ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 8 Hausa Novel 2023

 🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️


*ALJANAR FATIMA BOOK 2*


🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️
By *Kingboy Isah* 


°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*Zamani writers Association*

•••••••••••••√••••√••••••••••••••••

_$$ Free book but support us read in our site $$_

https://youtu.be/jEISNufi6_E


*^ Part 8 ^*Haka dai rayuwa take ta gudana kullum al'amura cabewa Fatsuma da yarta Mairo suke, ranar wata alhamis daya daga cikin akuyoyi guda biyu da Fatsuma take kiwo ta haihu, haihuwa farko wanda ya kasance na mai kiwo ne wato na Fatsuma ne. Ranar Fatsuma da Mairo ba karamin farin ciki suka shiga ba. Yayin da a bangaren su Kubura da Laure kuwa bakin ciki kamar zai kashesu. Sai cika suke suna batsewa ai kuwa Mairo banda zarya ba abinda take wajen yar akuyar da aka haifa musu. Ba'a fi kwana takwas da haihuwar yar akuyan ba Kubura na dakan fura a karkashin bedi ita da yarta Talatu garin tsalle-tsallen yar akuyar taje wajensu tana shishine-shinshine Kubura kamar jira take, ta daga tabarya sama saitin yar akuyar ji kake kwaram tabarya ta fada dai-dai kan yar akuyar"Innalillahi wa'inna illahir raji'un" Fatsuma ta fada hade da yadda butar da ke rike a hannunta ta nufi wajen a guje ta daga yar akuyar da tuni rai yayi halinsa. Luare ce ta fito daga daki "Lafiya ake mana innalillahi a gida da tsakar ranar nan tamkar anyi mutuwa". ta fada tana kallon Fatsuma da tuni kwalla sun cika mata ido, Kubura tace, "Itama wannan yar akuya da k'wawar tsiya take yau na koreta daga madakar nan ya fi sau hamsin amma dan maita sai ta tafi ta dawo yanzu gashi tabarya ta sille mun dsga hannu ta fada mata a kai dama abinda ake gudu kenan". Fatsuma dai tana jinsu bata ce kala ba taje daki ta daukko hijab ta dauki yar akuyar ta tafi ta yar a bayan gari. Tana fita suka kalli juna hade da kwashewa da dariya Laure tace "Yaya kin mun dai-dai na rantse da Allah, sai yanzu hankalina ya kwanta amma da har mafarki nake na rasa yadda zan bullowa lamarin nan ace ina da akuya biyu Fatsuma ma ta mallaki akuya abun ai ba tsari". Kubura cikin dariya tace, "Ashe ba ni daya nake fargaba ba, ai na rantse ko kaza Fatsuma ba zata mallaka ba in dai ina lumfashi a cikin gidan nan, yadda na tsani Fatsuma haka na tsani abunda zaiyi sanadin mutuwata". A hanya Fatsuma ta hadu da Mairo ta bata yar akuyar taje ta yar a bayan gari, Mairo na ta tambayar me ya kashe yar akuyar amma Fatsuma tace kwananta ne ya kare. Ranar har dare wajen bacci Mairo na tambaya amma Fatsuma taki fadi mata dalilin mutuwar yar akuyar domin ta san halin Mairo duk da tana kwabarta bata san lokacin da zataje ta aikata wani abunba idan har ta sani. Bayan kwana biyu, fada suke ba ji ba gani, Wasila da Asabe na gefe suna kallo, sai kuma sauran yaran yan mata dake aikin zugawa duk da kasancewar gaba daya a bayan Talatu suke in banda "Ci ubanta! Nausheta! Yauwa kadata!" Babu abinda suke fada yayinta ita kuma Talatu tana iya kokarinta duk da kasancewar tafi karfin Mairo amma ta kasa saka yarinyar kuka saboda juriyarta. A bangaren Mairo kuwa sa'a kawai take nema domin ta sama wajen cizo a jikin Talatu domin ba sau daya ba tana kai hakori da niyar cizon sai Talatun ta ture mata kai, ana cikin haka Talatu tayiwa Mairo wani irin turewa da yasa ta fadi kasa kanta ya bugu da kasa. Tabbas taji zafin turewar amma taki yin kuka ta taso cikin fusata da gudu ta rarumo Talatu ta dankara mata wawan cizo a kunne. Wani irin kara ta saki hade da rushe da kuka tana fadin "Ta cire min kunne na shiga uku wayyo Kubura" Nan ta fadi kamar yar yaye tana birgima Wasila na ganin haka ta ce "kai-kai kai-kai na rantse da Allah sai mun fadawa Mama. Asabe ruga gida kice ga Mairo nan ta cirewa Talatu kunne da cizo". Da fadar haka Asabe ta kwasa da gudu gida, ita kuma Wasila ta nufi Mairo bayan ta cire dankwali ta daura a kugu "Yau ko ke mayya ce ba cizo ba sai na ci ubanki". Mairo da ke tsaya a wajen tana sosa kanta inda ya bugu kallo kawai take bin Wasila da Talatu da shi. Su kuwa yan zuga tuni kowa ta ja bakinta tayi shiru, cikin sauri Wasila ta kama Mairo da kokowa ba wuya ta kayar da ita dake ta fita karfi sai dai da faruwar hakan Mairo ta sama damar galla mata cizo a hannu yayin da take kokarin danne kan Mairon.Ai kuwa itama ta kwalla ihu tare da mikewa tana yarfa hannu, Mairo ta mike tana bin sauran yaran da kallo "Wata ma ta zo in kun isa". Wata yar bakar yarinya tayi tsaki hade da cewa "Kinsan dai ba tsoronki ake ji ba, banza bata iya komai ba sai cizo". Mairo tace "Eh din cizon ma iyawa ne wani ma yayi in zai iya". Tun daga nesa ya fara fadin "Talatu Wasila wa ya dakeku".


Gaba daya suka juya kawunansu zuwa inda kiran ya fito, Zubairu suka hango ya fito daga daji hannunsa rike da danko na harbin tsuntsaye, cikin kuka Wasila tace, "Mairo ce ta cijemu". Duban da zaiyi wajen Mairo bata nan can ya hangota ta zuba a guje ta nufi cikin gari ai kuwa ya rufa mata baya a guje. Bai wani sha wahala ba ya kamota yana zuwa kuwa ya sa kafafu ya kwalfeta ko tausayinta baiji ba balle ya ga karantarta ya fara wanka mata mari. Ai kuwa Mairo ta fara kuka hade da ihu kamar wacce ake cirewa raiWani Dattijo ne ya karaso wajen cikin hanzari ganin irin dukan da Zubairu kewa Mairon da kyar ya iya hangaje Zubairu daga kan Mairo yana fadin "Zubairu baka da hankaline baka ganin yarinya ce ko so kake ka kasheta". Zubairu dake cika yana batsewa yace "Ai gwara in kasheta tunda bata da amfani sai dai taita cizon mutane kamar mayya sai na ci ubanki yau kuma sai na cire hakoran nan da kike cizo da su inga ta tsiya" Ya sake nufarta ai kuwa cikin hanzari Mairo ta mike hade da shekawa da gudu, "Allah ya isa mugu azzalumi ba zan taba yafe ma ba ko kabarinka na ci da wut...". Bata karasa maganar ba ta sake juyawa ta zuba a guje ganin ya rugo gareta.Bata zame ko'ina ba sai gidan Inna Ma'u ta fada daki da gudu Inna Ma'u na bacci a kan tsohon gadonta taji mutum ya tsallaka bayanta. "Innalillahi miye wannan". Ta fada da sauri hade da tashi ta juya sai ganin Mairo tayi har zata fara tambayarta gudun me take Zubairu ya fado dakin yana fadin "Ina take?". Cikin fushi Inna Ma'u tace "To masifaffe ashe kaine kai kullum baka da aiki sai duka da zaluntar Mairo sai kace ba kanwarka ba? Yaushe zakayi hankali ne Zubairu dubi yadda ka shigo gida ka fado daki ko sallama babu". Yana wuci yace "Dan Allah Inna karki hanani cin uban Mairo zagina fa tayi bayan ta cicije jikin su Talatu dan na dan doketa shine take mun Allah ya isa". Inna Ma'u tace "Kai dai wallahi anyi sakaran banza ko dan kana dan fari, yanzu kaine zaka shigarwa su Talatu tarayya a kan Mairo sai kace Mairon finsu tayi. To fice ka bar mun gida ba zaka daketa ba kaji na fadama".................


Muje zuwa


Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

Post a Comment

0 Comments

Ads