Murja Ta Nemi Afuwar Kotu Daga Gidan Yari

Matashiyar nan mai tashe a TikTok wadda kotun Musulunci ta tura zaman wakafi ta nemi afuwar kotun.


Matashiyar nan mai tashe a TikTok wadda kotun Musulunci ta tura zaman wakafi ta nemi afuwar kotun.

Murja ta aike wa kotun da ke zamanta a Filin Hockey takarda cewa ta tuba ne a ranar Alhamis, a yayin wata shari’a ta daban da ake zargin ta da lalata tarbiyya da kuma yada batsa a TikTok tare da Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da kuma Sadiq Shehu Shariff wanda ya yi wakar ‘A Daidaita’.

Da farko kotun ta tura Murja Kunya zuwa gidan yari ne bayan an gurfanar da ita kan zargin bata suna da kuma barazana ga Aisha Najamu ta Izzar So da kuma Ashiru Idris Mai Wushirya wadanda dukanninsu abokananta ne.

Aminiya ta kawo rahoto cewa a zaman kotun na a ranar Alhamis karkashin jagorancin Mai Shari’a Abdullahi Halliru, ta fara sauraran wata sabuwar tuhuma da ake yi Murja da wasu matasa uku, bisa laifin amfani da shafukan sada zumunta wajen yada batsa da kuma lalata tarbiyar yara.

An gurfanar da su — TikTok tare da Idris Mai Wushirya, Aminu BBC da kuma Sadiq Shehu Shariff — ne bayan karar Majalisar Malaman Kano ta shigar.

A karshe dai kotun ta yi watsi da rokonsu na beli, sannan ta aike da su zuwa gidan yari, sai ranar 23 ga watan Fabrairu za ta ci gaba da shari’ar.

Post a Comment

0 Comments

Ads