Yanda zaka haɗa wayarka da TV ko Computer


Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Barkanmu da sake kasancewa a wannan shafi namu mai albarka, inda muke kawo muku abubuwa daban-daban na ilimi don amfanuwar ku.


Yau mun kawo muku wasu Applications guda biyu masu abun mamaki kuma masu matuƙar amfanin gaske, waɗannan applications zasu ba mutum dama ne ya haɗa wayarsa da kuma computer ɗin sa, ko kuma wayarsa da TV ɗin sa.


Abun nufi shine idan ka haɗa wayarka da computer ɗin ka to screen ɗin wayar taka zai fito akan Computer ɗin taka, duk abinda kake gani a cikin wayarka zaka riƙa gani a computer ɗin taka, wannan shi ake kira da (screen casting) a turance, to haka kuma idan ka haɗa wayar da TV ɗin ka shima zaka ga screen ɗin wayar taka ya fito akan TV ɗin


Wannan hanyar zaka iya amfani da ita wajen kamar nunawa mutane wani abu a cikin wayarka, zata iya yiwuwa mutanen suna da yawa to kaga screen na waya yayi kaɗan, to idan kana da smart TV ko Computer sai ka haɗa su da wayar taka domin cikin wayar taka ya fito akan Computer ɗin ko a TV


Sannan idan za a haɗa waya da TV ba kowace TV ake amfani da ita ba dole sai Smart TV, saboda ita ce za a iya haɗa WiFi da ita. 

Smart TV Tibi ce da take da operating system akan ta kuma tana da Internet connection, ana iya yin browsing da ita kuma ana yin install na Applications akan ta.

Yanda ake haɗa wayar da computer

Da farko zaka je playstore ka sauke wannan application ɗin mai suna Screen Cast, ga Link nan a ƙasa sai ka danna domin saukewa.

Domin Sauke Application Din Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!


Bayan ka sauke sai ka buɗe shi, bayan ka buɗe zaka ga ya nuna maka hanyoyin da zaka iya haɗa wayar taka da computer ɗin. Sai ka zaɓi Mobile Hotspot ka danna.


Bayan ka danna zai nuna maka nan wajen sai ka danna madannin da aka rubuta START BROADCASTING


bayan ka kunna sai ka dawo cikin Application ɗin ka ƙara danna START BROADCASTING, zai nuna maka nan sai ka danna Start now 


Bayan nan zai kawo nan shafin, a jiki akwai inda aka rubuta URL: Sai kuma wasu nambobi a gaba 
http://192.168.200.54:6868
Waɗannan nambobin da su zaka yi amfani a computer ɗin kaSai ka koma kan Computer ɗin taka ka kunna WiFi sai ka nemo sunan Hotspot na wayar ka, sai kayi connecting ɗin wayar da computer ɗin, bayan ka haɗa sai ka koma kan Browser dake kan computer ɗin sai ka buɗe, daga sama inda ake rubuta url address, sai ka rubuta waɗancan nambobin da aka baka a cikin Application ɗin, sai ka danna Enter shikenan Screen ɗin wayarka zai fito akan computer ɗin.

Sai kuma yanda ake haɗa waya da TV

Farko zaka sauke wannan application ɗin a playstore mai suna Screen Mirroring - Castto

Domin Sauke Application Din Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Bayan ka sauke sai ka buɗe shi, sai ka koma kan Smart TV ɗin ka ka nemo Miracast Display sai ka kunna shi

Sai ka dawo cikin application ɗin ka danna madannin da aka rubuta SELECT TV

Bayan nan zai kawo ka wannan shafin, daga sama sai ka danna wannan alamar

Zaka ga an rubuta Enable wireless display sai ka kunna shi, kana kunnawa zaka ga sunan TV ɗin ka ya fito a jiki sai ka danna sunan TV ɗin, shikenan screen ɗin wayar taka zai fito a jikin TV ɗin.

Domin Sauke Application Din Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!Post a Comment

0 Comments

Ads