ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 45 Hausa Novel 2023


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/AB4u7gJG9C0

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-45-hausa.html


*^ Part 45 ^*


Hannu Mama Dije ta sa ta share zufar da ke goshinta, gaba daya kanta ya kulle sai bin Murja da kallo take, a zuciyarta take tunani, idan har ya tabbata wannan yarinyar Murja ce ta gaskiya to ya akayi ta kubuta, tayaya ma akayi ta sama lafiya daga haukatar da ita da Boka Kare Dangi yayi?. Kallonta ta kai ga Hajiya Lami, nan take ta ga tashin hankalin da Hajiya Lami ta shiga ita bata shiga irinsa ba ma. A bangaren Hajiya Lami kuma kalaman boka ne suke mata yawo a kwakwalwa, tabbas bata manta ba ya tabbatar musu cewa idan har asirin da sukayiwa Murja ya karye wani mummunar al'amari zai faru da ita, ko kuma ma ta mutu baki daya. Mikewa tsaye tayi tamkar zararriya tana nuna Murja da yatsa tana fadin, "Karya kike yi, ke ba Murja bace, Murja ta dade da mutuwa. Idan har wani makircin kike kullawa wallahi ba zaiyi tasiri a kaina ba na fi karfinki". Dariya Murja ta tuntsire da ita, nan take ta juya ta kara juyawa a gabansu tana fadin, "Ni ce dai Murja yar gatan baba, da Boka Kare Dangi ya haukatar, tabbas na sha wahala a shekarun da nayi a haukace amma dake rayuwa da mutuwa duka suna hannun Allah gani har zuwa yanzu a raye ban mutu ba".  


A sankare Hajiya Lami ta fada kan kujera cikin matukar kidima, "Mama itace, wallahi itace bata mutu ba mama, na shiga uku na lalace". Ganin Hajiya Lami na abubuwa kamar wacce ta zare yasa Mama Dije ta ririketa tana fadin, "Ke Lami ki natsu, ki natsu na ce miki, zamu san abinda zamuyi a kan lamarin nan, yanzu dai kiyi gaggawar tashi ki daukko mata kudin da ta bukata". Hajiya Lami tayi kokari ta tattara natsuwarta waje daya jin furucin uwar tata, hade da cewa, "To". Jamsy dake ta binsu da ido gaba daya ta kasa gane inda aka dosa ganin Hajiya Lami na kokarin tashi ta daukko kudi ya sa ta ce, "Mom wallahi ba za'a bata kudin nan ba, ai banga dalilin da zaisa a bata kudi masu yawa haka ba". "Ke Jamsy kiyi mana shiru, maza tashi ki bar wajen nan". Mama Dije ta fada tana zazzare mata idanu. "To amma ya za'a...". "Idan baki tashi kin bar wajen nan ba, zan tafka miki rashin mutunci". Tashi kawai tayi ta nufi dakinta a sama tana gunguni. Yayin da itama Hajiya Lami ta bita sama domin daukko wa Murja kudin da ta bukata.


Bayan Hajiya Lami ta kawo wa Murja kudin kai tsaye ta koma ta daukko gyalenta sannan ta fita ta nemo driver ta ce ya kaita supermarket. Rantsuwa yayi da Allah ba zai je ba sai dai in Hajiya ce ta ce ya kaita. Murmurshi tayi hade da cewa yaje ya tambayota. Yayi mamaki yadda yaji Hajiya Lami ta ce ya kai Murja duk inda take so. Bayan sun fita Hajiya Lami ta kalli Mama Dije cikin hawaye hade da cewa, "Mama na shiga uku, Wallahi dama na fada Murja ta ganni lokacin da ina waya dake sadda za'a kashe babanta, amma nayi tunanin lokacin tayi karama sosai ba zata fahimci me nake nufi ba, amma kinji tana sane kuma tasan mu mukayi sanadin kashe Babanta". Mama Dije ta ce, "Ni fa babu abinda ya daure min kai illa yadda akayi ta san Boka Kare Dangi". "Innalillahi Mama don Allah ki kira Inna Sailuba ki fada mata, domin bana son na mutu don Allah a yi gaggawar daukar mataki a kan lamarin nan". Mama Dije ta ce, "Daukko wayar tawa tana can a daki na baro". Da sauri Hajiya Lami ta je ta daukko, dokawar farko Sailuba ta dauka waya bayan an kirata, cikin raha ta fara fadin, "Dije alhazai mutanen Allah, ai daga jin kiranki hannuna har karkawa yake na dauka na san samune". Yanayin Mama Dije ta ji cikin damuwa ba kamar yadda ta santa ba. 


"Bar wasan nan Sailuba wallahi muna cikin matsananciyar damuwa". "Innalillahi me kuma ya faru". Mama Dije ta sauke ajiyar zuciya hade da cewa, "Murja ta dawo gida, kuma ta warke daga ciwon hauka, hakan na nufin asirin ya karye". Sallallami ta kwada hade da cewa, "Anya kuwa Hajiya Dije ba kuskure kukayi ba? Bana tunanin Murja tana raye ma balle kuma ace wai ta warke, kai wata kil wata dai kuka gani ba Murja ba". Cikin damuwa Mama Dije ta kora mata dukkan bayanin abubuwan da suka faru, don haka Sailuba ta ce, su kwantar da hankalinsu gobe zatayi musu jagora su koma wajen Boka Kare Dangi domin jin yadda lamarin yake. Sai wajejen magariba Murja ta dawo daga sayayya bayan sun baje a daki Safuratu na gefenta ta dingi daga kayan tana kallo cikin farin ciki, domin duk abinda mace take bukata sun sayo har da hijabai, domin bata da ko daya. 


Wajejen karfe biyun dare kowa yayi bacci a gidan, sanye take da bakar abaya mai hula ta rufe kanta da hullar, abayar doguwa ce wacce take har kasa, hannunta rike da yar karamar wuka mai kaifi sai walkiya take, a hankali take takowa kasan bene gidan shiru baka jin komai sai sautin karaton Tv dake faman yi wanda Murja ce ta tsiri bidi'ar kunnawa duk dare ganin inji kwana yake ya wuni a kunne. Kai tsaye dakin su Murja ta nufa tana zuwa hannun kofar ta murza bisa mamaki sai ji tayi kofar ta bude. A hankali ta kunna gulof nan take haske ya gauraye dakin, a tsakiyar gado ta hangi Murja sai sharar baccinta take hankali kwance. Kan gadon ta hau ta daga wukar sama saitin wuyan Murja sannan ta fara magana kasa-kasa, "Karyarki ta sha karya Murja, kinyi kadan ki rabani da farin cikin da na sha gwagwarmayar kwata a cikin shekaru masu yawa. Yanzu zan kasheki kema in shafe tarihinki kamar yanda na shafe na mahaifinki, kafin ke ki kasheni da bakin ciki". Cikin barci Murja take jin maganar kasa-kasa, a hankali ta bude ido jin ana ambaton kasheta, dai-dai lokacin ta ga mutum ya daga wuka yana kokarin caka mata a ciki. Wani irin ihu mai rikitarwa ta kwalla yayin da tayi kundunbala daga kan gado ta fado kasa sai ihu take. Kafin tayi yunkurin tashi tuni matar ta fita waje a guje. 


Sai a lokacin Murja ta lura da Safuratu dake ta sharar bacci a gefen gado nan take ta fara jijigata tana fadin, "Safuratu! Safuratu ki tashi!". Ta dan dade tana jijigata sannan ta tashi zaune tana murtsike ido alamun bacci ne a idon. "Lafiya kuwa Murja kike tayar dani da tsakar daren nan?". Safuratu na kallon yadda Murja ta rikice ta fita hayyacinta saboda tsoro, "Wallahi mutum na gani da wuka zai kasheni, Innalillahi! Don Allah ki tashi mu bar gidan nan". Safuratu ta ce, "Ke dai wallahi matsoraciya ce watakil ma mafarki ne kikayi". Tana fadar haka ta koma ta kwanta, ai kuwa Murja ta cigaba da jijigata, "Na rantse da Allah ba mafarki bane, da idona na ga bakin mutum ya daga wuka a saitina zai caka mini, nayi ihu shine ya tashi ya ruga da gudu waje". Dariya ce fall a cikin Safuratu, amma a zahiri tayi kokarin dakewa ta nuna tamkar bata san me ke faruwa ba. Safuratu ta cewa Murja, "Amma ni banji ihun ba". "Taya zakiji bayan kina wannan baccin naki mai kamar baccin mutuwa, ni bansan haka aljannu suke baccinsu ba, wallahi ba don na farka ba da yanzu sai dai a tsinci gawata". Safuratu ta mike tsaye hade da cewa, "Kinga zauna bari na lalleka na ga ko zanga mutumin, idan na ganshi sai inyi ihu a kawo dauki". Murja ta ce, "Wallahi ba zaki fita ki barni ba ya dawo ya kasheni, sai dai mu fita tare". Ba yadda Safuratu ba tayi ba a kan Murja ta tsaya a daki amma taki, domin Safuratu tasan Hajiya Lami ce ta zo da wuka da niyar kashe Murja, amma ko lokacin da ta daga wukar Safuratu na gefenta, tayi niyar rike wukar da zarar tayi yunkurin cakawa, sai aka sama akasi Murja ta tashi, yanzu kuma so take ta bar Murja ta koma wajen Hajiya Lami amma Murja ta ce ba zata zauna a daki ba, kuma ta san cewa idan har ta fadawa Murja cewa Hajiya Lami ce ta zo kasheta tsoron da take mata karuwa zaiyi, ita kuma so take Murja ta daina tsoron su Hajiya Lami baki daya.


Tafe suke a tankamemen falon Murja na rike da hannun Safuratu cikin tsoro suna waige-waige, dif suka ga an dauke wutar falon, ai kuwa Murja ta kwada ihu hade da yin tsalle ta makalkale Safuratu tana fadin, "Innalillahi shikenan ya kashe wuta zai kashe mu, mu gudu". Safuratu ma ihu ta kwada hade da cewa, "Wayyo Allah na ga mutum da bakakken kaya ya wuce ta bayanmu". Kuka Murja ta fashe da shi tana karanto duk addu'ar da ta fado bakinta. Wutar dakin ce ta dawo, sai dai kuma lokaci guda suka ga mutum cikin bakaken kaya a gabansu, da faruwar haka Murja ta sume a jikin Safuratu. Dariya Safuratu tayi har tana rike ciki saboda masifaffen tsoro irin na Murja, in batayi mata haka ba ko bacci ba lalai ta samu tayi ba, kai tsaye daukarta tayi ta kaita daki ta kwantar da ita a gado, sannan ta yayyafa mata ruwa ba jimawa ta farfado, tana shirin yin magana kenan taji wani masifaffen bacci nan take idonta ya rufe ta hau bacci. Zaune take a gefen gado bayan ta cire doguwar bakar rigar da ta sa, hannu ta dunkule ta buga a jikin katifa saboda tsabar bakin ciki da takaici.


A ranta take ayyana in da ace ta sama nasarar kashe Murja a wannan farmakin da ta kai, da shikenan duk wani ciwon kai nata ya warke. Dariya da ihu ta rika ji a waje, da alama a kasan benen ne, tashi tayi ta bude kofa kai tsaye ta nufi kasar bene. Tun kafin ta karasa saukkowa daga saman bene ta hangi mutum cikin hajjayen kaya a daya daga cikin kujerun falon ya juya mata baya kuma shine yake dariyar da ihu lokaci bayan lokaci. "Waye a nan?". Ta fada yayin da ta rage saurin tafiyarta, domin ta kasa bambance muryar macece ko ta namiji. "Murja ce?". A wannan karon ma shiru taji ba'ayi magana ba, don haka ta cigaba da sakkowa daga kan benen domin ganin ko wane mahaukaci ne yake musu hauka a gida tsakar dare. Ta kusa saukkowa kenan ta ga wutar dakin ta dauke, ai kuwa ta tsaya cik a inda take.


 Ba'a jima ba kuma ta ga wutar ta dawo, yayin da a lokacin ta ji falon yayi shiru babu mutum da ta hanga a zaune kuma babu dariya da ihu da take ji. Tsoronta ne ya kara karuwa, domin idanunta da kunnuwanta ba karya sukayi mata ba, tabbas taji kuma ta gani amma lokaci guda kuma ta nemi mutumin ta rasa. Saukkowa tayi ta duduba ko'ina a falon har waje tsakar gida sai da ta lalleka a tsorace amma bata ga komai ba. Ta juya da nufin komawa saman bene ta ji kafarta ta taka wani abu mai laushi, tana kai idanunta ga kafar domin ganin abinda ta taka, ai kuwa ta ga wani katon kadangare ne mai jan kai ya kura mata ido yana bude baki bayan ta taka cikinsa. Tsale tayi hade da ihu a lokaci guda ta zuba a guje, da tasan cewa idan ta zo hawa matakalar bene daya bayan daya take takawa, amma a wannan lokacin ita kanta bata san ko guda nawa take tsallakewa ba, domin gudun da take ya fi kama da gudun fanfalaki don a duniya Allah ya zuba mata tsoron kadangare.


Bayan ta shiga daki ta kulle kofa, ta zauna a bakin gado tunani kala-kala na zuwa mata a kwakwalwa, ko can a salinta lokacin da tana kauye ta sha jin labari da a wajen mutane masu cewa sun ga Aljani, amma ita a zahiri ko abu mai kama da aljani ba ta taba gani ba sai yau, tabbas idan ba aljani ta gani ba to fatalwa ce. Ta dade a zaune jin ta fara gyangyadi yasa ta tashi ta kashe wuta domin ta kwanta, sai dai me tana dafa gado da niyar hawa ta ji ta cafko wani abu mai kaushi, kara shafa abun tayi don tabbatarwa, amma sai taji tamkar kan kadangarene...........


Tsoro ya kamani 🥶

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Post a Comment

0 Comments

Ads