Ga Matar Data Auri Mijin Daya Fi Karfinta Ga Hanyoyin Da Zata Bi

 MATAR DA TA AURI NAMIJIN DA YAFI KARFINTA YAYA ZATAYI?? TAMBAYA TA 3056

*******************

Assalamu alaikum

Don Allah tambaya na anan shine menene hukunci matar da ta auri mijin da yafi karfinta lokacin jima'i?? Yaya zatayi? 


AMSA

*******

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. 

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Idan har fin karfin yakai yadda yana chutar da lafiyarta, ko haddasa mata raunuka a gabobinta na jima'i, kuma babu damar da zata iya jurewa ko kuma shi mijin yabita ahankali, to addini ya bawa wliyyan auren damar u zauna atsakaninsu domin u sulhuna u samar da mafita ga wadannan ma'auratan kamar yadda umurnin yazo acikin suratun Nisa'i.

Karanta>>> Amfanin Cin Ƙwai Kafin Saduwar Aure

Amma idan ya zamto dama Qaramar yarinya ce wacce shekarunta basu yawaita ba, Ko kuma budurwa ce wacce bata ta'ba sanin 'da namiji ba,  zata iya yiwuwa hakan yana faruwa ne ta dalilin Qarancin shekarunta da rashin sabawarta, kuma dama irin wannan yakan faru sosai musamman ga matan da suka tsare mutuncinsu kuma akayi aurensu tun suna da Qananan shekaru. 

Karanta>>> Dalilan Dake Zawo Rashin Sha'awa Ga Mata

Tabbas idan ta fahimtar da mijin nata halin da take ciki, wato yanayin wahalar da take fuskanta, shi kuma sai ya sassauta mata ya bata lokaci ta huta, kuma ya rika mu'amalantar iyalinsa cikin tausasawa da sassautawa har dai ta saba. 

Karanta>>> Ingantaccen Matsi  Da Bashi Da Illah

Da haka da haka har zata goge, shikenan komai zai daidaita... 


Amma ita matar ta guji bin miyagun shawarwari daga Qawayenta. Musamman Qawar da ta ta'ba yin aure ta fito. Mafiya yawansu suna bin gidajen sabobbin amare ne domin su hure musu kunne. Gara idan an bi dukkan hanyoyin da zaaka fa'da asama mma ba'a  samu mafita ba, to tana da damar neman rabuwa dashi ta hanyar saki daga gareshi, ko kuma Khul'i agaban alkali. 

Karanta>>> Amfanin Ƴaƴan Gwanda Musamman Ga Mata

Masu tambaya kumin magana ta inbox

Post a Comment

0 Comments

Ads