Naga Rayuwa Chapter 1

 NAGA RAYUWA CHAPTER 1


By Nazifa Sabo Nashe


FARKON LABARI


Yaune karshen shagalin da ake gudanarwa

a ranan bikina. Yaune dinner party wacce a

ka shirya ta ta mata zalla a golden dragon

Chinese restaurant. Ban hada dinata da

maza ba Kasancewar daga ni har angon

ustazaine, bamason abinda zai kawo

nakasu a rayuwar aurenmu. Ina zaune a

gurin dinnar zuciyata fari kal cike da

madaukakin farin ciki sakamakon Yaune

ranar da zan angwance da gwarzon Mijina,

Wanda nake matukar sonsa tabbas Ina

matukar doki zakwadi da zuwan wannan

rana ranar dazan tare a gidan USTAZ

AHMAD SULAIMAN SA'EED. duk dana

kasance cikin matukar sanyin jiki

sakamakon sallama da iyayena danayi da

yayyena maza wadanda basu halarci wajen

dinar ba Kuma daga nan gidan Mijina zaa

wuce Dani Kai tsaye Wanda yake nasarawa

G.R.A cikin kwaryar birnin KANO. Kowa ka

Gani awajen cikin farin ciki yake Don haka

nima dole nake kago murmushi, saboda

alhini Na rabuwa da gidanmu.

Download>>> Auren Karin Kasa Book 1 Complete Document

Karfe tara daidai aka tashi daga wajen dinar

sai sannan zuciyata ta sake tsinkewa na

rukunkume mamina da ita ma na lura

jikinta a sanyaye yake Don Tunda aka Fara

bikin na lura Sam mamina bata yi naam da

abin ba Don dai ba yadda zatayi ne a

matsayin ta na kishiyar mahaifiyata, Batada

damar nuna hakan. Mamina da kanta ta

shigar dani dakina hannuna damke cikin

nata, tana sake karantamin adduoi a kunne

na sannan ta rungume ni tana kuka nima

kukan na saka da kyar mutane suka

rarrashe mu Saidai Babu Wanda yayi

mamaki saboda ansan tsananin shakuwar

mu da mamina.

Tsit gidan yayi bayan kowa ya tafi sai

sannan na sake jin fargaba, Gashi har

shadaya ta gota ba Ango Babu labarin sa ni

kuma inajin kunyar na kira lambar wayarsa

don Dagaske Allah ya zuba min kunya

kasance wata tsatson Fulani .

Sai Sha biyun dare angona ya shigo Sanye

cikin wata jallabiya data ke ta walwali sai

alkyabba a samansa. Daga gani kayan zasuyi

tsada shigar larabawa yayi sosai

Kasancewar da ma ako Yaushe shigar ustaz

Dina kenan sai zanga kamshin tsadaddun

turaruka yake, wadanda ya saba sasu a ko

Yaushe har sun riga sun ratsa shi. Da sauri

na kudundune kaina duk danayi mamakin

ganin fuskar sa a hade murtuk. Duk da

kasan cewar sa maabocin murmushi ako

yaushe badai ya dariya sosai don afadarsa

yawan dariya yana rage imani. Mayafi

nasake ja na kudundune kaina don har

yanzu Ina matukar jin kunyar ustaz Dina.

Ina jiyo takunsa har ya iso bakin gado ya

tsaya.

AYSHA yafada cikin jarumar muryar sa.

Saidai nayi matukar mamaki Don ba haka ya

saba kirana ba AYSHATA shine sunan daya

saba kirana dashi ako yaushe har kowa ma

ya sani, Duk da haka banyi nawar dagowaba

da sauri na dago na kalle shi tabbas

yanayinsa ya firgitani. Ungo wannan. Leda

ya miko min daga haka ya fice a tunanina

zaije ya kimtsa amma mai yasa ustazuna ya

hade ransa haka kodai namasa wani laifine

ban saniba?

Download>>> Mijin Malama Complete Document

Da azama na jawo ledar na ciro kunshin

kazar yahuza suya da ice cream mai sanyi

na Fara ci Sai dana koshi sannan na jawo

ledar Dan na dau lemo .idona yakai wata

envelope a tsanmanina ustazuna mantuwa

yayi Don haka na jawo kwalin exotic na

bude shi daga shi sama kawai nayi na fara

daddaka Don dama da azababbiyar yunwa

na wuni. Idona ne yakara kaiwa kan

envelope din saina ga sunanane a jiki

maana Aysha imam khalil don haka da

azama Na dauko na fara karantawa

Assalamu........ni AHMAD SULAIMAN SA'EED

na saki Matata Aysha saki daya. Batare da

iddataba Idan ta samu.......

Ai kasa karasawa nayi na runtuma ihu fadi

nake.

Tabbas NAGA RAYUWA meyake shirin

faruwa da ni a daren farko a gidan Mijina

abin sona ya sakeni mai nayi masa? Kuka

ne ya kufce mini Saikuma na tintsire da

dariya Dana tuna cewa kadan daga cikin

aikin da namiji kenan. Koma zolayata yake

yanaso yagawada mizanin soyayyar sa a

zuciyata, Amma kuwa anya an taba wasa da

maganar saki a daren farko? Baridai naje

naji dahir.

Tsam na Mike na shiga laluben sashen nasa

kasancewata bakuwa agidan ban Sha

wahala wajen gano kofar sashen nasa ba

babban falo ne ya rabamu a hankali na

murda kofar na shiga shiru sashen nasa sai

sautin kiraa ne yake tashi Wanda ya kunna

a radio cikin muryan gwanin nasa Malam

Ahmad sulaiman. Nagama lalubena a

babban falon ban ganshiba donhaka na

shiga karamin falon.

Yana zaune akan sallaya na sameshi ya kife

kansa a gwiwa. Jin motsin tahowata yasa shi

daga Kai ganin nice yasa shi mayar da

kansa da wuri da alama baya son haduwar

mu da shi. Zuciyata a jagule na isa wajen sa

a darare na zauna a gefensa cikin kasa da

murya nace.

Ustazuna wata takarda nagani acikin kayan

da kakawo sainaga ina tantama da abin

dana karanta aciki ban Kuma fahimceka ba.

Daga idanunsa yayi da suka rine suka zama

jajaye Duk da Kasancewar su farare tas

kamar madara.

Download>>> Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete

Duk abinda kika kiranta aciki Babu kuskure

hakan nake nufi. Saki ustaz?

Kwarai da gaske Don haka ki tabbatar kin

fice min daga gida kafin karfe bakwai na

safe...... Daga haka ya shige daki Don kuwa

kukane yake neman kufce masa yabarni da

budaddan baki.

Sam Banji takaicin hakan ba Don nasan

kadan daga halayyar mazan yanzu ne

Amma kuwa ustazu zaiyi dana sanin sakin

nan dayayi min na tozarci da wulakanci

zuciyata fes na koma sashena matsalata

daya ce yanzu mai zan je Nafada a gidan

mu? Yaya kuma mutane zasu dau alamarin

duk wacce akaji labarin an saketa daren

farko a gidan Mijin ta tabbas sai an jefa

mata ayar tambaya tabbas NAGA RAYUWA

ni Aysha Sam na kasa runtsawa nayi a

daren ranan saboda radadi da zuciyata

keyi.

Kwarai ustaz ya cuceni da kyar na samu na

Mike. Ban daki na shiga nayi alwala ina

fitowa na tada kabbarar sallah. Jallah zan

kaiwa kukana ko naji sanyi a zuciyata.

Tun karfe uku bani nabar kan sallaya ba sai

danayi sallar asuba sannan na Mike Duk da

tsananin sanyin da akeyi hakan Bai hanani

saka hijabina Na fice daga gidan. Motata

na shige kirar Kia nabata wuta aguje, Sai

gidan mu dake sharada phase II.

Duk da a tsorace nake hakan Bai hanani

shiga gidan da karfin guiwa ba yan biki ko

watsewa basuyiba gabadaya an idar da

sallah an kwanta kenan na ratsa falon. Ba

kowa saboda muku mukun sanyin da akeyi

sashen mamina da tura Sadaf Sadaf na

shiga gabadaya Kanne na da yayyena da

sukazo biki sunanan baki bude suka bini da

kallo mami kuwa hangame baki tayi tace

Ni fadima, aysher Meya fito dake da asubar

fari? Nadama saidanafada Wa alhaji kinyi

kankanta da aure shekara Sha bakwai yanzu

haka bakon al amari kika gani ko? Lumshe

ido nayi hawaye na Gudu a fuskata mami

tsam ta Mike ta shige dani dakinta.

Aysher Meya kaiki fitowa Don Kinga sabon

abu? Auren fa kenan kowacce mace daga

haka fa girma yake zuwar mata Kuma ba

kyau tona asirin miji Don haka tun kafin

Mutanen gida su ganki tashi maza ki tafi

kafin ma abban ki yaji kiyi hakuri kinji

Aysha.

Shiru nayi ina kallonta Don na fuskanci ita

abin da take hange daban sake katseni tayi

da fadin tashi mana aysher so kike har sai

maganar ta yadu ayita kallon ki a matsayin

mara wayo mai gudun miji. Sake Lumshe

ido nayi cikin dashasahiyar murya

nace.mamina ya sake ni da .me? Mami ta

fada cikin matukar razana da kidima. mika

mata takardar nayi ina fadin Gashi dai.

Hannunta yana rawa ta bude tana

karantawa hawaye kawai take Amma tana

gamawa sai naga tana ninkewa tana dariya

tace sharrin da namiji saiki tashi muje

wajen abban ki yaga sakamakon alkhairin

da Ahmad ya aiko masa.

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete Novel

Kwalalo ido waje nayi nace mami Allah

bazan iya zuwa gurin abba ba Don bansan

yadda zai dau lamarin ba .tashi nace miki

muje ko iyakacinsa da kefa fada Bai isa ya

ce zai raba ki da rankiba ta fada a fusace ta

kuma fincikeni mukayi waje gabadaya,

jamaa an fito an tsaya cirko cirko yan son

kwasar gulma Tunda anji labarin amaryar

da aaka kai jiya da daddare gata ta dawo

da safe...

Post a Comment

0 Comments

Ads