Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 1


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba

Book 1 

Part 1

Author: Abdulaziz Sani Madakin Gini

Typing: Abubakar Saleh


*****************************************

Bayan iskar KUNDIN TSATSUBA ta gama zuƙe su Jafar, sun faɗa cikin shafi na goma sha biyu, sai suka tsinci kan su a tsakiyar wani makeken gari mai manya-manyan gine-gine iri-iri na zamani. Wasu gidajen an gina su ne da dutse zallah wasu da ƙarfe wasu kuma da itatuwa. Duk ginin da ka duba sai ka kamu da sha'awarsa saboda tsananin kyawunsa da irin hikimar da aka yi wajen gina shi.

Dirar su Jafar ke da wuya a cikin garin sai ga jama'a na ta ɓulɓulowa daga cikin gidajensu, kai ka ce ramukan tururuwa ne ya bude suka yi fitar burgu.

Kafin ƙiftawar ido miliyoyin jama'ar sun kewaye su Jafar suka zamo tamkar mitsitsin tsibiri a tsakiyar teku, koda su Jatar suka dubi jama'ar garin sai suka ga ashe halittar jikinsu wata iri ce, ba irin ta bila'adama ba sak. Kowannensu na da zagayayyen ƙaho guda biyu a gefen kunnuwansu, tamkar lauje,kunnuwansu fankama-fankama ne, haka kuma hancinsu dogaye ne sirara tamkar sillan kara, amma sauran abubuwan jikin na su irin na mutane ne sosai,babu wani bambanci. Mazan su da matan su na ɗauke da makamai kala-kala. Wasu sun rike takubba, wasu gudumomi manya-manya, wasu masu, kowannansu sai muzurai yake kamar su cinye su Jafar ɗanyu.

A wannan lokaci tuni jikin Yelisa, Mashrila da Gulzum ya fara karkarwa. Jafar ne ka dai bai tsorata ba, domin tsayawa yai ƙyam ya riƙe ƙugu yana kallon mutanen kawai. Ba zato ba tsammani sai ga wani ƙaramin yaro wanda bai wuce shekara tara ba, ya fito daga cikin mutane ya iso gaban su Jafar akan sa akwai hular karfe irin ta sarakai. Cikin ɗagawa da nuna isa ya dubi su Jafar yace,

"Ba ma maraba da baƙi a garin nan, in zaku iya komawa inda kuka fito ku koma don bamu yarda da ku ba."

Ko da jin wannan batu, sai Jafar ya dubi yaron cikin mamaki yace,

"Me ya sa ba ku yarda da mu ba?"

Yaron ya ce, "Saboda za ku iya zama irin mutanen Galbasa."

"Waye kuma Galbasa, mene ne tsakaninku da shi?" Ko da jin wannan tambaya sai yaron ya matso kusa da Jafar ya tsikare shi da tsinin farcen hannunsa mai kama da allura. Jafar ya ƙwala ihu saboda jin zafin tsikarin, domin har sai da jini ya fito.

Ƙaramin yaron ya bushe da dariya, sannan ya tsikari Yelisa, Mashrila da Gulzum, kamar yadda ya yiwa Jafar suma kowannensu ya yi ihu,jini ya zuba a  jikinsu.

Nan take gaba dayan jama'ar garn suka bushe da dariya suna cewa, "Ba su ba ne, ba su bane."

Lokaci guda ƙaramin yaron nan ya ɗaga hannu sai kowa ya shiru,wurin ya yi tsit, kamar babu mai numfashi a wajeu, sannan yace,

"Ni sunana sarki Azbir, gaba ɗaya jama'ar garin nan a ƙarƙashin mulkina suke.Yaku waɗannan baƙi ku biyo ni izuwa fadata domin mu zauna mu tattauna na sanar da ku halaiyarmu, rayuwarmu da kuma masifar da ke adddabarmu, ko za ku iya kawo mana ƙarshen ta."

Nan take ƙaramin yaron ya juya ya yi gaba jama'a suka dare hanya ta samu ya keta ta tsakiyarsu.

Ba tare da wata fargaba ba su Jafar suka bi shi a baya. Suna tafe suna kalle-kalle. Nan fa suka fara ganin abubuwan al'ajabi iri-iri. Abin da suka fara gani shi ne wata ƙatuwar mace mai nono goma sha biyu a zaune tana shayar da jarirai goma sha biyu, a cikin wata rumfar kasuwa, sannan suka ga wani gabjejen mutum ya goyo jaki, jakin na riƙe da wata igiya a bakinsa wadda ta sarƙale wuyan mutumin.

Koda ganin sa sai Jafar ya bushe da dariya yace,

"TabÉ—i jan yau kuma garin da dabbobi ke mayar da mutane abin hawansu muka zo, kai amma fa an ci mutuncin mutuntaka a wajen nan......"

Kafin Jafar ya gama rufe bakinsa sai suka ga wani mutum a kwaɓe tsirara kare na zane shi da wata tsumagiya. A can gefe guda kuma sai suka ga

birirrika na tallan ya'yan itatuwa bisa faranti,mutane na siya, suna ba su kuɗi, har ma sai sun ƙirga kuɗin, sannan suke bayar da kayan. Nan fa su Jafar suka daɗa cika da tsananin mamaki.

Yayin da suka ƙara gaba kuma sai suka ga curin dinare, lu'u-lu'u, jauhar da demon tsubi-tsubi kasuwar boka,yara na wasa akai wani ma saika ga dabbobi na yin kashi da fitsari akai, irin n kuɗin da mutanen garin ke amfani da su kuwa ba komai bane face guntattakin fatar damisa.

Haka dai su Jafar suka yi ta ganin abubuwa al'ajabi iri-iri har suka isa wata tangamemiyar fada mai tsananin ƙawatuwa,komai ka gani a cikin fadar an yi shine da dangin su lu'u lu'u,hatta shimfiɗun fadar kuwa.

A inda aka ajiye karagar mulki kuwa bisa wani gilashi ne mai kaurin gaske a cikinsa ruwa ne da kifaye iri-iri,manya da ƙanana suna ta zilliya, idan mutum bai lura da kyau ba, sai ya yi zaton ƙaramin teku ne a wajen domin tuni su Jafar sun fara tattare rigunansu suna zaton ta cikin ruwan sarkin zai ratsa da su,amma bisa mamaki sai suka ga ya taka fadamar da ƙafafuwansa yana tafiya akai har ya isa kan karagar mulkin ya zauna a binsa.

Take ya yi musu nuni ga wasu kujeru da ke kewaye da karagar ta sa. Cikin alamun ƙauyanci su Jafar suka ƙarasa suka zazzauna akan kujerun,cikin ɗari-ɗari, su Jafar suka yi ta kalle-kalle don gani suke kamar a ko yaushe gilashin da suke kai zai iya ruftawa da su.

Sarki Azbir ya dube su ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Yaku baƙina ku kwantar da hankalin ku domin ko girgizar ƙasa za'a yi wannan fada tawa ba za ta ruguje ba, wannan gilashin da kuke kai ba gilashi bane,ƙarfen deman ne zalla. Kamar yadda na gaya muku a baya cewa ni da jama'ata muna cikin mummunan tashin hankali sakamakon farmakin jama'ar Galbasa.

Galbasa wani tsohon maye ne wanda ya shahara a zamaninsa, don sai da ta kai ta kawo cewa ya mamaye dukkanin ƙasashen da ke nahiyarsa.

Galbasa ba ya cin komai baya shan komai face jinin bil'adama. Babu wani makami da ke iya saran jikinsa kuma yana iya juya siffarsa izuwa ga kowanne irin siffa,duk mutumin da Galbasa ya zuƙi jininsa, shi kenan wannan mutum ya zama maye kamarsa, kuma zai iya yin duk abin da Galbasa zai yi na rikiɗa da rashin saruwa da makami. Kai komai kaifin makami da tsininsa baya huda jikin mutanen Galbasa, idan ma kuwa ya huda su din sai ka ga sun zare shi sun yar kuma, in da ya huje a jikin nasu sai ya koma ya manne tamkar ba a taba sukar wajen ba.

Suna tashi sama kamar tsuntsaye, kuma mutum É—aya daga cikinsu na iya surar mutum goma ya tafi da su izuwa can fadar Galbasa inda za'a shanye jininsu, su kan zo mana nan bayan kowanne mako guda. Da saukar su za su fara yi mana É“arna su hau shan jinin mutanenmu, duk wanda suka sha jininsa ya zama na su, sai ka ga shima ya afkawa mutanenmu, sai sun sha jinin mutum dubu sannan su É—ebi mutum hamsin su tafi da su.

Babbar illar waɗannan mutane ita ce yawan jinin mutanen da suka sha shi ke ƙara musu girma, karfi da tsawon rai,

wanda ya fi kowa shan jini a cikinsu yafi kowa girma, shi yasa har kullum ƙoƙarin kowanne shi ne ya sha jinin mutane da yawa."

Yayin da sarki Azbir ya zo nan a zancen sa sai Mashrila ta tari numfashinsa tace,

"Yanzu kenan kana nufin cewa Galbasa yafi kowa girma da ƙarfi a cikin mutanensa?"

"Ƙwarai kuwa domin a lissafi yanzu Galbasa ya sha jinin bil'adama miliyan dubu casa'in daidai,idan aka bari ya cike dubu ɗari sai gaba ɗayan mutanen duniya sun zama irinsa. Yau saura kwana uku jama'ar Galbasa su kawo mana farmaki, shin kuna da wata hikima da za ku iya ceton rayuwarmu?"

Sarki Azbir ya tambaya yana mai duban fuskokin su Jafar É—aya bayan É—aya. Jafar yace,

"Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa me rai baya rasa motsi,lallai zamu yi tunanin mafita kafin kwana ukun, amma ina son ka sanar da ni wai shin mutum na wane suka kawo wannan farmakin?"

Sarki Azbir yace, "Ai mutum biyar ne kacal kuma mata ne,waÉ—anda masifarsu ta wuce iyakar tunaninku."

Koda jin wannan batu sai Gulzum ya yı tsaki yace,

"Yanzu saboda abin kunya a ce mata biyar kacal suke addabar duk miliyoyin jama'ar garin nan."

Cikin fusata Azbir ya dubi Gulzum ya daka masa tsawa, yace, "Kai shashasha ka bar ganin kai aljani ne, kai tsammanin za ka iya kafsawa da su ne?

Na rantse da girman wannan karaga tawa idan aka tura mace É—aya daga cikin mutanen Galbasa za ta iya hallaka gaba É—ayan aljanun da ke duniyarku."

Azbir na gama faÉ—in haka ya juya ya dubi wata doguwar kuyanga da ke tsaye a gefen hagunsa yace,

"Yake Marzul ki kai waɗannan baƙi masauƙinsu, domin su hutu in ya so gobe mu ci gaba da tattaumawa."

Nan take kuyanga Marzul ta wuce gaba su Jafar suka bita a baya, har izuwa wani ɓangare daban, na wannan fada. Inda suka tarar da wani ƙasaitaccen gini mai tarin ɗakuna bila adadin, domin ko a kwana uku mutum bai isa ya ƙirga yawan su ba.

Kai tsaye Marzul ta shige da su cikin ɗaya daga cikin ɗakunan. Da shigarsu suka cika da mamaki domin kawai sun tsinci kansu ne a cikin wani ƙaton falo wanda kiris ya rage girmansa ya ninka na fadar sarki Azbir. Duk wani abu na jin daɗin rayuwa akwai shi a cikin falon. Koda ganin haka sai Mashrila ta dubi kuyanga Marzul tace,

"Shin idan na yi miki tambaya za ki ba ni amsa?"

Marzul ta yi murmushi tace,

"FaÉ—i tambayarki amfanina kenan a gareku."

"Shin duk sauran É—akunan da muka gani a waje haka suke da girma kamar wannan da muke ciki yanzu?"

"Ƙwarai kuwa,kuma sun fi wannan ɗin ma girma, abin bi da bi ne, ma'ana na gaba ya linka na baya har izuwa na ƙarshe."

Koda jin haka sai Mashrila da su Jafar suka dubi junansu cikin tsananin mamaki kowa ya jinjina kai.

Yelisa tace, "Nima ga tawa tambayar in ba zaki damu ba."

Marzul ta sake yin murmushi a karo na biyu ta ce, "Ai na faÉ—a muku amfanina kenan a tare da ku duk abin da ya shige muku duhu ni ce zan wayar muku da kai, face akan abin da ya wuce sanina saidai sarki da kansa."

Yelisa tace, "Yake Marzul kin ga dai kusan halittar jikinku da tamu iri ɗaya ce bambancin kawai shine kuna da ƙaho a ka bamu da shi, kuma kuna manyan kunnuwa da dogayen hanci, shi ne dama can haka kuke ko kuwa wata masifar ce ta sauya muku kamanni?"

Marzul tace, "Haƙiƙa wannan tambayar taki tana buƙatar dogon bayani a ƙalla muyi kwana goma ina baku labari,zai fi kyau ku bari mu ga abinda zai faru nan da kwana uku,idan mun tsira da rayukan mu daga sharrin mutanen Galbasa,zan baku labarin na ɗauki alƙawari akan hakan,yanzu sai ku zauna ku ci, ku sha idan da mai buƙatar yin wanka ga kewaye can."

Marzul ta yi musu nuni da wata ƙofa ta zinare, sannan ta fice ta bar su a tsaitsaye sun yi cirko-cirko suna masu kalle-kalle da al'ajabin wannan wuri. Kawai sai Gulzum ya dubi Jafar yace,

"To sarkin kankanba É—azu ka ce za ka yi tunani a kan hanyar da za'a samu nasara akan mutanen Galbasa? Shin ka yi tunanin ne ko kuwa sai nan gaba?"

Jafar ya dubi Gulzum cikin yanayın raini yace, "Wannan tambayar ai ba taka ba ce, domin wanda ya yi min ita da farko shi ya cancanta ya san amsarta."

Koda faɗin haka sai Gulzum ya fusata, ya yunƙura da nufin ya cafko Jafar da yatsu biyu, amma sai ya haɗa fuska da Yelisa ya ga ta daka masa harara. Bisa dole Gulzum ya maida nufinsa zuci,cikin alamun takaici ya ja da baya ya koma gefe guda yayi tagumi, kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa.

Yelisa ta matsa daf da Jafar suka fuskanci juna sosai, ta yi tattausan murmushi a gare shi tace,

"Ya kai masoyina shin wace dabara ka ke ganin zamu yi mu tsira daga sharrin waÉ—annan mutane da aka ce za su zo nan da kwana biyu?"

Jafar ya yi shiru bai ce komai ba. Sannan ya dubi Mashrila wacce ke tsaye a gefe guda zuciyarta cike da kishi saboda ganin irin kallon da Yelisa ke yi masa ya ce, "Yake Mashrila shin kina da wata dabara ko wani tunani akan mutanen Galbasa?

Maganar gaskiya fa ni har yanzu ban tuno wata dabara ba."

Koda jin wannan tambaya sai Mashrila ta tuntsire da dariya,sannan ta haÉ—e fuska tace,

"Ni kam ina da dabara amma sai idan kai da Yelisa da Gulzum kun gaza sannan zan faÉ—i tawa."

Caraf sai Gulzum yace,

"Ni kam kadama ku sani a cikin wannan magana, ku na ji fa É—azu sarki Azbir ya ce É—aya daga cikin mutanen Galbasn zai iya hallaka gaba É—aya aljanun garinmu,ai kuwa kunga kenan ba ni da wata dabara akan su."

Jafar ya dubi Yelisa yace,

"Ke kuma fa me za ki iya cewa?"

Yelisa ta yi shiru tana tunani, har tsawon ɗan lokaci, sannan ta ɗaga kai ta dubi Jafar cikin alamun karayar zuciya ta ce, ''Gaskiya tunanina ya ƙare na kasa gano mafita."

Jafar ya sake duban Mashrila yace,

"Na dawo gareki, ki sani cewa nima fa bani da wata dabara don haka mun baki wuƙa da nama."

Mashrila ta ƙyalƙyale da dariya, sannan ta juya baya tayi tafiya taku uku cikin ƙasaita da yarda da kai,sannan ta waigo ta fuskance su su uku tace,

"Ba zan faÉ—i hikima ta ba sai gobe a fadar sarki Azbir kuma bisa sharaÉ—i guda."

Cikin fushi Yelisa tace,

"Mene ne sharÉ—in ki?"

Mashrila ta yi murmushi, tace, "Sharaɗina shi ne ba zan faɗi hikima ta ba har sai idan ku ukun nan kun amince cewa idan har hikimar tawa ta yi nasara zan zama shugabarku a cikin tafiyarmu ya kasance za ku dunga bin umarnina, har mu gama karance sauran shafükan KUNDIN TSATSUBA."

Koda jin haka sai Yelisa ta kurma ihu, cikin fushi ta ce, "Ƙaryar ki ta sha ƙarya yarinya, ki dube ni da kyau ki sani cewa ba ki fini kyau ba, kuma ba ki fini shekaru ba, ya za'a yi na yarda ki zama shugabata mai bani umarni, kuma in ban dama tsaurin ido da rashin kunya ya za ki dubi Jafar da Gulzum ki ce kin zama shugabarsu alhalin ko a haihuwar tumaki baki isa ki zama tattaɓa kunnen Gulzum ba."

Wannan furuci ba ƙaramin fusata Mashrila ya yi ba, don haka sai suka fara kace-nace kafin Jafar ya ankara tuni Yelisa da Mashrila sun kaure da faɗa. Nan fa suka hau bugun juna, suka hau kokowa da ƙyar Jafar ya sami damar raba su ya tsaya a tsakaninsu, shi kuwa Gulzum abin ya bashi dariya kawai sai ya hau ƙyaƙƙyatawa har sai da Yelisa ta daka masa harara, sannan ya yi tsit, kamar wanda ruwa ya cinye.

Jafar ya dubi Mashrila da Yelisa yace, ''Abinda nake so da ku shi ne ku bar wannan gardama taku izuwa gobe babu mai warwareta face sarki Azbir."

"Ƙwarai kuwa." Gulzum ne ya faɗi, yana muzurai.

Nan take Jafar ya tafi kan wata shimfiɗa ya kwanta,kawai sai Yelisa ta je kusa da shi ta kwanta,kawai sai itama Mashrila sai ta a kwanta a bayansa, koda ganin haka sai Yelisa ta ƙara fusata ta mike wuf da shirin ta cakumi Mashrila,cikin zafin nama Jafar ya ruƙota ya ce, "Bana son ɗaya daga cikinku ta kwanta kusa da ni, don haka sai duk ku sauya makwanci."

Cikin alamun borin kunya da fushi kowacce ta miƙe ta je ta kwanta a waje dabam.

Kashe gari da hantsi su Jafar suka ƙara hallara a fadar sarki Azbir inda suka iske fadar ta cika maƙil da gaba ɗayan mutanen garin. Al'amarin da ya matuƙar ɗaure musu kai kenan suka shiga tunanin dalilin taruwar jama'ar haka.

Haka kuma sai suka ga an ajiye wani dogon kejin ƙarfe a tsakiyar fadar, A can karshen saman kejin an rataye wata takobi tana reto. Ganin wannan keji ma ya ƙara jefa su Jafar cikin jimami, tun kafin su ƙarasa gaban sarki Azbir sai suka ga ya miƙe ya tare su yana mai murmushi.

Kafin É—aya ya buÉ—i baki ya ce wani abu,sai Azbir ya tari numfashinsu yace,

"Yaku waɗannan baƙi namu masu albarka kuyi sani cewa duk abinda ya faru a tsakaninku jiya da daddare mun gani don haka yanzu ba tare da ɓata lokaci ba ina son na warware gardamar da ke tsakanin Yelisa da Mashrila, don kowa ma ya san matsayinsa. Ku yi duba izuwa ga wannan keji mai tsawo, ina son Yelisa da Mashrila su shiga cikin wannan keji sannan su kulle ƙofar daga ciki, duk wadda ta sami nasarar hawa har can saman kejin ta ɗauko takobin da ke rataye, ita ce ta yi galaba bisa gardamarsu."

Yayin da sarki Azbir ya zo nan a zancensa,sai Jafar ya dube shi cikin yanayin al'ajabi yace, "Ya kai wannan sarki ya aka yi kuka ga abin da ya faru tsakanin Yelisa da Mashrila jiya da daddare alhalin bakwa tare da mu, asalima a cikin É—aki muke a kulle mu huÉ—u kacal?"

Koda jin wannan tambaya sai sarki Azbir yayi murmushi, ya ce, ''Yakai Jafar ka yi sani cewa a halin yanzu bamu da lokaci na zama yin bayani face mun ga mun sami mafita bisa masifar da ke tunkarar mu nan da kwana biyu, ka yi haƙuri za ka ji abubuwan al'ajabi idan har kai da yan'uwanka kun sami nasarar yi mana maganin mutanen Galbasa."

Yana gama fadin haka sai ya dubi Yelisa da Mashrila ya ce, "Ku muke jira sai ku shiga cikin kejin domin kuna É“ata mana lokaci."

Yelisa, Mashrila suka dubi kejin wanda tsawonsa ya kai zira'i ɗari, sannan suka dubi junansu sai kowacce jikinta ya kama ƙyarma. Koda suka dubi Jafar ya fuskanci sun karaya sai ya yi murmushi a gare su yace,

"Nasararku itra ce karin matsayinku a wajena."

Yayin da suka ji wannan furuci sai kowaccen su ta ji ƙwarin gwiwa tare da rashin tsoro don tsananin kishin ƙaunarsa, domin su a zaton su yana nufin cewa duk wadda tayi nasara itace zata samu soyayyarsa. Cikin hanzari suka ruga suka shiga cikin kejin suka rufe ƙofar. Kafin Mashrila ta yunƙura Yelisa takama kejin ta fara hawa tamkar biri akan bishiya, cikin zafin nama Mashrila ta daka tsalle ta kama ƙafar Yelisa da hannu ɗaya sannan ta riƙe kejin da hannu guda ta fara ƙoƙarin finciko ƙafar Yelisa don ta jehota ƙasa. Yelisa ta ƙanƙame ƙarfen kejın da hannayenta biyu,iya ƙarfinta.(😅😅😅)


Matsatsubi Cigaban Kundin Tsatsuba Book 1 Part 2


Domin sauke Audio kuma sai ku taba bidiyon dake kasa 👇👇





Post a Comment

0 Comments

Ads