Allahu Akbar Garin Da Allah Ya Hallaka Ta Hanyar Girgizar Kasa Bayan Zuwan Annabi Isa

Girgizar Kasa A Birnin Pompeii Na Kasar Italy 62 Miladiyya 
A Rana mai Kamar Ta Yau 5 Ga Watan Fabrairu 62 Miladiyya a Kayi Girgizar kasa Da Aman Wuta (Volcano) Daga Dutsen Vesuvius a Pompeii, Italiya

A ranar 5 ga watan Fabrairu 62, girgizar kasa mai girman awo tsakanin 5 zuwa 6 da ma'aunin karfin IX ko X a ma'aunin Mercalli Da Aman Wuta (Volcano) a Dutsen Vesuvius ta afkawa garuruwan Pompeii da Herculaneum, in da ta yi musu barna sosai.

Girgizar kasa a shekara ta 62 ta yi babbar barna a Pompeii da Herculaneum. Har yanzu garuruwan ba su farfaɗo daga wannan bala’i ba.

Girgizar kasar ta ɗauki sa'o'i 18. Ta binne Birnin Pompeii a ƙasa da ƙafa 14 zuwa 17 na toka da Tururi Da iskar Gas Mai Guba, kuma bakin tekun da ke kusa ya canza sosai.

Pompeii Wani Tsohon Gari A Kasar Italy Wanda A Shekaru 62 Bayan Haihuwar Annabi Isa (AS) ALLAH Madaukakin Sarki Ya Jarrabe Su Da Wani Irin Mummunan Aman Wuta (Volcano) Daga Dutsen Vesuvius Da Girgizar Kasa Mai Karfin Gaske (Earthquake) 

Wanda Turawa Suke Wa Bala'in Lakabi Da (Eruption of Mount Vesuvius) Wanda Yayi Sanadiyar Rasa Rayukan Mutane Dubu 16, Amma A Wata Fadar Yawan Yafi Haka, In da Dutsen Ya Rinka Fitar Da Wata Toka Mai Tsananin Zafi.

Wacce Yawan Ta Yakai Tons Miliyan Daya Da Dubu 500 A Second Daya, Karfin Lamarin Yakai Ninki Dubu 100 Sama Da Karfin Bom Din Nuclear Da Kasar Amurka Ta Jefa A Biranen Hiroshima Da Nagazaki Dake Kasar Japan A 1945, Gwari-Gwari A Turance (thermal energy) Domin Kuwa Wasu Da Yawa Daga Cikin Mutanen Garin Zafin Toka Ne Ya Daskarar Dasu, Kuma Ko Yau Kaje Garin Pompeii Idon Ka Zai Gane Maka.

A Shekara ta 2014 Anyi Film Din Cinemarsa.

Post a Comment

0 Comments

Ads