NI DA FATALWA PART 3 Hausa Novel

      ↫ NI DA FATALWA! ↬

          {gajeran labari}

Part {3}

@KINGBOY ISAH
 
 
  *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
  
  [WARNING; MAI TSORO KAR TA KARANTA. IN KUMA TSORON BA SOSAI BA TO KI KARANTA DA RANA]
  
Ai tuni ta fara karkarwa, Kuuwwuuuuuu! karan da taji ya wuce shiff! ta gefan kunnenta kenan da sauri ta waiga sai bata ga komai ba. Tuni ta fara karkarwa amma tsabar maita taki hakura da kallon. Ji tayi an shafi bayanta da hannu. Bata san lokacin da ta saki dan kara ba. Karan yayi sanadiyar fitowar mu ni dai dama a tsorace nake ina kankame da Habib domin ko sanda muka shiga daki ma a like da shi nake kamar cingum. "Aunty Hauwa lafiya naji kinyi kara". Habib ya tambaye ta, Rau-rau tayi da ido ta hade tsoron ta hade da kakalo murmushi "Lafiya lau wallahi wani abu ne akayi a film din nan da ya burgeni shine fa nayi karar jin dadi". Habib yayi murmushi "Lalai aunty Hauwa ke ko gajiya ma bakya yi da kallo? Yanzu fa karfe sha biyu da rabi. Mu dai tuni mun kama gobe". Habib ya fada hade da komawa cikin daki. A yanayin da naga Aunty Hauwa na tabbata a tsorace take naje nayi mata tambayar duniyar nan amma tace wai ba tsorata tayi ba. na lurs dai bata so na gano ta tsorata watakil dan kar na rama dariyar da tayi mun. Tayi nayi na nufi dakina dama gidan falo ne sai dakuna uku wanda ko wanne akwai bandaki a ciki sai kuma kitchin. nace Aunty Hauwa in zaki kwanta dai kiyi addu'ah ni dai na gaya miki halin gidan nan". Aunty Hauwa tuni har jubi ya fara keto mata domin ta tsorata matuka kallon take amma bata fahimtar abunda ake yi ma. hakan yasa ta kashe TV din ta tashi ta nufi dakin baki inda Na share mata domin ta kwanta. Ta fara tafiya ta je tsakiyar falo kenan nepa suka dauke wuta dif hakan yasa ta tsaya cik! tayi saurin latsa switch off na wayar tana karkarwa amma sai wayar ta subuce daga hannunta ta fadi kasa. Aunty Hauwa tsoro ya kamata kamar zata fashe da kuka tsabar tsoro ta tsugunna ta hau laluban waya. Karar tafiya taji kamar anyo wajenta hakan yasa ta fara cewa "waye waye". amma shiru bata ji ance komai ba. "Me kike nema a cikin duhun nan". abunda taji an fada da muryar mace kenan a zaton ta ni ce hakan yasa tace "Khadija wallahi wayata ce ta fadi shine nake nema domin duhu yayi yawa bazan gane hanyar dakin ba". Dai-dai wannan lokacin nepa ta dawo fuw! aka kawo wuta bisa mamaki sai gani tayi bata ga kowa ba da sauri ta dauki wayarta ta ruga daki a guje tana shiga bata tsaya dubawa ba ta banko kofa jamuluck ya shiga. Juyawar da zatayi sai tayi arba da wata doguwar mata siririya wacce take sanye da wata doguwar riga fara sai wani mayafi da ta yafa a kafada gashin kanta duk ya barbazu a bayanta dake matar ta juya ne Aunty Hauwa bata ganin fuskarta. Nan take gabanta ya fara dukan uku-uku duk illahirin jikinta ya dau rawa. "Wace ce". Aunty Hauwa ta fada cikin muryar tsoro dake fitowa a hankula. Shiru taji Matar batayi magana ba. Ta sake maimaita tambayar har sau uku, a na hudun kawai sai matar ta juyo fuskarta fari fat kamar wacce ta shafagari amma kuma idanunta ko kadan ba fari a ciki baki kirin da su ga wani irin gashin gira dogo da Aunty Hauwa bata taba ganin kalarsa ba tunda take. "Ni ce Fatalwa Indo". Abunda matar ta fada kenan. "Wayyo Allah na dan Allah dan annabi fatalwa kiyo hakuri ban san nan dakin ki bane. Na rantse yanzu zan fita". Kulululu cikin Aunty Hauwa ya kada sai zawo kafin kace me tuni ta jika zanin ta da fitsari. Ita sam ta kasa yin addu'ah kamar an mantar da ita kuma ta kasa bude dakin ta fito a guje. Kawai sai ihu take. Fatalwar nan kuwa ba abunda take sai kyalkyala dariya. Ni da Habib muna daki har barci ya fara daukar mu muka jiyo ihun Aunty Hauwa can kasa-kasa. Dake ni na fara tashi nayi sauri na tada Habib nace ihu nake ji. Yace "kwarai kuma kamar a gidan nan ma". Da sauri ya tashi ya yo falo ni ma da nake a tsorace a guje nabi bayansa. Mukaje kofar daki mukayi mukayi Aunty Hauwa ta bude amma ta ki budewa ihu take har muryar na shakewa. Da gudu Habib ya koma domin ya daukko makolin dakin nima kuwa na bishi dan bazan yarda ya barni ba wannan yanayi. Muna dawowa mukaji Aunty Hauwa ta daina ihu. Habib na budewa muka tarar da Aunty Hauwa bakin kofa a yashe a kasa ga dukan Alamu dai suma tayi Habib ya debo ruwa ya yayyafa mata ta farko. Hade da sakin razanannen kara. Sai kawai gani mukayi ta tashi ta baza a guje ta fito daga dakin tayi hanyar kofa. Da sauri Habib ya riko hannuta. "Ina zaki Ke Hauwa lafiya kuwa". Habib yake yake tambayar ta cikin tashin hankali. Ita kuwa kokarin kwacewa take kamar mai aljannu sai kuka take tana fadin "Wayyo Allah ka barni in tafi gida fatalwa wallahi bazan kwana a gidan nan ba". Nima tambaya nake lafiya lafiya amma ina hankalinta ya matukar tashi ga dukkan alamu dai tayi matukar razana ne. Habib ya juyo yana tambayana wai ko tana da iskokai ne ai kuwa ta gallamai cizo a hannu dan dole ya sake ta ta ruga da gudu waje na bita a guje ina fadin ta dawo. Kafin ta kai gate naga taja wani uban birki ta saki razanannen kara. Ta juyo a guje, Nima ihun na saki na juya a millon sakamakon ganin abunda ta gani. Fatalwar nan ce zaune cikin fararen kaya tasa wani abu wanda shima kamar gawa ce dai cikin likafani sai dariya take hasken glof din tsakar gida ya haska mana ita. Sai gamu muna tsere da Aunty Hauwa da da take niyar bude gida ta gudu. Ina zuwa na rukunkume Habib ina fadin "Fatalwa Fatalwa". Aunty Hauwa ma da gudu ta zo ta makalkale ni. Habib yace "Wai ku wane irin mutane ne in ma fatalwar ce ba zakuyi addu'ah ba sai ihu?. oya ku sake ni naje na ga miye". Ai maimakon in sake sa ma kara rukunkume shi nayi.Aunty Hauwa da sai maida numfashi take hauwaye kam sun cika fuskar share-share. itama kara matse ni tayi kam. Nace "Dan Allah karkaje Habib Fatalwa ce". Tsaki yayi yace "Oya to muje dakin iyayen tsoro ku kama karanta ayatul qursiyyu. Ai tun kafin ya rufe baki Aunty Hauwa kamar an kunnata ta fara karantawa. A haka muka tafi daki kamar yara Ni ina rike da Habib Aunty Hauwa kuwa na rike da ni. Mukaje wajen kwanciya aunty Hauwa ta kwanta a kasa tace Alquran ba mai raba ni da ita. Habib yace to mu kwanta a kan gadon shi zai kwanta a kasa. Ni ma nace wallahi ba zan rabu da kai ba, ni da Aunty Hauwa ai duk jirgi daya ya kwaso mu tunda itama fatalwar ta rainata. Ba yanda baiyi ba a kan shi ba zai kwanta gado daya ba da Aunty Hauwa Amma abu yaci tura domin nima nace bazan rabu da shi ba itama kuma bazata rabu dani ba. ganin muna shirin yin kwanan zaune ga barci a idanunmu sannan ya aminta ya kwanta can gefan ni kuma na rungume shi aunty Hauwa itama ta kankame ni. ya zmana ni ce a tsakiya. Aunty Hauwa a jike take sharaf da fitsari amma tsoro baza zai barta ta canza ko nawa ne bama. rokon Allah kawai take gari ya waye ta bar mana gidan. Cikinta ne yayi kara kulululuuuu "Aunty Hauwa lafiya kuwa". Tace "Wallahi zawo ne kuma bzan iya shiga toilet ba ni kadai wallahi tsoro nake ji. g zawan ya matse ni"..............


Post a Comment

0 Comments

Ads