NI DA FATALWA Part 1 Hausa Novel

      ↫ NI DA FATALWA! ↬

          {gajeran labari}

Part {1}

@KINGBOY ISAH

 

NOTE:
IN KASAN KANA/KINA DA TSORO KARKA/KI KARANTA. DOMIN LABARI NE MAI CIKE DA ABUBUWAN TSORO DA NA DARIYA. IN KUWA KA KARANTA KAYI MAFARKIN FATALWA BA RUWAN KING.LOL


"Habib da gaske wai fita zakiyi ka barni ni kadai? Wallahi na gaya ma akwai fatalwa a gidan nan, ni fa na ganta da idanuna dan Allah in dai fitarka ta zama dole to ka barni in tafi gida da yamma in ka dawo daga wajen aikin sai ka biya ka dauko ni kaji angona tsoro nake ji". Tsaki naji yaja abunda bai taba mun ba tun kafin ma muyi aure balle yau da na zama amaryarsa yau duka kwana takwas nayi a gidan nasa. "Khadija naga alamun so kike ki bata mun rai kuma nima in bata miki. Wai ku mata me yasa komai sai kun canfa shi ne? Shegen tsoro ne ya miki yauwa amma ba wani fatalwa a gidan nan, ni a rayuwata kwata-kwata ma ban yarda cewa akwai fatalwa ba. Ni zan tafi kuma wallahi in kika yarda kika sa kafa kika fita daga gidan nan ko? Zakiyi mamakin hukuncin da zan yanke". Yana fadar haka ya shige motar sa ya fita sannan ya dawo ya rufe get din. Da sauri na karasa bakin get din na zukulkula kubobi hade da kule get din. Zuciyata cike take da tsoro amma ya na iya? zaman aure ya ja mun. Shima Habib sai da nace ya nema wani gidan- ya nema wani gidan amma yaki gida kusa da makabarta ai dole ma fatalwa ta takura ma. Tsaye nake tsakar gida ni kadai nake zancen zuci. Ta wutsiyar idona na hangi kamar wani farin abu ya shigar mun daki. Hakan tasa na nufi dakin a tsorace na bude labule. Sai da na leka ko'ina a falon naga ba kowa sannan na sauke ajiyar zuciya. Domin bana mantawa sau biyu naga fatalwar nan kuma fararen kaya ne a jikinta. Jikin socket ma naje na ciro wayata na bude data na kwanata kan kujera sofa, na shiga whatsapp na fara chat da kawayena domin shi ne kadai nake tunanin zai deben kewa. Message naga ya shiga na bakuwar number nayi saurin shiga hoto ne aka turo ba sallama ba komai. Na sa hannu na danna kan hotan don ya bude. Ihu na kwada hade da yin wulli da wayar. Domin kuwa hotan wannan fatalwar ta jiya ne na gani. Da gudu nayo waje daga cikin dakin. Fitowata yayi dai-dai da sallamar wata mata. Turus na tsaya ina maida numfashi ina kare mata kallo wani dogon farin hijabi ne dogo a jikin matar gata doguwa. Girman idanunta kadai abun tsorone gata dattijuwa. Cikin tsoro muryata na rawa na amsa sallamar. Sai ji nayi tace "Sunana Indo ni makwabciyar ki ce ga gida na nan gaba da gidan ki. Gani nayi an kawo amarya yau har kwana takwas nace bari na leko mu gaisa". murmushin karfi da yaji nayi cikin karfin hali nace "Bismillah to mu shiga ciki". Gabana ne ya fadi da na tuna cewa na fa kulle gidan nasa kubobi da jamuluck amma ta ina matar nan ta shigo anya kuwa ba fatalwar bace? na tambayi kaina da kaina tambayar da bata da amsa. Sofa na nuna mata nace ta zauna ni kuma na daukko mata juice a cikin kofin glass a tsorace na kawo gabanta na ajiye sananan na koma Can kuryan falon kan archair na zauna domin a matukar tsorace nake da matar nan. "Amarya banga angonba ko ya fita ne". abunda matar nan tace kenan da muryarta marar dadin saurare. "Eh dazun ya fita office". Na bata amsa. "Kina nufin ke kadai aka bari a gida? bakisan akwai fatalwa a gida nan ba". Tuni tsoro biyu suka farmake ni. Ga tsoron matar nan ga kuma ta kara tabbatar min da zargina."Fatalwa kuma Inna Indo? ashe da gaske akwai fatalwa dama sau biyu ina ganinta na fadawa Habib amma yace wai tsorata nayi". "Ba tsorata bane bari kiji na baki labarin gidan nan". Na kara gyara zama hade da mika hankalina gare ta, ta fara da cewa, "gidan nan gida ne mai hatsari nan baya da shekara biyar aka gida shi. kinga ai katanga daya ta raba ku da makabarta ko". Nayi saurin girgiz kai Alamun eh. "To da nan gidan da kike ciki makabarta ne an taba binne wata mata ce a saitin gidan nan. Matar nan kuma itace take fatalwa taki barin a zauna a gidan nan. Fatalwar nan tana da matukar hatsari gata da siffofin tsoro na tabbata mijinki ma bai san cewa haka gidan nan yake". Wani sabon tsoro ne ya sake ziyartar zuciyata lokaci guda, na daga kai ina kare wa gidan kallo. A raina nace ko habib yana so ko baya so wallahi sai ya canza min gida. taya zan zauna a gida Ni da fatalwa?...................

Autan writers ne...

Post a Comment

0 Comments

Ads