ALJANIN ABOKINA Part 5 By Ameesha MD

ALJANIN ABOKI NA) DAGA ALKALAMIN AMEESHA MD

To be continued....

Daukaka ta Allah ce 

05
TRUE LIFE STORY

ALJANIN ABOKI NA

NOBLE WRITER ASSOCIATION

Zame wayar ta yi daga kunnan ta,ta na ambatar innalilahi wainna ilaihi rajiun da sauri na yo kan ta ina fadin ”mama lafiya kuwa?”

bata ko kalle ni ba ta,ajiye min wayar a kasa ta shige cikin daki. to ko,Muhsin ne ya mutu? abinda ya zo raina kenan to amma in Muhsin ne ya mutu ai ba boye min ya,kamata,ta yi ba sai dai in wani abinne daban tashi na,yi,na shige dakin na ta, a kwance,na same ta,tana jan charbi ta na gani na tai saurin kau da,kanta kamar dai ta,na jin haushi na “mama Dan Allah ki fadamin mai ke faruwa,zuciya ta ta,kasa natsuwa kin sanya,ni cikin rudani ko muhsin dinne ya mutu ?“sai a sannnan ta,kalle ni irin,kallon tuhumarnan kallon da,sai da,ya sa hantar,cikina ta,kada

”mai zai hana ka kira wayar,mahaifiyar ta sa ka tambaya kaga koma mainene sai kaji daga,bakin ta kaga shikenan ka cire kan ka daga rudanin da na saka ka” ta mika min wayar hannun ta dai_dai lokacin na ji cikina ya kada,na nufi hanyar bandaki da sauri kafin,naje ma ta fara,zubowa tabbas,ina cikin tsaka,mai wuya Allah kadai ne zai iya fidda,ni.

Ranar haka nai ta famar zaryar zuwa bandaki gashi tazarar da ke tsakanin dakina da bandakin gidan namu,da,yar tafiya.

duk wannan zaryar da,na ke mahaifiya ta,na kallo na amma bata,ce tatafas sauke ba, ba kamar da,da ko mura muke tai ta famar tattalin mu kenan tabbas akwai wata,a kasa akwai wani abin da mahaifiyar muhsin da fadama mamar mu ni zargin da na ke ma Allah ya sa ba Aljanin muhsin din bane yai muryar mahaifiyar ta sa ya fada mata Karya da gaskiya dan ya ga ya,lalata,min rayuwa kamar yadda ya dau,alwashin yin hakan.

Haka na kwanta ina ta,famar tunane tunane haka kawai na soma jin kamar wani abu na tsunguni na a jiki, na tashi na karkade riga ta na chanja wata dan a tunani na ko kiyashi ne amma hausawa su ka ce wasa farin girki duka illahirin,jiki na,ya kama kaikayi da zugi,da radadi,tamkar cizon kunama yadda na ga dare haka,na ga,rana da safe,kuwa da,na tashi jikina yai rudu_rudu kamar mai borin jini zazabi mai zafi ya kama ni. 

ji nai ana yayyafa min ruwa da kyar na iya samu na bude idanuwa,na a hankali saboda nauyin da su kai min mahaifi na ne tsaye,a kai na cikin shirin fita sai a sannan na tuna da cewa zamu gidan su muhsin”mashkur ka manta da,tafiyar ne na ganka ko wanka ma ba ka yi ba ka tashi ka shirya ka same ni a cikin mota“ na amsa da to ya na fita na tashi na watsa ruwa na dauro alwala sannan na saka wata doguwar tallabiya fara bayan na idar da sallar na dauki charbi na na fice ko mai ban shafa ba abin da ya dauran kai har da mahaifiya ta a cikin motar to ita ina za ta je kenan? Na tambayi zuciya ta “Mashkur tunanin mai kake haka ka san fa na makara ka tsaya kana bata mana lokaci” 

“ya hakuri baba” abinda na fada kenan na ja baki na nai shiru ina satar kallon mahaifiya ta ta mudubi yayin da kwakwalwa ta ke yin tunani mabanbanta iskar mota ta fara kada ni sai kuwa na soma gyangyadi kasancewar jiya ban rintsa ba kamar a mafarki na ji an taka burkin motar an tsaya firgigit na bude ido a razane da wani katon asibiti idanuwa na su ka fara tozali asibitin ba dai girma ba benen asibitin ya kai hawa hudu kuma kowanne da tsayin sa mutane na ta zirga zirga da masu lafiya da marasa ita nan na hango an fito da gawar wani bawan allah daga dakin emergency nai saurin rintse idanuwa na mai kuma zami a asibiti na dubimahaifi na wanda ya ke duba wayar sa da alma wani abin ya ke kallo na dawo da kallo na ga mahaifiya ta wacce ta zabga uban tagumi “mama mai kuma zami a asibiti ba gidan su muhsin za mu je ba “

Ajiyar zuciya tayi sannan ta ce”ba ni za ka yiwa wannan tambayar ba ka tambayi mahaifin ka “ da sauri na juya gare sa ina kokarin tambayar sa ya katse ni “ku taso mu je wai su na room 4 hawa na uku “

Baba wai wane ne bashi da lafiya ,Mai za mi a asibiti?”

Ya dube ni da mamaki”wai ka na nufin ka ce mahaifiyar ka ba ta sanar da kai abinda ke faruwa ba?” na gyada kai yayin da mahaifiya ta ta ke sharce hawaye ya dafa kafada ta “Mashkur wannan babban Alamari ne da bai kamata a tatauna sa anan ba ka bari idan mun shiga daga ciki zan fada maka koma mai nene”

Post a Comment

0 Comments

Ads