ALJANIN ABOKINA Episode 1 By Ameesha MD

ALJANIN ABOKINA

 TURE LIFE STORY

Dare aka ce mahutar bawa Kwance nake a kan katifa ta wacce ta side ta lome ta koma tamkar tabarma marabar ta da kasa kadanne wanda idan nayi wani kwakwaran juyi sai dai na ji ni a kan dandamalin siminti bacci nake rabi da rabi kasancewar kai na da ya ke min wani matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu, karar message ne ya shigo waya ta na zabura na mike zaune shaf na manta na bar data na a kunne na mika hannu na wanda sukai min nauyi na dau wayar na shiga shafin Facebook din babban aboki na ne ya min message din Muhsin da ganin wanda ya min message din kirji na yai wani irin mummunar faduwa jiki na ya dau rawa ciwon kan nawa ya dadu na tabbata da,lokacin a tsaye nake ba bu abinda zai hana ni faduwa kasa muhsin babban aboki na ne kuma amini na wanda ya zame min tamkar dan uwa na jini wanda na ke ganin sa zuciya ta tayi dadi muhsin mun hadu da shine ta manhajar Facebook daga nan kawancen mu ya soma, yakan zo gidan mu yai kwanaki idan an basu hutu kamar yadda nima nake yin wasu kwanaki a gidan su kasancewar ba garin,mu daya ba ni ina kano shi kuma ya na kaduna hatta iyayen mu mun hada su zumunci .


tun lokacin da Allah ya dorawa muhsin wata matsananciyar rashin lafiya mai kama da ta shafar Aljanu soyayyar da nake ma muhsin ta dawo zallar tsoro da,kiyayya kasancewar Aljannin da ke jikin sa ya ci alwashin in dai ban fita daga sabgar muhsin ba sai ya halaka ni har lahira,wani karar message dinne ya kara,shigowa cikin waya ta shine din dai ba wani ba ban san lokacin da na soma salati ba ina kokarin bude message din, dogon rubutu akayi sosai, na soma karanta message din a zuciya ta,kamar haka”ina sane da yawan adduoin da kake yi ma muhsin akan na fita daga rayuwar sa to wallahi kai kuka da kan ka yanzu na gama da muhsin bazai taba moruwa ba saura kai ka shirya ina nan dawowa kan ka kar ka dauki abin da wasa da gaske nake domin ka gazgata hakan za ka iya daga kan ka sama zaka ganni yanzu haka ina kallon ka” 


ya kare message din da sa stickar dariya ya rubuta sako daga malik Aljanin Muhsin ba hantar ciki na ba gaba daya abubuwan da Allah ya halitta a cikin sai da suka motsa tsabar firgici,lokaci daya jiki na ya soma karkarwa matsanancin tsoro ya kama ni nai saurin kashe wayar ina haki numfashi na ya soma sama sama ya na kokarin barin jiki na. 

Post a Comment

0 Comments

Ads