ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 28 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IV1i4scamcs

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-28-hausa.html


*^ Part 28 ^*Murja ta cigaba da cewa, "A lokacin ta juyo take tambaya yaushe na shigo dakin na ce mata yanzu na shigo. Haka dai ta karbi sakonta tare da balbaleni da masifa wai bani da tarbiyya shiyasa bana sallama idan zan shigo cikin daki, duk a tunaninta ban fahimci abinda take nufi ba, bayan kuma da wayona na fahimci duk abinda take nufi. Dare nayi Babana ya dawo na fada mai duk abinda kunnuwana suka ji Lami na fada, amma sai ya mayar da zancen shiririta a tunaninsa fahimtata ce kawai amma ba haka Lami take nufi ba. Washe gari kuwa tun da safe aka zo aka tasheni daga bacci tun lokacin da naga makwabtanmu maza sun cika gidan hankalina ya tashi wai Babana ya mutu. Nayi kuka a ranar kamar raina zai fita, daga karshe ma da na rungume gawar Babana da kyar aka kankareni in ta kuka, ita kuwa Lami sai lalashina take itama tana kuka irin na munafurci a gaban mutane.


Sai da nayi kwana biyu bana iya cin abinci kullum sai kuka, yayin da ita kuma Lami da sauran makwabta da ake zaman makoki da su suke lalabona wani lokacin da kyar ake samu in ci abincin. Daga bangaren yan uwan Babana na nesa wasu sun zo, amma Yayanshi Alhaji Sadi bai zo ba haka bai bar wani daga bangarenshi ya zo ba, dama mutum ne mai tsatsauran ra'ayi. Bayan anyi sadakar bakwai ne kowa ya watse ni kuma na fara fuskantar wata sabuwar rayuwa a gidan. Domin babu kalar zalinci da muguntar da Lami bata yi mun. 


Bayan Lami ta gama Idda sai ta auri wani saurayi mai suna Lawal yayin da ta tatare dukkan dukiyar Babana suka koma karkashinta, sabon mijinta yake juya mata dukiyarta. Mahaifiyarta ma Baba Larai ta kwaso kayanta daga kauye ta dawo gidan. Nayi tunanin zan iya samun sauki a wajen Baba Larai ko kuma sabon mijin Lami amma sai na ga ashe duk halinsu daya ne, sun tsaneni basa sona ko kadan , ko a lokacin na tabbata dama kadan suke so su samu su hallakani ba don komai ba kawai saboda dukiyar da mahaifina ya bari ta zama mallakinsu gaba daya" Murja Ta share hawayen da suke ta zarya a fuskarta sannan ta cigaba da cewa, "Na azabtu iya azabtuwa a wajen su Inna Larai da Lami, a kullum ni nake share gida na wanke musu kaya abubuwa da yawa tun ban iya ba suke sakani kuma idan nayi ba dai-dai ba su sameni suyi min dukan tsiya. 


Akwai ranar da Lami tana zaune a falo tana kallo ta sakani dafa Indomie, duk da na fada mata ban iya ba amma ta ce sai na dafa, da naje na dafa na kawo mata tana sakawa a baki ta zubar wai na cika yaji so nake na kasheta. Don haka ta tsareni ta sani dole sai da na cinye Indomie din da zafi duk sai da na ƙoƙone baki da hannu, washe garin ranar har zazzabi nayi. Baaba Larai kuma haka zata daukko kayanta wanda ta san cewa ba zan iya wankewa ba domin ni kaina ban wuce a rika min wanki ba, amma ta ce sai na wanke su, idan na wanke ta ce bai fita ba haka zata tsareni ko zan wuni ne a wajen sai na wanke ya fita yadda take so.


Bayan shekara da wani abu Lami ta haifi yaro mai suna Khalil, a kan yaron nan ma nasha azaba, domin haka zata bani rainonsa amma da zarar yayi kuka ko bansan dalili ba haka zata sameni taita duka wai ina son in kashe mata yaro. Lokacin da na ga lalai-lalai so suke su kasheni a gidan, wataran bayan isha'i na saka kayana kala biyu a leda na faki idon mai gadi na tsere daga gidan. Na san dai cewa nayi gararanba a cikin gari na tsawon sati guda da wani abu, watarana da daddare ina bacci a rumfar wani mai shayi, domin a nan nake kwana kan benci idan sun tashi, kawai naji wani irin masifafden ciwon kai wanda ban taba jin kalarsa ba.


To daga wannan ranar dai zan iya cewa ban kuma sanin a wane hali nake ba, raye ko a mace sai fa yau da na farka daga bacci na tsinci kaina a cikin wannan yanayi". Safuratu ta sauke wani gwauron lumfashi hade da cewa, "Tabbas kinga rayuwa, kuma rayuwarki kadai darasi ce babba a cikin al'uma, daga labarinki na karu da abubuwa masu yawa. Farko dai kin taso cikin gata da hutun rayuwa a wajen babanki, daga karshe kuma kika tsinci kanki cikin maraici na rashin uba tare da rayuwa cikin kunci da wahala a wajen Lami, duk da haka kaddarar Allah bata barki iya nan ba sai da kika dandani rayuwa cikin hauka na tsawon lokaci. Ba komai dama mumini yana tare da jarabtar rayuwa kala-kala". Kuka kawo Murja ta fashe da shi, Safuratu ta rungumeta ita kuwa ta kwanta a jikinta tana kuka irin mai sosa zuciya. 


Sai da tayi kuka mai isarta yayin da ita kuma Safuratu na ta tunanin ta yadda zata bullowa lamarin, domin ta san cewa har zuwa yanzu Murja bata san cewa ita Aljana ce ba mutum ba, kuma yadda Murja ke tsoron Lami ba lalai ta yadda ta koma gidan cikin dadin rai ba. Safuratu ta bata rai hade da cewa, "Kiyi hakuri Murja ki daina kuka, na sha alwashin kwato miki yancinki a wajen Lami, insha Allah sai ta girbi abinda ta shuka ba ita kadai ba ma hatta Baaba Larai din da mijinta ba zasu tsira ba. Don haka yanzu kiyi hakuri ki tashi muje mu hau mota mu je gidan naku".  


Murja dagowa tayi daga jikin Safuratu, duk da dai bata san wacece ita ba amma taga alamun akwai tausayi a tare da ita musamman yanda ko kyamarta bata yi, ta ce, "Baiwar Allah kiyi hakuri duk da ban san ko ke wacece ba amma bana sha'awar komawa gidan nan, saboda idan ma na koma babu abinda zai canza. Don bani da dangi wanda zasu tsaya min balle su kwatar min yancina. Na taba zuwa har gidan Baba Sadi na fada masa da sa hannun Aunty Lami a mutuwar Babana amma daga karshe ma koroni yayi yace baya son ganina kuma idan ya sake ganina a gidanshi duk abinda yayi min ni na jawa kaina".


Safuratu ta ce, "Ki yarda dani kiyi hakuri ki tashi muje gidan, bayan nan zaki ga abunda zai faru ni nan da kike gani ni zan tsaya miki zan samo yan sanda da lauyoyi wanda zasu kwato miki hakkinki a wajen wadannan azzaluman mutanen kuma nayi miki alkawarin za'a hukunta Lami bisa laifin kashe mahaifinki idan har aka gano da sa hannunta a mutuwarsa". Murja tayi shiru na lokaci mai tsawo kamar ba zatayi magana ba kuma dai zuwa can ta kalli Safuratu ta ce, 


"Duk da kasancewar na fiki shekaru ma'ana na girmeki a halin da ake ciki yanzu bani da wani gata sai Allah sai kuma ke saboda babu wanda na sani sai ke, saboda haka bani da wani zabi da ya wuce in yarda dake, na tabbata in dai da gaske kina da hanyar da zaki saka yan sanda su kama Lami to ni kuma zan bada hujjoji da yawa a kanta. Sai dai kuma ina fargabar zuwa yanzu Aunty Lami ta zama babbar hajiya mai kudi, watakil zuwa yanzu ta tara iyali da dukiya mai yawa don haka shari'a da ita kamar zai bada wahala". Safuratu tayi murmushi hade da cewa, "Karki damu ina da hanyoyi da yawa kuma nasan cewa a kasar nan masu kudi da masu aiko su suke da alfarma ta fada aji, ni dai fatana ki amince mu koma gidan". A zuciya kuwa murmushi Safuratu tayi tana fadin, "Ni ce yan sanda da lauyoyin kaina da kaina da sannu zaki gane hakan". 


Bayan dan nazari Murja ta amince su je gidan bayan tace a garin Kuje take kuma idan sukaje garin zata gane gidansu ko dake dama babanta sananne ne a garin ko da bata gane gidan ba da anyi tambaya za'a kai mutum har gidan. Sai da sukayi tafiya mai dan tsawo tukun suka fito bakin titi daga cikin dajin, sun dade a bakin hanya suna tsaida motoci basu samu ba, da kyar suka sama wata doguwar mota mai cike da fasinjoji suka shiga. Ana cikin tafiya direban ya hada wani mahaukacin birki, yayin da ya fara kokarin juya kan motar kamar yadda motacin dake gabanshi da bayanshi suke kokarin juyawa suma.


 Su Safuratu suna cikin mota duk sun hargitse saboda yanayin taka birki da akayi sai jin karan bindigo sukayi ta ko'ina. Nan take suka ga matasa rike da bindiga suna fitowa ta ko'ina daga cikin daji. Babu abinda mutane suke sai innalillahi ciki kuwa harda Murja da bata taba ganin tashin hankali irin wannan ba musamman da taji ana cewa yan fashin daji ne masu garkuwa da mutane. Cikin lokaci kankani aka fiddosu daga motoci, mota ta fi goma sha biyar aka kada su cikin daji wai anyi garkuwa da su..................


Ni kuma na gaji 😁

Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Post a Comment

0 Comments

Ads