Ra’ayoyin Kanawa Kan Tsawaita Wa’adin Tsohuwar Takardar N200 Da Buhari Ya Yi

An jinjina wa Buhari kan tsawaita wa’adin tsohuwar takardar Naira 200.


Wasu mazauna Jihar Kano sun bayyana ra’ayinsu game da umarnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na tsawaita wa’adin karbar tsohuwar takardar Naira 200.

A tattaunawarsu da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), Kanawan sun yaba wa Gwamnatin Tarayya kan kara wa’adin yayin da wasu suka bayyana akasin hakan.

Sai dai dukkaninsu sun bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN), da ya samar da isassun takardun kudi na 1000 da 500.

Wani karamin dan kasuwa mai suna Malam Shehu Bala, ya ce karin wa’adin ci gaba da karbar tsohuwar takardar N200 abun a yaba ne.

Shehu ya ce umarnin da CBN ya bayar na daina karbar tsofaffin takardun kudin daga ranar 10 ga watan Fabrairu ya shafi kasuwancinsu, inda wasu da dama suka daina fitowa kasuwa.

Sai dai ya ce karin wa’adin takardar N200 da Shugaban Kasa ya yi, zai taimaka na wani lokaci.

Shi ma wani Malam Garba Gezawa wanda matukin babur din Adaidaita Sahu ne, ya jinjina wa gwamnati kan tsawaita wa’adin, inda ya ce rashin takardun kudi ya shafi sana’arsu.

Ya ce takardar N200 ita ce wadda ’yan makaranta da mata suka fi amfani da ita wajen biyan kudin abun hawa.

Sai dai ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta kara wa’adin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin na 1000 da 500.

Alhaji Mamman Suraj, ma’aikacin gwamnati ne a jihar, shi ma roko ya yi da a samar da isassun sabbin takardun kudi don rage wa jama’a wahalar da suke fuskanta a yanzu.

Wani masanin tattalin arziki, Malam Ali Bakari, cewa ya yi buga karin sabbin takardun kudi abu ne mai wahala ga CBN, amma ya ce bankin zai iya barin mutane su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudi don saukaka rayuwar yau da kullum.

Wata mai gyaran gashi a jihar, Misis Agnes George cewa ta yi wannan dama ce ga daukacin mutanen jihar da su yi kokarin sauya tsofaffin takardun kudin da ke hannunsu kafin cikar sabon wa’adin.

Ta jinjina wa Shugaban Kasa na tsawaita wa’adin wata biyu don ci gaba da amfani da takardar Naira 200.

Kazalika, ta ce karin wa’adin zai rage dogayen layuka a injin ATM, da kuma wahalar da mutane ke sha a yanzu sanadiyyar karancin kudin.

Post a Comment

0 Comments

Ads