ALJANAR FATIMA BOOK 2 Part 3 Hausa Novel 2023

🧟‍♀️🧟‍♀️ 🧟‍♀️🧟‍♀️

*ALJANAR FATIMA BOOK 2*

🧟‍♀️🧟‍♀️ _Wata Sabuwa_ 🧟‍♀️🧟‍♀️

By *Kingboy Isah* 

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
*Zamani writers Association*
•••••••••••••√••••√••••••••••••••••
_$$ Free book but support us read in our site $$_*^ Part 3 ^*


Gaba daya kan Fatsuma ya kule ta kidime tama rasa me zatayi domin ceton rayuwar yarta kwal daya da take gani tana jin dadi gata tana kokarin rasa ranta. Da sauri ta dauketa ta nufi daki da ita, Zubairu ne ya shigo a fusace yana huce "Ina Mairon aradu yau sai na babbalata" Fatsuma na jin shigowarsa bata kula ba ta fada daki da Mairo ya nufi dakin da nufin daukko Mairo Kubura ta ce "Kai zo nan dan ubanka karkaje ka karasa gawar da ba taka ba". Ya juyo yana kallon uwar tasa "Haba Innata ki barni kawai na balla yarinyar nan tunda har an kai lokacin da zata iya sa hannu ta daki su Talatu, wallahi ji nake dukan da na mata bai isheni ba hannuna kai-kayi yake".


Kubura tace "Gaske naga ta shigo tana kuka dama kaine ka daketa?" "Eh ai can daji Talatu ta sameni take fada mun abinda ya faru shine na ciri lafiyayyar bulalar gwanda cikin sa'a kuwa mun bi ta layin gidan Inna Ma'u muka ganta tayi niyar rugawa ma ta koma gidan Inna Ma'u amma na tare kofa na kamata na jata bayan layin na ci ubanta dakyar mutane suka ririkeni aka kwaceta na tabbata ma na fafasa mata baya shine fa ta rugo gida". Da jin haka su Kubura suka balle da dariyar mugunta cikin dariya take fada masa abinda ya faru da Mairo har lumfashinta ya fara daukewa watakil ma mutuwa zatayi. Da jin haka shima yace ai gwara ma ta mutu wai daga ita har uwarta basu da amfani a gidan.

A bangaren Fatsuma kuwa duk abinda Zubairu ke fada tana jinsa hawayene kawai ke zuba daga idanunta duk wata dabara da ta fado mata a rai yi take a kan Mairo domin ceto rayuwarta har iska ta rika busa mata a baki. Ta dade a haka sannan taga lumfashinta ya fara dai-daituwa sai dai zazzabi ne ya rufeta don har bacci ya kwasheta. Fatsuma kallon yar tata tayi hade da fashewa da wani irin matsanancin kuka mai ban tausayi "Ya Allah ka dubeni ka dubi 'yata ka kawo min canji mafi alkhairi a rayuwata na gaji da wannan zaman ya Allah ka tausaya mun". Tashi tayi ta daukko sauran robb da take da shi ta shafawa Mairo a baya domin duk bayanta yayi rudu-rudu da sawun bulala inda Zubairu ya daketa. 


A hankali ta rungume yarta tana sauke ajiyar zuciya yunwar da take cinta ma ta nemeta ta rasa fuskarta kuwa inda aka mareta har jini ya kwanta abinka da farar fata, a haka bacci yayi gaba da ita. Gidan Bukar kenan wanda wasu suke kira Abubakari ba za'a kerashi da dattijo ba domin shekarunsa ba zasu haura 40 ba. Yana da mata uku Kubura 'ya'yanta shida biyu sun mutu yanzu sauran hudu sune Zubairu matashi dan shekara 18 kanwarsa ta uku Talatu mai shekaru 12 kanwarta Wasila shekararta 10 sai karamar kanwarsu Asabe mai shekara biyar. Matarsa ta biyu Laure 'ya'yanta uku Halimatu wacce suke kira Intuwa sa'ar Talatu ce sai kannanta maza biyu Sani Da Lawali duk yan shekara takwas zuwa goma ne.


 Matarsa kuma Amarya Fatima wacce suke kira Fatsuma 'yarta daya Maryam wacce suke kira Mairo shekararta 8 zata shiga ta tara. Fatima yarinya ce duka-duka ba zata haura shekara ashirin da biyu ba amma wahal-halu da yunwa sun sa ta rakwar-kwabe ta zama tamkar yar shekara 35 ko 40, rabon Fatima da farin ciki a rayuwarta har ta manta domin ko lokacin aurensu maimakon farin ciki da amare suke ji ita da tilin bakin ciki ta tare a cikin gidanta, tun bayan daren amarci Bukar bai sake kwana a dakinta ba balle ya kusanceta daga karshe zargi ma yake Mairo ba yarsa bace wai. 


Tun bayan aurensu kallan arziki bai taba shiga tsakaninta da Bukar ba ko dake can dama ba son juna suke ba tana iya cewa auren dole aka mata da Bukar amma duk-da haka wanda akayiwa auren dole sun fita jin dadin rayuwar zaman aure. Kubura da Laure babu irin azabar da basa gana mata ita da yarta a gidan. Sun iya tuggu da makirci duk yadda zasuyi su saka Bukar ya kuntata mata shi sukeyi. Haka zalika suma duk abinda suka mata babu wani mataki da Bukar yake dauka balle ita ta dauka da kanta. Fatima tana iya cewa a duk zuri'ar Inna Ma'u ce kawai take tausaya mata. Amma hatta Baban Bukar mijin Inna Ma'u wato Kawun Fatima ko kadan baya tausayinta. Asalima da sa hannunsa a cikin duk abubuwan da Bukar yake mata domin shi ya aura mata Bukar


Kafin ta fahimci irin zaman gidan tasha bakar wuya da yunwa. Domin sau daya suke bata abinci a rana in ba ranar girkinta bane. Daga karshe Bukar yace baya iya cin abincinta dan haka ta daina girkin ma gaba daya. Rayuwa ta kara mata kunci domin a lokacin ta fahimci cewa in ta cigaba da rayuwa haka yunwa ce zata kasheta. Tasha kai karar Bukar wajen Inna Ma'u wacce take zaunar da shi ta mai fada sosai a gabanta sai yayi kamar ya canza amma in ya dawo gida sai ya sa Fatima daki ya mata dukan kawo wuka. Da haka har ta gaji ta daina kai kararsa a cikin haka ta fara nemarwa kanta mafita


Ta fara karbar dakan fura da surfen makwabta da kuma diban ruwa wa yan gatan kauyen suna biyanta kudi wanda da su take malejin rayuwata ita da yarta. Suma tanayi tana boyewa don duk ranar da Bukar ya fahimci akwai kudi a wajenta kwacewa yake. Da tana tambayarsa duk lokacin da zata fita diban ruwa ko makwabta domin kare hakkinsa daga karshe yace karta kara tambayarsa duk inda taga dama ta fita ba ruwansa. Kubura da Laure ba yadda basuyi ba domin su saka Bukar ya saki Fatima amma Inna Ma'u tace idan ya saki Fatima sai ta tsine masa shine ma abinda ya dakatar da shi bai saketa ba.


Don yana tsoron tsinuwa akwai wanda uwarsa ta tsine masa a kauyen ya haukace. Tabbas rayuwa ba karamin tsananin takewa Fatima a gidan ba, kullum cikin kuka da bakin ciki take tare da mika kokon bararta wajen Allah domin shine kadai gatanta kuma shi kadai zai iya fitar da ita daga halin kunci da take ciki. Duk tsaftar Fatima sai da ta koma kazamar dole a gidan, domin Bukar baya mata dinki ita da yarta idan kuma ta dinka da yan kudin aiki da ta tara sai su Kubura sunyi yadda zasuyi su rabata da shi. Har ta kai ga hatta wanki idan tayi suka ga kaya da dan haske zasu kwace ko su saka Bukar ya kwace ya ba yaransu don dole ta hakura take zama da kazanta haka ta bar Mairo ma cikin datti ba don son ranta ba.

Post a Comment

0 Comments

Ads