ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 11 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️                        🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️


By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_
https://youtu.be/i_1jj2TTNzY*^ Part 11 ^*


 "Ni zaki cewa marar tsoron Allah dan ubanki? To yau zan nuna miki rashin tsoron Allah kamar yadda kike ikirarin bani da shi". Bukar ne ke fadan hakan yayin da yake dukan Fatsuma ta ko'ina. Ita kuwa banda ihu babu abinda take, makwabta ne suka shigo suka kwaceta don sai da ya mata lillis ita kanta tayi nadamar nasihar da tayi masa, domin tasan abinda ka iya biyo baya kenan. 


"Haba Malam Bukar wannan wace irin rayuwa ce ka maida matarka tamkar wata baiwa dukan safe daban na dare daban?".  "Sakkanni Malam Tsalha yau sai na kakkaryata a cikin gidan nan, wannan matar da kake gani ko kadan bata da mutunci, wai har ni zata kalli kwayar idanuna tace bana tsoron Allah".


Dakyar Malam Tsalha makwabcinsu ya hana Bukar ya cigaba da dukan Fatsuma shi da sauran makwabtan da suka shigo mata, daga karshe har ya juya kan su Talatu yana mai nuna musu rashin dacewar abinda suke wa Fatsuma na musgunawa a cikin gidan, ai kuwa nan take suka hayayyako masa da masifa tamkar zasu cinyesa danye, dole tasa yayi saurin barin gidan. Fatsuma sai da tayi kwana biyu tana jinya jikinta duk yayi tsami. Yau ma zaune take kan tsohuwar sallaryata bayan ta idar da sallah, ta daga hannu tana mai kai kukanta ga Allah a game da matsalolin rayuwar da take fuskanta. 


Mairo ce ta shigo gidan sanye da hijab dinta sai fara'a take, ta wuce dakinsu Laure na zaune tana tankadan fura haka kawai zuciyarta ta raya mata akwai wani abu a kasa, don haka ta kalli danta karami hade da cewa "Sani maza tashi ka bi Mairo baya na ga ta shiga daki cikin farin ciki ka gano mana me suke yi". "To ya fada hade da tashi jikinsa yayi busu-busu da wasan kasa tamkar wanda aka tono daga cikin kasa. Kai tsaye ya fada dakin ko sallama baiyi ba ita kuwa har lokacin Mairo na zaune kan tsohon gadonsu tana jiran mahaifiyar tata ta gama addua domin ta nuna mata sabon dinkin da Baban su Salame yayi mata, ta ga shigowar sani yayi tsaye yana kalle-kalle tamkar wani dogari


"Kai miye akayi ka wani shigowa mutane ko sallama babu, me za'a baka?". Murguda mata baki yayi hade da cewa "Ba'a sani ba" "Ni sa'ar wasanka ce ni kake cewa ba'a sani ba?".  "Eh din ance ba'a sani ba, ba'a sani ba ke uwata ce?".  Mikewa tayi da niyar dukansu Fatsuma tayi mata gyaran murya hakan yasa ta fasa dukan nashi ta koma kan gadon ta zauna. "Fitar mana daga daki". "Ba za'a fita din ba ki zo ki fitar dani". Ya fada yana hararenta "Sani ni sa'arka ce? Ka rainani ko? To na rantse ba dan Umma ta hanani ba sai na faffallamaka mari a dakin nan sai dai duk abinda za'ayi ayi, shege magulnaci tun kana karami ka koyi gulma irin na iyayenka".


"Ni ba shege bane kece shegiya mayya" a hanzarce ta tashi zata kai masa duka dai-dai lokacin Fatsuma ta shafa addu'a ta rike ta "Baby ba na hanaki ba". "Haba Umma kina ji fa wai ni yake cewa mayya". Mairo ta fada ta tabe fuska tamkar zatayi kuka don ta so ta kwada masa mari, "To ke mayyar ce da gaske da har hakan zai dameki? Kuma ai ba yau kika fara jin an danganta ki da kalmar mayya ba, su kansu yaran iyayensu suka ji suna fada. Kuma ina gargadinki karki kara cewa wani shege ko ba yanzu ba kinji na fada miki, ko baki san ma'anar shege bane?".  "Yi hakuri Umma insha Allah na daina". Ta fada hade da komawa ta zauna.


"Sani aiko ka akayi?". Fatsuma ta tambaya yayin da take kallon Sanin dake binsu da idanu, shiru yayi baice kala ba Mairo tace "Kinga irin rainin wayon na su ko ana masa magana amma yayi banza da mutane". "Eh din anyi shirun Laure tace kar na kara yiwa mayya magana karta cinyeni".  Lebe Mairo ta cije domin kawai danne zuciyarta take yi ji take kamar ta hau yaron da duka, wato yana nufin ummanta ce mayya. Fatsuma tace, "Rabu da shi Mairo yarinta ce".  Kwafa tayi hade da cewa "Ai zamu hadu a waje".  "Mu hadu din idan kika dakeni sai na fadawa Laure ta ci ubanki". 


Mairo zatayi magana Fatsuma tace, "Ya isa haka karki kuma cewa komai, kuma karki sake ki dake shi kinji na fada miki". Shiru tayi ba tare da tace komai ba. Sai da ya gaji da tsayuwarsa ya koma yace wa Laure babu abinda suke. Da fitarsa Mairo cikin murna ta fito da kayan sallah da Baban Salame ya dinka musu iri daya ita da Salame tana nunawa Mamanta, kamar daga sama sukaji ance, "Innalillahi Wa'inna Illahir Raji'un Yaya Kubura zo ki gani". Suna wai-wayawa suka ga Laure tsaye a bakin kofa tana kallon kayan dake hannun Fatsuma.......Muje zuwa

Join Aljanar Fatima Book 2 Fans Group 
https://chat.whatsapp.com/FfUTRuLiKrJLmRHqnNoR4N

Post a Comment

0 Comments

Ads