ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 20 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/LgVOwZek43U


http://www.bonitomi.com/2023/05/aljanar-fatima-book-2-part-19-hausa.html*^ Part 20 ^*


A fadar mai gari suka tarar da Mairo a zaune sai raraba idanu take tana kallonsu daya bayan daya, kusa da iya Fatsuma ta je ta zauna yayin da Bukar ya zaune gefen da maza suke, Kubura, Laure da Ladi ma suka sama waje gefen Fatsuma suka zauna, babu abunda su Kubura suke sai watsawa Mairo harara da gatsine kala-kala harda su cije lebe. Bayan sun gaishe da mai gari yayi gyaran murya hade da cewa, "Malam Bukar yarka Mairo ce ta kawo kararka ga ta nan zaune ta ce ka kama akuyar da mahaifiyarta take kiwo ka sayar da ita ba tare da amincewarta ba, da dai ban dauki zancen da mahimmanci ba kasancewarta yarinya amma su Malam Bashir suka bada shawarar a gayyatoku baki daya domin a ko da yaushe mu adalci muka sa gaba". 


Rike baki Bukar yayi hade da cewa, "A duniyar nan dai idan baka mutum ba kasha kallo, ban tari lumfashinka ba Mai Gari kuma yarinya ba karya tayi ba, sai dai a cikin zancenta akwai kuskure. Sanin kowa ne fahimtar babba da ta yaro ba daya bane, domin kuwa maganar nan da ta kawo akwai gyara a cikinta na cewa na kama akuya na sayar ba da sanin mahaifiyarta ba wato Fatsuma. Alhalin kuma ita Fatsuma ita ce da kanta ta bani akuyar ta ce in je in sayar inyi jari da kudin sauran kudi kuma zata biya Kubura gata nan kudin tinkiyarta". Ya kalli Kubura hade da cewa "Ko ba haka akayi ba tsakaninku da Allah?". Cikin hadin baki ita da Laure suka cewa, "Wallahi haka akayi". Kallonshi Fatsuma tayi suka hada ido yayin da ya aka mata da wata irin harara wacce sai da ta sa ta faduwar gaba.


Mai gari ya kalli Fatsuma hade da cewa, "Ke Fatsuma haka akayi? Kece da hannunki kika bashi akuya ko kuwa kamawa yayi ba da amincewarki ba kamar yadda Mairo ta fada". Daga kai tayi ta sake kallon Bukar yayin da shi kuma ya murtuke fuska alamun ba mutunci sai hararenta yake, zata daga baki tayi magana Bukar yayi sauri ya ce, "Wallahi Mai Gari a cikin abinda na fadi ma babu karya ga Kubura nan ga kuma Laure nan sune shaidata har a wajen Allah". Da sauri Kubura da Laure suka cewa, "Wannan magana haka take mune shaida a gabanmu akayi komai Fatsuma da kanta ta ba Bukar akuyar nan". Malam Bashir ne ya ce, "Kunga ba ku aka ce kuyi magana ba, da ake maganar shaida waye bai san irin zaman da kuke da Fatsuma ma ba a garin nan. Kowa ya san ba zaku iya shaidar alkhairi ba a kan Fatsuma don haka ku barta tayi magana da bakinta". Sadda kai kasa sukayi suna gunguni. Fatsuma kuwa zuwa lokacin tsoro yayi matukar kamata na irin kallon da Bukar ke mata, fargaba take kar ya saketa don dama ba sau daya yana yunkurin sakinta ba tsoron Inna Ma'u yake hanashi, don haka ta yanke shawarar daukar wannan laifin a ganinta zai fi sauki.


Mairo ta dafa Fatsuma hade da cewa, "Umma dan Allah ki fada Mai Gari ya ce zai kwatowa Ladi kudinta idan har da gaske nake". Cikin kwalla Fatsuma ta kalli Mai Gari hade da cewa, "Abinda suka fada gaskiya ne ni ce na bashi akuyar na ce ya sayar sauran kudin kuma na biya Kubura bashi ba tilasta mun yayi ba". Hannu Ladi ta fara tafawa hade da cewa, "Innalillahi wa'inna Illaihir Raji'un wato Fatsuma duk koke-koken da kikeyi a gida kina cewa ba da son ranki Bukar ya sayar da akuya ba karya kike kenan? Dan Adam butulu wallahi kin bani kunya Fatsuma". Mai Gari ne ya dakatar da ita hade da cewa, "Ya Isa!". Ya kalli Fatsuma sannan ya ce, "Kinga Fatsuma ki fadi gaskiya karki ji tsoron Bukar idan ma kina tsoron zai yi miki wani abu ne yasa kika boye gaskiya, to ki sani babu abinda zai miki tunda magana ta zo nan idan kuwa ya kuskura yayi miki wani abu to kuwa zai hadu da fushinmu". Sake kallon Bukar tayi da yake ta kallonta yana muzurai sannan ta ce, "Ba tsoro bane da gaske ni na bashi". 


Mairo ta fashe da kuka hade da cewa, "Mama dan Allah karki ji tsoron baba ki fadawa Mai Gari gaskiya". Bata rai Fatsuma tayi hade da cewa Mairo tayi shiru, ba yadda ta iya haka tayi shiru. Mai gari yayi iya yinsa domin ya fuskanci kamar akwai tsoro a tattare da Fatsuma domin ta cire tsoro ta fadi gaskiya amma ta ki fada. Don haka ya ce "To ke Ladi yanzu ya za'ayi kenan". "Ranka ya dade ni kam akuyata za'a biyani wallahi".


 Mai Gari ya kalli Fatsuma ya ce "To Fatsuma kinji yanzu sai ki fiddo kudin akuya da aka sayar a bawa Ladi tunda ta ce bata laminta ba". Fatsuma ta kalli Bukar, da sauri ya ce, "Ya kike kallona kin dai fi kowa sanin abinda ya faru Mai Gari na rantse maka da Allah kudin nan babu su an sace su. Tun da safe na hau mota na nufi kasuwar Garki domin saro kaya ina sauka, kaga aljihuna an farke an kwashe kudin wallahi da roko na samu na dawo gida don bani da ko sisi". 


Ajiyar zuciya Mai Gari yayi hade da cewa, "To ke Fatsuma kina da wasu kudi ne da zaki biya Ladi akuyarta ko kuwa?". Kuka Fatsuma ta fashe da shi hade da cewa, "Wallahi bani da kudi kuma bani da abinda zan sayar na biyata, wannan abun kaddara ne kawai amma ina neman alfarama a wajen Ladi da ta lamince in rika biyan kudin a hankali ko ta wajenka ne idan na tara dari biyar ko dubu sai in rika kawowa ana ajiyewa har a biyata". Nan fa Ladi ta nuna kin amincewa da haka ta nuna kudinta kawai take so da kyar Mai Gari ya shawo kanta ta ce zata amince amma da sharadin a fara karbo dubu goma ta wajen Kubura a bata.


Ai kuwa nan hauka ya tashi Kubura ta nuna tuni ta kashe kudi, dole dai Ladi ta hakura aka kashe magana a kan Fatsuma zata rika kawo kudinta ana tarawa a wajen Mai Gari har a hada kudin akuyar dubu talatin da biyar. Lokacin da suka koma gida Mairo ba karamin duka ta ci a wajen Bukar ba don har zazzabi sai da tayi, daga karshe ma ya koreta wai ta fita ta bar masa gida. Sai da Inna Ma'u tayi masa tatas ta ci masa mutunci sannan ya bar Mairo ta koma gidan.


  Tun daga lokacin Mairo ta yanke shawarar ajiye makamanta na duk wani rashin ji da take ko kuma daukar mataki a kan abinda su Talatu suke mata, domin ta fuskanci cewa duk abinda ta tsokalo yawanci a kan mahaifiyarta yake karewa. Yanzu ta maida hankalinta a kan neman kudi ita da kanta take zuwa daji ta yo ciyawa ko itace domin ta saida tana tara kudi a wajen Inna Ma'u a haka suka tara kudi ita fa Fatsuma suka fara kasuwanci suna ajiye kudin da kayan kasuwancin a gidan Inna Ma'u domin a can gidan an hanasu sakat

********************************
 BAYAN SHEKARA BIYU

Gudu yake tsakaninsa da Allah tamkar wani abun tsoro ne ya biyo shi, kai yatse ya kutse kanshi cikin dajin dake bakin babban rafin dake kauyen nasu wai ashe duk gudun da yake yi ba wani abu bane bahaya yake ji. Bayan ya samu wajen labewa hankalinsa kwance yake bahaya harda rufe ido, tun daga nesa ya fara hango wata kwalba wacce ke rufe da jan kyalle a bakin rafi da alama ruwa ne ya jawo ta. Don haka yana idarwa ya karasa wajen, duk karanbani irin na shi sai da gabanshi ya fadi domin wani abu ya gani yana yawo a cikin kwalbar tamkar hayaki.


 "To fa yau kuma me muka samu, shiyasa fa nake son zuwa bakin ruwan nan domin in dai zaka zo zakayi tsince-tsince abubuwan da ruwa ya jawo, amma wannan kamar kayan sihiri!" Ya fada shi kadai yake magana yayin da ya cire tsoro ya sa ice ya mirgina kwalbar. Da hausarsa irin ta fulani ya ce, "Watakil ma irin asirin nan ne da ake wa mutane ake jefawa a cikin ruwa, ko ma miye na rantse da Allah sai na fasa kwalbar nan, tunda na iya Ayatul kursiyyu bana tsoron ko wane asiri tunda Malam ya fada mana ko aljani yana tsoron ayar". Da fadar haka yayi murmushi nan take ya karanto ayatul kursiyyun da bai fi sati biyu da hardacewa ba nan take ya sa hannu ya dauki kwalbar ya buga ta da kasa.


Suman tsaye yayi, baki daya jikinsa ya daina motsi bayan ganin wannan hayaki da ya fito daga cikin kwalbar da ya fasa ya rikide ya zama zankadadiyar budurwa fara irin wacce ake kira son kowa kin wanda ya rasa. Wata irin mika tayi tare da hamma hade da cewa "Alhamdulillah Allah na gode maka shekara sha takwas kenan yau ka fitar dani daga wannan kwalba wacce ta kasance kurkuku a gareni. Tabbas Allah kaine maji rokon bawa". A lokacin ne ta kai kallonta ga kyakykyawan dan fulanin da ya tsareta da kallo tamkar gunki ko kiftawa bayayi. "Bawan Allah! Bawan Allah! Karka ji tsoro ni aljana ce amma ba muguwar aljana ba, sunana Safuratu, an daureni a cikin kwalbar nan ne sai yau Allah ya fitar dani ta sanadiyarka. Don haka ka fadi duk abinda kake so insha Allah zan yi ma". "Na rantse da Allah Ina Sonki"........................


😢 Allah sarki finally ta bayyana ashe bata mutu ba

Masu son littafin daga farko, Ku ziyarci shafinmu Bonitomi.com.ng akwai book 2 tun daga part 1 har inda aka tsaya

Ko kuma ayi mun magana ta WhatsApp 08096831009


Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 

https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

😍

Post a Comment

0 Comments

Ads