Idan Maciji Ya Sareka, Abubuwa Biyar Da Zakayi Ka Tsira Da Rayuwarka

Idan Maciji ya sare ka?

Mai zai faru idan maciji ya sareka watakil tunanin mutuwa ko cigaba da rayuwa ne a kwakwalwarka amma mutane da yawa musamman hausawa na ganin cewo mutu ita ce ke biyo bayan cizon maciji

Shin ka taba ganin maciji?

Kana jin tsoron maciji?

Maciji ya taba cizonka

Ko kuma ya taba cizon waninka?
Watakil kana cikin masu tunanin cewa idan basu takurawa maciji ba to ba zai cizo su ba. Hakika tunaninka yayi dai-dai. Bincike ya tabbatar da cewa maciji yana cizo ne a matsayin kare kansa ba don cutar da mutane ba

Idan kana rayuwa a garuruwan da ke da macizai to ya zama wajibi a gareka kasan wadannan abubuwa biyar idan maciji ya sareka

1 abu na farko

Idan maciji ya sareka karka tsaya dubawa shin macijin mai dafi ne ko marar dafi. Gaba daya macizai suna kammani da juna, don haka taimako na farko da zaka fara yiwa kanka shine kwalla ihu idan wani na kusa tabbas za'a kawo ma dauki. Taimako na biyu da zaka farawa kanka yi gaggawa ka kira lambar duk wanda ka san zai iya kawoma dauki cikin gaggawa

2 abu na biyu ka natsu karka firgita karka motsa

Tabbas fadin wannan maganar ya fi sauki fiye da aikatawa, amma ka sani rashin motsawa bayan maciji ya sareka zai iya ceton rayuwarka. Tatsuniya ce cewar dafin maciji yana shiga cikin magudanan jinin mutum da zarar ya sari mutum. Maimakon hakan dafin macijin yana tafiya ne cikin tsarin lymph wasu kwayoyin halittane farare wadanda suke motsawa a yayin da kake motsa gabobin jikinka. Don haka idan zaka iya tsayawa ka natsu bayan cizon macijin dafen ba zai sama damar ratsa cikin jikinka ba na karin tsawon lokaci

Don haka Idan ka tabbata macijin ya tafi bayan ya sare ka kuma ba ka tunanin zai sake dawowa, ka tsaya a inda kake karka motsa. Idan kana tare da wasu mutane, su ma bai kamata su motsaka ba. Don haka ka kwantar da hankalinka yana wahala saran maciji ya kashe mutum musamman idan anbi shawara ta farko da muka bayar

3 Abu na uku ka rabu da macijin

 Kada ka yi ƙoƙarin gano Kalar macijin, kama shi, raunata shi ko kuma kashe macijin. Domin ma'aikatan asibiti suna yin gwaje-gwaje iri-iri da za su taimaka musu wajen yiwuwar gano kalar maciji da ya sare ka. wanda zai ba su damar ba ka magani da ya dace, idan maciji ya sareka wani na tare da kai yayi gaggawar nemo likita ko hanyar da zaa kaika asibiti

4 Yi kokari ka daure wajen gam


Idan maciji ya sareka kayi amfani da tsumma ko kuma idan ba tsumma a kusa ko rigarka ce ko tufafi kana iya yagawa ka daure wajen sosai sama da kasa domin kar dafin ya sama damar cigaba da gudana a cikin jikinka


5 Abu na biyar Karka Wanke Wajen Ko Tsotsewa ko kuma Yanke wajen


Akwai tsofaffin hanyoyin da ake bi idan maciji ya sari mutum a da. Wanda a yanzu an gano wannan hanyoyin suna kara cutar da wanda maciji ya sara fiye da taimaka masa. Idan har aka wanke wajen da maciji ya sari mutun dafin na wankewa wanda ta hanyar hakan likitoci ba zasu iya tantance macijin ba balle su bayar da maganin da ya dace

Idan kaga maciji ya ruga karka bishi, idan maciji ya biyoka ka ruga. Idan kai ka fara ganinsa bai ganka ba yi maza ka canza hanya

Kalli Full Bidiyon Da Wasu Karin Bayanai


Post a Comment

0 Comments

Ads