ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 24 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/IV1i4scamcs

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-23-hausa.html*^ Part 24 ^*

Aljana Marakisiyya ta fashe da dariya irin ta mugaye kuma azzalumai, kana ta ce, "Yau zaki ga ranar yarda da kuma aminci, daga yanzu ba zaki sake yarda da zancen duk wani azzalumin aljani irina ba". Dariyar ta sake fashewa da ita irin ta mugunta yayin da take kallon Safuratu lokacin da take iya kokarinta domin ta mike amma ta gagara ko da motsa dan yatsarta. Marakisiyya ta cigaba da cewa, "Dama kin daina wahalar da kanki na kokarin tashi ko kuma motsa jikinki, domin bayan ido babu abinda zaki iya motsawa a jikinki don kuwa zuwa yanzu dafin Sankarau ya gama gauraye sassan jikinki. Hakika kinyi min abinda babu wani mahaluki kama daga kan mutum ko aljani da ya taba mun, kin azabtar da ni azaba mai radadi, kuma tun daga wannan lokacin na dauri aniyar yakarki kuma yaki irin na sunkuru ta hanyar cin amana gashi kuwa nayi nasara".


Bata rai tayi yayinda fuskarta ta cika da fushi kana ta dora da cewa, "Ina miki albishir da cewa a cikin dabi'una babu abinda ya canza har yanzu haka nake bani da tausayi bani da imani, hatta mutanen da muka karya sihirin da na musu nayi ne kawai domin dana miki tarko don ki yarda dani ki aminta cewa na shiryu, amma duk yanzu bayan na gama dake zan koma in sake mayar da su ruwa, abinda ma baki sani ba duk abinda ke faruwa a tsakaninmu Boka Kare Dangi yana sane kuma shi yake tsara min wasu abubuwan na yadda zaki yarda dani. Yanzu haka wajenshi zan kaiki domin ya batar dake daga bayan kasa. Ki sani ba zan bari ya kashe ki ba domin idan aka kasheki ba zaki dandani dacin bakin ciki da radadi gami da kunar zuciya kamar yanda nake so ki ji ba, don haka na fi so ya daureki a cikin kurkuku inda ba zaki taba fitowa ba har karshen rayuwarki haka zaki mutu da tunanin bil adaman da kike son taimaka amma ba hali".


Ta sake bushewa da dariya irin ta shedanun aljannu sannan ta matsa kusa gaf da Safuratu ta dago habarta sannan ta ce, "Murja kuma na haukatata kenan har abada kuma a jikinta zan rayu har zuwa lokacin da zata mutu, domin ina jin dadin rayuwa a cikin farfajiyar ruhinta". Da gama fadar haka aljana Marakisiyya ta dafa kan Safuratu nan take suka bace bat.

^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
 Daji ne mai cike da duwatsu da dogayen itatuwa da kuma kanana wanda suke karawa yankin wajen duhu, musamman da damana idan korayen tsirrai sun fito. Tsakanin dajin da wani kauye mai suna Dawari tafiyar awa biyu ce, a mashin kuma ana iya kwashe mintuna talatin saboda duwatsu. 


Tun kafin ka karaso wajen kogon dake jikin wani babban dutse zaka fara cin karo da kwarangwal din kawuna rataye a jikin bishiyoyin da suka zagaye wajen wanda zaka kasa bambance kwarangwal din na mutanene ko na dabbobi. Bakin kogon dutsen kuwa kaya ne barkatai irin na tsafi a jikin dutsen duk an shafa wani jan abu wanda ya fi kama da jini, da zarar ka doshi kogon dutsen kuwa kunnuwanka zasu fara jiyo maka wani amon sauti dake fitowa daga cikin kogon wanda duk kwarewarka a iya tantance murya, ba zaka iya bambance muryar namiji kake ji ko ta mace ko ta jariri ba. Haka zalika ba zaka iya gane abinda muryar ke fada ba. 


Zaune yake a cikin kogon ya saka kaskon wuta gaba, bakinshi na ta motsi amma ba zaka ce ga abinda yake fada ba, tsoho ne da ya haura shekaru saba'in ya kasance sirir kuma gajere amma tsabar baƙi kanshi har walkiya yake kasancewar ya sha aski kwal-kwal, idonsa daya a kanne yake da ido daya yake amfani. Boka Kare Dangi kenan, shi kadai yake rayuwa a cikin wannan daji, a cikin dajin yayi iyaka wacce idan har ya kasance ba wajensa ka zo ba to da zarar ka tsallaka wannan iyakar sunanka gawa domin kuwa aljannunsa ne zasu shanye maka jini ka mutu. A da can baya boka Kare Dangi a cikin kauyen Dawari yake zaune, ganin irin hatsabibancishi yayi yawa yasa mutane suka koreshi daga garin, wannan yasa tun daga wannan lokacin gaba mai karfi ta shiga tsakaninsa da mutanen kauyen, har ta kai ga ya kafa wannan iyaka da duk wanda ya tsallako in dai ba da niyar zuwa wajenshi yaje ba to fa sunanshi gawa. 


 A dai-dai wannan lokaci ne wata irin rikitacciyar dariya ta bayyana wacce amonta ya cika baki daya kogon, jim kadan sai ga Aljana Marakisiyya ta bayyana dauke da Safuratu da ko motsa dan yatsanta bata iyawa. Nan take ta direta a gaban wannan Boka, bayan lokaci kadan ya bude idonshi kwara daya ya kalli Safuratu kana ya bushe da dariya daga bisani kuma ya bata rai tamkar bai taba yin dariya ba ya ce, "Ashe kece hatsabibiyar aljanar da kike kokarin bata mana aiki? To ki sani karyarki ta sha karya, na batar da mutane da aljannu da yawa wanda sukayi kokarin taka min birki ko kuma sukayi kokarin wargazawa wani aljanina aiki yayin da na tura shi wani waje aiki kamar yanda kikayi kokarin yiwa Marakisiyya".


"Ni Boka Kare Dangi gagarabadau ne, ni nan da kike gani murucin kan dutse ne ban fito ba sai da na shirya, haka zalika ke karamar koro ce a cikin jerin mutane da koma aljannu da sukayi niyar yakata ko kuma juya min baya, domin ina da aljannun da zasu yagal-galaki su cinye danya a cikin kankanin lokaci, tun asali na barki da Marakisiyya ne domin ni a wajena tamkar tururwa kike ko da yaushe zan iya murtsikeki in kasheki har lahira". Da gama fadar haka ya sake shekewa da wata dariyar irin ta wanda suka shahara a cikin shedanci, Marakisiyya ta dai-daita saitin kan Safuratu tayi kwallo da shi, don karfin dukan sai da Safuratu ta wulwula a kwancen da take, cikin zafin nama game da kunar rai Marakisiyya ta dinga dukan da kwallo da Safuratu sai da ta ga ta hada mata jini da majina kana ta dube ta a wulakance sannan ta ce,


"Wannan shine kadan daga cikin irin ramuwar gayya da nasha alwashin zan miki tun daga lokacin da kike daureni kika azabtar dani na kwana uku, kuma ki sani ni zan azabtar dake na tsawon rayuwarki ne, duk da nasan cewa rashin abinci ba lalai ya hallaka ki ba, amma ki sani zaman kadaici da tunanin mutanen da kike so ki taimaka shine zai zama silar ajalinki". 


Marakisiyya ta kai dubanta ga Boka Kare Dangi wanda tun sa'ada Marakisiyya take dukan Safuratu yake kyalkyala dariya ta dan russuna ta ce, "Kamar yadda na fada maka tun a baya ina fatan zaka cika min alkawari kamar yadda nima ban taba karya ma alkawari ba, so nake ka daure Safuratu a cikin kwalbar sihiri ka bani ita in kaita inda ba zata sake ganin ko farcen aljan ba balle dan Adam". Boka Kare Dangi ya murtuke fuska sannan ya ce, "Na san halin kafiya da naci irin naki Marakisiyya, domin idan kika saka kanki yin abu to ko ni ban isa in dakatar dake ba, amma ina kara gargadinki game da kwalbar kason nan, domin fa idan har aka samu akasi kwalbar da zan daure Safuratu ta fashe to daga nan daurin da nayi mata ya kunce, kuma abinda nake jiye miki shine ita wannan aljana sanin kanki ne ta fi karfinki a duk lokacin da ta samu nasarar kuncewa daga dauri na san cewa ba makawa sai ta kashe ki, musamman da kika ce zaki koma rayuwa a jikin wannan yarinya Murja". 


Marakisiyya ta fashe da dariya hade da cewa, "Ai ni ba dakikiya ba ce, ina maka alkawar da cewa inda zan kaita ko hasken rana ba zata sake gani ba balle kuma ayi tunanin fitowarta". Da fadar hakan Boka Kare Dangi ya daukko wata kwalba kana yayi sihirinsa wanda nan take Safuratu ta zama tamkar bak'in hayaki ta shiga cikin kwalbar, nan take ya sa murfi hade da wani jan kyalle ya daure saman kwalbar. Da faruwar haka ya ba Marakisiyya ita kuwa cikin farin ciki ta karba, nan take ta nufi wani babban teku tayi nutse a ciki sai da ta tarar da karshenshi sannan tayi rami mai zurfi ta saka kwalbar ta mayar da kasar hade da cewa, "Nan ne kabarinki".................


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

Wa.me/+2348096831009

😍

Post a Comment

0 Comments

Ads