NI DA FATALWA Part 5 Hausa Novel

      ↫ NI DA FATALWA! ↬

          {gajeran labari}

Part {5}

@KINGBOY ISAH
 
 
  *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*

(KU CI GABA DA HAKUR DA NI DAI. KUNSAN WAYATA BATA AMFANI SAI IN AKWAI NEPA. JIYA KUMA BA NEPA SHIYASA KUKA JINI SHIRU Autan writers ne)


 Hade da cewa "Innah Indo ke kuma fa Fatalwar bata taba tsorata ki bane halan". Ta yi murmushi wanda ya fito da jajayen hakoranta waje, Fuskar ta wani yamutse abun tsoro sannan tace "Watarana ina zaune a tsakar gida bayan isha'i na gama tuwo na da miya ina jiran mai gidana kurum sai ji nayi an yi sallama. Lokacin na dai ji ana cewa akwai fatalwa a nan amma ban taba ganinta ba hakan ne ma yasa bani da tsoro a sannan. Na amsa sallama. amma sai naji shiru ba a shigo ba.Aka kara sallama na kara amsawa ba a shigo ba sai da akayi sau biyar ina tambaya wacece amma ba cikakkiyar amsa sai dai naji ance ni ce. hakan tasa na mike hade da daukar torchlight dita na nufi zaure na hahaska ko ina amma banga kowa ba har kofar gida na haska banga kowa ba. Kawai ina komawa sai naga wani abu fari kamar mutum a zaune wajen da na taso. Nan take jikina ya fara karkarwa domin nasan ba kowa a gidan kuma yanzu na ta so, Hakan tasa na bude baki a hankali nace "Mine ne a nan?". Sai ji nayi anyi wata yar guntuwar dariya. Na kara cewa miye a nan?. Sai gani nayi abu ya mike sama wai ashe fatalwar ce. Na juya a guje na shiga makwabta. Ina zuwa zauren gidan ta mukayi karo da ita itama ta fito a guje wai fatalwa ta je ta kwanta mata a kan gado. Ba shiri muka fito a guje. A ranar dai ba irin wahalar da fatalwar nan bata bamu ba tsoro kuwa har suma sai da nayi. Bayan wannan ma cikin dare in na fito fitsari na sha ganinta da fararren kaya a zaune ko a tsaye a tsakar gida. Ranar nan munje gidan biki mukayo dare wajen karfe sha daya muka taho ni da Makwabciyata muna tafe a kasai tsoro ya cika mu sai sauri muke a saitin makabartar nan a muka ga fatalwar da bakar doguwar riga abun tsoron babu kai a jikinta. Muka kara sauri ni kam dan tsoro kamar in tashi sama. lokacin fa ban tsufa sosai ba. Kawai sai ji mukayi fatalwar nan tace kai ku zo nan". Cikin duhun dare ai kuwa sai muka zabura da gudun bala'i ai kuwa fatalwar nan ta biyo mu. babu kai a jikinta tana kiran mu tana dariya". Wani motsi naji a bayana ai kuwa na daka tsalle hade da kwada ihu. domin nayi matukar tsorata. Inna Indo ta bushe da dariya ni kuwa ido wuri-wuri na kama kallonta. ji nayi tace naje na dan debo mata ruwa. nace to abun mamkin kafin naje kitchen na daukko mata ruwan ina zuwa sai tararwa nayi falon wayam. na leka waje naga gida a rufe. a guje na koma daki na kulle. Wayata na dauka na kira Aunty Hauwa duka daya ta dauka. "Hello lafiya dai Khadija ya naji kina huci? ko fatalwar ce?". Nace "Eh wallahi wata mata ce take zuwa gidana mai wani hijab fari dogo. in kin ganta abun tsoro ni wallahi inaga ma itae fatalwar saboda fa sai na kulle gida amma sai kawai na ganta a cikin gida, Kuma in ta zo ba labaran da take bani sai na fatalwa wallahi na fara gajiya". "Shegiya mahaukaciya maza dai ki tsaya a gidan nan naki fatalwa ta kashe ki. Ai ni wallahi ko a mafarki naga na sake bin hanyar gidan ki sai na tashi na yi addu'o'i da nafiloli. Wai ke me yasa ba zaki dawo gida bane? Ya zaki tsaya gida sai ke da Fatalwa". Nace "Aunty Hauwa ke kanki kinsan halin Abban mu wallahi in na zo gida a kan wannan dalilin dan banzan duka zai yi mun kuma ya koro ni. Gashi shi kuma Habib yaki fahimta ta ni wallahi addu'ah nake ma Allah yasa shima fatalwar nan ta tsorata shi nasan a lokacin zai gaskata ni". Karan kwankwasa gida naji da karfi hakan yasa na mike a firgice. daga can Aunty Hauwa tace "Miye akayi". Nace "Wallahi gida naji ana bugawa watakil ma fatalwar ce". Dull sai ji nayi wayar ta katse. Na sake kira na dauka network ne ke rawa wai ashe Jin nace ana knocking watakil ma fatalwa ce yasa auntu Hauwa ta kashe wayanta. A hankali na fito daga falo bayan na gama leke-leke kamar marar gaskiya. A lokacin dan kwakkwaran motsi zanji kawai in ara a na kare. daga bakin kofa na fara fadin "Waye? Waye?" Shiru naji ba ayi magana ba an kuma kara kwankwasa gidan. A zuciya nace yau na shiga uku wai ni me nayi wa fatalwr nan ne da bazata bar ni in zauna lafiya ba?". "Waye ne?". Na kara fada da karfi cikin fada naji Habib yace "Dallah can sarkij tsoro ki zo ki bude gida waye zai zo yanzu in ba ni ba?". Shima a tsorace na karasa a hankali na bude sai da na leka naga shin sannan na bude sauran kubobin. Dariya yayi hade da cewa "To sarkin tsoro ni wani abu na manta na zo dauka"? Nayi murmushi hade da cewa "Ba zaka gane bane habib sai ranar da fatalwar nan ta makure ka". Yayi murmushi hade da cewa "Malama ba wani fatalwa kawai dai tsoro ne irin naku in ma fatalwar ce ai ina da addu'ah". A zuciya nace "Baka san lokacin da abun tsoron ya zo ji zakayi kamar an mantar da kai duk addu'o'in ba kenan. In takaice muku labari sati daya nayi a gidan Habib cikin tsoro da fargaba wataran kullum kuma Innaa Indo sai ta zo gidan nan haka kuma kullum da kalar salon labarin tsoron da take zuwa da shi. Tsakar dare kuwa daga inga fatalwa a tsaye sai inga Fatalwa kusa dani a kwance. mafarkai kuwa gasu nan barkatai ba irin wanda banayi. na taba yin mafarkin munje cikin makabarta ni da Inna Indo wai tace in shiga cikin kabarinta ni kuwa naki shiga kawai sai ji nayi an tura ni ciki da karfi. Ni tsoro ba irin wanda ba a bani ba. Wataran inga bakar mage da jan ido tana kukan gadawaa wataran inga mage na tafiya ba kai. Yau ma kamar kullum Inna Indo ta zo ta gama zazzaga labaranta na abun tsoro ta tashi ta tafi. Ina zaune a Falo naji shigowar waya kawayena ne su uku suka ce gasu nan zuwa zasu kawo min ziyara ne.................

Hhhhh yan kawo ziyara, Allah yasa dai ku fice lafita.lol

Post a Comment

0 Comments

Ads