ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 21 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/Cwm4wecksEE

http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-20-hausa.html*^ Part 21 ^*Da ido ta bishi da kallo, matashi ne dan kimanin shekara sha takwas, fari ne kyakykyawa dan siriri da ka ganshi ka ga dan fulanin asali. Ga dukkan alamu aljana Safuratu bata fahimci abinda yake nufi ba don haka ta ce, "Me kace? Dani kake?". Kallonta yayi ido cikin ido babu alamar tsoro a tare da shi ya ce, "Cewa nayi ina sonki". Murmushi tayi wanda yake cike da mamaki, a tunaninta tsoro ne ya sa saurayin kamewa waje daya ashe ba haka abin yake ba yanzu ta gane ko kadan babu alamun tsoro a tare da shi, "Ni fa Aljana ce ka taba ganin inda mutum yayi soyayya da aljani?" Shiru yayi hade da dora hannu kan habarsa da alamu tunanin yake, can ya dago ya kalleta hade da cewa "Na sha jin labarin mata da ake cewa aljani ya auresu, ban sani ba lamarin gaskiya ne ko karya amma ni har ga Allah tunda nayi ido hudu dake naji na kamu da sonki, ni ji nake ba aljana ba ko ifiritu ce ke ina sonki kuma ina fatan ke ma zaki so ni". 


Dariya Aljana Safuratu tayi hade da cewa "Ya sunanka?". "Sunana Sadiq amma yan garinmu suna kirana da Dan Malama, saboda babanmu shine malamin kauyenmu ban dade da dawowa daga birni wajen almajirci ba kuma duk a cikin abokaina na kauyenmu na fi kowa kokari wajen karatu. Ban ma fada miki ba na iya ayatul kursiyyu in karanto miki kiji?" Ba tare da ta tanka mishi ba ya karance ayatul kursiyyu tsaf kana ya dora da cewa, "Duka yan matan kauyenmu babu wacce bata sona, yar gidan Hardo Sani mai kudin garinmu ma ni take so, ban sani ba ko don saboda kyauna ko kuma saboda ilimina suke sona. Ni kuma duk a kauyenmu babu wacce nake so har na ji zan iya aura. Ko a birni ma da mukaje karatu har muka dawo banga wacce tayi min har naji zan iya aurenta ba. Amma ke daga kallon farko na ji zan iya aurenki in rayuwa dake ko da a kan garwashi ne. Ina nufin zan iya jure tafiyar kasa ko da ta kai daga nan zuwa bangon duniya ne domin zuwa neman aurenki". 


Wata dariyar Safuratu ta kyalkyale da ita hade da cewa, "Wai kai kam bakinka baya gajiya ne wannan surutu haka kamar aku? So nake in tambayeka, me yasa bakaji tsorona ba bayan na san a rayuwarka baka taba ganin makamancin abinda ka gani yanzu ba, hayaki ya rikide ya zama mutum kuma na fada ma ni aljana ce amma na ga ko kadan babu alamar tsoro a tare da kai". Murmushi yayi tare da girgiza kai sannan ya ce, "Ni ma nayi mamaki rashin jin tsoron da nayi, amma a wani bangare na tunanina yana fadamin da ace dukkan aljanun duniya haka suke da suffa kyakykyawa irin taki to babu wanda zai ji tsoron aljani sai dai ya so shi kamar yanda na afka sonki a yanzu, don Allah ki taimaka muje gidanmu in gabatar dake wajen babana a matsayin matar da zan aura na tabbata zaiyi farin ciki, domin tun yanzu ya fara min maganar aure ni kuma na ce mashi bani da budurwa".


Dariya Safuratu tayi hade da cewa, "Naga alama da gaske kake, to bari kaji in fadama yanzu haka na haura shekara dari biyar a duniya, kwalbar nan da kake gani wacce ka fiddani daga cikinta tun kafin a haifeka na ke cikinta kaga kenan ni kakar kakar kakar kakar ka ce". Ta karashe maganar tare da murmushi. Shima martanin murmushi ya mayar mata hade da cewa, "Ai shi so babu ruwanshi da shekaru, in da so yana duba girman shekaru da tun a matakin farko ba zanji na kamu da sonki ba, bayan wannan ma dubi a suffar da kike, kinfi kama da matashiyar budurwa yar shekara ashiri, kinga kenan a ganina na zahiri in ma kin girmeni bai wuce ki girmeni da shekara daya ko biyu ba". 


Dariya aljana Safuratu tayi lokaci guda kuma ta hade rai tamkar bata taba yin dariya a rayuwarta ba, nan take kwakwalwarta ta shiga tunane-tunane kamar yadda ta saba a cikin kwalba, ita a kalla yau kusan shekara sha takwas kenan batayi dariya ba, kullum tunaninta wane hali Murja take ciki? Wane hali Fatima zata tsinci kanta a wajen su Mama Asiya idan suka wayi gari suka gano cewa bana nan. Akwai mutanen da yawa masu bakin hali da take bibiyar rayuwarsu wanda zuwa wannan lokaci da tayi a cikin kwalba bata san ko a wane hali suke ba. "Baiwar Allah! Baiwar Allah!" A hankali ta dawo daga duniyar tunanin da ta lulu, ita gabaki daya ma ta manta da wanzuwar Sadiq a wajen, kallonshi tayi da murmushi akwai abubuwa da yawa a gabanta amma dole ta ba shi lokacinta ko da kadan ne tunda shine ya ceto rayuwarta ya kubutar da ita daga shu'umar kwalbar da ta kasance tamkar kurkuku na daurin rai-da-rai a gareta, gashi kuma ya ce baya bukatar komai a wajenta, daga kalamanshi ta gane cewa mutum ne mai matukar hikima da iya tsara zance amma ga dukkan alamu shiririta tayi yawa a kwakwalwarsa. 


"Na ga kinyi shiru ne don Allah karki ce ba zakije wajen mahaifin nawa ba". Sake kallonshi tayi ta girgiza kai hade da cewa, "Aa ai dole ne zanyi maka sakayya tunda kai ka ceci rayuwata don haka muje gidan naku". Farin ciki ne sosai ya ziyarci zuciyar Sadiq saboda hauka irin nashi haka suka jero suna tafe yana ta zafga mata surutu kasancewar yamma ta fara yi duk wanda ya hadu da shi a hanya sai yayi masa magana, ko ya daga wa mutum hannu wai don su ganshi tare da kyakykywar budurwa, duk haukan da yake bai son cewa shi kadai yake ganin Safuratu ba sauran mutanen ba mai ganinta, kallonshi ma suke tamkar mahaukaci yadda yake tafe yana surutu shi kadai. Sunje dai-dai kofar gidansu ya waiwayo domin yayi wa Safuratu magana nan take yaga wayam ba kowa a wajen ta bace. Dube-dube ya kama yi harda komawa baya da gudu yana waige amma bai ga Safuratu ba, don haka ya tsaya hade da daga kai sama ya bude murya da karfi hade da cewa, "Ina sonki Safuratu don Allah ki zo muyi aure".


 Ba karamin dariya ya ba wasu daga cikin dai-daikun mutanen dan kauyen nasu na fulani ba, ko da yake in da sabo sun saba idan Sadiq yayi wani abun kamar sakarai da yawa sukan ce ko don ya kasance dan fari ne domin shi kadai iyayenshi suka haifa. Aljana Safuratu na gefe tana kallonshi duk abinda yake yi amma shi baya iya ganinta tayi murmushi hade da cewa, "Sadiq ko? Ashe akwai sauran mutane irinku dole ka ce yan matan kauyenku suna rububinka domin mutane irinku akwai shiga rai saboda kuna da abun dariya da saka nishadi, idan na sama lokaci zan waiwayo ka dole nayi maka sakayya bisa taimakon da kayi min Sadiq". Da fadar haka ta bace bat tamkar bata taba wanzuwa a wajen ba.

*********************************

Yara ne fiye da biyar sun zagayeta suna fadin "Mahaukaciya, yar macukule! mahaukaciya, yar macukule". Ita kuwa babu abinda ya dameta rawa kawai take ba ji ba gani, Safuratu dake tafe a kan iska yau kusan kwana biyar kenan tana neman Murja a cikin garin na Kuje lungo da sako take dubawa duk inda ta san za'a iya samun mutum bai tabin hankali tana dubawa amma ba ta ga Murja ba har ta fara hakura, daga sama ta ji hayaniyar yara har zata wuce ta kalli kasa cikin saurinsu irin na aljannu ta ce, "Murja!" Nan take ta bace ta bayyana a gaban Murjan yaran da ke wakar ji kawai sukayi ana wanwanka musu mari don haka da gudu suka bar wajen suna kuka. Tsaki aljana Safuratu tayi abun ya bata haushi musamman yadda ta ga mutane kowa na uzurin gabansu amma sun bar yara na tsokalan Murja wai don kawai tana da tabin hankali, to ai itama mutum ce ko mantawa suke suma Allah zai iya jarabtar su da irin wannan cuta na hauka? Tunanin ta ne ya tsaya yayin da ta ga Aljana Marakisiyya tana kokarin fita daga jikin Murja ta gudu...............


Masu son littafin daga farko, Ku ziyarci shafinmu Bonitomi.com.ng akwai book 2 tun daga part 1 har inda aka tsaya

Ko kuma ayi mun magana ta WhatsApp 08096831009


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

😍

Post a Comment

0 Comments

Ads