Ta Faru Ta Kare Bayan Kotu Ta Tasa Keyar Murja Ibrahim Zuwa Gidan Gyaran Hali

Ta faru ta kare Kotu ta aike da Murja Kunya zuwa gidan yari
Kotun shari'ar Muslunci da ke Filin Hoki a Kano ƙarƙashin mai Shari'a Abdullahi Halliru ta aike da Ƴar TikTok ɗin nan Mai suna Murja Ibrahim Kunya zuwa gidan yari.

Lauya Barrister Lamiɗo Abba Soron Ɗinki ya karanto mata ƙunshin tuhume-tuhumen da ake mata wanda ta musanta.

Ana zargin Murja da ɓata suna da barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris mai wushirya wanda dukanninsu abokananta ne.

Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 16 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Sai dai Lauyan Murja Barrister Yasir Musa ya nemi a tura ta zuwa Hisbah maimakon gidan Yari sai dai Kotun bata amince ba.

Goma da Ashirin: TikTok sun sake banning account ɗin Murja Ibrahim Kunya a karo na biyu.


Kalli bidiyonDama a baya sun sheƙe account ɗinta mai mabiya sama da Miliyan guda, yanzu kuma sun rufe asusunta na biyu mai mabiya sama da Dubu Ɗari Biyar.

Post a Comment

0 Comments

Ads