ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 62 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/DT-uH4043IM
http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-62-hausa.html


*Sorry I'm busy* 🥱


*^ Part 62 ^*


Tafe suke a mota yayin da suke ta tsula uban gudu tamkar wasu ma'aikata na binsu a baya. A haka har suka fita daga cikin gari yayin da suka nufi hanyar wani daji. Ana cikin tafiya a daji ba zato ba tsammani sai ji sukayi Oga Jan Zaki ya tsaya. Juyowa yayi baya ya kallesu hade da cewa, "Wai ku me yasa mahaukata ne, waye dazun na sa ya sha mana mai?". Da sauri suka nuna Biri, "Oga nine nan kuma Full tank na yo kamar yanda ka umarta". A cewar Biri. Jan Zaki ya ce, "Idan full tank kayi ina muka je ne da har mai zai kare yanzu?". Zare ido yayi hade da duba gaba da baya ya ga lalai a tsakiyar daji suke, sannan ya ce, "Alquran zamu sha turi, da alama kafin mu karasa garinsu Tanimu sai mun ci kwakwa". Jan Zaki ya ce, "Uban waye zaiyi ma turi? Nan zamu bar motar a kasa zamu karasa". Biri yace, "Oga baka tunanin yan sanda na iya biyo sawu su zo su tarar da motar a nan?". A fusace Jan Zaki ya ce, "Zan fallama tafi Biri, kai ko da yaushe bakinka ba zai furta alkhairi ba? To ta ya yan sandan zasu gane sawunmu bayan a titi muke tafiya yanzu da muka ratso dajin nan ne kawai muka sauka a titi". Saukkowa sukayi daga motar, su Murja da aka rufe musu idanu da kyalle suma aka fiddosu yayinda aka sasu gaba kai tsaye suka kutsa kai cikin daji suna haske-haske da fitilolin hannayensu masu shegen haske. Biri ne a baya da zureriyar fitilarsa, yana tafe yana tura keyar su Murja yana fadin "Kuyi sauri mana". Ba zato ba tsammani sai ji yayi an tura keyarsa hade da cewa "Kayi sauri mana", cikin wata irin murya mai ban tsoro. 


Da sauri ya juya baya, amma sai baiga komai ba, ya dan tsaya yana haske-haske a kwakwalwarsa yana ta nazarin abinda ya faru, ya tabbata turashi da akayi a keya da kuma maganar da yaji kunnuwansa basuyi masa karya ba, amma gashi ya juyo bai ga kowa ba. Ganin sun fara yi mishi nisa yasa ya ruga a guje ya tarar da su, ba'a dade da fara tafiyarsa ba sai ji yayi an kara turasa a keya hade da cewa yi sauri mana. Da sauri ya juya abinda ya gani ne ya sa shi faduwa kasa ya kurma ihu, cikin fadin, "Aljani-aljani". Ihu yake yana karawa yana ja da baya, baki daya suka juyo suka kalleshi amma basu ga komai ba sai shi da ya daina ihu shima yana rarraba idanu ganin abinda ya gani ya bace. Da sauri ya kwashi fitilarsa da bindiga ya ruga da gudu garesu, a lokacin Jan Zaki ya daka masa tsawa tare da cewa, "Biri zan ci ubanka a dajin nan fa, wai kai a ko ina sai ka nuna halinka ne, ya zaka rika mana ihu bayan kasan mu masu laifi ne". Biri da tuni sai karkarwa yake domin shi ya ji kuma ya ga abinda ya gani, ya ce, "Oga na rantse ma da Allah aljani na gani, wani baki mai fuskar zaki kuma jikinsa duk bakin gashi ne, in ka ganshi dogo wallahi oga bani kadai ba duk wanda ya ganshi sai yayi ihu, wani zai iya suma ma". Tsaki Jan Zaki ya ja hade da cewa, "Shirmen banza, dallah ku zo mu wuce". Wani wanda ake kira Mudi mugu ya kyalkyale da dariya, hade da cewa, "Wallahi kai dai Biri mugun zabo ne, a gidan ubanwa ka ga aljanin, malam ko dai kasha tayi maka yawa ne?". Hararar sa kawai Biri yayi, sannan yaje ya shige tsakiyar su, ya bar su Murja a baya, domin yayi rantsuwa ba zai koma baya ba, yana tsakiya duk abinda zai faru ya faru. 


Mudi mugu ne ya ja tsaki yayin da ya koma bayan su Murja, aka cigaba da tafiya. Ana cikin tafiya ne Murja tayi tuntube da jijiyar icce ta fadi kasa, ganin taki tashi Mudi mugu ya sa takalmi ya harbata hade da cewa, "Tashi dallah malama". Ihu ta kwalla, "Wayyo Allah zan mutu". Kara kai mata duka yayi yana fadin ta tashi, ita kuwa tana ganin haka sai ta idasa zama kasa ta fara kwalla ihu tamkar ana zare ranta. Da sauri Jan Zaki ya juyo yana fadin "Wai miye take wa mutane ihu". Dai-dai lokacin Mudi mugu ya saita bindiga a kan Murja yana fadin, "Idan baki tashi ba sai na fasa miki kai yaseen". Yayi-yayi da ita taki tashi wai ala dole sai an bude musu fuskoki don bata ganin baganta, ba yadda suka iya ganin irin ihu da Murja take, dole yasa Jan Zaki yace a bude musu idanu. An bude ana cikin tafiya kenan, tun daga Nesa Jan Zaki ya fara hasko wani abu kamar mutum cikin fararren kaya ya yo inda suke. Kara haske fitila yake domin tabbatarwa, abun kara matsosu yake, yayin da suma suna kara tunkarar abun. Sai da suka zo kusa-da-kusa sannan Jan Zaki ya ga ashe macece. Hasketa yayi yana kallonta, budurwa ce fara kyakyawa gata doguwa, ta sako wata farar jallabiya har kasa, bindiga ya haka, hade da saitata yana fadin, "Dakata a nan, tsaya a nan ko na harbeki". Ita kuwa duk da ya haske mata ido, bata da alamar tsayawa, don kamar ba da ita yake maganar bama sai kara tunkararsu take. Ganin ta kusan zuwa gab da su ya harba bindiga gefenta ji kake faww! Domin ya tsoratata, amma bisa mamaki sai ya ga ko kallonsa ma batayi ba balle ta zabura. Tana zuwa saitinsu duka suka saitata da bindiga ita kuwa bata ma kallesu ba, kai tsaye ta bi gefen hanya ta wuce yayin da ta kara kutsa kai cikin daji. Tsayawa sukayi gaba daya suka saki baki suna kallonta, basu daina kallonta ba har ta bace musu, ko wanne da abinda kwakwalwarsa take raya masa game da budurwar. 


Shi Jan Zaki mamakin da yake yi, ya za'ayi budurwa kamar wannan ta biyo hanya tsakar dare ita kadai, gashi ko fitila babu a hannunta, kuma wai ya harba bindiga a gefenta amma ko zabura bata yi ba, ya tabbata akwai alamar tambaya game da yarinya. Sun juya kenan da niyar tafiya, Jan Zaki ya ga wani yaro mai rankwalelen kai ya taho a guje shima ya nufo inda suke. Kara haka bindigoginsu sukayi, shi kuwa Biri a bayan Oga Jan Zaki ya labe yana leken yaron ta saman kafadar Jan Zaki. Sai da yaron ya zo gaf da su, bisa mamaki sai suka ga yaro ne da bai wuce dan shekara goma ba, amma kanshi wani kwalele yasha iski kwalkwal, bakinsa kuwa babu hakora sai wasu guda biyu, da ka kalli fuskarsa musamman in yayi magana sai ya baka dariya. Yana zuwa ya ce, "Sannunku yan fashi, don Allah baku ga kanwata ta wuce ta hanyar nan yanzu ba?". Yanayin yadda ya kwalala musu ido da rankwalelen kansa, ga kuma bakinshi da yayi wani iri tamkar katon gibi, ga kunnuwa fato-fato tamkar na zomo, shine ya ba su Jan Zaki dariya. Biri ne ya fara kyalkyalewa da dariya yana nuna yaron da yatsa, cikin dariya yana fadin, "Sunan wani abu wai shi arankwala". Da jin haka sauran ma suka bushe da dariya suna kallon yaron, ciki kuwa harda Jan Zaki. Wasu har rike ciki suke saboda dariya, Murja ma ta so tayi dariya, amma ganin irin halin da take ciki yasa ta kasa yin dariya, domin yar tafiyar da sukayi har tayi mugun gajiya. Yaron ne ya kalli su Biri hade da bata rai ya ce, "Wai ni kuke yiwa dariya?". Biri ne ya haske bakin yaron da fitilar hannunsa, nan take suka kara fashewa da dariya baki dayansu. Wata irin dariya suka ji, Hahahaha! Marar dadin saurare, ba shiri suka daina dariyar da suke suna waige-waige domin sun rasa daga ina dariyar take fitowa. Ji sukayi an daka musu tsawa cikin wata murya mai karfin gaske sannan aka ce, "Ku cigaba da dariya mana taya ku nake yi nima".Biri ne ya kalli yaron, ya ga bakinshi ne yake motsawa, cikin sauri ya ce, "Na rantse da Allah yaron nan ne ke wannan maganar?". Da sauri suka haska yaron suna kallonsa, shi kuwa dariya ya cigaba da yi, wanda karfinta ya cika duk dajin, tsoro ne ya fara shigar su Jan Zaki, Mudi mugu yayi tsaki hade da saita yaron da bindiga, kafin kace kwabo ya bude masa wuta, ya dan dade yana harbinsa sannan ya daina, hayakin yana lafawa suka ga yaron kwance jikinsa duk jini, daga baya suka ji wani irin uban ihu wanda yasa sai da kowa ya rufe kunnensa, suna juyawa suka ga wani jifgegen mutum ya rugo yana ihu, mutumin suffarshi da girmanshi yayi dai-dai da wanda Biri ya fada. Ihu yake yana fadin, "Na shiga sun kashe min yaro". Su kuwa gaba daya suna ganin katon mutumin, ba sai an fada musu ba sun san cewa aljanine, tun kafin ya karaso garesu suka ce kafa me na ci ban baki ba. Cikin yan gudu harda su Oga Jan Zaki domin shine a gaba-gaba, su tuni sun manta da wasu su Murja ma, don kowa ta kanshi yake cikin su shidan. Katoton aljanin yana zuwa ya daga dan yaron ya ga ya mutu, nan take ya kwarara uban ihu, sannan ya fara magana cikin kara yana cewa, "Tunda kuka kashe dan karami hukuncinku kisa ne, a cikinku ba wanda zai tsira". Duk da kasancewar tuni sun bazu cikin daji amma daga inda suke sun jiyo maganar da aljanin yayi, don haka duk sai suka kara tsurewa, domin sun tabbata a yadda sukaga aljanin nan kashesu a wajensa abu ne mai sauki, Shiyasa ma basuyi yunkurin harbinsa da bindigogin hannunsa ba, don wannan da gani bindiga ba zata yi wani tasiri a jikinsa ba, mafita daya ce kawai su gudu su boye domin tsira da rayuwarsu. Murja kanta ba karamin tsorata tayi ba da taga aljanin, har ta tashi zata zafga da gudu Safuratu ta rikota. Safuratu ta kalleta hade da cewa, "Wai ke Murja yaushe zaki daina wannan shegen tsoron naki ne? Haka fa kika rika kuka wai dan wadannan kanannun yan fashin sun ce zasu taho da ke, duk da kuwa kinsan ina tare dake kuma zan ceto ki". Murja tana karkarwa domin tsoro bai saketa ba ta ce, "Wallahi nima bansan me yasa nake da tsoron ba". Safuratu tayi dariya hade da cewa, "To kinga kuwa ba zan iya mallaka miki dukiyarki a hannunki ba, dole zamu samu ko wannan kawun naki ne a bashi dukiyar. domin da shegen tsoron nan naki ko zare miki ido mutum yayi kina iya bashi abinda kika mallaka baki daya". Murja ta ce, "Nima bansan me yasa nake da tsoro haka ba, amma ina so in daina. Kuma naji kina maganar Kawuna kina nufin Uncle Sadi kenan? Ai ba lalai ya karba ba ai na fada miki yanda suka rabu da babana". Safuratu ta ce, "Karki damu zai karba in dai na bincika na tabbatar zai iya rikeki amana zan sa ya karba, yanzu dai bari na ji da wadancan yan fashin". Murja ta ce, "Me zaki musu?". "Kashesu zanyi". Safuratu ta bata amsa a takaice, Murja ta ce, "Amma sata fa sukayi ai kamata yayi kiyi musu hukuncin sata kawai".


 Safuratu tayi murmushi hade da cewa, "Allah sarki Murja, har yanzu dai babu abinda kika sani a rayuwar duniyar nan taku ta mutane. Ai wadannan da kike ganinsu, basu da wani amfani a duniya, domin rayuwarsu ta gama gurbacewa, wanda kika ji yana ikirarin zai kashe mace ta hanyar fyade kinsan cewa imaninsa yayi nisa. Kuma ki kalla yanda daya daga cikinsu ya sa bindiga ya harbe wannan yaron, wanda dama nayi haka ne duk a cikin gwaji, kinga kenan sun dauki kashe rai ba a bakin komai ba". Murja ta kada kai hade da cewa, "Gaskiya basu da imani, ji fa yanda wannan ya rika kwallo dake". Safuratu ta ce, "Bashi ya ci, ai yanzu zan rama". Suna labe a can saman bishiya Biri ya kalli Jan Zaki cikin rada yace, "Oga kamar fa aljanin nan bai biyo mu ba". Da sauri Jan Zaki ya sa hannu a lebansa hade da cewa, "Shiit yi shiru karka sa ya jimu dan ubanka". Ji sukayi ance, "Ai gani nan". Ai kuwa suna duba gefensu suka ga wannan rusheshen aljanin a saman wani reshe yana kallonsu. Garin sauka Biri ya fado kasa tun daga can saman bishiya, shi kuwa Jan Zaki ihu ya kamayi a sama yana ba aljanin hakuri. Aljanin ya nunashi da hannu hade da matse hannun, nan take yaji kamar an shake masa wuya cikin lokaci kadan lumfashinsa ya dauke ya fado kasa bayan ya mutu. Biri ma aljanin ya yo kasa ya murde masa wuya. Sauran yan ta'addan duk suna lalabe wasu a karkashin kalgo wasu kuma a cikin ciyayi, daya bayan daya aljanin ya rika binsu sai da ya kashesu baki daya. Bayan Safuratu ta gama da su ta koma ta dauki Murja suka nufi gida. 


Da safe su Hajiya Lami su ka ga Murja ta zo tayar da su sallah, bakin ciki kamar su hadiyi zuciya su mutu. Don a tunaninsu su da Murja har abada, tunda yan ta'adda sun sace su, su kuma ba zasu kai kudin fansa ba tunda sunji yan ta'addan sunce zasu kashe su Murja idan basu kai kudin bansa ba. Bayan kwana guda Sailuba ta nemo musu wani katon boka, duk ya hayake gidan da hayaki irin na tarkacen bokanci, yayi haukansa iya hauka amma daga karshe a gabansu ya zo ya wuce a guje ana zanesa da bulala. Su kansu abun ya basu mamaki domin a lokacin da ya fito daga falo gani suke kamar ana dukansa da bulala amma basa ganin mai dukansa. Cikin kwana biyu gidan ya rikice baki daya, domin zaman gida yayiwa su Hajiya Lami zafi, basu da natsuwa ko kadan abu kadan sukeyi suji an wanka musu mari, bulala kuwa suna shanta a kullum babu adadi. Khalil da Jamsy tserewa sukayi da suka ga abin yayi yawa. Domin da dare ma ba'a barinsu suyi bacci, idan ka kwanta zakaji ana kwankwasa maka kofa in kuma ka bude kaga babu kowa.


Haka kana kwance sai kaji kamar mutum yana shafaka, ko kuma kana cikin gida ka rika ganin halittu na zirga-zirga suna ratsa bango. Abubuwan sunyi yawa, su Saratu har mamaki suke jin yadda su Nana suke basu labarin irin tsoron da ake ba su Hajiya Lami, amma su sunce ba'a taba tsorata su ba. Hajiya Lami tana kuka ta kira Alhaji Lawal ta ce ita wallahi barin gidan zatayi, saboda aljannu na son kasheta. Jin haka ya ce ta kwantar da hankalinta zaiyi kokari ya zo cikin kwana biyu, don shi bai ma yarda da batun aljannun da suke yi ba. Bayan Alhaji Lawal ya dawo cikin lokaci kadan ya fahimci akwai matsaloli a cikin gidan, babu ma abinda yake takura masa tamkar Safuratu dake zuwa a suffar Murja tana masa bala'i wai ya tattaro duk dukiyarta ya bata, shi ya ma rasa gane a cikin Murjojin guda biyu waccece ta gaskiya. Akwai ranar da ya daukko bulala ya ce zai koresu baki daya su bar gidan, bayan Hajiya Lami ta tayar masa da rigima. Amma daga karshe yana fara dukan su Murja sai ji yayi dayar Murjar ta kwace bulalar hannunsa tana ta zuga masa, da gudu ya tsira. Zuwa lokacin shima ya fara tsoron lamarin su Murja. Suna zaune da wani abokinsa Usaini yake bashi labarin halinda yake ciki a gidansa. Abokin nasa yayi dariya hade da cewa, "Gaskiya Lawal ka bani kunya wallahi, duk ina wayonka da wayewarka da har zaka yarda da wannan tatsuniya irin ta yara, wai Aljana?". Ya sake kyalkyalewa da dariya. Bayan Lawal ya daure fuska abokin nasa ya ce, "Yi hakuri in dai da gaske kake, ni inda hanyoyin da za'a bi domin a kori yaran daga gidan baki daya, ko ka manta ni lauya ne?". 


Alhaji Lawal yayi murmushi sannan ya ce, "Haba abokina yanzu naji batu, amma da ka tsaya kana dariya, lamarin yaran ba karami bane wallahi ni naga abinda na gani". Usaini ya ce, "Yaran da kace basu da wasu gata, da karfin iko na kotu kawai zamuyi amfani mu koresu su bar gidan, tunda dama ba wani gata garesu ba, ko da gaske gidansu ne ma babu uwar da za'ayi"..................☹️ Zan Taimaka Muku A Koresu Nima Safuratu Ta Isheni. Readers ku dai cigaba da hakuri, I'm busy wallahi

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Post a Comment

0 Comments

Ads