NI DA FATALWA Part 6 Hausa Novel

NI DA FATALWA! ↬
{gajeran labari}
Part {6}


@KINGBOY ISAH
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


Tsalle nayi cikin murna domin dama na gaji da
zama ni kadai na bude datar ma chat ba dadi. Da
sauri na shiga kitchen na hau kiciniyar musu girki
kafin su karasu. Na dora tukunyar kenan naji
karar wayata na dauka. Salima tace gasu nan sun
iso bakin kofa. cikin zumudi naje na bude. Salima
Sadiya da kuma Najwa. Class mate dina ne kuma
kawaye na ne na kut da kut. Muka rungume juna
ana farin ciki sakamakon rabo na da su tun ranar
da suka kawo ni nan gidan Habib a matsayin
amarya. Suna shigowa nasa kobobi na garkame
gida muka runkuta ciki sai tsiya suke mun wai
auren nan ya karbe ni nayi fari na kuma kara
kiba.A parlour muka zube muka hau gaggaisawa
muna cikin hira na tuno da tukunyar da na dora
na ce Salima ta taso ta rakani kitchen ta tashi
muka tafi. Ganin mun dade a kitchen ya sa su
Najwa suka biyo mu. Muka hau shiririta ba mu
fita a kitchen din ba sai da muka gama abincin.
Taliya jalof a katan tire muka juye sunan muka
dawo falo a ka ajiye ta huce kafin mu ci. Muna
cikin hira nepa suka kawo wuta, da sauri Sadiya
ta mike uwar son kallo ta nufi TV tana kokarin
kunnawa. Mu kuwa duk muka zubawa TV ido
wani razanannen kara muka saki a tare tuni
Salima ta makalkale Najwa cike da tsoro. Sadiyar
ita kanta da gudu ta yo baya daga wajen TV. ba
komai ne ya jawo haka ba facce wani wata
Fatalwa mai ban tsoro da ta saki wani irin kara
mai firgitarwa da mukaji ya fito daga speaker
dake ajiye gaban TV. Mbc2 ne suka wani film din
horror wai shi Ghost house. Dai-dai lokacin da
wannan fatalwar mai abun tsoro ta kawo cafka ta
wangame baki hade da zaro jajayen idanunta
tamkar zata fito daga cikin TV din. Volume din
speakers yayi over gashi karar kadai ya isa ya
tsorata ka ba ma sai ka kalli TV ba. Cewa muke
Sadiya ta kashe tv ta kashe amma ina tuni itama
tsoro ya cikata ta bar wajen. Cikin karfin hali na
mike na nufi TV din nasa yatsu na rufe kunnuwa
kamar yanda suma sukayi. Cikin tsoro na kashe
Tv din yayin da naji su Salima sai ajiyar zuciya
suke. Sadiya na hanga kan kujera ta kudun dune
kamar wacce zata shige ciki ba shiri na barke da
dariya. gaba daya kowa ya kama dariya har da
rike ciki.
Nace "Sadiya ashe ba zaki iya zaman gidan nan
ba? duk tsoro na ashe kin fini?". Sadiya tace
"Dallah can malama miye a cikin gidan da zan
kasa zama dubi fa gida cancarere ga dakuna uku
ko wanne da bathroom ga kuma kitchen da
parlour ai wannan gidan ya hadu iya haduwa".
Nayi murmushi nace "To ai ba daga nan take ba
baki ga katanga daya ce tsakanin gidan da
makabarta ba".Salima ta zaro ido "Wai dama
katanga daya ce ta raba ku da makabartar nan?
tabb yaseen in ni ce ke bazan iya zama a gidan
nan ba". "Salima ai ba makwabtaka da
makabarta ne abun tashin hankalin ba. Babban
tashin hankali shine a nan gidan akwai fatalwa
kuma kullum da dare sai ta tsorata ni haka da
rana ma akwai matar da ta ke zuwa wai ita Indo
kuma nayi bincike an tabbatr min da cewa itace
fatalwar a nan kujerar da kike zama take zaunwa
kullum in tq zo tata bani labaran tsoro". Ina fadar
haka Salima da Najwa suka saki ihu suka tashi
da gudu jin nace a kan kujerar da suke Inna Indo
ke zama. Sadiya tuni ta fara karkarwa kamar
zatayi kuka wai dan Allah mu rakata ta fita a
gidan nqn ta tafi gida. Dariya muka hau yi mata.
Najwa tace "Khadija wai dan Allah da gaske kike
fatalwar na zuwa?". Nan take na kwashe duk
abunda ya faru na gaya musu har irin labaran
tsoro da Inna Indo ke bani. da kuma irin
abubuwan tsoro da nake gani kuma Habib yaki
yarda. Sadiya ta yi ajiyar zuciya tace "Yaseen
khadija ke jaruma ce domin wallahi in nice naga
fatalwa ko sau daya ne wallahi bazan kuma
kwana a gidan ba. Gidan mu zan tafi in ya so
Habib din ya sake ni Shimq kuma babban mu in
na gaya mai yaki yarda sai ya san yarda zaiyi
domin ba yanda za ayi na zauna gida NI DA
FATALWA". Nace "Hmm Sadiya baki san halin
Abba mu bane wallahi bazai taba goyan baya na
ba. Ni yanzu hakuri zanci gaba da yi kawai har
Allah ya kawo ranar da fatalwa nan zata razana
Habib nasan daga ranarn zai ce mu tashi daga
gidan nan". Najwa tace i have idea". Mu duk
muka ce Kawo ta. Sadiya kam tayi tsuru sai raba
idanu take kallo daya zaka mata ka gane a
tsorace take. Najwa tace "Naji ana cewa idan
fatalwa ta takura wa mutane zuwa ake a tono
gawarta sai a toya ta daga nan shikenan an huta
da ita". Muka kalli juna ni da Salima "To ke
Najwa in banda abunki ta ya Khadija zata iya
gane kabarin fatalwar bayan ta dade a mace
yanzu ma watakil ta zama kasa?". Cewar Salima.
Najwa tace "Ba kabarin zata to no ba in dai ta
tabbata wannan Inna Indo din fatalwa ce to ita
zata kona kinga tana konewa sai kiyi zamanki
lafiya ba tsoro ba firgita.
Na dan yi jim kadan sai kuma kawai naji na
aminta da shawarar nan domin fatalwar nan ta
takura min. Zan iya yin komai domin in rabu da
ita. Wani kwarin gwiwa naji zuciyata na ta kara
bani a kan in aminta da shawarar nan. Nace
"Najwa na amince da shawarara nan sai dai wani
hanzari ba gudu ba, taya zan kona Inna Indo
bayan tsoronta ma nake ji ko kusa da ita banna
zuwa". Salima tace yauwa ba dai kince a kujerar
nan take zama ba?". Nace Eh. tace "to ai konata
abu mai sauki ne kawai fetur zaki samo a cikin
bokiti sai ki ajiye a bayan kujerar daga ta zo tana
cikin bakj labari sai ki lalabo ta bayanta ki dauki
bokitin fetur din nan ki kwara mata a jiki kafin ta
tashi kawai ki wulla mata ashana kinga tuni zata
kamq da wuta". Dan tsallan murna nayi nace
"That's good wallahi har naji dadi gaskiya na
gode da shawarar nan. wallahi ni kuwa gobe sai
na toya Inna Indo. Yanzu dai ku saukko muci
abinci". Su biyun suka saukko domin cin abinci
amma Sadiya taki wai ita gida kawai take so ta
tafi. Muna cin abinci sai korafi take wai su
Salima su tashi su tafi. Bamuyi mamaki ba
domin mun santa da shege tsoro tun a school
haka take. Muna cikin hira ita ta takura wai ala
dole sai sun tafi gida. Ba shiri mukayi sallama na
basu kudin napepk hade da kayan makulace da
na zuba musu a leda har bakin get na raka su.
Nace ko me kenan gobe dai zasu ji ni a waya.
mukayi sallama suka tafi. Na kulle gidan na koma
ciki nan take na hau zirga zirga ina kulla yandda
zanyi in kona Inna Indo cikin sauki. Ba wuya
magariba tayi amma ni gani nake lokaci baya
gudu domin jira nake kawai gobe tayi in kona
Inna indo kamar in jawo goben nake ji.............
...............


Hhhhhh Dankari makarin fa kenan, Ai Khadija ba
ke kadai ba.Ni kaina King so nake gobe tayi naga
yadda zaku kare ke da Inna Indo. Masu karatu
nasan kuma haka ku dai biyo Autan writers gobe
zan kwaso muku labari in an kona Inna Indo in
ma ba a kona ta ba

Post a Comment

0 Comments

Ads