafi baya tasiri sai ƙarfin damtse?"

Gulzum ya yi murmushi, ya ce, "Kai yaro ne abin dana hango baka isa ka hango shi ba, idan na kashe ku yanzu ai na rasa abokan tafiya ni kaɗai zanci gaba da shan azabobin cikin KUNDIN TSATSUBA,kaga kuwa ai ance mutuwar yawa kaka ce,haka kuma ni na san in dai na kashe Yelisa koma daren daɗewa sai mahaifinta ya ɗauki fansa, kai nifa ba wawa ba ne da hankalina, na kan yi tunani kafin nayi abu."

Lokacin da Yelisa ta ga Mashrila na neman jefota ƙasa, sai ta yi amfani da ɗaya ƙafarta tana ta dukan fuskar Mashrila. Koda Mashrila taji raɗaɗin zafi a fuskarta ta sai ta sake ƙafar Yelisa.

Cikin sauri Yelisa ta ci gaba da ƙoƙarin hawa saman kejin don ta isa inda takobin nan take.

Yayin da Mashrila ta ɗaga kanta sama ta ga Yelisa tayi mata nisa,sai hankalinta ya dugunzuma. Ba zato ba tsammani sai aka ga Mashrila ta kama tsalle tana hawa saman kejin ba tare da taka ƙarafan ba da ƙafafunta tamkar biri. Al'amarin ya yi matuƙar baiwa kowa mamaki kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci ta riski Yelisa.

Nan fa suka kacame da sabon faɗa, wannan ta naushi wannan, kai suka yi ta bugun juna hannu da ƙafa. Sai da suka shafe rabin sa'a suna gumurzu ya zamana sun galaɓaita tare. Ana cikin haka ne Yelisa ta suɓuto ƙasa. Koda ganin haka sai Jafar ya kurma ihu, cikin firgici don ya tabbatar da cewa in dai ta faɗo ƙasa daga nisan saman kejin ta zama gawa.

Tuni a wannan lokaci Jafar ya runtse idanunsa ya fara kuka, amma bisa mamaki sai ya ji gaba ɗayan fadar ta yi tsit, tamkar babu wani abu mai rai a cikinta. Cikin hanzari Jafar ya buɗe idanunsa kawai sai ya ga Gulzum a cikin kejin Yelisa na shimfiɗe akan tafin hannunsa guda tana haki.

Ashe mamakin zafin naman Gulzum ne ya sa jama'a suka yi tsit. Kafin Yelisa ta fado ƙasa tuni ya ruga ya banke ƙofar kejin ta ɓalle ya shiga sannan ya tara hannunsa ta faɗo a kai. Nan take fadar ta ruɗe da shewa da tafi, ana yiwa Gulzum jinjina. Ita kuwa Mashrila tuni ta ɗauko takobin nan har ta sauko ƙasa,lokaci guda suka fito daga cikin kejin gaba ɗaya.

Sarki Azbir ya miƙe daga kan karagarsa ya tari Mashrila ya karɓi takobin sannan ya jata izuwa wata kujera da ke daf da karagarsa ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna.

Zaman sa ke da wuya ya dubi sauran jama'ar fadar yace,

"Yaku jama'a ku yi sani cewa a halin yanzu Mashrila ta ci gasa don haka ta warware gardamar ta tsakanin ta da Yelisa. Tabbas ta samu damar sanar da mu hikimar da ke ranta wacce da ita ne zamu samu nasara akan maƙiyan mu,kuma idan har muka yi amfani da hikimar aka dace zata shugabanci su Jafar yayin da suka ci gaba da tafiyarsu. Yake Mashrila yanzu ke muke sauraro sai ki sanar da mu wannan hikima ta ki."

Koda sarki Azbir ya zo nan a zancen sa sai fadar ta sake yin tsit, kowa ya kasa kunnuwansa aka ƙurawa Mashrila idanu. Ita kuma Yelisa wacce ke zaune a gefe kusa da Jafar sai hararar Mashrila take zuciyarta na tafarfasa, kamar ta miƙe ta je ta rufe ta da duka.(😅😅😅su Yelisa iyayen kishi,inye kaga mai masoyi😝😝).

Mashrila ta yi gyaran murya, sannan tace,

"Hanyar da ta dace ta samun nasara akan mutanen Galbasa, kamar yadda kuka yi sani cewa makami baya tasiri a jikinsu haka kuma wuta bata ƙona su,wato dai a taƙaice basa mutuwa, komai aka musu a suna iya tashi.

To ga dabara guda ɗaya,ina so a ƙera kibiyar ƙarfe mai kaurin bishiya kuma mai akwa tsananin nauyi wacce za'a rinƙa harbata daga jikin akwatin ƙarfe, mai kama da nau'ura, ina son karshen kibiyar ya kasance dunƙulallen ƙarfe ne mai faɗi da surar faranti.

Na tabbatar idan aka harbi mutanen Galbasa da wannan kibiya za ta iya fasa cikinsu ko ƙirjinsu ta ɓullo gadon bayansu. Na tabbata ba za su iya zare kibiyar ba daga jikinsu saboda kaurinta da nauyinta.

Kun ga daga sannan sai mu yi ta jarraba hanyoyin hallakar da su har mu dace, tun da ba za su iya guduwa ba, ba za su iya ceton kansu ba."

Koda Mashrila ta zo nan a zancenta, sai mamaki ya kama kowa da kowa, har shi kansa sarki Azbir. Fadar ta sake yin tsit aka rasa wanda zai ce uffan kowa sai tunanin al'amarin yake a zuciyarsa.

Ita kanta Yelisa duk da tana adawa da Mashrila sai da jikinta ya yi sanyi, don ta tabbatar da cewa haƙiƙa Mashrila ta zo da babbar hikima.

Sarki Azbir ya miƙe tsaye, ya yi tafiya yana mai kaiwa da komowa a gaban Mashrila, sannan ya tsaya cak ya fuskanceta sosai yace,

"Yake Mashrila haƙiƙa kin zo da dabara babba to amma fa ki sani cewa bana zaton maƙerana suna da hikimar da za su iya ƙera wannan kibiya da na'urar harbata a cikin kwanakin nan biyu kacal, da suka rage mana."

Koda jin haka sai Mashrila ta yi murmushi tace, "Abin da na ke so da kai kawai kasa a kaini maƙerarku kuma a sanar da maƙeran cewa duk umarnin da na basu su bi ba musu, ko gardama,kuma zan yi aiki tare da su dare da rana."

Sarki Azbir yace, "Wannna mai sauƙi ne."

Nan take aka kira wani mutum wai shi Karfan wanda shi ne sarkin maƙera aka haɗa shi da Mashrila kuma aka umarce su da tafiya maƙera.


#########################

Jafar ya dubi Mashrila yace,

"Ina neman alfarmarki ki amince mu biku ni da Yelisa da Gulzum koma ƙaru da irin hikimarki da basirarki.''

Mashrila ta yi murmushi tace, "Wannan ai ba matsala ba ce ai dama bai kamata a ce baku ga komai ba da idanunku. Babu mamaki ku sami basirar kare mu daga wata masifar ta nan gaba albarkacin wannan basirar tawa."

Ba tare da ɓata lokaci ba Karfan ya wuce gaba Mashrila,Yelisa da Gulzum suka bishi a baya.

Bayan fitarsu daga cikin fadar sai da suka yi tafiya mai nisan rabin zango, sannan suka iso bakin wata kullaliyar rijiya. Da zuwa sai Karfan ya zaro wata kuba daga cikin aljihunsa ya buɗe rijiyar, kawai sai suka ga ashe matattakala ce a ciki, kai tsaye Karfan ya sanya ƙafafunsa ciki ya kutsa kai ciki ba tare da fargabar komai ba, su Jafar suka bi bayansa.

Koda suka gama ƙure matattakalar, sai suka tsinci kansu a cikin wani sabon babban gari wanda ya ninka inda fadar sarki Azbir take sau uku.

Babu komai a garin face maƙera da kayan ƙira,ga jama'a nan fululu amma babu guda ɗaya mai zaman banza,kowa ka gani a cikin aikin ƙira yake mazan su da matansu, yara da manya.

Lokacin da Karfan ya fuskanci cewar su Jafar sun zama 'yan ƙauye don banda kalle-kalle da al'ajabi babu abin da suke yi sai ya ƙyalƙyale da dariya ya dube su, yace, "Ina yi muku marhaban da shigowa birnin ƙirarnmu, ku yi sani cewa fiye da shekaru dubu baya haka wannan birni yake a kullum dare da rana. Babu wani kalar ƙarfe da babu shi anan kuma muna iya sarrafa shi izuwa duk abin da muka so."

Nan fa suka yi ta shiga saƙo-saƙo, lungu-lungu, gida-gida suna kalle-kallen kayayyaki iri-iri har da masu ɗumbin tarihi. Bayan sun gama kewaye ne Mashrila ta sa aka kawo mata tahuda da alƙalami da takarda, ta zana taswirar wannan ƙaton mashin da na'urar harba shi.

A wannan lokaci gaba ɗayan manyan maƙeran mafiya basira sun kewayeta, koda suka ga taswirar sai duk suka kiɗime saboda tsananin mamaki. Nan fa kowannansu ya shiga faɗin albarkacin bakinsa. Wani ya ce zai iya kera kibiyar a cikin wata biyu, wani sati biyu, ita kuwa na'urar babu wanda ma ya ce zai iya ƙerata a cikin wata uku.

Yayin da hayaniyar maƙeran ta yi yawa sai Karfan ya daka musu tsawa, kowa ya yi shiru,sannan yace, "Yaku mutanen birnin ƙira ku yi sani cewa ban taraku anan don ku yi hayaniya da faɗin abin da kuke so ba, sai don kawai ku bi umarni.

Abin da nake so da ku kawai shi ne ku yi abin wannan yarinya Mashrila ta umarce ku."

Karfan na gama jawabi ya juya ga Mashrila yace, 

"Mene ne abin yi?"

Ba tare da ta ce uffan ba, ta shiga ware maƙeran nan ta kasa su izuwa kaso uku. Kaso na farko su ne mafīya basira don haka sai ta dube su tace, "Ku na zaɓa ku ƙera mini na'urar harba kibiyar,ina son ku haɗa basirarku waje guda kuma kada ku yi komai face abin da na yi muku nuni da yi."

Mashrila ta dubi kaso na biyu tace, "Ku kuma ku na zaɓa ku ƙera mini wannan babbar kibiya, kuma ku yi amfani da umarnina kawai. Ku kuma kaso na uku ba za ku yi komai ba, face zuwa ɗebo irin ƙarafunan da na umarce ku."

Nan take Mashrila ta fara zayyana musu irin ƙarafan da take buƙata da kuma irin kayan aikin da take buƙata. Sai da ta lissafa ƙarafa kala ɗari uku arba'in sannan ta lissafa kayan aiki kala ɗari bakwai da sittin da huɗu. Al'amarin da ya matuƙar ɗaure kansu Jafar kenan, suka yi ta mamakin ya akayi Mashrila ta san harkar ƙira haka. 

Kai bama su ba,su kansu maƙeran sun tsorata da al'amarin Mashrila, domin waɗansu kayan aikin ma ko sunansu basu taɓa ji ba, sai a bakinta kuma ba sa ganewa sai tayi musu kwatance da cikakken bayani.

Nan da nan kaso na uku suka baza neman ƙarafa da kayan aiki. Ai kuwa rabin sa'a bata cika ba,suka zo da dukkanin abin da ake buƙata. Nan take Mashrila ta shiga basu umarni ta nuna musu yadda za'a sarrafa ƙarafan. Masu aikin kibiya na yi,masu aikin na'urar harba kibiya na yi.

Haka dai aka ci gaba da aiki ba dare ba rana har tsawon kwana guda da yini ɗaya. A sannan ne aka kammala ƙera na'urar kuma aka kammala ƙera ƙatuwar kibiyar guda biyar. Koda su maƙeran da su Jafar suka dubi waɗannan abubuwa da aka gama ƙerawa sai suka ruɗe da shewa aka ɗaga Mashrila sama ana yi mata jinjina.

Koda jiwo shewarsu sai sarki Azbir da sauran jama'ar garin suka rugo izuwa cikin birnin ƙira, don su ganewa idanunsu abin da aka ƙera.

Kowa ya zo ya ga kibiyoyi biyar da na'urar harba su sai ya yi turus ya zama cikakken ɗan ƙauye. Ita dai na'urar babbace ainun kuma za'a iya ɗana gaba ɗaya kibiyoyi biyar a jikinta. A jikin na'urar akwai wani kwarkwaro wanda ake wana shi, yana nannaɗe da wata igiya wadda ita ce ke taɓe kibiyoyin,sannan akwai kunama a ƙasan kowacce kibiya wacce da zarar mutum ya jata sai ka ga kibiyar ta yi fitar burgu.

Sarki Azbir ya dubi Mashrila yace, "Yake wannan yarinya mai dumbin basira haƙiƙa mun ga aikinki, kuma ya yi kyau mun gamsu da cewa wannan makami zai ya yin tasiri akan mutanen Galbasa. To amma muna son a yi gwaji don mu sami nutsuwa."

Koda jin haka sai Mashrila ta yi

murmushi tace, "Ɗauko kibiyoyin a aza su akan na'urar, kuma a ɗana su."

Sannan a fito da na'urar izuwa saman gari inda fadar sarki Azbir take. Nan fa ma'aikata suka karɓi umarni. Kowacce kibiya guda sai da mutum hamsin majiya ƙarfi suka taru, sannan suka iya ɗaukarta. Da ƙyar aka ɗorata akan ƙatuwar na'urar mai ƙafafun keken doki. Sannan aka tura izuwa fadar sarki Azbir. Sai da aka zo tsakiyar fadar sannan aka ajiye na'urar. Mashrila ta yi umarni kowa da kowa ya koma gefe guda, sannan ta hau kan na'urar ta zauna. Ta saita wata ƙatuwar bishiya mai tsananin kaurin gaske da tsawo ta sakar mata kibiya guda. Tamkar tauraruwa mai wutsiya haka ƙatuwar

kibiyar ta yi fitar burgu ta je ta sami tsakiyar bishiyar ta huda ta ta ɓullo ta can ƙarshen ta. Saboda ƙarfin harbin da kuma kaurin kibiyar sai da bishiyar ta ɓaɓɓako daga cikin ƙasa gaba ɗaya,jijiyoyin suka tunɓuko waje ta faɗi ƙasa rikica.

Nan fa jama'a suka ruga gaban bishiyar suna kallon abin al'ajabi. Sai da aka shafe sa'a uku cur ana ƙoƙarin zare kibiyar daga jikin bishiyar. Da ƙyar da siɗin goshi mutum ɗari biyu suka haɗa ƙarfi suka zare kibiyar, suna gama zareta bishiyar ta ratattake.

Koda ganin haka sai gaba ɗaya mutanen garin suka ɓarke da shewar farin ciki. Ita kuwa Mashrila wadda ke zaune akan na'urar sai murmushin murna kawai take yi.

Sarki Azbir, Jafar, Yelisa da Gulzum kuwe duk sun kasa rufe baki don tsananin mamaki da al'amarin Mashrila. Ana cikin wannan hali ne kawai aka ji wata gagarumar guguwa ta taso daga sama.

Koda jin guguwar nan sai gari ya hargitse, jama'a suka fara guje-guje da iface-iface, shi kansa sarki Azbir wurgi ya yi da hular sarautarsa ya cika wandonsa da iska. Cikin hanzari Mashrila, Yelisa,Jafar da Gulzum suka ɗaga kawunansu sama ai kuwa sai suka yi arba da su. Ba wasu ,ba ne face mutanen Galbasu mutum biyar.

A rayuwar Gulzum ta duniya bai taɓa ganin ɗan adam mai siffa irin ta waɗannan mutanen ba.

Domin girmansu ya kai girma. Suna da manyan fükafukai tamkar na jemagu masu tsananin ƙwari,domin da zarar sun bugi ginin gidaje da fukafukan sai ka ga gidajen suna rushewa. Kuma ko iskar bakin su suka huro sai ka ga ta kwashi mutane sama ta fyaɗa su a jikin gini.

Mutanen sun kasance da siffofin mata suna da dogayen gashi da cikakken ƙirji amma zanƙala-zanƙalan hannayensu da faratansu sun kara musu muni ainun. Haka kuma haƙoransu zaftara-zaftara ne masu tsini tamkar allura. Nan fa suka fara ɗauki ɗai-ɗai sai dai ka ga sun cafko mutum kamar kare ya danƙi kyanwa. Da zarar sun kafa haƙoransu a wuyan mutum sai ka ga sun zuƙe jinin jikinsa nan take.

Koda ganin abin da ke faruwa sai Jafar,Yelisa da Gulzum suka ruga kan na'urar inda Mashrila take suka zauna tare da ita, ita kuwa dama tuni ta fara ƙoƙarin saita su da kibiyoyin. Yayin mutanen Galbasan suka hango wannan na'ura waɗanda ke kanta kuma suka fuskanci manufarsu suka rinƙa huro musu iskar bakinsu, saboda ƙarfin iskar sai na'urar ta kama katantanwa. Take iskar tayi wurgi da Mashrila,Jafar da Yelisa ta maka su a jikin bango suka zube ƙasa sumammu.

 Gulzum ne kawai ya rage akan na'urar shi ma don yana da ƙarfi ne sosai,kuma ya riƙeta gam iya yinsa.

Har yanzu mutanen Galbasan ba su daina ɓarna ba. Kai ko ƙarƙashin ƙasa mutum ya shiga saidai ka ga sun soka hannunsu cikin ƙasar sun zaƙulo shi, sun zuƙe masa jini. Mutane kuwa ba su fasa gudu da îhu ba. Cikin tsananin juriya Gulzum ya saita ɗaya daga cikin mutanen Galbasan ya sakar mata kibiya. Ai kuwa aka yi sa'a kibiyar nan ta nutse a tsakiyar ƙirjinta ta hudo gadan bayanta, ta faɗo ƙasa tana kururuwa. Idan ta yi kururuwa sai kaga wuta na fita daga bakinta. Ta yi, ta yi iya ƙarfin ta akan ta zare kibiyar daga jikinta ta kasa.

Koda ganin haka sai sauran 'yan uwanta mutum hudu suka kai mata ɗauki suma suka yi iya yinsu suka kasa cire mata kibiyar,suna cikin ƙoƙarin hakan ne Gulzum ya sake harbo kibiyoyi biyu,yayi nasarar cake biyu daga cikinsu suka zube ƙasa suna gurnani da kururuwa. Guda biyun da suka rage suna ganin abin da ya faru ga 'yan uwansu suka firgice suka yi sama da niyyar guduwa.

Nan ma Gulzum ya ɗaga na'urar nan sama ya saito ɗaya daga cikinsu ya harbota ta faɗo ƙasa.

Ita kuwa ɗayar tuni ta ƙule a cikin sararin samaniya.

Gulzum ya ciza leɓensa cikin tsananin baƙin ciki yayi takaicin ƙarewar kibiyar akan nau'urar,domin inda akwai sauran kibiya da guda ɗayar ma ba ta tsira ba. Dama kibiyoyin guda biyar ne kacal kuma an yi amfani da guda ɗaya sa'adda aka yi gwaji akan ƙatuwar bishiyar nan ta kuka.

Koda aka ga babu sauran mutanen Galbasa sai mutane suka dawo cikin hayyacinsu. Nan da nan sarki Azbir ya sa aka tattare gawarwakin mutanen da aka shanye jininsu aka bunka musu wuta. A lokacin ne su Jafar suka farfaɗo daga doguwan suman da suka yi, suka ga sarki Azbir da jama'arsa sun taru a waje guda sunyi zugum-zugum suna kallom mutanen Galbasa guda huɗu waɗanda ke kwance kibiya ta tsire su har yanzu ba su daina kururuwa ba,kuma ba su fasa ƙoƙarin cire kibiyoyin ba, amma sun kasa.

Koda Jafar ya ga ana ƙona gawarwaki sai ya ruga gaban sarki Azbir yace, "Yakai wannan sarki ina dalilin ƙona waɗannan gawarwakin?"

Sarki Azbir yace, "Ashe ka manta da

bayanin da na yi muku tun a farko. Ai idan ba mu ƙone su ba,suma zasu zama irin mutanen Galbasa ne su zoƙe mana jini."

Azbir ya dubi Mashrila ya ce, "Yanzu ya zamu yi da waɗannan mutanen Galbasan waɗanda ba su mutu ba, kuma ba su kasance rayayyu ba, tun da ba za su iya tsinana komai ba?"

Mashrila ta yi ɗan jim, ta ce, "Babu abinda zamu iyayi akan su face sa ido domin zamu iya aikata kuskuren da zai janyo su tashi."

Azbir ya yi ajiyar zuciya, sannan ya sake duban Mashrila yana mai murmushi, yace, "Godiya gareki ya ma'abociyar hikima, haƙiƙa kin cece mu daga shairrin mutanen Galbasa. Yanzu zan bayar da umarni a shirya ƙasaitacciyar walimar girmamawa a gare ki,saboda wannan gagarumar nasara da kika kawo mana, kuma a wajen walimar ne zamu gabatar da babbar kyauta a gare ki da kuma ta Aljani Gulzum bisa ƙoƙarin da ya yi na harbo waɗannan mutanen Galbasa guda huɗu."

Koda jin haka sai mutane suka ɓarke da shewa. Cikin hanzari Jafar ya kama mumbarin ya hau can sama, sannan ya ɗaga hannu sama. Take wurin ya yi tsit.

"Ku yi sani cewa da ku da mu baƙin ku muna cikin mugun haɗari. Ku tuna cewa ɗaya daga cikin mutanen Galbasa ta tsere,kuma tabbas zata je ta sanar da Galbasa abinda ya faru ga 'yan uwanta.

Shin bakwa tsammanin cewa Galbasa zai yi gagarumin shiri ya taho da kansa ya zo ya ƙarar da mu gaba ɗaya,tun da ya san cewa in ya ƙyale nan gaba ma za'a iya yiwa jama'arsa ɓarna?"

Sa'adda Jafar ya zo nan a zancesa, sai hankalin kowa ya tashi aka fara kace-nace. Koda ganin haka sai sarki Azbir ya miƙe ya ce, "Yaku jama'ata haƙiƙa batun wannan yaro gaskiya ne,amma ina son kowa ya kwantar da hankalinsa domin kafin labari ya riski Galbasa sai nan da kwana bakwai. Kun ga ashe muna da isasshen lokaci na tunanin abin yi."

"A'a ranka ya daɗe bamu da wani lokaci lallai tun daga yanzu ya kamata mu fara shirye-shiryen tunkarar gagarumin yaƙin da ke gabanmu."

Koda jin haka sai sarki Azbir ya yi

murmushi ya dafa kafadar Jafar, ya ce,

"Yaro kar ka damu babu abin da zai faru."

Nan take aka fara kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, masu shirya walima kuwa suka tafi suka fara aiwatar da aikinsu. Jafar, Yelisa,Mashrila da Gulzum kowa suka yi zugum cikin tsananin damuwa. Ita kanta Mashrila da Gulzum kuwa waɗanda ya kamata su fara farin cikin walimar da aka shirya musu sai suka kasance masu taya su Jafar jimami.

Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar yayin da suka faɗa cikin wani gari shafi na goma sha biyu na KUNDIN TSATSUBA.


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 3


Domin Sauke cikakken Audio sai ku danna hoton dake kasa 👇👇Post a Comment

0 Comments

Ads