ALJANIN ABOKINA Part 6 By Ameesha MD

ALJANIN ABOKI NA) MALLAKAR AMEESHA MD

To be continued..

Dauka ta allah ce

06

TRUE LIFE STORY

ALJANIN ABOKINA

Haka mu ka nufi cikin Asibitin jiki na a sanyaye ina ambaton Allah a rai na wani katon dakin jinya mahaifin mu yai mana jagora mu ka shiga .abinda idanuwa na su ka fara tozali da shi ya sanya kafafuwa na gaza daukar gangar jiki na,Muhsin ne kwance akan gadon jinyar jini na fita ta kunnan sa baya ko motsi an saka masa robar shakar numfashi ya rame ya kode farar fatannan tasa kamar ka taba fatar jini ya fito ta koma baka kirin, idan baka san sa a baya ba ka gansa a wannan lokacin sai ka rantse ba fari bane hatta ni da na ke baki na tabbata a lokacin fata ta, ta fi tasa haske.

tabbas ko kai zuciyar firauna gare ka idan ka gan sa a wannan lokacin sai ka tausaya masa ban san lokacin da na fashe da kuka ba mahaifi na ya ja hannu na zuwa wajen amma na ki karasawa kasancewar kashedin da Aljanin na sa ya min na raba ni da duniya idan har na kusanci inda ya ke ,nan mahaifiyar sa ta shiga lallashi na dan dukan su sun dauka larurar ta sa na ke wa kuka basu san rasa rayuwa ta na ke wa kuka ba ganin ba ni da niyar tashi balle na karasa kan gadon da Muhsin din ya ke ya sanya mahaifin na sa jan hannu na mu ka fito reception din asibitin ya mika min robar ruwa da wata wainar shinkafa mai zafi nan na shiga ci ina korawa da ruwa kasancewar balaaiyar yunwar da na kunso tun daga gida sai da ya tabbatar na koshi na dawo cikin hayyaci na sannan ya soma min magana cikin hikima “na san iyayen ka sun maka bayanin abin da ke faruwa ko?”

Na girgiza kai da sauri cikin zakuwa na rike hannayen sa”ba su fadamin ba dan Allah ka sanar da ni ka taimaka ko zuciya ta za ta fita daga cikin kokonto”

Kallon mamaki ya ke bi na da shi na yadda ya,ga na kidime Ina neman sanin abin da ke faruwa

Ya dafa kafada ta” ka kwantar da hankalin ka Mashkur ba abinda ka ke tunani bane na san za Kai yi zaton Muhsin ne ya mutu to ba haka bane muhsin ya na raye sai dai zamu iya kiran sa da gawa da rai Numfashi ne kawai banbancin sa da gawa Muhsin ba ya cin abinci ba ya shan ruwa ba ya motsi tsawon wata biyu kenan Muhsin ya na bukatar taimakon ka a yanzu“

Ya kalli cikin idanuwa na yayin da nai kasa da kai kirjina na dukan uku_ uku wane irin taimako kuma Muhsin ya ke bukata a waje na bayan ya saka ni cikin tsaka mai wuya baki na,na rawa na ce”wane irin taimako muhsin ya ke bukata daga gare ni”

Alhaji Muwafak wato Mahaifin Muhsin ya sauke ajiyar zuciya”wato tun lokacin da Muhsin ya soma wannan rashin lafiyar ta sa kafin ya yi wannan doguwar sumar Babu sunan wanda ya ke ambata idan ya farka sai kai”innalilahi wa inna ilaihi rajiun abinda na ke ambata a cikin zuciya ta kenan tabbas na kade rayuwa ta, ta zo karshe babu wani muhsin da ya ke ambatar suna na Aljanin sa ne, ya cigaba da fadin“tabbas Da na Muhsin ya na kaunar ka sosai Akwai wani wajen mai magani da mu ka je shine ya ce ya na so ku yi magana da shi wannan ne dalilin da ya sa na roki Alfarma wajen iyayen ka ka zo, nan da awa biyu malamin za su karaso daga kasar gabas abinda na ke so da kai dan Allah duk abinda ya tambaye ka ka fada mai gaskiya”

Na gyada kai, wanda ban san ma na gyada shi ba da sauri na dauki ragowar ruwan da na rage na soma kwankwada.

Ba yacce bai yi da ni ba akan na taso mu koma ciki na ki dan gaba daya tsoron Muhsin na ke ji,nan ya tafi ya barni zaune in saka wannan in kunce wancen gajiya nai da zaman na tashi tsaye ina famar zazagaye asibitin ko zan rabu da tunani .

Kicibus mu kai da Mahaifi na har na dan tsorata ganin shine ya sanya na sauke ajiyar zuciya “mai ka ke anan tun dazu ana ta famar neman ka malamin ya zo”

Gabana ya yanke ya fadi baki na na rawa na ce”ba komai kawai dai na gaji da zama ne”

“to sai ka taho mu je dan ni yanzu ma zan tafi na makara idan an gama komai sai ku kira ni a waya na zo na dauke ku dan nima ba kwana zan yi ba kaya kawai zan kai na dawo “

Nan mu ka nufi saman benan dakin da aka kwantar da muhsin kirji na na famar dukan uku uku .

Mu na shiga cikin Dakin jinyar ina tsoma kafa ta a ciki muhsin ya farka tare da kwarma wani irin gigitaccen ihu na juya zan gudu mahaifi na ya riko ni yayin da Malamin da iyayen sa su ka yo kan sa da sauri nan malamin ya soma zuba mai wani ruwan magani a fuska sunana kawai ya ke ambata tare da zazzare min ido ya na kokarin chakumo ni nan fa hantar ciki na ta soma kadawa hatta likitoci sun yi mamakin farkawar da muhsin ya yi dan babu abinda basu yi masa ba dan ganin ya farfado daga dogon suman da ya ke amma abu ya gagara, ganin ya na kokarin kifar da gadon ya sa su ka tsira masa allurar bacci amma Sam batai tasiri ba Kai kace Allurar doki a kai masa mutum kusan ashirin ne a kan sa harda security’s din asibitin masu murdadden jiki lokacin da aka ga abu ya taazzara aka kirawo su amma nema ya ke ya zubar da su gashi ba inda ya ke harin zuwa sai waje na gashi mahaifi na ya rike ni gagam balle na samu hanyar guduwa shi ma kan sa malamin abin ya fi karfin sa sai zubawa sarautar Allah ido yayi ya koma gefe to malan ma ya koma gefe abu ya fi karfin sa ina ga mu kananin kwari

Post a Comment

0 Comments

Ads