Yadda Za'a Magance Duhun Matse-Matsi Ga Mata Da Maza

 DUHUN MATSE-MATSI [DARKNESS OF INNER THIGH]

⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘⚘Duhun matse-matsi ko tsakankanin cinyoyi kai wani lokacin harma da mazaunai wannan kusan abune da mutane da yawa cikin mata da maza kan fuskancesa...... wasu kanji kunya ma su kasa tattauna matsalar, musamman masu fama da matsalar hade da stretch marks a duwawu kaca kaca... 


Toh saide stretches marks galibi yau da kullum ce kama daga yawan zama, kwanciya, da sanya matsi agame da fata wato kamar juna biyu duk yakan haddasa shi.


Saide dangane da duhun wanda shine zan bayani kansa akwai mabambantan dalilan dake jawosa kama daga:


■- Kiba

■- Tangardar sinadaran halitta (imbalance)

■- Wani magani da mutum kesha

■- Ciwon sugar

■- Ciwon fata

■- Fitar sinadarin dake sanya duhun fata fiye da kima

■- Karancin lura da tsaftar al'aura


KARANTA>> Cututtukan Dake Hana Mace Jin Dadin Jima'i


Dukkansu na iya haifar da wannan yanayin a fata. Toh saide akwai wani abu da ya dan bambanta; Ga masu fama da duhu sosai wanda zakagani a wuya, ha6ar wuya, hammata, da cinya duk lokaci 1 galibi wannan ACANTHOSIS Nigricans muke kiransa da wuya ka samu basu da larurar ciwon sugar ta Diabetes.


Wannan yasa masu acanthosis ko sun sai mai' sun shafe-shafe sun gyara gurin... ahankali xai kara komawa bakikkirin domin maganin kurum shine; sui control din sugar din, toh saide galibi basusan suna da ciwon sugar ba... tunda bata basu wani canji ajika matakin farko... saika shekara 5 da ciwon sugar baka sani ba, Sai a karshe ta soma lalata ma koda jikinka ya rikice lokaci guda... 


Wannan tasa ko yaushe akeson check up domin a asibiti ne kadai za'a iya gano haka su masu saida maya-mayen gyaran jiki kasuwancinsu kurum suke basu san menene ba.. kaine zakaga kana da tsafta amma gashi sai fama kake.


🌳

Toh saide ga masu irin wancan duhun na matse-matsi da insunje wanka wani bun insuna dirza fatar suke ganin kamar datti a duqunqule na fita... Galibi hakan na faruwa ne amutanen da jikinsu ke sakin sinadarin (melanin) da yawa wanda sinadarine dake sanya duhun fata domin bata kala dinta, da kuma kareta daga zafin rana da sauransu. 


Saide a wasu sinadarin kanfi yawa wajen matse matsi da hammata saboda ba gurarene da iska ke ratsasu ba ko yaushe. Wannan wasu tasa suita mamaki suga ko yaushe suna wanka amma ga datti suita zargin tsaftarsu....


Toh saide duk da hakan inya hadu da karancin tsafta toh duhun kanyi muni ya dau lokaci ana fama. Don haka mu a LIKITANCE bama kallonsa a matsayin larura shyasa ma babu maganin sa a likitance sama da mu karfafe ka kara kula da tsafta... Ba kazanta bace dead skin ce da melanin.


Mukan ba mutum shawara ya rubanya lura da tsafta musamman a maza wata hanya shine; 

Sanda kukayi gudu ko irin wasan kwallo kukai zufa! Da zakuje tsuguno ko ya kuka dirza cinyarku zakuga dattin hade matacciyar fatar ya taso koda hannu da farce zakuga kuna ta kankarosa saboda ya jika da zufa


Hakan yasa nakan ba masu shi shawara duk wanda yai irin motsa jikin kuma yasan yana da abun toh kar ya jinkirta wanke cinyoyinsa. 


Ba'a son wanka sanda ake zufa domin dashi da babu duk daya ne a lokacin toh amma koda za'a jinkirta wanka... ka daure ka shiga bandaki lokacin da ka taso ka wanke cinyoyin koda hannunka mutum zaiga yana durzo matacciyar fatar me duhun wacce ta macen domin inka sha iska ko kaje wanka bazata fita haka ba. 


KARANTA WANNAN>>> Bambancin Mace Doguwa Da Gajera A Wajen Jima'i


🌳

Amma wanda suke da swimming pool galibi basu da wannan matsalar domin suna jika sosai su shafe dogayen mintuna a ruwa shyasa duk dead skin dinsu saita taso sama sun wanke suke fita... 


Toh kuma da baku da swimming pool zaku iya zuba ruwan a babban bowl inkunje wanka ku shiga ku zauna kurum ku shafe mintoci zaune sai kun jika sosai sannan ku fara wankewar koda kuna amfani da man gyara jikin zakufi ganin tasirinsa....


Kamar yadda nace a likitance bawani magani da zan iya cemuku gashi Guarantee saboda larurar amma galibi wasu:


- Kanyi amfani da man shafawa na ALOE VERA koma ruwan aloe vera din kai tsaye shima mutanen da suka gwada sunce yana fitarwa... idan aka shashshafe cinyoyin da mazaunen sai aci gaba da harkoki kar a wanke sai bayan awa 1 ko fiye... kullum mutum ya rika hakan kafin wanka sau biyu ayini sunce yana taimakawa


Ko amfani da Aloe vera da lemon tsami hade arika shafawa


Ko amfani da Baking powder da man Olive... Toh amma de kamar yadda nace wannan duk ba binkice a likitance bane yace.


Saide a likitancen Creams irinsu; Ellagic acid cream, Hydroquinone, Lignin peroxidase, Isotretinion ko Niacinamide cream munsan suna da Lighting property 


Toh amma de kafin kai komi ya dace in abun na damunka ka nemi shawarar likita, saboda fatar kowa ta bambanta wajen daukar sako, abunda yaima wani bai zama dole yai aiki awani ba.


TOH AMMA BAKI DAYA NAKAN CE 


1. Mutum ya rika amfani da ruwan dumi yana zama aciki mintuna 15 zuwa 30 kullum kafin ya soma wanka koda ya shafa wadancan abubuwan hakan zaisa ya jiku... kai koda aski zakui ku tsaftace kanku in kuna zama cikin ruwan dumi minti 10 zuwa 15 kafin gabanku bazaike kuraje ba abunda muke kira FOLLICULITIS. 


2. Sannan mutum ya qara adadin yawan wankansa! Galibi maza sau 1 suke wanka ayini, kasani kana bukatar fiye da haka, inda zaka iya harda rana sanda kai zufa kafin ka rika yi da kuma kafin kwanciya bacci....


3. Sannan arika canza gajeren wandon ciki kullum, tare da Aski akai akai shine ma mahimmi akalla duk sati 2 ko 3 mutum ya tsaya ya tsaftace kansa. Kada kaga matarka bata korafi amma de akwai tozarta kai gaskiya ka zauna haka kaca-kaca... rashin lura da tsaftar matse matsi da hammata na hana jin dadin Jima'i kansa....


4. Ga masu saida maya-mayai nan na gyatan duhun fata duk zaku iya samun su ku jaraba basai mata kadai ba

DUBA WANNAN>>> Alamomin Da Za'a Gane Cewa Mace Ta Gamsu

5. Duk sanda kai zufa kaji matsematsinka ya jika.... har kana iya turzo fatar to tsaya ka sami ruwa musamman na dumi ka shiga bandaki ka tsaftace kanka...inta kama ko dutsen goge kaushi zaka sa ka dirza inde yana fita bakuma kajin zafi to tsaya kayi... direct zakaga yana haske debris din na fita....
6. Idan kiba gareka saboda cinyoyinka na gogar juna suna iska ratsawa toh kai/ki kokarin rage kibar.


7. Inkaga kayi kayi duhun bai tafi ba, ko kuma inya tafi yana dawowa toh ka daure kaje kaga likitan fata... ta yiwu akwai wata larura ajikinka da bata bayyana ba tukun amma zuwan zaisa aganota.


Fatan mun ilmantu.

Post a Comment

0 Comments

Ads