ALJANIN ABOKINA Part 2 By Ameesha MD

(ALJANIN ABOKI NA) DAGA ALKALAMIN AMEESHA MD

2 be continued....✍🏻

Daukaka ta allah ce👌

02

[Wed/4/26/2023]

ALJANIN ABOKINA

TRUE LIFE STORY

Tunowa,nai da maganganun Malan mudassir wanda ya ke ce mana idan zamu kwanta mu dinga yin Alwala idan,mu,kai,hakan babu wani halitta da ya isa ya cutar da mu ka na kariyar ubangiji, tashi nai da sauri kai na a sunkuye na rankwafa kamar mai kusumbi. tunowar da nai da dogon soron gidan,mu mai shegen duhunnan soron da a yanzu dole sai na wuce sa Zan fita waje domin gabatar da Alwalar da ban,niya ba babu lada ba alhaki domin ko,lokacin da malan,mudassir ya,ke,koya mana adduoin kwanciya bacci da kwadaitar da mu ladan da ke tattare da yin Alwalar jin sa kawai na ke, shiga su,ke ta kunne su fita ta bayan,keya dama hausawa sun ce duk wanda bai sharar,masallaci ba zai yi ta kasuwa .haka na kutsa cikin soron ina salati,gami da kiran sunan allah har,na,idar da alwalar kai na ya,na kallon kasa baya,na ya kage har kusa tuntubena yi amma hakan bai sa,na dago ba gudun kar in daga kai na sama na yi,mummunan gamo na dubi dakin mahaifiya ta da kanwa ta wadanda su ke,baccin su hankali kwance ina iya jiyo minsharin su, tabbas babu abinda ya ke damun su ina ma ni ne na ke bacci haka hankali kwance dan rabona da na yi ishashen bacci na fi wata biyu tun lokacin da Aboki na muhsin ya kamu da shafar Aljanu ba na iya bacci saboda tsoro da firgici haka na koma cikin daki na ina mai dana sanin haduwa da babban aboki na kuma Amini na muhsin Dan duk shi ya jefa ni a cikin irin mawuyacin halinnan a ranar da,ruf da ciki na kwanta wanda ake,ma lakabi da,kwanciyar yan wuta asubar fari karab akan,kunne na dama ba bacin na yi ba a,lokacin tsoro da firgici ya ragu a cikin zuciya ta Alwala nayi sannan na shiga dakin mahaifi na, na tashe shi, mamaki ne karara akan fuskar sa wai yau ni ne na,ke tashin sa sallar asuba bayan kafin ya tashe ni sai ya hada da bulala, na san abinda ya ke tunani kenan na sunkuyar da,kai na kasa murmushi yayi ya gabatar da alwala sannan ya dau darduma mu ka,nufi masallaci ko da mu ka dawo baccin da na saba komawa idan na yi sallar asuba ban koma sa ba zama nayi kusa da mahaifiya ta, ta na girki ina mata surutai barkatai duk dan na mance da abinda ya faru a daren jiya da alama surutun da na ke,mata ya soma cika mata ciki ta dube ni “Mashkur da wannan surutun da ka ke kamar kanyar da ba zaki ya kamata ace litafin ka ka dauko ka na bitar su dan,an baku,hutu a makaranta ba ya,na nufin kai watsi da karatu ba”

“hakane kuwa umma Dan kinga muna komawa,makaranta baza,mu dade ba zamu rubuta jarabawar waec “

“to ka gani yar sati ukun da aka baku ya isa kai karatu sosai”

“hakane” na fada hade da,mikewa tsaye har na nufi hanyar daki na ta kira suna na, na juyo hade da amsawa “nikam ya jikin abokinnan naka muhsin ya kamata fa ace ka je ka dubo sa tunda an muku hutun makaranta “

Tsigar jiki na naji ta na tashi jiki na ya soma karkarwa da kyar na samu na jingina da bangon dakin jin Ina kokarin faduwa kasa tabbas mahifiya ta bata San kalar lalurar da ke damun aboki na muhsin ba ni dai kawai na ce mata ya na fama da ciwon Kai ne. a duk lokacin da na tashi fadama mahaifiya ta barazanar da Ake min na neman rayuwa ta sai na kasa fada mata ni kadai na san irin ukubar da na ke karba a wajen Aljanin abokina  .........


Post a Comment

0 Comments

Ads