Amfanin Ganyen Dalbejiya Guda 16 Musamman Ga Mata

 

- Itacen dalbejiya ya kasance mai matukar amfani ko a la’adar bahaushe


- Yana yin magunguna daban-daban na cutukan da ke addabar jikin dan Adam

Karanta>>> Mene ne Budurci Da Kuma Yadda Ake Dawo Da Shi Idan Aka Rasa Shi

- Ganyen na tsarin iyali, maganin dafi, maganin kwari,hana kamuwa da cutukan jima’i da sauransu


Itacen dogon yaro ko kuma dalbejiya ya kasance ice mai matukar amfani ko a al’adar bahaushe. Ana kiran itacen da ‘Neem tree’ a turance. Tana da daci amma tana da matukar amfani a jikin dan Adam.


Karanta>>> Yadda Ake Amfani Da Tumfafiya Wajen Gyaran Nono 


Ga wasu amfanin dalbejiya a jikin mutum:


1. Ganyen dalbejiya na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya, musamman idan aka dafa ganyen ana shan ruwan kamar shayi.


2. Yana taimakawa wajen tacewa da tsaftace jinin jikin mutum.


3. Ganyen na maganin cutar zazzabin cizon sauro da typhoid.

Karanta>>> Yadda Zaki Gyara Nononki Cikin Sauki Tare Da Tumfafiya

4. Yana maganin cutar ciwon ciki, musamman idan mutum ya murde saboda wani abinci da aka ci.


5. Ganyen dalbejiya da man shi na gyara fatar jikin mutum.


6. Ganyen na maganain saiko, amosanin kai da kuma sa tsawon gashin kai.

Karanta>>> Yadda Zaki Magance Sanyi Ko Wane iri, musamman mai wahalar magani

7. Ana iya amfani da man dalbejiya a matsayin dabarar bada tazarar iyali.


8. Ganyen na kawar da cutar daji, musamman na nono da ‘ya’yan maraina.


9. Ganyen na maganin cutar gyambon ciki da rauni a jiki.

Karanta>>> Yadda Zaki hada Sabulun da zai saki samtsi, kyalli da kuma shiki

10. Yana rage kiba a jiki musamman ga masu fama da ita.


11. Yana warkar da ciwon gabobi da ciwon kai.


12. Yana kare mutum daga kamuwa da cutukan da ake samu ta hanyar yin jima’ai.

Karanta>>> YYadda zaki yi matsi domin jin dadin mai gida

13. Yana warkar da cutar kuturta.


14. Yana maganin ciwon ido.

Karanta>>> Yadda Zaki yi matsi da bashi da illa kuma mai saukin kudi

15. Yana maganin guba da ake samu daga jikin dabba kamar cizon cinnaka, maciji da sauransu.


16. Ganyen na maganin kwari musamman wadanda ke lalata amfanin gona.


Ku Taɓa Bulun Nan Domin Sanin Yadda Zaku Yi Amfani Da Ganyen Dalbejiya Wajen Gyara Fuskantar ku

Post a Comment

0 Comments

Ads