ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 9 Hausa Novel 2023


🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/i_1jj2TTNzY


*^ Part 9 ^*


Yana kunbura ya nufi Mairo dake bayan Inna Ma'u da nufin ya falla mata mari, ai kuwa sai saukar duka yaji da sauri yaja baya yana sosa wajen Inna Ma'u ta daga hannu hade da cewa "Fice mun daga gida majanunu kawai a gaban nawa zaka daki mamana ashe kuwa kana so ranka ya baci yau". Baya yaja yana gunguni ya san halin Inna Ma'u sarai ba karamin aikinta bane ta ci mai mutunci a wajen. Kubura tafe take gudu-gudu sauri-sauri Asabe na biye da ita a baya a hanya sukayi kicibus da su Wasila dake faman kuka nan ta balbale su da masifa tana fadin "Wallahi bakuyo halina ba, lokacin da ina kamarku a duk garin nan ba sa'ana da nake tsoro balle wanda na girma ya sani kuka. Amma jibeku manyan banza karamar kanwarku na saku kuka wallahi kun bani kunya, ina take mayyar don ubanta?" 


Talatu tana share hawaye tace, "Zubairu ya mata dan banzan duka shine tayi mai Allah ya isa ta ruga a guje ya bita watakil gidan Inna Ma'u ta gudu". "Yauwa ai gwara da ya lakada mata duka kuma nima ba kyaleta zanyi ba zata iskani a gidan, maza ku wuce muje ragwgwagen banza". Kubura ta fada hade da iza keyarsu sukayi gida. 


Inna Ma'u ta kalli Mairo dake bayanta idonta cike da kwalla sai muzurai take wa Zubairu da yayi tsaye a kofar dakin Inna Ma'u. "Ke kuma me ya hadaki da su a kullum ina miki kashedin abinda zai hadaki da yan gidan nan naku amma bakya ji, ko so kike wataran su illataki musamman wannan mai kwalelen kan ko kadan nasan ba imani ba gareshi". Mairo cikin hawaye tace, "Wai fa Inna su Talatu ne suke min dariya akuyar Ummana da aka haifa mata ta mutu, shine nace ai Allah ne mai badawa kuma shi ya kasheta ba wani ba. Shine Talatu take fada min wai ai da gangan mamarsu ta sa tabarya ta kashe mana akuya, shine dan nace mamarsu muguwa ce azzaluma ta dakeni nima na rama".


Sallalami Inna ta kwasa hade da cewa "Yanzu bakin halin na Kubura har ya kai haka, barni da shi dan nan zai zo ya sameni har gida dake ya zama solobiyo a gida ya kyalesu suna ta shuka tsiyarsu. To kai Zubairu maza jeka duk inda uban naka yake ka nemo min shi". Fita yayi yana gunguni.

Bayan la'asar Mairo ta koma gida ita kam har ta manta da abinda ya faru da rana, da shigarta gidan Kubura ta hau masifa dama tun rana take balbalawa Fatsuma. "Shegiya mayya na rantse da Allah yau sai sun rama cizon da kika musu, ji idanunta kananu kamar na mage amma duk wani salon mugunta ta sani ke Asabe maza jeki duk inda Wasila da Talatu suke ki nemo min su suzo su rama cizonsu". Kubura ke fadan haka yayin da ta kama hannayen Mairo ta matse gam ta zauna a gefen turmi. 


Laure dake zaune bisa kujera tayani gulma tace, "Yauwa yaya wallahi hakan yayi dai-dai ai ba finsu hakora tayi ba da take cizonsu kamar wata kura". Ba dadewa sai ga Wasila da Talatu da gudunsu harda yara abokai yan rakiya, ba kunya ba tsoron Allah Kubura ta rike Mairo su Talatu suka rama cizon a hannu. Duk abinda ke faruwa Fatsuma na kallo domin tun lokacin da Kubura ta rike Mairo take bata hakuri amma taki hakura da ta matsa kusa da ita ma har bangajeta tayi da hannu guda. 


Mairo na kuka ta karasa wajen mamartata suka shige daki tana share mata hawaye hade da duba hannun da aka cijeta, bayan sun zauna tace, "Haba Baby yanzu ke duk maganar da nake miki me yasa bakya ji, kinfi so kullum ki rika taba yan gidan nan ana zaluntarki ki. Kin riga kinsan cewa ko ba'a musu komai ba ma ba kyalemu sukayi ba balle kuma kin taba musu yara". Cikin kuka tace, "Umma kiyi hakuri su fa suka fara tsokanana kuma suka ce wai Yaya Kubura ce ta kashe mana akuya da tabarya da gangan".


Ko kadan Fatsuma bata so Mairo ta san hakan ba amma matsalar a gaban su Talatu akayi su kuma yara basu da sirri don haka tace, "Kinga ba komai Mairo akuya dai Allah ne ya bamu kuma ya dauki abinsa, nasha fada miki kaddarar halitta a rubuce take duk abinda ya faru da bawa to Allah ya rubuta dama haka zai faru". Mairo tayi farar tace, "Cizon da nawa su Talatu ma tuntuni Allah ya rubuta kenan?". 


Duk da tana cikin kunar rai sai da ta saki yar dariya hade da cewa "Kwarai komai da kika sani Allah ya rubuta kuma yasan duk abinda zai faru da bawa, don haka bana so ki aikata wani abun kuma a game da mutuwar akuyar nan tun farko ma shiyasa naki in fada miki cewa Kubura ce ta kashe akuyar saboda karki ce zakiyi wani abun". Mairo ta girgiza kai alamun ta gamsu a zuciyarta kuwa sake-sake kawai take tana mai tunanin ai tunda Allah ya rubuta komai duk wani abu da zatayi dama a rubuce yake. A dayan bangaren kuma tana tunanin ta hanyar da fanshe don ba zata yafe kashe akuyarsu da akayi.......

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 
https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

Post a Comment

0 Comments

Ads