ALJANIN ABOKINA PART 4 By Ameesha Md

ALJANIN ABOKINA) DAGA ALKALAMIN AMEESHA MD

To be continued....

Daukaka Ta Allah ce

04
TRUE LIFE STORY

ALJANIN ABOKI NA“wai yau Muhsin ya akai ka riga ni tashi da Asuba?kai da zan ta fama da kai ka tashi baza ka tashi ba sai na hada da bulala”

Muryar mahaifi na ta katse ni daga tunanin da nake firgigit na dago kai na dube sa yayin da,ya ke kokarin zama kan kujera “kaga yanzu na ke masa maganar tafiyar ka zaria shi ne nace ko za ka rage masa hanya “

Mahaifi na ya dube ta da mamaki na rage masa hanya kaman ya fa ina za shi”

Abokin sa Muhsin na kadunanna ne bashi da lafiya ya dade a kwance ya na jinya shine nace ko zai je ya dubo sa”

“Allah sarki yaro mai hankali to ai ba damuwa sai na rage masa hanyar Allah ya basa lafiya”

Ya juyo ya dube ni “mai ke damun abokin na ka?”

Lokaci daya nai tsamo tsamo kamar akuyar da ruwa yai wa duka nai shiru na kasa basa amsa har sai da ya daka min tsawa ban san lokacin da nace ciwon kai ba.

Shiryawa nayi na tafi makaranta ko kanwa ta ihsan ban jira ba jiki na duk a sanyaye na nemi guri na zauna nai shiru ba kamar yadda na saba yi ba na tsokani wannnan na tsokani wancen ganin na yi shirun ya sanya abokai na fara tambaya ta ko bani da lafiya ne amma nai musu shiru sai kawar da kai da na yi gefe ina yan tunane_tunane na ganin bani da niyar tanka musu ya sanya su tashi su ka bar ni wajen sai aboki na Sabir da shi ya tsaya ya na kara tambaya ta mai ke damu na cikin yanayin damuwa. Sabir babban aboki na ne wanda mu ke kashewa mu rufe ya san sirri na na san na sa kafin mu hadu da Muhsin da zuwan Muhsin komai ya chanja na daina abota da shi amma hakan bai sa ya watsar da ni ya daina kula ni ba kamar yadda ni na yada shi akan muhsin sai da mu kai fada dashi ya fi a irga yanzumma,bamu dade da shiryawa ba, ya sake tabo ni ajiyar zuciya na yi Sannan na ce

”sabir ko da ace na fada,maka abinda ke damuna babu maganin da,zai yi “

“da dai,ka samu ka fada min din ko da addua ne sai in taya ka da shi”

“ina cikin tashin hankali sabir ka taya ni da Addua”na sharce hawayen da ke,kokarin zubo,min

“insha allah abokina” nan mu,kai ta fira da shi ya, na ban labarurukan da,ya san za su sani dariya a haka har na soma mancewa da kalubalan dake gaba na. ko da aka tashi daga makarantar ma ba gida mu kai ba filin ball mu ka nufa sai kusan magariba likis na koma gida ina yan wake wake,na na shiga cire kayan makaranta na sauya da na gida bayan kintsa na nufi tsakar gida da,nufin na dauro alwala kasancewar kiraye kirayen Sallar magaribar da na ji ana yi waya tace ta shiga ringin na zaro ta da sauri dan duk dauka ta Sabir ne saboda ya mance jakar sa a waje na sai naji akasin hakan muryar mace ce dattijuwa yar kimanin shekaru shitin zuwa sama tai sallama na amsa a sanyaye”da Mashkur na ke magana ne”tai maganar bayan ta min sallamar “ “eh shine amma bangane dawa na ke magana ba”

“allah saki dama na san ba lallai ka gane ba to mahaifiyar Muhsin ce”

Ban San lokacin da na dauke wayar daga kan kunne na ba tsabar kidima jiki na ya soma karkawa dan ko kadan bana son a ambaci sunan muhsin dan tsoro ne da,fargaba su ka kama ni

“idan ba damuwa ina son ka mikawa mahaifiyar ka waya ina son muyi wata muhimmiyar magana da ita “

na tsinkayi,maganarta ta, ta cikin spickar wayar kasancewar a Hans free take dai_dai lokacin mahaifiya ta ta,fito daga cikin dakin nai saurin cire Hans free din wayar, ganin waya a hannu na jiki na a sanyaye ya sanya ta karbi wayan tana fadin

”mai ya faru Mashkur?” 

“mamar muhsin ce ta ce ta na son magana da ke “na fada cikin karfin hali

”allah sa ba jikin na sa bane ya matsa “

Nan ta kara wayar a kunne suka gaisa daga bisani kuma tai shiru ta na sauraren mahaifiyar muhsin da alama abinda ta ke fada mata mai muhimmanci ne kamar yacce ta fada tun farko,dan gaba daya,jikin ta ya yi sanyi tsoro da firgici su ka wanzu akan fuskar ta ,ta kalle ni yayin da,na ji hantar ciki na tai wata irin muguwar kadawa 

Post a Comment

0 Comments

Ads