NI DA FATALWA Part 2 By Kingboy Isah

      ↫   NI DA FATALWA!    ↬

          {gajeran labari}Part {2}

@KINGBOY ISAH

 note; 
Mai tsoro kar ta karanta!...
 
Maganar matar nan ce ta dawo dani daga tunanin da nake, "Shin kinsan me ya faru da matar da ta fara zama a gidan nan kuwa?". Na kada kai alamun Aa. "Itama amaryace kamar ki tun ranar da aka kawo ta gidan nan fatalwa ta fara firgita ta. Wata rana da daddare mijinta baya nan ya tafi wajen aiki bai dawo ba har dare wajen magariba. Tana zaune a falo ita kadai tana kallon tv kawai sai gani tayi wuyar dakin ta dauke, nan take fanka ta fara wulwulawa da karfi. Yarinyar nan tsoro ya kamata kawai gani tayi TV ta kawo ciki kuwa wata doguwar mata ce mai dogayen faracina domin farcen ta na hannu har kasa yake tabowa gashin kanta kuwa baki ne wulf amma yana da tsayi sai hakora zako-zako abun tsoro". Ina jin haka tuni na makalkale kafafuna kan kujera na kame waje daya kamar ni ce naga fatalwar. "Kina ji nan take sai fatalwar nan ta cikin TV ta kyalkyale da dariya mai firgitarwa yarinyar nan ta kwalla ihu ta yunkura zata tashi amma sai taji kamar an daure ta. Fatalwar nan ta daka mata tsawa tace "Ina zakije? ko ina zaki ba zaki guje mun ba sai kin gaya mun dalilin da yasa kuka shigo mun gida. Yarinyar nan ta fashe da kuka tace "Dan Allah kiyi hakuri wallahi bansan nan gidan ki ne ba" fatalwar nan ta bushe da dariya kawai yarinyar nan sai gani tayi fatalwar ta zuro hannu daga cikin TV zata kama ta kawai sai ta sulale kasa a sume". A firgice nace "Wayyo Allah na Fatalwar ta kashe ta?". Matar tayi murmushi tace ai ita bata kashe mutum sai dai ta basa wahala domin tana ganin yarinyar nan ta  suma sai ta barta. shi kuma mai gidanta wata rana yayo dare karfe goma ya nufo gida sai sauri yake domin shi kanshi tsoron unguwar yake kasancewar dare yayi ga kuma duhun dare. yana cikin tafiya kwatsam sai ganin wani abu yayi fari tass a gaban shi. Da ya lura da kyau sai yaga kamar mutum ne a kwance cikin fararen kaya hakan yasa ya tsaya cik ya fara cewa "Waye a nan? waye ne". amma sai yaji shiru hakan tasa ya dan rabe da nufin yabi ta gefe ya wuce bai sani ba ashe fatalwa ce, Ya kusan wucewa kenan ta mirgina ta rike masa kafa a lokacin ta dago fuskarta abun tsoro da gashi baja baja ta fashe da dariya marar dadin saurare. suna hada ido kuwa ya kwallah ihun neman agaji amma ina ba wanda ya kawo mai dauki domin kowa yasan halin unguwar nan ba a zuwa da dare daga bakin isha'i duk wanda ya fito to ba shakka sai ya hadu da fatalwar nan". Ai tuni jubi ya kwaranyo min. naji tsoro ya dabai baye ni. Nace "To Inna Indo ya kike ganin za'ayi domin nima na ganta wata abun tsoro mai fararen kaya jini na zuba a idonta". Wata irin dariya naji Inna ma'au ta kyalkyale da ita wacce har sai da ta ban tsoro ma. "Kwarai yarinya kin ganta domin nima ina ganinta sosai jarumta nake kawai ina nuna mata rashin tsoro. Yanzu dai mafita daya ce ku tattara ku bar gidan nan in ba haka ba komai zai iya faruwa daku kullum kina cikin tsoro ne da fargaba. Yauwa yar nan ni bari na tashi na shiga gida gobe ma zan zo in dan debe miki kyauwa". Inji Inna Indo ta fadi haka hade da mikewa ni tuni tsoro ya kamani ita kanta tsoronta nake domin hijab din jikinta yayi kama da likafani gashi fari har kas. Tana tashi tayo waje nima na dau wayata na biyo ta da sauri domin in rufe kofar gidan. Wani sabon tsoron ne ya kara ziyarta ta domin gani nayi Babu Inna Indo gashi banji karar bude gida ba haka kuma na duba naga kubobi a makale kamar yanda nasa su dazun. Bansan lokacin da kuka ya kubce mun ba. da sauri na kira number Aunty na Hauwa. dake tana gida sun sama sabani da mijinta. "Hello amarya kinsha kamshi sai yau aka tuno damu wata amarci yasa an manta da mu ma". itace mai fadar haka kuka taji na fashe da shi ina fadin "Aunty Hauwa Dan Allah kizo yanzu akwai matsala wallahi". "Kuka kike khadija? Me ya faru ne? Innalillahi gani nan zuwa". Daga ji hankalinta ya tashi amma kin kashe wayar nayi domin tsoron da nake ji ya baci. Ban koma daki ba ba dadewa sai gata ta iso a napepk nayi sauri na bude mata kofa ta shigo tana tambayana. ban mata magana ba sai da naga mun shiga falo nace "Aunty Hauwa Wallahi gidan nan akwai fatalwa. Ni na ganta da ido n kuma yanzu wata mata ma ta shigo itama abun tsoro, take bani labarin akwai fatalwa. A gidan nan shiyasa na kira ki dan wallahi bazan iya zama ni kadai ba. dama sai da nace wa Habib ya barni na tafi gida yaki". Aunty Hauwa ta kwashe da dariya ta dade tana yi na tambaye ta me take wa dariya?  wai ni take wa dariya domin ita ma wai bata yarda akwai fatalwa ba ni kuwa na kyale ta nace naji din. Haka muka wuni duk inda tayi ina biye da ita bana bari ta bace mun a gani ko kadan. Da yamma Habib ya dawo daga aiki suka gaisa da Hauwa bayan sun gaisa ne take bashi labarin zuwana da kuma irin tsorona nan fa suka hadu su biyun sukai ta mun dariya ni kam kallon su kawai nake domin ni kadai naga abunda na gani. Aunty Hauwa tace zata tafi gida na kuwa tashi hankali nace wallahi bazata tafi ba sai dai ta tsaya a nan in yaya habib ya tafi aiki ta ringa taya ni hira. Da kyar na samu na shawo kanta ta yarda da hakan a kan zata tsaya ta kwana din. Wani irin dadi naji da kaina naje na gyara mata dayan daki wanda dama saboda baki aka tanade shi. Da dare bayan munci abinci mun dade a falo muna hira sai wajen sha daya tukun muka shiga daki nida Habib Aunty Hauwa kuwa mayyar kallo tace sai ta tsaya ta idasa kallon wani indian film da ake a bollywood wani irin kuka kuka kamar na jariri ta fara ji kafin wutar dakin ta dauke dif lokaci guda kuma sai ta dawo. Wata irin firgita Aunty Hauwa tayi da ta tuna cewa Khadija ta fa gaya mata akwai fatalwa a gidan nan.................

ZANCI GABA

Post a Comment

0 Comments

Ads