ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 47 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/kGY_i0VKnqg 

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-47-hausa.html


*^ Part 47 ^*


Ruwa ake shekawa da iska tamkar da bakin kwarya, ga duhu ya fara yi kasancewar magariba ta kawo kai. Zaune suke a daki ko ina rawa yake bayan zuba da rufin dakin yake, sun saka abun taron ruwa fiye da biyar amma duk da haka ruwan na cigaba da tsiyaya daga wasu wuraren. Addu'a kawai take a ranta Allah yasa su ga wucewar ruwan lafiya, don dama a kullum cikin fargaba suke kwana a gidan kasancewar rufin dakin da shi kanshi dakin sun tsufa sosai, ga bangwayen dakin duk sun tsage Ummi ta ce, "Mama wallahi tsoro nake ji, ji yadda bangon nan yake motsi kamar zai fado". Saratu ta ce, "Ki ta addu'a Ummi insha Allah ba zai fado ba". Ba ta dade da rufe baki ba suka ga tamkar ginin na tahowa a hankali, don haka da gudu Ummi ta kama hannun kaninta, yayin da Saratu ta daukko dayan suka fita tsakar gida suna masu zubawa dakunan ido. Basu jima da fitowa ba sai ji suke rigijif! Baki daya dakunan suka zube. Kuka Ummi ta fashe da shi, yayin da ita kuma Saratu ta ke ta maimaita Innalillahi a zahiri da kuma zuciyarta. Godiya take ga Allah da ya sa sai da suka fito daga dakin sannan ya zube, yanzu da suna ciki ai sai dai a kwankwalo gawarwakinsu. 


Suna zaune a falo kowa na sha'anin gabansa, Murja ma na duba karatun da sukayi da Safuratu domin ita take kara mata ayoyi idan ta hardace wasu. Gani sukayi Murja ta rike kanta da hannaye biyu hade da runtse ido, lokaci daya kuma suka ga ta mike tsaye ta nufi waje a guje. Kallo suka bita da shi baki daya har Khalil dake latse-latsen waya. "Kai wannan yarinyar ba lafiya ba, ku dubi yadda ta fita waje a guje ana ruwa haka, ko dai haukan nata ne ya dawo?". Hajiya Lami ta kyalkyale da dariya hade da cewa, "Allah ubangiji ya sa dama haukan lafawa ne yayi kuma yanzu ya dawo, ai gwara ta fitar mana daga gida ta je can ta karata". "Karki raba dayan biyu, hauka ne domin in ba mahaukaci ba, babu wanda zai fita waje ana cikin wannan ruwa mai karfi ga kuma iska". Suna cikin dakinsu irin na masu gadi dake cikin gida daga bakin kofa, suka ji kamar an zare sakatar gida an fita. Sunusi ya ce, "Ni fa na ji kamar wani ya fita daga cikin gidan nan". "Haba dai yo hauka ake a cikin gidan nan waye zai yarda ya fito ana wannan ruwa da iska mai karfi? Watakil kawai iska ne ya kada kyauren domin nima naji karansa, ai da alama ruwan nan zaiyi gyara da yawa, don in ba sa'a ba wasu daga cikin katangun makwabtanan nan namu sun zube don naji kara kamar na zubewar katanga". Hamza ya fada yana kallon Sunusi dake kwance a yar katifarsa irin ta mutum daya. Dai-dai lokacin da Murja ta fito, Saratu da yaranta suna bakin kofar gidan makwabtansu sai bubbuga gida suke da karfi amma da alama ba'a ma jisu ba balle a zo a bude musu. Murja ce ta karaso wajen a guje cikin ruwa, su kansu sunyi mamakin ganinta, da sauri ta kama hannun Affan da Jibrin ta kalli Saratu hade da cewa, "Ku biyo ni". Ba musu suka bita da gudu suka shiga gidan. Kai tsaye dayan bangaren da take tunani na baki ne ta nufa da su. Tana zuwa ta tarar da kofar falon a rufe, don haka ta ce su jira ta je ta daukko makulli, su dai kallonta suke cike da mamakin kirkin yarinyar. 


Fadowarta dakin a guje sai da Hajiya Lami ta zabura, Murja ta je gabanta kayan jikinta a jike sharkaf sai tsiyayyar ruwa suke, "Ina makullin wancan bangaren bakin?". Hajiya Lami ta kalleta cikin rashin fahimta hade da cewa, "Wane bangaren bak'i?". "Wancan bangaren da nake tunanin na baki ne shi nake so ki daukko min makulinsa". Hajiya Lami ta ce, "Me za'ayi da shi?". Ran Murja ya fara baci ta ce, "Ina ruwanki? Na ga nan din gidan ubanane ina da ikon yin abinda na ga dama ba tare da wani ya tambayan dalili ba". Kauda kai Hajiya Lami tayi cikin isa tace, "Ai sai ki dauke shi a inda kika ajiye shi tunda gidan ubanki ne". Ganin Hajiya Lami zata bata mata lokaci ta kalleta hade da girgiza kai ta ce, "Zanyi maganinki?". Da fadar haka ta haura sama da gudu. Mama Dije ta ce, "Kin ga mayyar ta dawo ko? Wallahi ina tunanin yarinyar nan ba hauka ba ko mutuwa zatayi sai tayi fatalwa ta dawo gidan nan". "Wallahi Mama da ta shigo gabana har faduwa yayi, na zata ta tafi kenan, amma wai kina ji wai in daukko mata makulin bangaren baki". Mama Dije ta ce, "Ko uwar me zatayi a can kuma". Suna cikin haka sai gata ta saukko rike da keys a hannunta, gaba daya sunyi mamakin ganin ta daukko key din bayan bata san inda aka ajiye ba. "To ga makulin na daukko idan mutum ya isa ya zo ya kwata, kuma bari kiji babu ke a cikin aikin ladan da zanyi, domin gidan marayu ne ya rushe ni kuma na kawo su nan su zauna a ciki kafin a gyara nasu".


Wucewa tayi ta barsu baki sake suna ta mamaki. Tana zuwa ta bude wa su Saratu falon ta kunna wuta, bisa mamaki sai ta ga ashe akwai wuta a bangaren ma sai dai dakin yayi kura. A waje suka tsaya suka matse kayan jikinsu da duk sun jike, sai da suka tabbatar kayan sun sha iska sanan suka shiga ciki, tare da ita suka hau share-share da gyaran dakunan. Wanda daki biyu ne ko wane da toilet sai kuma falo a tsakiya komai akwai a cikin part din don har Murja ta kunnawa su Affan tv suna kallon cartoon. Jamsy ce ta mike tsaye ranta a bace tamkar zatayi kuka ta ce, "Mom kinji abinda take fada? Wai part din baki inda in munyi baki muke basu suna zama, haka kawayena ma ko abokan Yaya Khalil idan sun zo daga wani gari a nan suke zama, shine zata dauka ta ba wasu mutane? Izinin wa ta nema? Na rantse da Allah bata isa ba sai naje na tayar da su daga part din nan". Khalil ya ce, "Wallahi ina bayanki sister ni fa na tsani matar nan, ko kadan bana so in shigo gidan nan in ganta sai inji zuciyata har tashi take, dubi fa yadda ta jikawa mutane falo da ruwan kazamin jikinta da ta jiko a cikin ruwa". 


Hajiya Lami tayi murmushi irin nasu na manya hade da cewa, "Yara ku kwantar da hankalinku, in dai a kan Murja ne tana gaf da barin gidan nan na har abada". Cikin fushi Jamsy ta nufi hanyar fita tana fadin, "Haba Mom tun yaushe kike cewa zakiyi maganinta yau fa wajen kwananta hudu a cikin gidan nan amma kin kasa daukar mataki. Yanzu zan je na ci musu mutunci ita da wanda ta kawo din". Suna mata magana bata saurara ba fuuu! Ta wuce. A falo ta tarar da su a zazzaune Saratu na maidawa Murja yadda akayi game da zubewar dakunansu, tana cewa dama Allah-Allah take ta sama kudi ta sai siminti ayi mata filista domin dama ta lura da katangun suna gaf da faduwa. "Ina Murjar take?". Jamsy suka ga ta fado dakin tana kare musu kallo. "Dama wannan matsiyatan ne kika kwaso mana kika kawo mana gida?". Ta fada tana kallon su, da sauri Ummi ta sadda kai kasa, saboda sanin irin rashin mutuncin Jamsy, tun farko Jamsy ta tsaneta hanya bata hadasu wai don kawai sun kasance talakawa ita kuma yar masu kudi. "To wallahi tun kafin dare yayi muku ku tashi ku bar gidan nan, kun san halina ba mutunci gareni ba, idan baku bar gidan nan ba zan karta muku rashin mutuncin da sai kunyi dana sanin shigowa gidan nan". 


Tsoro ne ya kama su, don haka da sauri Ummi ta tashi hade da cewa, "Affan ku tashi mu tafi, Mama tashi mu bar musu gidansu mutunci ya fi kudi". Saratu ta kalli Murja hade da cewa, "Murja mun gode da irin kokarin da kikayi mana, amma tunda sauran yan gidan basa so gwara muyi hakuri mu tafi Allah ba zai hanamu wajen kwana ba". Ta fara yunkurin tashi, Murja da take binsu da ido ta ce, "Koma ki zauna Aunty Saratu, kema Ummi koma inda kike a zaune". Juyawa Ummi tayi zata koma, ai kuwa Jamsy cikin tsiwa ta cigaba da masifa "Wane irin su koma su zauna gidan ubansu ne, ko na ubanki ne ke? Ke har kin isa a cikin gidan nan in bada umarnin ki...". Marin da ta ji Murja ta wanka mata ne ya sa ta kasa karasa fadin abinda tayi niyar fada. Zata sake daga baki Murja ta sake sharara mata mari, ba shiri ta fashe da kuka hade da fita waje. Bayan Jamsy ta fita Murja ta kalli Saratu hade da yin murmushi ta ce, "Don Allah kuyi hakuri, kunsan akwai yarinta a kanta amma zan saita mata kan nata". Cikin sanyi Saratu ta ce, "Aa Murja in kinsan Hajiya Lami ba zata amince da zama a nan na dan wani lokaci ba, kar mu jawo miki matsala gwara kawai ki bari mu fita ko gidan makwabta da abokan arziki ba zamu rasa matsugunni ba". Murja ta ce, "Aa wallahi karki damu Hajiya ba zata ce kuma ba, dangane da yarinyar nan kuma nayi muku alkawarin wannan ne na farko kuma na karshe ba zata sake muku irin wannan ba". Shiru sukayi na dan lokaci, tun daga kofa kuma suka fara jiyo bala'in Hajiya Lami.


Kai tsaye ta fado dakin ko sallama babu, ta jawo hannun Jamsy dake kuka, Khalil ma na biye da su a baya. "Ina Murjar take? Bari kiji in fada miki wannan shine kashedi na farko kuma na karshe da zanyi miki, 'ya'yana ba jakai bane karki sake dukansu, idan kuma kika kara dukar min yara duk abinda na miki ke kika sayo". Malalacin kallo Murja ta watsa mata hade da cewa, "An daketa din ko zaki rama mata ne? A wajena ke din ma baki fi karfin mari ba, tunda kece kika daure musu gindi suke rashin kunyar da suka ga dama". Zuwa tayi da nufin in ta sama dama ta wawwanaka Murja mari amma suna hada ido sai taji Murja tayi mata kwarjini, kanta daurewa yake game da lamarin Murja, domin wani lokacin sai su ganta kamar sakarai har kasa take durkusawa ta gaishesu, wani lokacin kuma sai ta rika basu tsoro. Ko me ta tuna kuma sai ta cije lebe tayi kwafa hade da jan Jamsy ta ce, "Zo mu tafi, ke kuma zanyi maganinki". Bayan sun fita Saratu ta ce, "Murja haka kuke zaune da Aunty Lami kuma yanzu? Da fa sanin da nayi so ne da kauna da shakuwa a tsakaninku". Murja tayi murmushi hade da cewa, "Da kenan".


Kitchen Murja ta je ta sa Nana Da Karima su ka rika jido kayan abinci suna kawowa su Saratu, haka zalika Murja ta hadasu da masu gadi suka koma gidan suka kwaso sauran kayansu wanda kasa bata rufe ba. Tsakar dare kowa ya watse a falon sai Mama Dije da Hajiya Lami dake zaune Allah kadai yasan abinda suke tsarawa a zukatansu, misalin karfe sha biyi da rabi Mama Dije ta kalli Hajiya Lami da sai hamma take amma don bala'i ta ki zuwa tayi bacci, ta ce, "Yauwa yanzu ina kyautata zaton yarinyar nan tayi bacci". Hajiya Lami ta danna wayarta ta kalli agogo hade da cewa, "Eh lalai yanzu zata iya yin bacci bari na tashi na je". Mama Dije ta ce, "Bari na biyo ki baya watakil zan iya taimaka miki". A hankali suke tafe saboda tsabar sanda su kansu basa iya jin motsin takun sawun juna. Bayan sun karasa kofar Lami ta murda a hankali nan take suka hango Murja a gado ta juya baya sai kwasar baccinta take hankali kwance. Kamar barayi haka suka kutsa kai suka shiga, Hajiya Lami ta je ta gaban Murja ta saita wayarta domin daukar hoton Murja, amma sai ta ga ba'a ganin fuskar, don haka cikin rada ta cewa Mama Dije ta bi a hankali ta juya mata Murja tayi rai-ran yadda zataji dadin daukar hoton. Haka kuwa akayi, a hankali Mama Dije ta juya Murja ta kalli sama, nan take Hajiya Lami ta saita waya ta dauki hoton Murja. Wani irin farin ciki ne ya lulube zukatansu ganin hoton ya fita fess! Don haka suka tashi suka lalaba suka fita daga dakin..............


Na gaji fa. 🙄 bansan me ke faruwa ba sai inyi dogon rubutu amma ace yayi kadan, kullum korafi ake wai in kara yawan page

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Post a Comment

0 Comments

Ads