ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 53 Hausa Novel 2023


๐ŸงŸ‍♀️๐ŸงŸ‍♀️ ๐ŸงŸ‍♀️๐ŸงŸ‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

๐ŸงŸ‍♀️๐ŸงŸ‍♀️ _Wata Sabuwa_ ๐ŸงŸ‍♀️๐ŸงŸ‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/e0CWjiZhO6Q

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-53-hausa.html


*^ Part53 ^*


Addu'a take a zuciyarta kar Allah yasa abinda take zargi shine ne, wato aljanar ce ta sake dawo mata. Ta kusan mintuna biyu a wajen ko motsin kirki ta kasa yi, balle ta iya matsawa gaba ko kuma tayi baya, Allah kadai yasan irin tsoron da ke kunshe a ranta a lokacin. "Ke wai ba dake na ke magana ba" . Abinda ta ji an fada kenan da karfi, wanda yasa har sai da ta zabura, don haka ta juya ta kalli saitin wajen tv din. Ihu ta fara kurmawa tamkar wacce ta ga mutuwarta, saboda ganin fuskar matar a cikin tv sai kifta manyan idanunta take, tana kallonta haka zalika a wannan karan fuskarta ta kara muni da ban tsoro fiye da jiya da ta ganta. "Yi mun shiru, ko in fito in babbalaki". Da sauri ta kama bakinta tayi shiru jikinta sai karkarwa yake saboda tsoro, a zahiri ganin abin take tamkar a mafarki, wai mutumin dake cikin tv ne yake kallonta yana mata magana, yau Allah ya taimaketa ta rike karatun sosai, domin lokacin da Ummi ta dawo daga makaranta ta biya mata karatun kuma ta tabbata ta rike ayoyin guda biyar gam a kwakwalwarta, don ita kanta bata san ko sau nawa ta nanata su ba shiyasa karatun ya zauna mata a zuciya. Bayan ta karantawa aljanar ayoyin aljanar ta kyalkyale da dariya hade da cewa, "Tabbas kinyi kokari kuma karatun nan da kikayi yasa zan rage hukuncin da nayi niyar mike a kan wulakanta su Saratu da na kula har yanzu baki daina ba". 


Cikin kuka-kuka ta fara fadin, "Don girman Allah kiyi hakuri, wallahi daga yau ko kallon banza ba zan sake musu ba". Ta fada tana girgizawa aljanar hannu alamar ta daina, amma ba zato ba tsammani sai ta ga aljanar ta zuro kafarta daga cikin tv din tana kokarin fitowa tana fadin, "Karya kike zaki kara mana, amma nasan idan na hukunta ki yanzu ba lalai ki kara ba". Duk kalar magiya da rokon da ya fado bakinta yi take ga aljanar, ganin yadda take zuro sassan jikinta daga cikin tv tsoronta ya lunku domin bata san wane irin hukunci aljanar zatayi mata a wannan karon ba. Baya ta fara ja yayin da ta ga aljanar ta nufo kanta muryarta har sarkewa yake saboda magiya da rokon aljanar da take, duk da kasancewar da ac a dakin amma tana jin yadda zufa ke keto mata a jiki, wani uban ihu ta fasa hade da zubewa kasa a sume, lokacin da aljanar ta zo dai-dai kanta ta mika zankalelen hannunta mai kama da kafar tsuntsu tana niyar kama kanta. Ganin Jamsy ta sume aljanar ta kyalkyale da dariya hade da cewa, "Mu hadu a wani karon da sannu zanyi maganin rashin tarbiyarki". 


Mama Dije ce tsaye ta kara kunnenta a jikin kofar daki, tamkar wata munafuka zuwa can ta juyo ta kalli Hajiya Lami da ta tsura mata ido tana jiran ta ji abinda zata ce, "Naji dakin shiru da alamu fa yarinyar tayi bacci". Ta fada cikin rada murya kasa-kasa. Hajiya Lami ta washe baki itama murya kasa-kasa ta ce, "Mu shiga to". Kofar dakin ta kama ta murza da nufin ta bude su shiga dakin Murjar domin su sake daukarta hoto kamar yadda sukayi jiya. Bisa mamaki sai ji sukayi kofar a kulle, Hajiya Lami ta bata rai, "Amma yarinyar nan anyi yar iska wato kulle dakin tayi? Ko da yake in ta san wata bata san wata ba, Mama jira na daukko wani key din a daki". Tana fadar haka ta juya da sauri taje ta daukko key din ta zo ta sa a kofar ta bude tana murmushi. Kai tsaye suka fada dakin ko sallam babu, turus suka ja suka tsaya suna kallon saman gadon, itama su take kallo. Ko kadan basuyi zaton haka ba, su da suke tunanin tuni Murja tayi bacci domin suna falo suna jiran tayi bacci yanzu misalin karfe 1 na dare ai ya ci ace tayi bacci. Mama Dije ce ta ce, "Assalamu Alaikum, Aa Murja bakiyi bacci ba? Zuwa mukayi mu ga ko lafiya munji ana ta ihu kuma kamar daga nan dakin ihun ke fitowa". Shiru ta ji Murja tayi bata ce kala ba sai idanu da ta kwalala musu, tana binsu da kallo ko kiftawa batayi.


Hajiya Lami ta ce, "Ashe lafiyarki kalau ba abinda ya sameki? Mama juya mu tafi tunda lafiyarta lau ba abinda ya sameta". Haka suka juya da sauri suka bar dakin, bayan sun ja mata dakin ita dai ko motsawa batayi ba balle tayi musu magana, kai tsaye sukayi saman bene Hjiya Lami ta ce, "Mama anya yarinyar nan lafiyarta daya kuwa? Ni fa har tsoro ta bani wallahi, tsakar dare haka amma kin ganta zaune a kan gado ba komai take ba kuma ta tsura mana ido taki yin magana". Mama Dije ta ce, "Ai ni har yanzu gabana faduwa yake wallahi, to ko uwar me ya hana ta yin bacci har zuwa wannan lokacin? Ita dai naga yar wayar dake hana matasa bacci ba wani damuwa tayi da dannawa ba, duk da ina zargin bata iya bane". "To Mama ko mu koma ne mu dan jira zuwa anjima watakil zata iya yin baccin". "Ke ni dai ba zan iya ba, gaba na sai dukan uku-uku yake yi tun bayan da muka shiga dakin yarinyar can". Hajiya Lami ta ce, "To shikenan kawai bari mu bari sai gobe dama bacci nake ji". Dai-dai dakin Jamsy basu ankara ba suka ga mutum ya fito a guje, ihu suka zunduma baki daya suka kankanme juna. Jamsy da har tuntube tayi wajen fitowa daga dakin tana ganin uwartata da kakarta sai taji wani sanyi, domin farkawarta kenan bayan aljana ta zo kanta tana kokarin taba kanta ta sume bata sake sanin halin da ake ciki ba sai yanzu da ta farka ta ga ba kowa a dakin.


"Mom Mama Dije ni ce, wallahi ba zan kwana a dakin nan ba, aljana tana nan, ba'a koreta ba wallahi aljana". Sakin juna sukayi suna kallonta, duk a firgice take, maganar ma yi take tamkar zararriya, Mama Dije ta daka mata tsawa hade da cewa, "Ke dallah ki natsu kiyi magana, ashe kece kika tsorata mutane, ji yadda kika fito daga daki a guje kamar kinga mutuwa". Ba abinda take nanatawa sai aljana aljana. Ganin hakan Hajiya Lami ta kama hannunta suka nufi dakinta baki daya. Bayan sun zauna ne ta kora musu bayanin aljanar da ta gani, amma daga karshe karyatata sukayi a cewarsu tuni Naziru mai aljannu ya fatattaki aljannun gidan kuma sun tabbata ba karya yayi musu ba, ta tabbatar musu har ihu ta rikayi amma suka ce basu ji ihunta ba sun dai ji karar speaker da ta cika gidan.


Tafe suke su biyu a mota kallo daya zakayi wa idanunsu ka tabbatar a bige suke, sai dai ba bugawa irin can-can ba, Khalil ne ke tuka motar idanunsa har rufewa suke, lokaci zuwa lokaci yana sa hannu ya bigi kansa kamar wani tababbe. Dayan matashin dake gefensa ya kyalkyale da dariya shima yana laya kai irin na wanda ya bugu ya ce, "Gaskiya Khalil kanka karami ne, wai yar kodin din da ka shaka ne ta sa kake neman losing control? Ka ga bani tukun nan idan ba zaka iya ba, gwara in ka kaini gida na sauka sai ka ja motar kai kadai ko mutuwa kaiyi a hanya ba ruwana karamin kanka ne ya ja ma". Tsaki yayi hade da kallonsa ta gefen ido ya ce, "Dallah gafara malam, kai dai Junaid ka san cewa kaina ya fi karfin naka, abinda kan nan nawa zai dauka kanka bai isa ya dauka ba kum...". Da dukkan karfinsa ya take birkin motar hade da riketa gam bisa ganin wani abu tsaye a saman titin tamkar mutum ne yake daga musu hannu, yayi niyar kada kan motar gefe domin ya gocewa mutumin amma ya san cewa a irin gudun da yake idan ya ce zai gocewa mutumin suna iya kaiwa bango ko wata bishiyar karo. Da kyar ya samu ya kautar da kan motar bai bige mutumin ba bayan ya take birki ya tsaya. A fusace suka bude motar suka fito suka nufi mutumin, sai a lokacin ma suka lura ashe macece tsohuwa sanye da doguwar riga baka, ita ma su ta nufa, tun kafin ta karasa garesu ta fara fadin, "Yara kuyi hakuri dan Allah rage min hanya zakuyi nayi dare gashi babu ababen hawa kuma gidana da nisa". 


A bangarensu kuwa ashar suka fara wulla mata kala-kala suna karasawa gareta Khalil ya daga hannu ya wanka mata mari ba tare da ganin tsufanta ba. "Baki da hankali ne? Dan kina so a rage miki hanya sai ki hau kan titi ki tare mutane, yanzu da kika sa muka fadi muka mutu fa? Kina so ki sa iyayenmu cikin bala'i ne kinsan yadda ake son mu kuwa?". Dafe kumatu tayi tana kallonsa, a haife dai ta haifeshi amma yaron ba kunya balle tsoron ido ya daga ,hannu ya sharara mata mari kuma ya rufeta da fada, dayan abokin nashi ma fadan yake ma. Ko dake kallo daya tayi musu ta gane cewa a bige suke cikakken hankalinsu baya tare da su. "Yanzu yaro ko darajar furfura banci ba a wajenka da har ka iya daga hannu ka wanka min mari tamkar ka sama sa'arka?". Tsawa ya daka mata, "An mareki din ko zaki rama ne? Wallahi zaki sa in sake daukeki da mari tsohuwar banza kawai, kuma ba za'a rage miki hanya din ba". Junaid ya ce, "Dallah rabu da ita baka ganin tayi kama da almajirai? Idan kana bata lokacinka a kan irin wadannan mutanen ba zaka cigaba a rayuwa ba, mu wuce dallah". Hannun Khalil ya kama ya ja shi har lokacin shi kuwa masifa yake wa matar. Titin ba kowa mutane duk an shiga gida, kafin ka ga mota ko mashin ya gitta sai an dauki lokaci, ga garin ya dau hadari sai walkiya ake da alamu ana iya sakin ruwa a ko wane irin lokaci. Suna zuwa dai-dai motar Khalil ya sake juyawa ga matar da nufin ya kara balbaleta da masifa, bisa mamakinsa sai ya ga wayam ko kurarta babu a wajen, ya duduba gefen titin ko ina bata nan, gashi dai babu wani gida a kusa balle yayi tunanin ciki ta shiga shaguna ne kuma duk an kulle su. "Me kuke jira ku shigo mu tafi mana". Abinda suka ji an fada daga cikin motar kenan.............,....


Bari na sa glass ๐Ÿ˜Ž Tunanin wani shegen rashin mutunci da zanyiwa mutanen da basa comment a littafin nan nake, ban damu ba a whatsapp ne ko a Facebook, ko a ina comment yana da tasiri domin yana karawa marubuci kwarin gwiwa a lokacin da yake posting. Amma ya za'a ce sai ranar da banyi typing bane idan anji shiru nake sanin akwai masu bibiyar littafin da yawa. Korafi aka kawo min kuma na karba, na san cewa a kalla a dan typing din nan ina iya bata awa biyu zuwa uku, shi kuwa comment bana tunanin zai wuce minti daya, kai wasu ko irin tnx din da ake cewa basa iyawa. ๐Ÿ˜‚ nasan akwai masu yi, kuma ba dan su ba wallahi in tattara littafin in ajiye a gefe wato in daina typing ba karamin aikina bane tuna ba na kudi bane ba wanda zai ce min dan me na daina typing © Aljana Safuratu tayi Allah wadai da masu karantawa su wuce ba comment

One Love Kawai Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

๐Ÿ˜

Post a Comment

0 Comments

Ads