ALJANIN ABOKINA Part 3 By Ameesha Md

ALJANIN ABOKINA)DAGA ALKALAMIN AMEESHA MD

2 be continued..

Daukaka ta allah ce

03
TRUE LIFE STORY

ALJANIN ABOKI NA

NOBLE WRITER ASSOCIATION

Tabbas ya kamata yau na fito na fada mata gaskiya, na dube ta yayin da ita ma ta ke kallo na cike da mamaki da kyar na iya daga baki na ce mata ”mama yau dai ya kamata na fada miki gaskiyar abinda ke faruwa “

wacce gaskiya kenan mai ne kuma abinda ke faruwa? “ kanwa ta ce ihsan yar kimanin shekaru goma sha hudu da rabi a duniya ta katse mu daga zancen da mu ke ta hanyar shigowa da gudu cikin gidan ta na murna wai an basu sadakar kosai ni da mama mu ka ja tsaki dan ta tsorata mu sosai mama ta maida hankalin ta gare ni “kyale wannan yarinyar mu dawo maganar mu ta dazu”

Wani sabon tsoro ne ya shige ni yayin da na tuna cewa Aljanin aboki na fa ya shaida min Matukar na fadawa wani abinda ke faruwa sai ya kashe ni na sharce zufar da ke karyo min ta ko ina nan na fara tunanin wacce karyar zan yi ma mama dan na wanke kai na ga abinda na ce zan fada mata, na daga kai na dube ta gaba daya ta tattara hankalin ta zuwa gare ni dan wannan karon harda kanwa ta ihsan yar kimanin shekara goma sha hudu da rabi a duniya suka zuba min na mujiya “ke ni sa’an ki ne da za ki zo muna magana da mama ki zo tsakiyar mu ki zauna ki na jin maganar manya“ hakan ba sabon abu bane gare ni dan akwai ni da son girma duk da ba wasu shekarun arziki na bata ba tsirar mu da ita shekara daya da rabi ne ina da shekara goma sha shida da rabi ita kuma tana da shekara goma sha hudu da rabi. nan ihsan ta zunburo baki mama tai dariya kaza aka ce huce kan dami nan na soma dungure mata keya ina tisa ta har sai da na dangana ta ga daki na na ce ta share min shi tas shine hukuncin da zan mata a bisa zuwa da tai wajen manya ta zauna har tana so ta ji maganar da su ke wajen mama na dawo na zauna yayin da mu ke jiyo gungunin ihsan “mama ki na ji na?” “eh Ina jin ka mashkur” “Muhsin ya daina kula ni shiyasa nima na fita daga harkar sa fada mu ka yi”

“to ai in dai fadan ku ne kun saba kuma ku shirya wannan ne zai hana ka zuwa gidan su ka duba shi bashi da lafiya ” “mama da bakin sa fa yace na rabu dashi yanzu ya tsane ni” mama ta zaro ido waje “shi muhsin dinne ya fada maka haka?”

“kwarai kuwa mama kinga kuwa wanda ya bude baki ya fada maka haka ba amfanin kara zama dashi”

A yadda na fahimta mama ta gama gamsuwa da magana ta Dan gaba daya jikin ta ya yi sanyi “to ai shikenan tunda ya ce haka”

Nan na sauke ajiyar zuciya dan na tabbata mama baza ta kara min maganar muhsin ba dan na gano tsantsar,kiyayyar muhsin a cikin idanuwan ta kunga shikenan babu ni babu kisan Aljanin muhsin cikin damuwa ta kashi goma ya ragu a kashi dari wanda zai je sama ya taka tabarma ai ya rage

“amma wannan alamarin da ya faru bai kai ka ki zuwa dubo sa ba a matsayin ka na babban abokin sa idan ka dakata na sai an maka abu za ka yi kai ma to tabbas ba abinda za kai gobe mahaifin ku za shi zaria sai ku tafi tare ya sauke ka a gidan nasu”

Tamkar saukar aradu haka na ji maganar ta, ta kasancewar na san mama bata magana biyu indai tace abu to kamar an yisa an gama ne maganar ta tamkar yakan wuka ce a yadda ta yanka haka za’a bi a dinki batare da an karkata allurar wajen da ba yankan ba , yanzu mai ne mafita a gare ni zan fadawa mama ainahin abinda ke faruwa Aljanin muhsin ya kashe ni ko kuma in hakura in je dubo sa in kai kaina mahallaka na dafe goshi na da na ke jin sa tamkar zai fado kasa tsabar ciwo...


Post a Comment

0 Comments

Ads