NI DA FATALWA PART 4 Hausa Novel

     ↫ NI DA FATALWA! ↬

          {gajeran labari}

Part {4}

@KINGBOY ISAH
 
 
  *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
  
 

Nace "Aunty Hauwa ki daure ki matse shi wallahi ni dai in kika fita fatalwa ta kamaki ba ruwana" Karan tusa naji. Aunty Hauwa kaman tayi kuka "Wallahi ya matsen Dan Allah muje ki rakani na rantse in ba haka ba a wando zanyi". Da sauri Habib ya mike zaune yace "Khadija maza tashi ki raka ta". Na tashi zaune nace wallahi ni dai bazan iya zuwa ni kadai ba dole sai dai a tafi da kai domin nima tsoro nake ji". "Khadija kina da hankali bn dakin zan bi ku?. Dallah kinga ki tashi ki rakata muje na jira ku a kofa. Haka muka tashi a tsorace sai waige-waige muke. Aunty Hauwa na tura kofan ban dakin tayo baya da gudu. Habib yace "Miye kuma?" "Faa.... tall... wa". Ta fada cikin in'ina Habib da shima zuwa yanzu ya dan fara tsorata a hankali yaje ya tura ban dakin ya tura kafar haggun gaba ya dan like kamar marar gaskiya, ganin ba komai ya juyo yayi tsaki yace "Kawai tsorata kukayi amma ba komai a ciki". Da kyar aunty Hauwa ta shiga kusan sau uku tana shiga tana bazowa da gudu daga karshe dai tare muka shiga na juya baya nima tsorace tayi toilet din Habib na jiran mu a kofa sannan muk fito. Bayan mun kwanta wani irin kara muka ringa ji daga falo kamar kuka kamar dariya ba shiri na kara makalkale Habib Aunty Hauwa ta makalkale ni itama. A daren nan bamuyi barcin kirki ba. Kiran sallar fari Aunty Hauwa tace gida zata da kyar muka lalabata ta tsaya sai karfe shida Nima ban yarda an barni a gidan ba tare muka shigo mota aka kawo ta gida sannan muka koma. Wajejen karfe goma lokacin Habib tuni ya fita aikj zaune nake a Falo rike da waya ina chat da kawayena whatsapp amma sam ba a cikin natsuwa nake ba kallo daya zaka mun kq tabbar da hakan, "Salamu Alaikum" Naji ance durum! Gabana yayi mumunar faduwa Inna Indo ce ta shigo yau ma dai cikin dogon hijabinta fari har kasa. Fuskarta kam kallo daya nayi mata na kauda kai dan tsoro. Abun da ya dugunzuma hankalina shine ta ina matar nan ta ke shigowa bayan kuma yau ma na tabbata na makala kubabin gidan baki dayansu?. "Wa'alaiki salam" Na amsa sallamar hade da cewa ga waje zauna. Bayan ta zauna ne nace "Inna Indo naga na rufe gidan da kubobi ta ina kika shigo?". "Aa ni kuma ai a bude na ganshi leka ma ki gani a bude yake". Na tashi na dan rabe na wuce, abun mamaki kuma tabbas gidan a bude yake. bayan na dawo na zauna n naji tace "Ki daina barin gida a bude fatalwar nan da rana ma fa zata iya shigo miki gida". Nace "Wallahi nima na rufe". Sai ji nayi tace "Kin san me ya faru da matar da ta zauna a nan gidan ta biyu kuwa?". A dan tsorace nace "Aa". Nan take ta shiga bani labarin. "Bayan matar nan ta farko wacce aka tsorata ita da mijinta sun tashi. Sai wani mutum ya kama hayar gidan nan dan kasuwa ne shi sai karfe sha dayan dare yake dawowa gida. Yana da mata da yara biyu, Wata rana wajejen karfe sha dayan dare lokacin mijinta bai dawo gida ba yaranta kuwa tuni sunyi barci, Itama din ta kwanta har ta fara barci kawai sai taji kamar ana surutu a falo. To lokacin nepa basu kawo wuta ba. Fitila dayace kuma suke da babba. hakan yasa ta tashi ta sauko daga kan gadon ta dau fitilar nan ta nufi falo. Tana zuwa falo sai tayi curus sakamakon ganin wasu mutane biyu masu fararen kaya a zazzaune kan kujera sun juya mata baya wato bata ganin fuskarsu". Tuni tsoro ya rufe ni nace "Inna Indo kuma ba mijinta bane?". Tace "Tsaya kiji mana, Lokacin da ta gansu sai tsoro ya kamata cikin muryar tsoro tace "Su waye?". Maimakon taji an manta magana sai ji tayi su biyun sun gagabe da dariya, Tsoro ya rufe ta kamar zata ruga cikin daki a guje amma sai ta dake a tsorace ta kara furta "Su waye". Nan take taji sun kara fashewa da dariya kuma sai gani tayi su biyun sun mike tsaye a tare. Mata ne gashin kansu baki wul ya zuba kan bayansu kuma duk dogayen riguna ne farare ajikinsu. Matar nan taji sunyi shiru hakan yasa ta kara magana sai kawai gani tayi kawunan su sun juyo baya maimakon su waigo. Fuskokin su abun tsoro ba kyan gani domin sam ba irin fuskokin mutane ne da su ba. Wani irin dogon hanci ne lauyayye da shi bakin kuwa wangameme ga wasu hakora sun zuro daga ciki jini na zuba idanunsu kuwa jawur gasu da girma. Abun dai baya lissafuwa. ". Nace wayyo Allah na, basu kashe ta badai ko?". Tayi dariyar nan wacce tafi haushin kare ban tsoro hade da cewa "Ai tana ganin haka sai jikinta ya hau rawa ta koma daki a guje. Tana zuwa dakin ta iske wannan halittun a kan gado kusa da yaranta a kwance a nan wajen ta sulale kasa sumammiya. Lokacin da mijinta ya dawo ya tayarda ita kuwa ta hau rikici tace wallahi bazata kwana a gidan ba ta tashi. Ai kuwa haka akayi tun a daren ta kwashe yaranta suka bar gidan da safe sai canza gida mijinta yayi har yau bata ko yarda ta biyo ta nan kofar gida". Na sauke ajiyar zuciya hade da cewa "To ke kuma fa Inna Indo fatalwar bata taba tsorata ki bane halan". Tayi murmushi wanda ya karawa fuskar tata ban tsoro tace..................................

Zanci gaba

Post a Comment

0 Comments

Ads